Sashe 56
Zakin Sarakai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
datako kamar wani mai manyan shekaru, bawan Allah bai taba ganninsa da yannayi irin na fara'a haka ba, tunda yake, Haba ya dan dafe ya ce" Kuma kana ji?, Yawanci fitsararun nan sun fi tsaye mana tak a rai, ka duba ka ga maman Safwan, ranar nace kar a min wake a gida bana so, ta yi ta kwaliye shi na rangada, sai da na gama take ce min shine, kuma idona idonta kurrrr sai ni na kawar da kai, kuma har ga Allah na fi jinta a raina" ASADEEK ya yi dan tsam, sai kuma ya yi murmushi ya girgiza kai ya ce" Aa, ni dai ba zata kamo min mar'atusaliha ba, haba dai ai mai jin magana da marar ji ba daya bane, SHEIK yaya maganar nan take ne?, Cewar kar kowa ya sani" SHEIK ya ce" Ka yi hakuri, ka karra bani lokaci, kar wanda ya sani, ciki harda Ummanka na roke ka" Bakinsa ya dan tabe ya ci gaba da shan lipton din nan yana jin yana sake sakar masa jijiyoyin jikinsa ................................................................................................ A hankali ta bude ta shiga tana salama Turus ta yi sakamakon abinda idannuwanta ke ganni HINDU tsaye tana salalami tana bin NADIRAH da kallo wace ke Kwonce tana birgima bihaki tana ihun a kan me innarta zata ce sai ta fada mata rigar nan ta waye Hindu ta bi matar da kallo, mace mai cike da kamala, yannayinta akoy kamala, sai dai duda haka ba zata yi gaggawar sakin jiki ko fuska ba, dan haka ta ce" *NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS ```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, al alaminmu ancinmu.``` *https://www.facebook.com/106494781436168/* *OUMOUGHLOUK ITIBEL* _(ZAKIN SARAKAI)_ _FREE BOOK_ *Na* *SAJIDA NIGER* 4 Fuskarta ba yabo ba falasa ta ce" Bakuwa muka yi?, Sannu dai....." Sai kuma ta kalli Indi a kausashe da yaren buzanci ta ce" Dan ubanki zaki daina burgimar da iface ifacen nan ko sai na tatakaki ne a gaban wannan, wacece ita ne na ga ta biyo ta nan itama ko hanya ce da kowama zai iya bi?" Murmushi matar ta yi tana dan sake dubansu, zuciyarta ta cika da matsanancin mamaki mai masifar girman gaske, haka kuma Hindu ta bata daria, ko dan ta ga fatarta baka tana tunanin bata jin yaren? Abinda dai ya fi dan cika mata zuciya da tunani shine, Sarauniyar garin Tanut ce akace, kuma uwa ga yayan Agadaz ke burgimar nan ko yaya? Gannin ta ki bada amsa ama kuma ta dakatar da burgimar ya saka Matar SHEIK yin murmushi ta ce" Ki yi hakuri Hajia, dama ni din Matar SHEIK ce, kuma likita ce, na zo dan na duba Uwar Agadasawa ne" Dan shiru HINDU ta yi, matar Sheikh? Wannan kamilalen mutumen da akace sunnansa SHEIK, na gefen UMUGHLUK ITIBEL? Lah ha ila ha ilalahu muhamadu Rasulullah salalahu alaihi Wasallam, yau gata ga matarsa Murmushi ta saki tana kikifta ido, sai kuma ta kalli NADIRAH dake kallonsu fuskarta na nuna dukkan wani tashin hankali da Rigima a tare da ita yake Yawu ta hadiye, kwarai kuwa abinda take tunanin ya faru fa da gaske ya faru Wayo Allah ga abin rangada buda da dimar rawa ama ba hali Nadirah ta mata tsuru da ido Da sauri ta karasa inda take ta duka ta kamata tana fadin" Tashi mana, mu je ciki, baiwar Allah Bismillah shigo shigo, dan rikici ke damunta, zo mu je dakinta ai in dai dubawar da nake tunani ce sai a daka ko?" Ita dai Matar SHEIK biye take da su, baiwar Allah NADIRAH da kyar take takawa, wajen ne ya karra yin tsami, ga rikicin dake damun kanta mai yawan gaske Bakun makeken gadonta mai kalar gidan sarauta ta zauna tana sada kanta, Inna ta yi murmushi kasa kasa ta ce da Matar SHEIK " baea na barku, zan zaga bayi cikina ya fara murdawa" Da ido ta rakata sannan ta maido dubanta Kan NADIRAH Dan murmushi ta saki ta cire hijabinta da nikaf dinta hakan ya bayanar da nutsatsiyar kamilaliyar fuskarta Jakar ta bude ta dauko safar hannu ta likitoci tana kallonta ta ce" Bismillah Allah ya karra maki lafia" NADIRAH ta dago tana kallonta, Bismillah me? Matar SHEIK ta karasa tana fadin" Baya zaku kwonta sai ki cire wandon ki janye rigar baya na duba da kyau kin ji?" Ido ta zarro da matsanancin faduwar gaba da tsoro Bakinta har yana rawa ta ce" Na cire wandona kuma? A kan me za'a wani dubani? Babu abinda ya sameni fa ni" Ido ta zuba mata itams, karara ta fahimci ko me yake damun Yarinyar A hankali ta zauna cikin yaren French ta ce" Excusez moi, je ne me suis pas pr sent , je suis LUBNA MUHAMMAD, je suis la 4eme femme du Cheikh, et je suis m decin gyn cologue je suis enchant de vous conna tre et je serais honor tre votre m decin " (Ki yi hakuri, ban gabatar da kaina ba, sunna na LUBNA MUHAMMAD, nice matar SHEIK ta hudu sannan ni docter ce a fannin mata, ina farin cikin sanninki, sannan zan kasance cikin farin cikin zamtowa likitarki) 'kan ubancen kayasa' shine abinda zuciyar NADIRAH ke ayannawa a lokacin da ta kure bakin wannan yar gayun dake yi mata yaren aljannu tana makokwaltu da baki tana hirar da sam bata san me take nufi ba har ta dire maganarta tana sake kallonta Wannan lamari ya saka LUBNA dan sake karantar Nadirah Magana ake a kan matar da aka ce ya ce a wajen sarkin Tanut, ba zata taba kawo cewar bata ji yaren da ta yi mata ba, sai dai ko kawai bata yi mata bane Sake sasauta muryarta ta yi a sanyaye wannan karron da hausa ta ce" Allah ya huci zuciyarki, idan har na bata maki ki yi hakuri dan Allah, idan kuwa wani likitan kike so a kirawo bara na koma na sanar sai a kirawo ko wani likita kike so in sha Allah" Kasa kasa NADIRAH na rage girman idannuwanta da sansanyar muryarta ta ce" Likita kuma? Ya min me?" Matar SHEIK ta fuskanceta da duba irin na tsanaki, a hankali ta dan kara matsawa kusa da ita kadan ta ce" ki yi hakuri Hajia, kin san wajen nan waje ne mai matukar hatsari, waje ne da ba'a so a yi wasa da shi, bale ke da iliminki da hankalinki, idan har ya zamto an yi wasa da wajen nan kuma ya raunata akoy katsala, kin ga a wannan fannin ba maganar ka ji kunya, domin ciwo ne, idan ya giga kaine ka shiga uku, idan ya zama gagarare kaine a babar matsala, zai iya gagaraka shiga mutanema bale har ka anfana da shi, yana iya hannaka zaman aure gaba daya, shi yasa nake so ki bada hadin kai a duba ki, a duba wajen dan kowace mace da kika gani ta haka ta girma, wata bata samun matsala kwata kwata, wata kuwa tana samun matsala kadan ne da ruwan zafi kadai ya isa ya warkar da wajen, watan kuwa har tsagewa take yi watau ta damu karuwar da sai an yi mata dinki kin fahimta?" A tsorace ainun, a matukar tsorace NADIRAH ta sake rage amon muryarta tana sada kai irin bata son hada ido da Lubnar nan ta ce" Hala kin san abinda ya faru da ni?" Itama LUBNA sai ta samu kanta da kafeta da ido, a zuciyarta kuwa tana ayana wai me yake faruwa ne?, Turewa ta yi ta fito mata a mutun ta ce" Ba shine sanadiyar kirana ba? Ko ba kin kawo budurcinki bane?" "Innalilahi wa inna ilaihi rajune, wayo na shiga uku kin ga, ki yiwa huwa rahamanu kar ki sanarwa Innata maganar nan, wayo Allahna bayan cin amanar kuma yamadidi ASADEEK zai yi da ni a duniya? Oh ni jikar mutun hudu na ga rana" NADIRAH ta karashe tana riko hannun LUBNA wace ta kusan zurmawa da gudu da ta ji sunnan da ta kama da kukan da take yi NADIRAH ta dora da fadin" Amanatul amana maganar nan, kuma abinda kika fada da yaren ko shima dai maganar wannan din dai ne?" A hankali LUBNA ta shiga tuna kiran da ya samu SHEIK a lokacin da suke zaune shekaran jiya da dare , kasancewar wayarsa ba wani rikaken sirri ne da ita ba, domun sun sha fada masa idan zai yi maganar sirri a cikin mutane ya ringa fita, wayarsa tanada amsa amo mai dan karfin da mutun mai kaifin ji zai iya jiyo hirarsa, Maganar da ta san ta ji daya ce kafin da hannu SHEIK ya mata alamun ta bashi waje, watau *WACECE SUKA AURA MIN?* Sake zubawa NADIRAH ido ta yi, a hankali ta koma ta zauna tana tunani da kuma ba kanta amsa A nutse ta sauke ajiyar zuciya tana sake duban NADIRAH Bata jin French, bata son a san baban abinda kowace mace zata iya yin tinkaho ace itace ta wayi gari a haka, kuma ta kama sunnan UMUGHLUK ITIBEL Ajiyar zuciya ta sake saukewa, a nutse ta yakice tunanin nan, tana karra tanatarwa kanta cewa babu ruwanta a wannan lamari, dan haka sai shiga assuring din NADIRAH, cewa babu wanda zai sani, ai sirrin likita da marar lafiya tsakanin patient da docter ne, sannan ta sake bata hankalinta gaba daya tana sake kwatanta mata girma da darajar abinda ta kawo da kuma maganar dubata, a kalla sun dauki awa ana abu guda, daga karshe ta yarda ama sallar da bata yi ba sai da ta yita kusan sha biyun rana tana ayana ba laifinta bane na maci amana ne, sannan ta zauna gaba daya hankalinta ba wani a jikinta ba, jikinta du ba a sake ba da kyar da walahauli ta iya bude jikinta LUBNA ta dubata Da tausayawa take yi mata bayani kamar Haka" Alhamdulilah baki yi kariwar da sai an maki dinki ba, sai dai kin yi mugun jin jiki ta yadda sai kina shafa maganin da za'a kawo maki sannan kina hadiye na hadiyar, domin wajen daga ciki ya kumburo hakama daga fatar gefe da gefe sannan kin dan karru kadan ba sai an dinke wajen ba, ki samu isashen hutu sannan ku ringa anfani da ruwan dumi kina zama a ciki kin fahimta?" NADIRAH