Sashe 18
Zakin Sarakai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ta karasa suka shiga lamarin gabansu ita da innarta, sunna yi sunna tadi da kyakyata dariya. ( Alhamdulilah, idan har da salatin annabi da wadatar zuci, zaka fi mai kudin farin ciki da kwonciyar hankali, Allah mun gode maka ka karra haskaka mana zukatanmu bijahi Rasulullah salalahu alaihi Wasallam) ______________________________ Tafia ce ta dan kankanin lokaci, duda rashin kyan hanya, da wuri suka karaso GARIN AGADAZ Ba tsaye tsaye suka nufi gidan sarki, sai dai tun daga nesa da hanyar karasawa babar fadar suka fahimci ana wani abin mai mahinmanci, domin taron motoci sun cika wajen sosai Dogarin da ya bada damar a barsu su shige ne yake sanar masu cewa baban taron saukar alku'ani ta aliban babar makarantar islamiyar garin, wace ta yi sunna ta kuma zaga garuruwa dan kwazonsu da kokarinsu a harkar adini Baki ya tabe yana duban gimbiya yana fadin" Ki sauka ku karasa , ni zan je a yi da ni" Itama bakin ta tabe ta kai dubanta daga gaba, inda Fadime ke zaune ta yi gyaran murya *NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS ```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, al alaminmu ancinmu.``` *https://www.facebook.com/106494781436168/* *OUMOUGHLOUK ITIBEL* _(ZAKIN SARAKAI)_ _FREE BOOK_ *Na* *SAJIDA NIGER* 1 Fadime ta fito tana sake kallon jama'ar zuciyarta na wani irin farin ciki ta bude mata motar sannan ta gyara mata alkyabarta ta amshi jakarta ta rike ta tsaya jiran ta fito Murmushi ta yi ta kalli mijinta, cikin kissa ta ce" FADIME, da ace tana cikin matan da kake iya karrawa, da ka huta Uban gidana....., Matar nan akoy biyaya!" Da sauri ya kalleta, sai kuma ya sake zubawa Fadime ido na dan takaitacen lokaci sannan ya dauke dubansa yana sake hade fuskarsa Murmushi ta yi ta bude ta fita daga cikin motar sannan ta yi gaba Fadime na biye da ita a baya Direct bangaren da ake sauke su ta nufa , domin karya ne walahi ba zata je ta gaisar da matar sarki ba!, Ita din banza ita din wofi, ba zata je ba! Sunna shiga ta karasa tana cire alkyabarta ta yar a nan Da sauri Fadime ta dauke ta karasa wajen makala kaya ta makala alkyabar, sannan ta dawo ta zauna daf da ita ta shiga cire mata safar kafarta sannan ta shiga dan mamatsa mata kafafuwan a hankali a hankali, har aka gabatar da kayan saukar baki Kwanonin take kallo, kwanoni ne da ita bata san ina zata shiga ta samo irinsu ba dan itama a ringa mata anfani da su a bangarenta, yanzu haka tana kallon kishiyoyinta kowace rai bace tana son sannin ina mijinsu zai fita da ita, ama ya masu banza, ta yi murmushi tana girgiza kai, su a tunaninsu fitar gadara ce? Koda yake haka take so su yi ta tunani, watau fitar gadara ce ta soyaya ce Kai ta maida wajen labulen dakin baki, to yaya na masu gidan zai kasance kennan? Ita bata taba shiga bangaren Sarki ba, a kulun tana hasashen yaya nasa bangaren yake kennan? Sake mayar da dubanta ta yi kan FADIME, tana aikinta hankali kwonta, babu rawar jikin nan da son a birge irin na wasu ma'aikatan gidan nasu Sake gyara zamanta ta yi da kyau tana ringesawa kadan a saman kujerar ta alfarma kasa kasa ta ce" Kin kasance mai biyaya a gareni Fadime, kin kuwa san na san da haka kuma ina gani?" Da mamaki Fadime ta dan dago ta kalleta kadan, sai kuma ta sake sada kanta bata ce komai ba Gimbiya ta cire daurin dan kwalinta tana sake lumshe ido dan barci zata yi a hakan tunda ta yiwu su kwana ko kuma idan sun taki Sa'a su ganshi a yau?, A hankali ta ce" Ban san yarinyarki ko tanada BIYAYA wa manyanta ba?" Dan tsam Fadime ta yi gabanta na dukan uku uku, ba dai Gimbiya hasashen saka NADIRAH a layin bayin masarautar garin Tanut take ba? Ai kuwa da ta fadi ba nauyi, domin a wannan karron babu maganar biyaya wa manya, bata cikin wannan, ita ta saba da bautar, zata yi har lokacin da Allah ya cire mata, ama bata tunanin NADIRAH zata iya wannan aikin, sai dai ta yi abinda za'a iya gile kanta walahi! Sunna nan a yannayinsu, sallah ke tashin Fadime, da zarar ta gama kuma zata dawo ta zauna tana jiran tashin Gimbiya daga barci, har aka yi sallar la'asar sannan aka bugo waya cewat ta shirya zasu samu gannin sarki nan da minti talatin Ita dai Fadime na biye da ita har ta gama shiryawar , bata yi sallolin dake kanta ba tace idan ta fito zata yi sannan ta fito cikin shiga ta sabuwar alkyaba tana baza kamshi ana mata jagora har zuwa bangaren baban falo , falon amsar bakin cikin gida Takalmanta ta cire a nan kofa, sannan ta shiga tana jin yadda ake sanar da ko wacece ita, sannan ta kai dubanta wajen mijinta dake zaune barin hagu din Sarki a saman kujera, barin damarsa kuwa UMMA ce zaune ta hakimce tana murmushin da ta tsana a rayuwa tana kallonta Sake gyara alkyabarta ta yi ta idasa shigowa da kyau sannan ta tsaya, ta rage tsayinta sosai ta sada kanta ta shiga miko da gaisuwarta zuwa wajensa Umma ta sake yin murmushi ta kalli ASADEEK, gannin ya gyada kansa a hankali sannan ya sake cire idannuwwansa a kanta ya sakata sasauta zamanta a hankali ta ce" Yin hakan ba laifi bane adalina, yin hakan ba ramuwa bane, idan har ka amshi hakan ka sani an daki tsuntsu biyu ne da jifa daya" Dubansa ya sake kaiwa wajen Bafansa, hakan ya saka bafan nasa fuskantar matarsa ya ce" Ki karaso ki zauna, ki karra bada hakurin abinda ya zamto shirme wanda kika aikata, ki zo ki tabatar masa da bukatarki dan sake wanke kanki!" Wani irin nauyi ya dake dane mata gaban kirjinta, lalle ya zama wajibi ta dauki mataki a kan du wani wanda ke wulakantatata, lalle shawarar da ta yankewa zuciyarta itace daidai da shi!, A hankali kuma wannan mata mai sunna UMMA sai ta kwakule mata idannuwa da hannayenta, bata san wanda ya rigayeka kwonci sai ya rigayeka tashi bane! A kasa ta zauna, ta sake sada kanta, cikin tausasashiyar murya ta ce" Halaya ne irin na mata, shaci fade ne, domin banida tabas, ka yafema bakina da bashida tsaiko wajen yadda muguwar magana Allah ya taimakeka" Kaffafuwansa ya dan murza daya a jikin daya masu dauke da farin safa karkar yana sake sauraronsu baki daya A nutse, cikin fitar harufa a hankali ya dan dubeta ya ce" Ai ba muguwar magana bace, zan iya kiranta da gaskiya" Kai ta karra sadawa tana mai neman afuwa, haka kuma mijinta da Umma na dake tayata neman afuwa Murmushi ya yi, ya ringa kallon Mijinta da ita din kanta, a cen kasan zuciyarsa kuwa tunanin da yake yi shine, shin ko yarinyarsu ta san waye shi tun kafin ya fara sakata fadin abinda bata yi niyar ba? Idan haka ne me kennan?, Tabas shima yana so yarinyar ta kasance wata wace zai iya jin wani abu daga gareta a cikin tunanin dake damunsa a kan bafansa, sai dai yana cikin zulumin idan ya yi haka me ya yi kennan? Ya cutawa yarinyar fa? Me zai iya yi mata? Shi baya anfanar kowa, yana fama da lalura, wai menene a karkashin hadin nan nema? Ya kasa gasgata dan su wanke kansu suka dauke yarsu mace daya kwalin kwal zasu bashi, bayan sun san namiji yake a waje, daga cikin sai a hankali? Mutanen da son kansu yake a bayane ba a boye ba? Kai ya kasa gaskata wannan lamari kwata kwata A nutsensa ya ce" Aunty?" Watau gimbiya, dan haka ta dago tana dan kallonsa Murmushi ya yi ya ce" Yaya zaki iya yin hadin nan bayan babu riba a cikinsa?" Dan daburcewa ta so yi, kafin take daidaita kanta tana kallonsa ta ce" Naw aka zauna da namiji har aka mutu a wannan halin Allah ya karra maka lafiya?" "A wannan zamanin da ido ke tsakiyar kai?" Ya fada shima tamkar ba shi ya yi furucin ba Kai ta sake sadawa ta ce" Ka isa da mu ma, bale ita?" Baki ya dan tabe yana dage kafadunsa ya ce" Hakane kuma" Kallonsa Bafansa ya yi da sauri, kennan ya yarda y isa da su din? ASADEEK ya sake kallon bafansa ya ce" Yaya magana ta hakinta kuma?" Da iya layance abu Bafansa ya fuskanceshi ya ce" Na jima da nema ka bani dama na nemo maka magani, na tabata da tuni yan jikokina na yawo a gidan nan, ama a yanzu ina neman wannan alfarmar, ka bani dama na je na nemo maka magani, ba maganar shiga hakinta tunda muna neman magani, kuma na tabata Allah zai sakamu a hanyar da zamu samu Yarona" Murmushi ya kuma yi mai dauke da ma'anoni da yawa, ya sake dubansa da kyau, ya kalli Umma, sai kuma ya kalli Gimbiya Murmushi ya sake yi sannan ya mike tsaye a kan kaffafuwansa ya sake dubansu daya bayan daya A hankali ya ce" Hakane kuma, Allah bai saukar da cuta ba, sai da ya saukar da maganinta......Bafa ka daura auren kawai..............., Allah ya tabatar da alkhairi" Gaba dayansu ido suka zuba masa na mamaki, Bafansa ya yi gagawar tashi shima yana fadim" Kamar yaya na daura kawai ASADEEK? Aure ai abin a zauna a tatauna ne ko?, Kuma na ga aure mai daraja irin na yar uwarka ai ko sadaki sai mun girgiza mun girgiza sosai ko? Ga saka rana da sauransu?" UMUGHLUK ya dakata ya juyo Lalausan murmushi ya sauke masa ya ce" Ai yarda da na yi cewa, da kai da kaya duka malakar wuya ne ya sakani baka dama, sadaki kuwa ai dama kai kake biya min Bafana," "Ama......?" ...... A hankali ya dakatar da shi ta hanyar fadin" Auta nake son yiwa lesson kafin magariba ta shigo, tana falona zaune, Bafa du abinda ka yanke ka sanar min ta waya in sha Allah, a sauka lafiys" Daga wannan ya shige ciki ya barsu da kallon kallo kowa da abinda ke masa kai ko mo a ransa Babu wanda ya ce uffan sai bangarensu da suka nufa ,