Sashe 69
Zakin Sarakai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
kyau da ya karra yi mata tamkar aljani, ita kam ta shiga uku da ranta da soyayar wannan mutumen A sanyyaye ta shiga fadin" Tamkar ba maganana bane a gabanka , tamkar ba nu bace a gabanka, ka duba ka gani ko yaba kwaliyana baka yi ba bayan sai da na kirawo kwarariyar mai kwaliya ta yi min, gaba daya yanzu hankalina ya fara tashi, ina tsoron jin bayani a kan abinda ya shafe mu" Gannin idan ba sake sasautawa ya yi ba ba lalene ya samu dukkan abinda yake son samu ba ya saka shi dan sakin fuskarsa ya ajiye maganar NADIRAH gefe ya dan ringa biyewa shirmenta har ya kara minti biyar ya mike ya yi mata salama Nan hankalinta ya yi mugun tashi, gaba daya ta nemi rikicewa, Gani take yi idan ya tafi ta yiwu sai wata shekarar kuma?, Dan haka a birkicenta ta ringa tambayar sai yaushe kuma? A nutse ya ce" Na zo fa, kuma tafiyarki ce " Wannan kalamau su suka sakata kwonciyar hankali har ta so yi masa rakiya, ama ya nuna sam baya son hakan ta koma gida, a dole ta komawarta shi kuma cike da kamala yake takawa a cikin kebaben gidan da aka kebe NADIRAH har ya kawo baban get din da mai gadi da kuma mahaifin NADIRAH ke zaune sunna dafa shayi sunna dan hirarsu, a dazu baya nak su ASADEEK suka karaso, shi yasa bai ganshi ba sai yanzu Tunda ya yi masu salama bakin mahaifin NADIRAH ya katse da amsa salamar da ya dauko da nufin yi Kallonsa yake kamar ba gobe, har ya zo ya shigewa ganninsa Daga kafar da ya yi ya yi takun sauki har ya karada wajen motarsa nan da nan ya saka mahaifinta farga da binsa da kallo da ya yi Cikin takun sauki ya karasa wajen motar ta barin da SHEIK yake ya kama ya bude kansa tsaye Ido hudun da suka yi da Sheik, da zaburowar da SARKIN yanka ya yi daga maboyarsa haniniyar dokinsa ya fargar da ASADEEK abinda yake shirin yi watau sare hannun wanda ya bude motar da suke ciki ya saka shi saka hannunsa ya bude motar da karfi ya fito gaba dayansa da rawanin da yske shirin daurawa ya taka kafarsa taku biyu ya tarbi gaban SARKIN yanka da yaren buzance ya ce" Basssss! BASSSSSSSS ITBAL!" (JUYA , JUYA SARKI) "UMUGHLUK ITIBEL" MURYAR mahaifin NADIRAH ta furta a lokacin da ya kai gwuiwoyinsa gaba daya ya dire ya sada kansa dan girmama mutumen da koda ba zakin sarakai bane tabas ya ciri tutar amsar gaisuwarsa koda baya so Dif ASADEEK ya yi daga tsayen nan ya kasa juyowa har sai da ya ji kokowa da kuma shirun da ya wakana a wajen sannan ya juyo a hanzarce ya shiga bayan motar ya rufe da kansa ya mayar da kan nasa jikin motar ya jinginar yana lumshe idannuwansa lokaci daya ya damki rawanin ya dafka shi da abin motar muryarsa a bace da amon bacin rai ya shiga fadin" *NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS ```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, al alaminmu ancinmu.``` *https://www.facebook.com/106494781436168/* *OUMOUGHLOUK ITIBEL* _(ZAKIN SARAKAI)_ _FREE BOOK_ *Na* *SAJIDA NIGER* 5 Mun bani an kuma dauke wutar nepa "shi kuma waye wannan?, Yaya aka yi ya Sanni?, Yaya zai kutso ya katse min binciken abinda ya kawo ni? Bayan dogon hakurin da na yi da wancen marar tarbiyar ya kuma lalatan lok aci? Hakan na nufin sai na kwana a garin nan ko me?, Babu inda zan je idan ban san ainahin abinda ke neman numfashina ba!, Bata isa ta ringa rayuwa da wani a tunaninta ba, bata isa ba!" Fada ne na mamaki, fada ne da duka rasa dalilinsa, hakan ya sa suka yi shiru gaba dayansu babu wanda ya furta koda A ne har suka karasa bakin jejin wani a rakumi ya yi masu ja gaba suka karasa boyayen gidansa na garin TANUT din wanda ke zagaye da dakarun buzaye a saman rakumansu sunna zagaye kowane shirye yake a mutu idan ta kama, dan babu wanda baya dauke da takobi mai kaifin balaki da kuma bindiga ta zamani Fita ya yi ya karasa cikin falon ya zauna ya zubawa waje daya ido kansa na sarawa, lokacin sallah da saura shi yasa ya dakata a nan Ya dauki lokaci a nan a zaune SHEIK ya shigo da salama a bakinsa cikin nutsuwa ya ja ya tsaya har sai da ya budi bakinsa a hankali ya amsa a saman lebensa sannan ya sauke ajiyar zuciya ya karaso ya zauna face da shi A sanyaye ya ce " KISHI?" ASADEEK ya yi tamkar bai ji abinda ya fada ba, har sai da SHEIK ya maimaita kalmar yana kallonsa Fuskarsa da yannayin rikicinta ya dube shi yana kausasa kallonsa ya ce" Me kake nufi da kalmar KISHI?" Sheikh ya sauke dubansa a cikin na ASADEEK, sai kuma ya dan girgiza kansa a hankali ya ce" Bana nufin komai,, gani na yi tunda muka taso yau jinninka yake kan Akaifa" ASADEEK ya juyar da kansa bai ce komai ba Sheikh ya sake sauke ajiyar zuciya a hankali ya ce" Shi din wannan mutumen shine wanda aka barmu a cikin masalacin mu hudu , a gabansa muka tatauna da sarkin garin nan, kuma yana cikin shedun da suka sheda daurin aurenka da ita, haka kuma ba zan manta fitarsa a lokacin ba, ana gama daurin aure ya fice da sauri , da ba dan ba kar nace hawayen me zai fito daga idannuwansa da nace har kamar hawaye na bin kumatunsa, ka ga dai yannayinsa ka san bashi da karfi, kusan shine marar karfi a wajen domin ko a ranar ba wata sutura mai tsada bace a jikinsa, sai dai yana tare da wata boyayiyar nutsuwa da sadadan kallo, a yanzu haka ganeka da ya yi kai ka san akoy wajen da ya sanka, da zaka amince idan ka huta ya shigo mu zauna da shi mu ji ta bakinsa, ta yiwu ya dan wani abu a cikin wannan kulli" Bayan Sheikh ya dire maganarsa ASADEEK ya dauki minti uku a kalla yana sauke ajiyar zuciya yana ta korar abinda ke cizo shi A hankali ya gyara zamansa ya ce" Ban gaji ba, a shigo da shi" Sheikh ya sake kure shi da kallo na yan sekwani, gaba daya da zai ji tashi da ya hakura har ya samu nutsuwar zuciya , sai dai tunda ya kiya babu yadda zai yi , a dole ya mike ya fice ba wani kwarin jiki ya fita dan sanyo bakon Su uku suka shigo, SHEIK a gaba, mahaifin NADIRAH a baya, sai sarkin yanka a baya hannunsa saman takobinsa dake jikin tsatsonta, fuskarsa kuwa sam ba alamun sasauci Sheikh kadai ya zauna saman kujera, Sarkin yanka ya ja ya tsaya ta hanyar wara kafafuwansa rawaninsa na sake rike zagayayiyar fuskarsa, Mahaifin NADIRAH kuwa a kasa ya duka a nesa sosai kansa a kasa ya yi shiru, domin ba'a bashi damar da kawo da gaisuwa bama bale ya kawo din Dan shiru wajen ya dauka har sai da SHEIK ya gama karewa ASADEEK kallo zuciyarsa cike da mamakin rashin hakuri a abinda ya shafeta wanda kiri kiri yake turewa ama bai san a bayane yake a fili bs SHEIK ya dubi bawan Allahn nan da haka kawai yake jin yana iya sauraronsa ya ce" Bismillah, ka yi hakuri ka sanar mana wanene kai? a ina ka san UMUGHLUK ITIBEL?, Yaya aka yi ka gane shi?" Mahaifin NADIRAH ya dago fuskarsa a sanyaye ya kalli SHEIK, sai kuma ya sake mayar da fuskar tasa muryarsa a sanyaye ainun ya ce" Allah ya taimakeka, a gafarceni, tunda na ga ABAN DATAWA a wajen nan hankalina ya gama rugunzuma ya tashi, gaba daya tsoro ya darsu a zuciyata, na tabata tunda na ganshi a wajen nan ya san yarinyar dake gidan ba ainahin ita bace aka .............mmmmm" "Yaya za'a baka umarnin wani abin daban, ka ringa yi mana bayani a kan wani daban!, Ka kama kanka!" Sarkin yanka ya fada a kausashe Hankalin Mahaifin NADIRAH sake tashi ya yi, ya rasa me zai ce yanzu kuma, ko dai rikicewarsa ce ke neman saka shi aikata abinda ba'a nufi cen da shi ba? Kar dai ba abinda yake tunani bane ya kawo su shi kuma ya bude baki yake sanar masu abinda ba'a tambayeshi ba? "Ka barshi ya yi bayanin abinda yake son fada ITBAL!" Muryar ASADEEK da ya dago daga jingine jin kalaman dake bakin wannan bako Dubansa ya maida kan Aba , ya zuba masa ido Ainun, daga irin tsugunnon da Aba ya yi a kasa kaffafuwansa a tankwashe a jikinsa da irin hade hannayensa da ya yi ya saka shi kallon saman cafet din nan a nutse ya ce" Bismillah ka dawo nan ka zauna" Aba ya sake sada kansa, cike da girmamawa ya ce" Allah ya huci zuciyarka, nanma daraja ne a wajena idan har a gabanka nake, a yafe min, a gaffarceni, na aikata kuskuren budar bakina a yi mib afuwa , zan sanar a inda na sanka, sanadiyar iyalina a lokacin da aka so yankewa mahaifiyarta hukuncin kisa, nine nan ka bayar masarautar Tanus cewar na zamto sarkin dawakai a bisa adalcinka da kuma tausayinka, na tabata ka manta kamanina, sunana SALIHU daga kauyen LABBA" ASADEEK ya Sake fuskantarsa, tabas an yi haka da jimawa, asalima a lokacin ba shine zai yi shara'ar ba, mahaifinsa dai ya saka shi ya bashi umarnin zuwa da yanke hukunci yadda ya dace A nutse ya ce" Bayan wannan , me ka sani dangane da maganar BAHIJA" Kansa ya dago, irin duban da ya yi masu babu wanda bai ga tashin hankalin da zuciyyarsa take ciki ba, ya yi hakan ya kai sau uku, ama a cikinsu babu wanda ya fahimci da ace zasu taimaka masa su ce da shi ba sai ya fadi komai ba da sun rufa masa asiri, baban tashin hankalinsa iyalinsa, yaya za'a yi da su? Wani irin hukunci zai hau kansu? Subahanalah yaya za'a yiwa NADIRAH?, Innarta fa? A dole hawaye ya shiga bin gefen kumatunsa Sosai ya karra sada kansa hankalinsa na tashi A sanyaye ya ce" RANAR talata ne, FATIME