← Book details Zakin Sarakai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 60 OF 87

Sashe 60

Zakin Sarakai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

isa su bata abinda take so ba, zata karra kaima wanda ya isa ya gyara batatacen al'amari kukanta , shi zai gyara mata cakulalen rikicin nan ___________________________________ *WASHE GARI* Kamar yadda ta saba shigowa a lati, yauma hakan ce, haka kuma tau a jikin nata babu alkyaba kwata kwata, wani lafcecen hijab ne ta saka har kasa mai hannaye ta fitar da hannayenta sannan ta daure abin daurewar a bayan kanta bayan ta saka baban abin daure gashi, kanshi ne dai take bazawa mai yawan gaske , hankali Kwonce ta ratsa tana tabe baki sanadiyar gannun sun zube kasa kowane kanda a sade ta tabata dan bata da alkyaba ne ba zasu iya yin ido hudu da ita ba Maimakun zuwanta a lati ya kasance sabo a wajensu, sai bai kasance din ba, asalima hijab din dake jikinta ya saka matan zuba mata ido cike da mamakinta har ita da kanta HUZNAH ta kasa dauke dubanta a kanta Dan tsai ta yi tana kallon kujerar da HUZNAH ke sama, wace take zama ce kwana biyun nan, wato ta kusa da shi sosai Kanta ta dauke ta karasa ta ja wata kujerar ta zauna tana dan dago idannuwanta daga lumshe su da take yi muryarta cen ciki ta furta" Sannunku da hutawa" Shiru ne ya biyo bayan tambayarta, ta kai dubanta wajen Auta ba alamun damuwa da rashin amsa matan kasa kasa ta yi mata kallon sannu fa, sannan ta maida dubanta wajen Umma da lamarin yarinyar ya fara tsoratar da ita kasa kasa ta dan sakar mata murmushin da yake a saman lebe ne kawai sannan ta kai kan HUZNAH Duban ido cikin ido suka yi tta yatsina fuskarta wanda kiri kiri ana kallo domin a bayane ta yi sai kuma ta sake maidawa kan wankakun farare tas din plate masu wani tsararen launi a ajiye da rantsatsu cokulai biyu a samansu masu ruwan golding an dan nade su da farin tissu abu dai a tsare masha Allah, sam bata yarda ta dubeshi ido cikin idon nan ba tunda ta zo, hasalima gabanta ke yankewa yana faduwa, kuma zaman da matarsa ta yi a kusan shi ya mata daidai domin koda bata yi haka ba itama yau ba zata iya zama a hakan ba Abincin ta zuzuba cike da isa irin tata itama, harda plate din Nadirar sannan ta koma ta zauna ta dauki cokalinta ta fara ci a hankali Idannuwanta ta lumshe sanadiyar goshinta da ya dauki gumi na zufa kamar zafi ke hura dakin bayan sanyin AC ne ke tashi A jikinta take jin kaifagun idannuwa a kanta, a yannayin kallon mutanen da take yi kuwa sai ta ga babu mai kallonta, ta yiwu wanda bata gaisar bane yake kallonta Murza gaban goshin nata ta yi ta dan dago idannuwanta ta sauke a saman hannayensa , a hankali ta murguda bakinta sannan ta gyatsine hancinta ta mayar da dubanta gefen Auta tana kallonta Idannuwansa ya lumshe hadi da yin murmushi boyaye sannan ya sake duban kalar abincin da aka yi yau, sai kuma ya dubi Auta dake ta faman tsakura ta kasa ci A hankali, furucinsa a nutse ya furta " Bakya son abincin ne?" Kasancewar magana ce ya yi bayan ya dauke dubansa a kan Auta ya saka su kallonsa su hudun baki daya sannan ukun suka dawo da dubansu kan bakuwar cikinsu, domin itace wace t zo masu da firgitaten lamari , kowane yana tunanin da ita yake Da mamaki HUZNAH ta sake dubansa gabanta na yankewa ya fadi da dan karfi, shi kuwa sai da ya dan yanka steek din dake gabansa ya saka kadan a bakinsa ya dan tauna ya hadiye sannan ya dago idannuwansa ya zuba dubansa a fuskar HUZNAH da ta tsatsareshi da ido Idannuwansa ya lumshe mata , sannan ya kkai dubansa kan fuskar NADIRAH Ya taki Sa'a itama a lokacin kallonsa take yi, hakan ya sa suka yi ido hudu da junna Faduwar gabanta ya sakata jin wani irin rauni ya taso mata a cen kasan zuciyarta da kuma gangar jikinta, tana kallonsa jiki ba karfi shi kuma ya saka kaifafun dubansa a kanta, idannuwan da a jiya ta ringa kallo a matsayin wani bijimin zaki, lebunnan da suka yi ta damkar kan mamanta da dogon karan hancin da ya yi ta saukar mata da zazafan nishi a wuyanta A hankali ta dauke dubanta tana tare hancinta da ta ji wani lumlumlum da sauri , watau wani dumi na neman biyowa ta hancin nata wanda ta yi tunanin ko tsinkakiyar majinar nan ce? Ta saka hijab dinta da sauri tana jin kanta na sara mata, wannan wani irin kallo ne yake yi mata haka?, Me yasa take ji kamar zata summa dan faduwar gaba? A hankali ya dauke zazafan idannuwansa daga kanta ya maida kan Auta da ta yi sumnar zaune tana kallon ikon Allah, fuskarsa a sake, sannan a birkice ya ce" Bakya son abincin ne?" Wata ajiyar zuciya ce HUZNAH ta saki da ta fahimci ba da BAHIJA yake ba, Ummama ta fauke dubanta ta yi kamar bata ga komai ba tana jinjina karfin halin NADIRAH Auta ta dan kalli madarar dake gabansa, wa'inda yau abu biyu ne a ajiye a shake da madarar sannan ta sada kanta ta kasa cewa komai *NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS ```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, al alaminmu ancinmu.``` *https://www.facebook.com/106494781436168/* *OUMOUGHLOUK ITIBEL* _(ZAKIN SARAKAI)_ _FREE BOOK_ *Na* *SAJIDA NIGER* 4 Ba edditing fa Madarar ya kalla shima, a hankali ya sake fadin" Dama kina son madara ama baki taba nuna min ba?" Umma ta yatsine fuskarta, a duniya idan ka ji yana magana a tausashen nan yana ta magana dama da mutun biyun nan ne, wancen mugun malamin sai wannan mahaukaciyar kanwar tasa Wani murmushi Auta ta saki tana dubansa da kula ta ce" Abahna, ina son madara sosai, la manta da ran marigayiya ana kawo min madara sosai?" Murmushin ya yi mata shima yana sake kallon yadda fuskarta ke kawatuwa da farin ciki, ya dora hannunsa ya tura mata jug din gabanta kasa kasa ya ce" Da ke, da du wani mai shanye min ga naku" Wannan karron daria ta yi harda dora hannunta saman bakinta cike da mamakinsa, gashi ya yi maganar kasa kasa, kuma ya gimtse kamar ba shi ba, dariarta kadai ta saka su zuba mata ido su dukansu ukun, Huznah da mamakin wai Auta ce ke daria?, Umma gananta ya fadi tana sakw duban Auta zuciyarta na shiga a uku da gannin daria ne take yi? Na menene? , NADIRAH kuwa ta zuba mata ido tana kallon dariar tata wace ta sakata jin kamar zata saki murmushi domin kana kallo zaka ga abinda ya sakata dariar mai girma ne a zuciyarta Hannunta ta cire wanda ke tare a gaban hancinta zata duba ta ga ko menene Da sauri ta zarro ido tana mikewa tsaye hakama Auta fa sauri ta furta" Subahanalah aunty Jinni ne?" Ihu NADIRAH ta saka ta tataro hijabin nata gaba daya ta cireshi tana karra saka ihu tana fadin" Na mutu jinni wayo Innata jinni, wayo jinni na mutu daga ina yake fitowa?........." Sumurta kokowa take yi da kanta tana cire hijabin gaba dayansa ta bayana daga ita sai zani daban riga dabsn, rigar mai siririn hannu, zannin kuwa ta masa wani dauri a cen saman gwuiwarta gashin kanta a daure a tsakiya ta ringa kai hannunta tana shafowa ta karra kwala ihu tana fadin" Na shiga uku Habo ne, walahi habo ne nake yi............................" Mutun biyu suka zabura suka nufota watau Auta da Umma, HUZNAH kuwa ta rafka tagumi tana tunanin anya tunda yarinyar nan ta fara cin abinci da su an taba zama aka wanye lafiya?, Shi kuma a hankali ya jingina da jikin royal kujerar ya zuba mata ido yadda take sumurtu tana kwala ihu tana gudu ta ki tsayawa bale su Umman su iya riketa karra fadi Take yi INNATA HABO NAKE YI A zabure ya mike tsaye daga zaunen da ya yi a lokacin da ya ga tsutsar kan nata zata izata waje a haka Taku uku ya yi a hanzarce ya damki hannunta na dama ya janyota gabansa sosai yana son dago fuskarta ama ta ki yarda da hakan sai zunduma ihu take tana a taimaketa habo take yi Umma dake fadin" BAHIJA ki saurara mana, tsaya a duba mana, ki daina dukar da kanki ba zai tsaya ba" ya duba a hankali ya furta" Umma, je ki ci abincin bara na wanke mata" Da mamaki Umman ta dakata da son rikotan tana kallon yadda ya saka hannunsa ya cicibata gaba dayanta ya dora a kafadarsa ya juya ya nufi hanyar sama da ita a lokacin kuwa bakinta fadi yake" Umma amsoni, umma dan Allah amsoni, UMMA kar ya tafi da ni, UMMA ki amsoni" Sunna tsaye kamar a summe su biyun haka matarsa na tsaye a gaban abincin tana hangensu har ya bacewa ganninsu sannan Umma ta juyo tana sake zarro idannuwanta sai idannuwan nata suka sauka a kan HUZNAH da ta yi wani iri kamar zata fashe da kuka tsabar hankalinta a tashe yake Dan murmushi ta samu kanta da saki, tabas idan har ta yi la'akari da maganar da yarinyar ke fada mata cewa ta barta ta yi aikinta yadda ya dace ya dace ta bartan, domin idan har hakan ne tabas yarinyar zata yi gagawar kaisu ga ci a mafarkin su, dan haka bara ta jefi tsuntsu biyu da jifa daya ta hanyar gumawa matarsa ta kasheta da kutu Zama ta yi saman kujera ta sake janyo abincin ta saka cokalinta hankali kwonce ta sake kallon HUZNAH dake kallon hanyar da ya bi da NADIRAH ta yi murmushi ta ce" ki zauna mana Gimbiya?" Gabann HUZNAH sai da ya karra faduwa, a hankali ta juyo tana kallon Umma Gimshewa ta yi tana kokarin boye damuwar dake shinfide a saman fuskarta ta zauna tana kokarin ci gaba da cin abincin Umma ta sake yin murmushi tana hangen Auta ta tafi falo ta zauna a ranta ta yi kwafa, a bayyane kuwa ta ce" Kin san ita fa mace, mai sunna mace bama sai ta zuba leshen daruruwa ta maka hodo a fuska ba ake kallonta, kuma ba zaki taba
Chapter 60 · 0% Book details