← Book details Zakin Sarakai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 87

Sashe 42

Zakin Sarakai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

yake tana karra kallon NADIRAH, sai dai gannin kamar bata masu kallon wulalanci ba sai ta samu kanta da dan sauke ajiyar zuciya Auta kuwa ta rasa me take ji a ranta game da matar, ita dai ta zuba mata ido tana son karantarta Ba tafiyarsa ta sheda saukowarsa ba, domin takalman dake kafarsa na fata ne, basa kara idan ana tafiya da su Fankamemen madubin dake kafe ya sheda mutun zai sauko, hakan ya sa a tare suka juya kowa ya daga kansa dan gannin ko wanene Abin mamaki, kasancewar rabonsu da shi tunda safe dole zasu masa gaisuwa irin ta dukawa, ciki harda Umma domin wannan din hakan yake, Uwa uba HINDU da har neman kwonci take yi bama dukawar kasa gaba dayanta ba, ya zamto NADIRAH ce a tsaye, kanta a sama tana kallon saukowarsa cikin nutsuwa, da sandar dake hannunsa mai ruwan zeba tana walwalwal, da alkyabar dake jikinsa, uwa uba da rawaninsa mai masifar kyau wanda ya hau da shigarsa mai tsari da kyan gaske, a gangaro zuwa farin hannunsa kar mai jimke da sandar, dayan kuwa a cikin Alkyabar, haka kuma girman jikinsa wanda koda a cikin alkyabar ne ana iya ganewa da bashida karamin jiki, da irin nagartar shigarsa mai dukkan kirji A hankali ta yi luuuuuuuuuu da idannuwanta a lokacin da idannuwan nata suka shiga cikin nasa, sai kuma ta gane jikinta babu abinda ke nufi da itace BAHIJA watau Alkyaba Juyawa ta yi ta karasa kusa da Umma ta rage tsayinta kadan ta ce" Bani abin na rufa" Umma ta dago daga sada kanta ta mika mata alkyabar ita kuma ta gyarata kawai ta wani yafata a kafadunta sannan ta sake duban Umma da ta fara mikewa tana sake yi masa sannu da saukowa ta karasa kusa da NADIRAH cikin dabara ta shiga fitar da hular alkyabar ta dora mata a saman kanta a tausashe tana murmushi ta ce" BAHIJA, ki karasa ki gaisar da Mijinki mana" A hankali ya karra zubawa wace aka kira da BAHIJA ido, wannan karron ba duba daya da dauke ido ba, duba irin na tsanake dan ya gane me kennan?, Tun daga kanta har kaffafuwanta yake kallo sannan ya sake kallon Umma wace sam bata gane abinda ke wakana ba, burinta su daidaita dan ya yarda Bahijar ce a gabansa Umma ta rike hannun Nadirah suka karasa wajen zaman , gefen daya, ba inda su Auta suka zauna ba ta nuna mata tana fadin" Zauna a nan kema sai ki kawo gaisuwa" Zaunawar ta yi tana sake leka Innarta, ko dai inna ta summa? Take ayannawa a zuciyarta, Haka kuma a koye koyen abubuwan nasu sun manta basu koya mata baban abin ba, watau gaishe da UMUGHLUK ITIBEL, ai su basuma kawowa ransu cewa sai an koyar da ita wannan ba, gannin ita fa yar bayi ce ko? Bata sake kallon idannuwansa irin na dazu ba, bale har ta lura cewa kallon da yake mata ya gane ba ita bace Bahija a fuzge ta ce" Sannu da saukowa" Ba Umma da su Auta ba, harta Innarta sai da ta ji kamar an gaura mata mari , irin da busashen hannun nan, marin nan mai zafi da bada sautin DAU a kunci! A rikice Umma ta dubeta , sannan ta dubi ASADEEK da ya sake komawa da kyau saman babar kujerar da take tasa ya hade kansa da kujerar ya afka tunanin me hakan ke nufi? Ta ce" *NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS ```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, al alaminmu ancinmu.``` *https://www.facebook.com/106494781436168/* *OUMOUGHLOUK ITIBEL* _(ZAKIN SARAKAI)_ _FREE BOOK_ *Na* *SAJIDA NIGER* 2 A rikice Ummaa ta ce" Har yanzu bataa dawo normal ba, Bahija ko mu mayar da ke bangarenki ne?" Shiru ne ya dauki wajen, domun Itama NADIRAH sai ta samu kanta da yin shiru tana ta auna me ya dace ace ta ce? Baba ne ai ya daace ta duka ne ai tana gannin ta gaishe shi a duke haka Ajiyar zuciya ta sauke ta dauke kanta daga kan Innarta wace dama sai da aka ce mata idan sun zo a matsayin baiwa zata kasance har su koma Idannuwanta ta sake orawa a kansa A facing dinta yake, domun kujerarsa na kallon su ne gaba daya Yawu ta hadiye aa hankali ta sauko kasa gaba dayanta kantga a kasa ta furta" Barka da warhaka, Fatan aan sauko lafiya?" Dama dama, watau gaisuwarta mafi dama da sauki kennan, mafi daraja kennan, sai dai kashhhh tun a nan ta tona kanta cewa ita din ba jinnin sarauta bace, domin ko Umma a yanzu ta wuce gaisuwar nan bale UMUGHLUK ITIBEL Ga mamakinta sai ta ji muryar mutanen da suka fi kusanci da shi sunna nema mata afuwa, bayan bata ga laifin da ta aikata na hakan ba Daya bayan daya ta shiga binsu da kallo, tun daga kan Ummar har wace keda fuska kamar ta yara sai shegen kallon tsiya Baki ta dan tabe ta nemi mikewa, Da sauri Umma ta mata alamun kar ta mike daga tsugunin nan, a dole ta sake gyara tsugunin nata tana girgiza kai irin abin nan fa ba zata iya ba walahi! A hankali ya dago kaansa dake jingine idannuwansa a lumshe y bude su y fara sauke dubansa a kan Umma, wace ke gurfane kanta a kasa Tambaya ce ke saman lebensa, wace take daf da fitowa daga bakinsa, itace wannan din kuma wacece? Sai kuma ya ji wani sashi na zuciyarsa na yi masa wata tambayar, shin UMMA bata san Bahijar bace aka miko mata wannan a matsayin Bahija? Wannan din wacece? Me yasa aka ce za'a bashi auren Bahija aka bashi na wata? A sanninsa bafansa y'arsa mace daya tak ce, itace wace suka yi tafiyar nan tare, bayanta a ina ya samo wannan?, Alamun wannan sun nuna ita din ba yar gidan sarauta bace, domin dan gidan sarauta ko yaro karami in dai ya fara iya hada magana ya iya gaisuwar sarki "Allah ya huci zuciyarka, yarinta ke dawainiya fa ita, a yafe mata, tana tuba in sha Allah ba zata kuma aikata makamancin wannan gangancin ba" Umma ta sake fadi a tausashe tana sake sada kanta "Yarinta?, Ganganci? Wannan din ai ya fi karfin ganganci ga mace aya tilo da aka bashi a matsayin BAHIJA, lalle sunne suka yi ganganci wajen manta abu mafi mahimmanci, to shi a yanzu tamabayar da ta maye gurbin wacece wannan din itace....menene dalilin yin hakan? Ko yace menene mission din da aka ba wannan din?, Shi sai yake gannin kamar fitsarariya ce yarinyar, jama'a wannan kallonsa da take yi ido cikin ido fa?, Ga kuma gaisuwa irin sako da sako A hankali NADIRAH ta sake satar kallon Umma, to wai ita a ina du ta fadi magangannun nan da ake cewa ta ce?, Uhum, wai yarinta ganganci, zaki ga aikin ganganci kuwa A hankali ya gyada kansa yana sake dauke dubansa ya sake mayarwa kan Auta Ido hudu suka yi da Auta, sai yake karantar kamar ta afka a tunanin son gane yarinyar nan a cikin mahaukatan ita baba ce ko? A hankali ya sauke dubansa a fuskar HUZNAH Idannuwanta cike da lamari irin na rarashi da girmamawa, shigarta ta birge shi sosai, itama HUZNAH leshen ne yanaga a jikinta, kuma dinkinta sakake sosai , Huznah kam akoy hankali Kan matar dake duke, wace yake kyautata zaton baiwarta ce ya sauke dubansa, tun dazu take duke haka, sai ya samu kansa da yin gyaran murya yana duban matar Shirun da ya gani bata tashi daga gurfanawarta ba ya saka shi sake dora dubansa a kan Umma Lalle matar nanma ba ta gidan sarauta bace, ba kuma baiwa bace Da sauri Umma ta mike, kafafuwanta har sunna neman yi mata nauyi, rabonta da shiga dimuwa irin haka tun wani lokaci da mahaifiyarsu ta tardota tana zane Auta, A hankali ta dafa Inna kasa kasa ta ce" yana nufin kina iya tashi" Inna ta dago tana jan hanci ta saci kallon y'arta, oh duniya yau ga abin jibga Indi ta yi ba halin ta zauneta ta jibgeta? Innalilahi ita HINDU ashe zata ga wannan rana irin haka? Dole yau ta Jibgi Indi walahi! Kanta a kasa ta shiga kokarin kamanta gaisuwa da neman afuwa kamar yadda ta ji matarsa da kanwarsa da Umma na yi, sai dai itama bata san a yi masa maganama masu wannan yancin kai tsaye makusantansa ne A hankali ya jimke hannunsa jin kamar bacin rai na neman hadasa masa mijirya a gaban jikinsa Umma ta salami HINDU fuskarta har tana gyatsine dan rikicewa A hankali ya budi bakinsa maganar farko ya ce" Umma, kina iya tafia" Umma ta kalle shi, hankalinta a tashe ainun, sai dai ba damar jan maganar dan an masa laifuka a jejere sosai A hankali ta karra neman afuwarsa sannan ta nemi da NADIRAH ta mike su tafi Da mamaki Auta ta kalleta, hakama HUZNAH HUZNAH ce ta yi karfin halin fadin" Aa umma ki je zata zo, bamu gaisa ba fa" Umma ji ta yi kamar ta karasa ta shaki wuyan HUZNAH ta gaura mata tagwayen mari, sai dai ba hali, a hankali ta saki.lalausan murmushi sannan ta kafe NADIRAH da ido, wace ke duke ba'a bata damar tashi ba, ita gaba daya bama fahimtar wannan magama kamar masu ciwon baki take yi ba, kamar ta yi kisa ? Wai shi sarkin adalci? Walahu harda zalunci a jerin sunnayen nasa , in ba wannan ba me ta masa daga haduwa? Koda yake mutumen da ya tsofi su Inna ai sai hakuri da hali, itafa kowama ya kama kansa fa, itafa bata zo wajen nan dan komai ba sai dan ceto, ceton kuwa zata yi shi ne ta hanya daya tak, idan sun tashi karshi ta fada masa, dan ba zata iya kayan takaici ba,wani zuwa gaishe gaishe da sauransu gaskiya bata so, ita da ta so ta fita bayan magaribar yau ta zazaga masarautar babu alkyaba? Ta gaji da zaman dakin ya fara hadasa mata ciwo Jiki ba karfi Umma ta juya ta fice, ji take dama tana iya zama kuda ta lane a jikin NADIRAH ta ringa daidaitata?, Ya Allah! Tana fita Auta ta sake kallon Yayanta A sanyaye ta ce" Abah, ta mike
Chapter 42 · 0% Book details