← Book details Zakin Sarakai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 87

Sashe 14

Zakin Sarakai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ido ta zarro sanadiyar gannin Bahija ta mike ta nufi inda suke din Sai dai kafin ta karasa ta ga rusheshen bodyguard dinsa ya tsaya a gabanta fuskarsa ba alamun dariya a kausashe ya ce" Ina zaki je?" Gabanta banda dokawa babu abinda yake yi, hakan ya haifar mata da fitar hawaye tana shirin bashi amsa suka ji muryar Balaraben nan ya umarta kan a barta ta karaso Wata irin ajiyar zuciya ta sauke jikinta har rawa yake ta karasa wajen da suke zaune ta yi salama muryarta har tana rawa rawa Sannin mahinmancin salama ya saka shi amsawa a saman lebensa sannan ya dan juyo kadan ya sake kallonta ya kuma dauke kansa Tsaye take tana murzar hannunta har sai da balaraben ya ce " Bismillah mana yan mata?" Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta zauna a kujerar dake face da su gabanta na ci gaba da faduwa Rasawa ta yi, shin kuka zata fashe da shi ko kuma ta ci gaba da kokari har ta gama abinda ya kawota? Nikaf din ta sake dagewa dan ta tabata bai ga kyanta da kyau bane wannan mutumi A sanyaye ta ce" Dama , dama zuwa na yi, ina so na ganshi......" Inda ta nuna din ya kalla, sai kuma ya sake kallonta Dan murmushi ya yi ya furta" Bismillah" Sake kallon balaraben ta yi da kyai, gannin ba zai basu waje ba ya sakata sauke ajiyar zuciya, kirjinta na ci gaba da dokawa ta sake kallon bawan Allahn nan A hankali ta ce" Sunnana BAHIJA, ni yar sarkin garin Tanut ce, mun yi tafia tare har gashi za'a fara komawa, ban san shi ba, kuma ina son na sanshi..... Ina matukar son na san shi" Da mamaki balaraben nan ya kalli ASADEEK, wanda idannuwansa kawai ya lumshe yana mamakin lalle lamarinta ya girmama, al'amarinta ya giga, Dan sake kallonta ya yi, a sanninsa masarautar TANUT da ta AGADAZ masarauta ce ta familly daya? Bata sanshi bane ko menene? Da mamaki ya ce" Aa, baki gane shi bane? To ai.................." "Hhhhhhhhhhhummmmmmm, " ya yi gyaran muryar da ta saka su kallonsa gaba dayansu A hankali ya kalli wajen pepper da byro ya janyo su cikin nutsuwa ya rubuta mata numbarsa ta sirri ya mika mata ta hanyar ajiyewa a saman table din hankali ya sake kallonta da firgitatun idannuwansa sannan ya ce" Cl me." Wata irin ajiyar zuciya ta sauke hadi da sakin lalausan murmushi ta dauki takardar har kamar ta duka wajen godiya ta juya ta nufi wajen kawarta kamar zata kwaso shoki dan farin ciki Da mamaki ya kalli ASADEEK ya ce " Me kennan MAN?" ASADEEK ya dube shi, yana basarwa ya ce" A ina fa?" Murmushi ya yi shima yana girgiza kansa kawai ASADEEK kuwa ya dantse lebensa a kasan zuciyarsa ya ayana' Yaro man kaza.... Koda yake ba laifinki bane laifin zuciya ne' Daria ta fashe da ita tana sake rike takardar nan da hannayenta biyu biyu, ta kai daidai hanci ra ta sinsina tana lumshe idannuwanta sannan ta dauki jakarta a hannun baiwarta ta saka tana kallonta ta ce" ki rike takardar nan Mudin ranki kin ji?" Kai ta gyada da sauri tana rikewa da kyau din Da mamaki kawarta ta tafa mata ta ce" Lalle na yarda, kin kamu sai gyaran Allah, Amma kawata bakya tsoron wulakanci irin na Da namiji?, Kika yarda ya san kina sonsa bakya tsoron abinda ke iya haifarwa? Kin san fa maza bale masu kudin nan" Murmushi ta yi ta ce" Ai koda ya yi girmansa ne, kawata kin ji hannuna har yanzu kanshin turarensa yake?, Zan bi ku gida jibi dan burina na je na samu mama da wannan albishir, na tabata sai ta fi kowa farin ciki domin irin burin namijin da take min kennan" Haka suka ci gaba da hirarsu cikin sakewa, wani tsare tsaren da basu yi a kwanakin da suka shude bama sai yau suka yi shi a sake hankalinta kwonce, domin gani take yi tunda har ta damu number wayar mutumen cen, komai ya gama sai shafa fatiha, ta yi miji na kece raini, dan kwalisa mai kanshi. __________________________________ Yan umarah masu babar tafia watau VIP tuni jiragensu sun fara dawo da su gida Tun da safe suka karaso garin Niamey, daga nan luma suka nufi AGADAZ a wani jirgin, hakan ya sa tunda ya samu ya shige, sallah kawai le fitar da shi ta boyayiyar hanya har dare ya shigo ya kwonta dan samun hutu ko yayane, domin ya sani a gobe zai yi fitar wuri Fada dan gannin abinda ya faru bayan baya nan ____________________________________ Tarba ce akai mata wace ko mahaifin nata ya sameta ya more Yayunta biyu suka daukota daga filin jirgi, sai sangarta take zuba masu irin ta sangartatun yaya, ga baban farin cikinta fa murnarta shine ta karasa gida dan ta sanar da abinda ke zuciyarta wa mahaifanta Gaisar da ita ake yi, ama sam hankalinta ba a kan kowa yake ba, ga alkyabar da ta dora sai walwali take hakoran makarta na wal wal wal A nutse Mahaifinta ya mike ya tarbota a jikinsa yana murmushi ya dago fuskarta ya furta" Farin cikin Aba?" Murmushi ta saki ta karra dubansa ta ce" Abana" Mhaifiyarta ta karaso itama fuskarta dauke da fara'a tana kamota jikinta ta ce" Mu karasa ciki, wannan farin cikin fa?" Ajiyar zuciya ta sauke tana daga idannuwanta tana hangensa a idannuwanta a lokacin da zasu tafi jiya, kamar ta biyo su su dawo tare Har sun shige mahaifinta ya dan biyo bayansu yiwa mahaifiyarta maganar ya ce" ki tabatar kin shirya tafiyar nan, da sasafe zamu fita, sannan ki tabatar a yau ba sai goben ba kin fara yi mata maganar dan ta san da abinda ke jiranta" Jiki ba karfi ta gyada kanta ta shige cikin tana kallon yar tata da ta cire Alkyabarta ta kuma cire abayar dake kasa daga ita sai Pant da bra ta dauki tawul ta nada a kirjinta tana murmushi ta ce" Mama, tsaya na fito mamana, mamana akoy hira" Mahaifiyarta ta dan zarro ido ta ce" Ke baki gaji bane hala? Aikin umura ga kuma zaman jirgi gaki da son jiki?" Murmushi ta yi tana girgiza kanta ta ce" Mama, ba zaki gane ba, abinda nake tare da shi ya bige maganar gajiyata, mama bani minti daya" Da murmushi ta rakata sannan ta mike ta janyo abubuwan da aka zuba mata abinci ta shiga zubawa a cikin plate tana dan duba wayarta ..........MAMA........ Ta fada a hankali bayan ta zauna daf da ita A hankali ta dora kanta a gefen kafadunta ta ce" Bam taba tunanin a Africa, a karamin gari irin namu zan hadu da shi ba.......,ama na tabata zuwa ya yi, da ganninsa ba haifafen kasar nan bane........, Mama ban taba gannin tsarin halita, nutsuwa, kyau, aji da nutsatsen arziki irin nasa ba, shi din ba tara bane, goma ne..... Mama tunda na je ko zama ban samu ba kulun tunaninsa, har kuka na yi............ Mama na samo maki sirikinki, wanda kike min fatan samowa, mama zan faranta maki ranki, zaki yi yadda kuke so, farin cikinki zai zaga duniya, zaki kece raini......idan kika ganshi sai kin yi farin cikin da baki taba yi ba....., Baban burina shine ya amsaniya kuma yarda da ni"...... Ta karashe maganar tana dora kanta a kafadar mahaifiyarta, wace ta yi mutuwar zaune Hankalinta tashe ta dago fuskarta tana kallonta, a sanyaye ta ce" BAHIJA, maganarki ke kaini wani tunani daban, kamar wace ta fara soyaya?" BAHIJA ta yi murmushi har idannuwanta suka cika da kwallah ta gyada kanta a hankali ta ce" Mamah, soyaya kam na shigeta mai karfin gaske Mamah" Da sauri uwar ta mike tsaye tana sake fuskantarta Ajiyar zuciya ta sauke mai zafi da kunna tana kallonta Sai kuma ta dawo ta zauna bakin bed tana dauko yannayi na serius ta ce" Ki saurareni da kyau BAHIJA, kina jinna, ko me kika dauko daga tafiyarki li ajiye shi ki zubar ki fuskanceni da kyau, wannan magana da kika dauko sam ba zata yiwu ba, domin mahaifinki ya bada ke wa UMUGHLUK ITIFAL!, A gobe gobe zamu je maganar nan in sha Allah, idanma me kika dauko ki barshi domin lin san ba maganar wasa ko ta kawo wasa a ciki!" Wata irin zubowa kasa ta yi har tawul dinta na kwoncewa daga kirjinta yana neman faduwa Bata damu da riko shi ba, sai idannuwanta da ta fitar waje gaba daya , Da wata irin muryar kuka tana kallon mahaifiyarta ta ce" Mama? Ni? Wa zakin sarakai?, Mama ni? Mama yaya ina maki maganar namiji, namijin da na gano da idannuwana, wanda na kasa zuwa masalaci dan kar ya bace min, ke kuma kina min maganar wani wai shi zakin sarakai? Mutumen da babu wanda zai ce ga kamaninsa? Aba kulun yana kwatanta kamaninsa dan shi kadai ke ganninsa ba rawani, ko ke kin taba ganninsa ba rawani? Ta yiwu wani nakasashe yake, ko wani mai cutar hauka ne irin na kanwarsa? Wai mema ya kawo maganata ni da wani ZAKIN SARAKAI? Mama, ki cireni a ciki, bana gaba bana baya Mama, dan girman Allah ki ga abana ki sanar masa walahi walahi idan ya saki ya aurani wa ZAKIN SARAKAI komai na iya faruwa, ciki harda mutuwata, uwa uba harda tonuwar asirin mutuwar GWAG.................." HADIYE maganarta ta yi, sakamakon gigitacen bakon abin da ya ziyarci fuskarta, wanda bata taba ganni ko hasashensa ba, HANNU ne mai zafi fa kunna ya sauka a fuskar da hannu bai taba hawanta ba dai dan ya shafata ko ya yi mata kissssssss, A haukace uwar ta mike tsaye, jikinta na rawa tana kallon mai aikin nan A haukace Yar ta budi baki zata sake kurma wani ihun ya dake saka bayan hannu ya kai mata ............ Asalamu alaikum wa rahamatullah *NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS ```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, al alaminmu ancinmu.``` *https://www.facebook.com/106494781436168/* *OUMOUGHLOUK ITIBEL* _(ZAKIN SARAKAI)_ _FREE BOOK_ *Na* *SAJIDA NIGER*
Chapter 14 · 0% Book details