Sashe 79
Zakin Sarakai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
filon kawai, sam bata da tsari kwata kwata fa sai kyan jaraba! "NADIRAH" ya fada a sanyaye yana so ta yi masa bayani, duda irin faduwar masa da gaba da bayanin nata ke yi na yanzu, dan sam baya so wani abu mai zafi ya fito daga bakinta a kan HUZNAH, anya zai jure na HUZNHA kuwa? Huznah matar rufin asirinsa ce, ya kirta nata ba dadi ta dawo ta likun masa, a ransa yake ji Huznah matar da zata tarbi mashin da aka harbo masa ce ba ta labe a bayansa ba, idan kuwa ya ga akasin haka an shige shi sosai Walahi Ita kuma da ta dago ta zubawa jajayen lebensa ido sai ta ji a nan fa gaskiya kamar sarki bai yi adalci ba, yo ta yaya zai ringa saka H a karshen sunnan HUZNAH yana wani karasa fada a sanyaye ita kuma ya wani ce NADIRA gatsau ba sakayawa? Oh wato shine namiji mai nuna ya fi son daya fite da daya ko? Irin wa'inda basa tsoron tashi da shanyayen jiki ko yayane? Gannin ta kure shin nan ya daka shi lumshe idannuwansa yana ayana' shikenan, kasheni zasu yi, zuciyata ba zata jure ba' Baki ta murguda tana sake rufe jikinta ta ce" Wannan kayanka ce, da ita ko ba ita duka lamarinka ne, ni ban sani ba gaskiya, na UMMARma ni ba komai na sani ba, kamar dai inaga harda kwartanci tana yi!" Tana gama fada ta mike tana jan bargon hadi da neme nemen atamparta a ranta sai mitar abinda bata san dalilinsa take yi ba........................................... *NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS ```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, al alaminmu ancinmu.``` *https://www.facebook.com/106494781436168/* *OUMOUGHLOUK ITIBEL* _(ZAKIN SARAKAI)_ _FREE BOOK_ *Na* *SAJIDA NIGER* 5 "Wani irin kwartanci kuma?" Ya fada yana juyo da ita bayan ya mike Lululu din da take ji ya sakata dan jinginuwa da jikinsa, muryarta cen ciki ta ce" Juwa nake ji ASADEEK, ina so na je kusa da Innata kafin hukuncinka ya same mu " Shiru ne ya wanzu a wajen na dan lokaci, a hankali ya dora hancinsa a saman kanta yana sinsina , muryarsa cen ciki ya ce" Me yake hadasa maki juwa ne? Ko baki da lafiya ne?" A hankali ta dora kanta a saman kirjin nasa tana sake lunshe idannuwanta, kanshin jikinsa daban ne, kanshin jikinsa mai dadin gaske ne, bata taba jin kanshi mai sakata jin nutsuwa irin haka ba, a hankali ta ringa dan matse kaffafuwanta, domin irin abinda zuciyarta ta raya mata daga jin kanshinsa sai da ta ji a ranta kamar ta zama yar iska fa? Muryarta a raunane ta ce" Walahi ban sani ba, ni dai dazu da na tsorata ne na jita sosai, dama ina jinta yan kwanakin nan ama ba wani sosai ba , inaga idan raina ya bace ne nake jinta" Hannunsa dayan ya saka ya rungumeta sosai a kirjinsa, ya karasa saman kujera da ita ya zauna tana saman kirjinsa Idannuwansa ya lumshe tana kwonce a kirjin nasa, bai san dalilin da ya sa yake ji a ransa a kanta yana iya jure komai, har ji yake yi koda da amincewarta ta amshi magani dan t kashe shi zai iya yafe mata, kome yasa? muryrsa a sanyaye sosai ya ce" Kin san UMMA, tamkar mamanmu muka dauketa, bama kamar Auta, idan ani abu ya fito Auta zata fi kowa shiga a halin tashin hankali ko?" Kanta ta dago tana kallon lebensa, tun dazu ranta raya mata yake yi ta kama ta yi ta tsotsa , bata san dalili ba, ita dai ba yar iska ba ama kuma abu irin wannan na mata yawo a tunaninta na kimtsatsiya? Kan nata ta maida da sauri dan kar ta aikatan, a hankali ta ce" Aa, Auta ta fi kowa shiga halin matsi sanadiyar matar da kake kira UMMA, mai sunnan maman Aba ta fi kowa shiga tsanani a tare da ita, sai ko matarka, kaima ka shiga ama ba a jikinka bane ai..............................." "Kina nufin, kin san da abinda ke jikin HUZNAH?, Kina nufin shima aikin Umma ne? Kina nufin itace ta saka bana iya shigar matata?" Matsar da ya yiwa hannayenta, da furucinsa suka karra zaffafa zuciyarta Tana kallon idannuwansa ta ce" Cikani " Sai a lokacin ya kula ya mata matsa mai dan karfin da take iya yi mata rauni A hankali ya sasauta mata , ita kuma ta mike ta karasa ta dauki kayanta ta kabe ta saka abinta ama ta dunkule pant dinta ta dauki dan kwalinta ta kabe ta daura sannan ta juyo ta ce" Babu iyayena a ciki, ko me zai tardoni ya sameni ni kadai , idan da hali dan Allah ka barni na je Tanus dan neman iyayena!" Dagowa ya yi yana mai gardama da tunaninsa cewa yar gidan Hindu ta yiwu tanada aljannu , a saukake ya ce" Babu inda zaki tafi!" Ja ta yi ta tsaya tana rike kugunta ta ce" Kana ji fa aka ce ba'a san inda inna take da aban birni ba?" Baki ya tabe yana sake kallonta ya ce" Eh , kuma nace ki je ki yi zamanki a dakinki, saura idan an jima kar ki dawo turaka ni sai in zo tunda na matsu" Wani haushi ya karra rike mata wuya, haka fa, tunda ita shine aikinta ai dole ya ce haka, ba zata zo din ba a yi gunduwa gunduwa da ita! Sai da ta karasa kusan katon hotonsu shi da HUZNAH ta zubawa hoton ido, haka kawai ta ji hoton ya mata mugun muni a idannuwanta, dan haka sai ta janyo kujera ta taka tsaf ta sauko shi kasa ta kifa shi sannan ta zagaye shi tana zabgawa hoton harara ta fice Idannuwansa a ware yana kallonta har ta fice ta bar wajen ranta a bayane da bacin rai, a fili ya samu kansa da sakin murmushi ya mike ya karasa yana lekenta harta sauka ta nufi corridor din , hakan ya saka shi sakin wani murmushin ya girgiza kansa ya juya ya nufi wajen wayar tafida gidanka ya shiga neman bangaren UMMA A kalla ya yi kira ya kai sau biyar sannan aka daga , aka kuma yi shiru Shima shirun ya yi har sai da ya ji muryar Umma kasa kasa tana tambayar waye? Hakan ya saka shi a kausashe ya ce" Bata wayar" Jiki na bari wace ta daga wayar ta mikawa UMMA wace ta ji kamar zata summa daga tsayen da take Muryarsa ya sakawa alamun tashin hankali ya ce" UMMA, taushe rabonki da Bafana? Ina nufin kun yi waya da su a kwanakin nan?" Cikin UMMA ya yi wani irin murdawa, zufa ta shiga karyo mata, muryarta na rawa ta ce" Wa, wa, wani abu yace na yi ne?" Lebensa ya dan dantse, sai kuma ya saki ya ce" Kamar yaya wani abu Ummana, wani abu ya faru ne ban sani ba? Yanzu Bahija ta zo tana kukan wai ba'a ga Bafa da sarauniya ba, wai an sace su, ni na rasama me zancen nan yake nufi, ama ganinan zan sauko na ji meye hakan kuma? Kafin na zo zan saka sarkin yanka ya fara yin gaba , inaga zan je tanut din yanzu yanzu in sha Allah, dan bana son karamin rikici irin na rebelle din garin nan!" Salama zata ce? Ko karin rikicewa da kidimewa? Ita dai ta ji wani abu mai sunna sasauci a kan dazu na zulumin an kaita gaba shikenan tata ta kare, a yanzu kuwa sai take tunanin tabas sunna iya gujewa hukuncinsa, hakan ya sa ta nuna rikicewarta a bayane harda su fadin bara ta shirya da ita za'a tafi, ba zata iya zama a nan ya tafi shi kadai ba, wani irin sacewa? Sarki guda? Lalle da an tsokalo tsuliyar dodo walahi! Katse kiran ya yi da wayar a hannunsa, sai kuma ya yi murmushi yana girgiza kai kasa ka sa ya ce" Ta yayama zan tashi kai tsaye na sawaka maki hukuncinki? Dole ne ki fuskanci fargaba, tashin hankali na yau daban na gibe daban, dole ki gane ba sai an kasheka kadai bane aka sakaka a uku, babu abinda ya fi tayar da hankali irin fargaba, da rashin sannin abinda ake ciki, in sha Allah zan sace sun summa a yau da taimakonki zan kawo ku na saka ku a halin rayuwa ko mutuwa!, Sai kun fadi su waye ku da bakunnanku! Da ASADEEK kuke magana!" Umma kuwa a rikice ta ringa doka wayoyin sarauniya da shi sarkin da kansa Da kyar ta samu aka daga, hankalinta a cakule take sanar masu abinda ya faru, har kiran da ASADEEK ya yi mata Bafan Tanus da ya ji hankalinsa na neman tashi da lamarin ya ce" Kina nufin, a tunaninsa mune aka sace?" Umma ta tabatar masa da eh Ya sake cewa" Yanzu nufinki zamu fita mu buya har a kashe shin ko me kike nufi?" Umma dake share zufarta ta ce" Haka nake nufi, yanzu haka da shi da ni zamu taho bincikar abinda yake faruwa, zan san yadda na yi aka bani madararsa na zuba maganin nan a ciki, gwara idan ya zama gawa mu san yadda zamu batar da dan balaki!, Bari ka ji ba zan taba yarda ya ritsa da Ni ba, muryarsa kadai abin tashin hankalina ce, bale ya kamani da mugun laifi!, Bana ciki, ina so a yau yau na kashe shi idan ya so ko me zai biyo baya ya biyo! Na rantse sai na zuba masa gubar nan a yau yau, ka shirya hawa kujerar garin AGADAZ, ka shirya yaki da du wani dan buro'uban da zai nuna bai san zancen ba, ka shirya birne gawa biyu a yau domin ina kashe shi zan kashe MARIYATU kanwarsa idan ya so sauran sai na wulakanta rayuwarsu, sai na yi fatafata da rayuwarsu kafin na halaka su, yadda ta sauke tafin hannunta a fuskata sai ta ci kashina da bakinta!, Maza ka shirya ka fita da banzar nan, saura ku yi yadda za'a gane, kubar abin a matsayin saceku aka yi, kowa da kowa ya gane haka kafin mu iso!" ...........Baki dadara fa buga wasan ba kennan?..........uhum wanda baya jin bari sai ya ga uwar bari ........ READERS MUN KUSA