Sashe 59
Zakin Sarakai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
kuma a hannunka ne in sha Allah " yana kaiwa karshe ya mike ya nufi sama dan gaba daya a yanzu sai ya ji yana son tsayuwa a gaban gadon da ya turmusana daren jiya Da kallo SHEIK ya rakashi sannan ya maido dubansa saman cafet yana tunanin me ya dace ya yi, idan ya tuna ba ita bace ainahin Bahija yakan ji tsoro a kasan zuciyarsa, ama yana fadawa Allah ya haska masu lamarin sannan ya kare su da boyayen rikicin dake iya jigata UMUGHLUK ITIBEL Har zai fita ya dawo a hankali ya zubawa gorar nan ido , a nutse ya duka ya dauka ya sake zuba mata ido, sai kawai ya mike ya yi gaba da ita yana dan jujuyata a hannunsa Ficewa ya yi ya nufi gidansa dan Matarsa ta fita, ta je maza maza ta hado abinda ya dace, yana tafe yana ta tsara dukkan abinda ya dace din Daga cen masalaci ya koma ya ja sallar Magariba sannan suka shiga karatu har isha'i ta yi suka gabatar sannan ya koma ya daukota da kansa ya kuma shige falo yana bada umarnin kar wace ta shigo yau UMUGHLUK ITIBEL zai kwonta barci da wuri _________________________________ A falo take a zaune, dadadan turaran wutar da ya gama dakin yana ta fitar da kanshi, gefenta kuwa danyar madarar shanu ce dauke da maganin zahi in ji innarta, ama ta ki sha tana dai kallon TV bakinta a cune tamkar za'a saka masa ribom , ga dukkan alamu a sama take, rigima take ji,jifa jifa kuma sai ta makawa madarar harara ta dauke kai Hindu na murmushi ta karaso hannunta dauke da abin shayi ta ce" Aa, yaya baki sha madarar ba indina?" Madarar ta sake kallo, haka kawai wannan maganin zahi da innarta ke bata ya fara saka mata tunani kala daban a ranta, to wai zahin mema? Kai ina ba zata sha ba, ta yiwu harda gudunmuwarsa wajen neman kasarata da wancen sadaukin ya yi! Shayin ta amsa ta shiga dan kurba bata cewa innarta komai ba, dan gana daya sake nanata hirarsu take yi a cen kasan zuciyarta tana ji anya zata iya kuwa? Baban burinta ta ganta a gefen iyayenta da innarta sunna rayuwarsu a gefe hankali kwonce Innarta kuwa dan murmushi ta yi boyaye tana godiya da Allah da yarta ta sha shayin, uhum NADIRAH kennan a tunaninta a shayin ba komai, bata san shi ya fi daukan abinda zai rikitata ba,da zarar namiji ya tabata kuwa, domin kakarfan maganin tayar da sha'awa ne a cikinsa ama wanda sai an tabata dole sha'awar ko zata tashi, dan kuwa haka kawai ba zai motsata ba Kafarta take dan kadawa tana kallon allon TVn dake karra bata mamaki, TV bango guda jama'a Sukur sukur da kaya alamun ana shigowa ta doguwar biyayiyar hanyar nan ya saka su zubawa hanyar ido su dukansu Bayanuwar matar SHEIK dauke da akwati mai dan girda da kuma karama ya saka Inna mikewa tana yi mata barka da zuwa ta tayata janyo akwatunnan har suka karaso falon suka ajiye sannan matar SHEIK ta duka har kasa cike da girmamawa tana tasbihi ga ubangijin da ya halici wannan halita, watau NADIRAH zaune take da yar riga marar nauyi ta kuma daure gashinta a tsakiyar kanta A tausashe ta furta" Barka da hutawa Gimbiya, Barka da wannan lokaci, Yaya karfin jiki? Ina fata da sauki?" Innarta ta saki murmushi da kafarta ta zunguri NADIRAH dake daf da kafar tata tana fadin" Amsata mana" NADIRAH ta girgiza kanta tana sada kanta kasa dan bata san amsar da zata ba mace mai daraja irin wannan da ta duka tana gaisheta ba Inna ta ce" Tashi mana hajia ki hau sama mana wanna fa kamar ta hadiyi kwado yau, maganar sam bata fitowa daga bakin" Da sauri Matar SHEIK ta girgiza kanta tana fadin" Aa, aa hajia, ba zan iya hawa sama ba, ai idan tana kasa babu wani dake iya hawa sama sai UMUGHLUK ITIBEL " Inna ta dan zarro ido ta ce" To fah Au au au haka abin yake? To bara na diro nima, ke dan kauce kadan na zauna....." Ta sauko din tana dungure kafadar NADIRAH dake sake zumburl bakinta a ranta tana ayana yanzu Innata du wajen nan bai isheki zama ba sai a nan Murmushi Matar SHEIK ta yi, gaba daya yannayinsu sai yake birgeta, har jin abin take a cen ranta A nutse ta gabatar masu da sha tara ta arziki, watau galeliyar alkyaba irin ta manyan matan sarakai da suka amshi sunnansu, sai sarkoki uku na zinari manya da awarwaraye, sai takardun tagwayen gida fa kys din motocin dake cikinsu su biyu A nutse ta furta magana kamar haka" Sako ne daga UMUGHLUK ITIBEL, an ce na gano yaya saukin jiki, sannan na sanar idan ba damuwa gimbiya ta je bangarensa Ido NADIRAH ta zarro ta maida dubanta kan innarta wace karara farin cikin kayan nan suka bayana a fuskarta har kamar ta bushe da daria take yi Baki ta turo ta mika hannu ta dauko dan tuntum din kujerun mai kyau ta yar ta kwonta tana juya masu baya ba tare da tace uffan ba a ranta ta sake ayana' Sai ku daukeni ku kaini na gani' Da mamaki su dukansu suke kallonta Innarta ta sauke ajiyar zuciya tana duban Matar SHEIK ta ce " *NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS ```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, al alaminmu ancinmu.``` *https://www.facebook.com/106494781436168/* *OUMOUGHLOUK ITIBEL* _(ZAKIN SARAKAI)_ _FREE BOOK_ *Na* *SAJIDA NIGER* 4 Tana sakin murmushi ta ce" Ki yi hakuri dan Allah, yarinta ce" Ajiyar zuciya ta sauke tana sake duban NADIRAH Muryarta ce ta nuna alamun abinda take son fadi daga zuciyarta zai fito A sanyaye ta ce" Dan Allah, ki yi hakuri idan har abinda zan fada zai bata maki, sannan ban sani ba ko hakan ba daidai bane?, Abinda na sani shine dubanmu hakan shine a zuciyarmu, kuma a bakinmuma haka ne" Dakatawa ta yi da maganar tana sake dubansu, gannin Inna ta fuskanceta sosai tana kallonta, ita kuwa NADIRAH ta yi dan tsai alamun tana sauraronta ta ce" Shi din uba ne a garemu, ya kasance mai kwana da damuwarmu a zuciyarsa da kuma aikinsa........, Bari ki ji, walahi shi din bango ne, majinginar talakawa ne,, majinginar masu da shi din ne, Abah muke kiransa, yaro da tsoho" A hankali ta fan juyo ta zuba mata ido, Muryarta ciki ciki ta furta" Yaya kuke kiransa Aba bayan bashi da shekaru sosai a kansa?" Matar SHEIK ta yi murmushi ta ce" Idan kika ga an yiwa ja gaban wata tafia sunna ko wani iri ne, ki dauka cencenta ta saka ya samu sunnan, kuma sunna ne da zai iya fitowa daga bakin talakawa, watau ba daga bakin masu yi masa fadanci ba, shekarunsa basu kai wajen da SHEIK zai duka ya kireshi ABAH ba, ama ko kwanan gobe Humaira Auta takan ce da Sheikh tanna so a kawota wajen Aban SHEIK, a tunaninta mahaifi ne a wajensa domin bakinsa kan girmamashi a bayan idannuwansa ta hanyar kiransa ABAN TALAKAWA, " NADIRAH ta tabe bakinta a hankali ta sake juyawa Matar SHEIK bata yi kasa da gwuiwa ba ta dora da fadin" Dalilin da ya sakani dauko maganar nan, dan na roki alfarmaa ne, dan Allah ki kasance cikon farin cikinsa ko yayane, ki yi hakuri idan har na bata maki " Shiru ne ta sake yi masu, hakan ya saka Innarta budar bakinta da ya yi mata nauyi kadan a hankali ta ce" In sha Allah, ita fin zata zamto daya daga cikin abinda zai kwontar masa da hankali, baki bats mats rai ba, asalima na ji dadin hakan, Allah ya biya, shi kuma Allah ya dafa masa" Da amen amen Matar SHEIK ta amsa sannan ta mike dan tafia Har kan kofar Inna ta rakata tans faman godiya Aa hankali tas dawo ta zauna tana duban kayan, gaba daya ta rasa me zata ce, kayan nan ya zamaa wajibi ta fitar da su cikin sirri tun kafin Umma ta san da zamansu bale har taa nemi sannin dalilin da ya sa aka bata su, gefe daya kuma yannayin y'arta na damunta matuka Muryarta a raunane ta ce" Ama, ina cewa dazu muka gama maganar cewaa kin amince, zaki karra yin hakuri kadan har mu gaa karshen abin nan ko?, Ki duba ki ga tarin dukiyar nan, shin bai cencenci ki yi masa godiya da namijin kokarinsa ba?" Muryarta a mugun raunane ta juyo ta ce " Innata, Innata na yarda fa, nace na amince zan ci gaba da kwatanta bin hanyar da zai fahimci abinda ya kawoni fadar nan, na ce na yarda a gobema zan je na yi zaman da suka saba, ama Innata............" A hankali ta lumshe idannuwanta tana nuna kayan muryarta na mugun rawa ta ce" Innata ama bana tare da irin wannan abubuwan, kayan nan bana so, ban zo dan su ba, asalima ya shiga hurumin da ba nashi bane, a kan me zai lalata min tsarin rayuwata???????" "Bakida hurumin da ya fi shi!, NADIRAH bakida tsarin rayuwar da ta fi tasa, " Innarta ta fada tana tsareta da kakausan kallo Numfashi taa fitar mai zafi, sannan ta ciciba a hankali ta mije tsaye tana jin sosai jikin nata da karfi yanzun Muryarta a rine ta ce " yanada masu sonsa, yanada mai matukar kishinsa, ta isheshi rayuwa, su suka saba da rayuwar nan, ni kam ina jina tamkar a kurkuku, wannan daula bana jinta na fi jina a kule a waje guda, ni ba matar gidan sarauta bace, inada nawa zabin nima, idan har na dube shi....dan kun isa da ni ne!" Tana kauwa karshe ta yi gaba ranta na sake yi mata kunna HINDU ta rasa me zata ce, walahi idan akoy abinda ke matukar dagaa mata hankali wannan rikici da take hangowa a tatare da y'arta Kayan nan ta mayar ta shiga shigar da su dakinta tana tura su karkashin gado kafin ta dawo ta kule ko'ina ta koma dakin NADIRAH, ama sai ta tarar ta yi barci, dan haka ta koma nata dakin ta daura alwallah ta haye saman salaya dan kaima mai duka kukanta, ta san karfinta ko dabararta basu