Sashe 51
Zakin Sarakai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
da za'a yi a makabartar, wasu kaburan sun bude kadan haka, wasu kasar ta baje dai da sauransu,nan ya bada umarnin a saka sanarwar ranar lahadi ana gayata dan a zo a yi gyaran gidan kowa, gidan gaskiya, du wanda yake da lokaci da talafin da ya samu ko menene ana maraba da shi, a saka a redio da TV, a haka har suka gama suka sake fitowa, abokan tafiyar tasa sai da suka masu rakiya har masarautar sannan suka tafi Ya kasance saura su biyu ne a saman dokin sunna tafe cikin nutsuwa ASADEEK ya sake tsayar da dokinsa ya kalli SHEIK ya ce" da ace zubewar nema ta yi da na san haka Allah ya hukunta ba rabona bace" SHEIK ya dube shi, a tausashe ya ce" Me ya samu madarar?" ASADEEK ya rintse ido, sai kuma ya bude ya dan kalli katon filin, da irin yadda wajen ya dauke sawaye tunda suka shigo, wa'inda ke tsaye du sun duka kawunnansu a kasa irin sunna masa gaisuwa da girmamawa ne A dan kufule ya ce" Yarinyar nan ta dauke, ta sha, ita da Auta" Da mamaki Sheikh ya ce" Yarinya?, Wace yarinya? Ko Hajia HUZNAH?" Baki ya tabe ya ce" HUZNAH ai nutsatsiya ce, baiwar Allah ce, wannan bakuwar dai mai kama da aljannu, itace ta dauka ko kadan bata rage min ba" Sosai SHEIK ya ji wani irin mamaki, hadi da dariya, bai san me yasa ba, abin ya dace ya bashi tsoro ko haushi? Aa shi dai dariya abin ya bashi, fuskarsa cike da yalwatacen farin ciki ya ce" Kwarai zan so na gaisheta Allah ya karra maka lafiya" Ido ya tsurawa SHEIK, sai kuma ya ce" Bata da hankali fa, wace gaisuwa zaka yi mata?, Da ta zo ce mana ta yi sasannunku fa, na yi lati ne dan na mance dan kwalina, latin awa daya ta yi ta zo mana ta dibe albarkar alkyabarta ta kallemu tsai tace sasanunmu fa akaramakalahu" A yanzu kam a dole ta fito dariyarsa, ya kai hannunsa yana tare bakinsa hadi da zarro ido , sai kuma ya sake waiwaigawa ya rage murya ainun ya ce" Kana tune a kulun idan Saraki na maka kirari , idan yace kai Zaki kake a dawa, a gidama zaki kake, sai nace uhum ko?, To yau ga amsarka, ina tsoron kaima ka shigo sahun maza masu sunnan maza masu iyali, a yanzu kake kokarin zama nama kiri kiri a gida, Allah ya karra maka lafiya" Gannin SHEIK ya mayar da abin na tsokana sai ya kada kai kawai ya ja Dokinsa ya nufi har kofar Fada ya sauko bayan Dogarai sun ririke dokin ana ta yi masa kirarin da aka saba Dubansa ya sake kaiwa kan SHEIK ya ce" Saraki bai yi karya ba, Me za'a nunawa HUZNAH ne?, Ni dama lalausar mace itace abin birgewata,..... SHEIK ka ji da kyau zaki nake har a kuryar daki" Dariya SHEIK ya saka sannan ta bi bayanshi suka shige domin ba zai tashi daga zaman fada ba yau sai azahar Shara'a ya gabatar ta wani mai gari, mutumen matansa hudu, yayansa arba'in da daya, matar tasa ta hudun ce da ya auro yarinya karama, domin sa'ar jikarsa ta goma sha hudu ce, ga yarinta, ga karamin jiki, abin dai ba'a cewa komai, ta samu kanta a cikin kishiyoyin da ba ruwansu da cewa yarinya take, aa kishiya ce sak, mutumen malami ne, ko nace malamin tsubu, a haka ya aure yar yarinyar iyayenta na zuwa amsar mata maganin iskokai dake damunta, aka wayi gari ta haukace shi take so Yar yarinya karama ta ringa tarda shi karshe dai mahaifinta ya daura masa fan gudun wata fitina ta bilo To fa tunda aka tare ne yarinya ta ringa tambayar me ta yi aka aura mata wannan mutumen? Shi kuwa ya yi iya yinsa ya karra daure mata baki, haka kuma tunda ta shigo a matsayin sabon abinci ya daina ziyartar kowace sai ita, karamin jiki yarinta ga abu ya girmameta sai rashin lafiya kala kala, tun ana daukan abin laulayi ne har aka gane cewa lafiya ce bata da ita kawai , kamar ana tsakurarta, fatarta ta dafe, komai dai sai handallah, tun mahaifinta na neman alfarmar a bashi ita ta kwana biyu a gida ta farfado sai a dawo da ita har abin ya fara tsoratar da shi, shi kam ita daya Allah ya bashi dan haka ya je ga yan sandan yankin ya sanar masu, ama babu yadda zasu yi da kai gari, domin da suka zo aka toshe masu baki, hakan ya saka shi neman hanyar da zai ga UMUGHLUK ITIBEL domin shine sarkin baban garin, domin kauyen na Agadaz ne Ya sha wahala ainun, domin sai da ya ringa haduwa da yan kasan shugaba masu lalata mulkin shugaba, wasu har kudi sun amsa a wajensa da nufin zasu masa hanya, abin dai ya gagara, a kadan ya dauki wata guda, gannin lamarin ya kasa samuwa ya je sallar juma'a a baban masalaci juma'ar da ta wuce Shi ya taya masu gyaran masalacin gyara da komai, yana nan masalacin ya cika har SHEIK ya karaso aka yi sallah aka gama Ana gamawa ya karasa ya bashi hannu ya fashe da kuka, domin lamarin na neman sakashi a halin ha'ula'i, matarsa kanta tana kwonce ba lafiyar sanadiyar wannan matsala, Allah ya taimakeshi ya fada kan SHEIK din, shine ya amshi numbarsa suka sake zaunawa ya sanar komai da komai Kwarai SHEIK ya ji haushin haka, har ya masa alkawarin sanar da ASADEEK, domin abu ne da ya shafi mai gari, ba su zasu yi shara'ar ba dole sai ASADEEK, Ya kuwa taki sa'a, da ya sanar masa menene sana'ar mai garin abin ya karra harzuka shi, Wannan zaman ne aka yi a yau, wanda ya kawo rikici sosai, rikici mai wiyar fade, ga dai yarinya a zaune ta fadi abinda take ciki ta kasa, haka kuma kishiyoyinta sun goyi bayan mijinsu sun fadi cewa tunda ta zo babu abinda akai mata , ita dai ta tsangwami kanta Abu ya so ya ja daga, domin su matayensa sunna tare da mijinsu da sarautar mijinsu, yarinya kuwa ta zama wata iri, wahala ta rikitata ta zama sai a hankali Sai da ya gama gane komai ya fara sauke masa rawanin , nan fa aka rikice, rawani a kasa sai hauka, abu ya cakule da kyar aka fadi gaskiyar sihirin da yake yiwa mata kafin ya aura, mulki na cin zali, babakere da kayan marayu, abubuwa dai babu dadi, sai da ya saketa aka wuce cel da shi dan yin bincike da fita hakkin masu haki a abinda ya rage masa, gunjin ihun da yake yi kan shi mai Aljani wane da wane za'a wulakanta kittt ya hadiye shi a lokacin da Murtala ya kafta masa mari a gabar haba da wuya har ya ji kamar fitar hakori a bakinsa, daga nan sai zanzana da kuka suka tafi da shi Basu tashi ba sai da suka saka ranar nada wani bayan dogon bincike, kafin nan aka wakilci limamin garin ya zama mai garin rikon kwarya bayan an samu shedar arziki a kansa A gajiye ainun ya koma bangarensa Ya samu ko'ina a kalkalce, a gyare yana fitar da kanshi Wanka ya yi ya sake shiryawa ya fice masallaci Bayan an gama sallah ya dawo ya koma dakinsa ya kwonta ba tare da ya nemi abinci ba, domin barci ke dan damunsa, dama ya raba dare yana aiki daga bisani ya yi nafila, kuma suka fita da sanyin safiya Lokacin sallar la'asar na gabatowa ya farka daga barcinsa ya sake shigewa bayi ya yi wanka ya kimtsa ya fice masalaci Yana dawowa ya zauna a falonsa na kasa yana duba wayoyinsa Tarin kiran da ya samu daga Bahija ya saka shi gyara zamansa ya yi kiranta Ba jan ajin nan ma, ba komai wayar na fara ringin ta daga tana mai sakar masa sansanyan kuka A yau kam ta kasa rike kanta cikin kukan ta ce" Haba bawan , Allah, me yasa zaka ringa wulakantani bayan ban cencenci wulakanci ba?" Zamansa ya gyara yana dan tausasa muryarsa dan son fara bin matakin da ya tsarawa kansa ya ce" Subahanalah, ki yi hakuri , bana wulakanci fa, Aure na yi kwanakin nan shi yasa bakya jina" Daga tsayen da take, sai da ta yanke jiki ta fadi, kukanta kuwa ya dauke cak ta yi wani irin zurru tamkar ta ga mutuwarta a gabanta A tausashe ya ce" Kina jina kuwa?" BAHIJA, bata taba sannin akoy wahalar da zata hannata kuka ba irin yau, wahalar da ta girmami kuka? Sam bata san akoyta a cikin duniya ba sai yau Muryata na rawa ta ce" Aure? Yanzu dan Allah aure ka tafi ka yi ni ina nan ina hauka? Wata ka je ka aura ni ina nan ?" Da yannayin mamakin furucinta ya ce" Ki yi hakuri, ban gane furucinki ba?, Kin san dama inada mata, sai na karra ta biyu ne" Ai kuwa, katon mikin da ya caki zuciyarta ita kadai ta san da zata ga matan nan nasa a yanzu ta yiwu da hannunta zata zama ajalinsu Da kyar take shalar iska ta bakinta tans dane kirjinta dan kar ya fashe mata Muryarta a cakule ta ce" Kana nufin, ka ce min, baka san ina sonka ba?, Ka san da har auren wani na kiya dan ina jiran na ji dagaa gareka?, Ni ina sonka, kuma ka san in ba so ba, ba zan zauna gadinka ba ko?" Shiru ya yi, har sai da ta dago wayar a tsorace tana kallo dan tsoron kar aje ko ya kashe din da ya saba ne? Gannin da haske ta sauke ajiyar zuciya ta sake karawa a kunnenta tana fadin" Hello? Dan Allah ka amsa ni" "Kina so na?, Kika kasa fada min?, Ai ba laifi bane fadin abinda yake zuciya, bale ina girmama soyaya ni" ya fada a sanyaye, yana sake sauraronta Sosai Bahija ta ji wani sanyi sanyi na ratsa mata zuciyarta A hankali ta ce" Na so na kwatanta, tsoro ya hanna ni, kanada mugun kwarjinin da na jima ban hangi dan Adam da shi ba, da na san zaka dubeni da na kwatanta" Bakinsa ya dan tabe,