Sashe 3
Zakin Sarakai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
duniya baki daya, yawancin filanin garin nan da aka ribanta a jeji suke zaune, sannin adinin musuluncin sama sama ne, bautar a hasashe ne, ana rayuwa ne da dabobi ana kiwatawa , wasu dabobin ma basu da su sunna rayuwa a wahalce...., Da bare gurbi suka shigo cikinmu sai suka shigo da dabara da wayo irin nasu....., Wani mutumen kauyen saboda magi sai ya rakaka wajen bautarka, wajen bautar da za'a tarar da kade kade dai da sauransu ..... wa'inda mun sani babu abinda yake da saurin yin tasiri a wajen dan Adam irinsu, domin shedan na ciki tsamo tsamo, bale kudade da cima mai kyau, asibitoci da ja a jiki, uwa uba da nunawa nasu abin bautar shi ne na alkhairi shi ne ya dace a bautawa, shi ne mai jin kai, gashi Har ya turo a talafe su? To fa da yawa a haka suka kauce hanya suka fada halaka, da yawa a haka suka kauce hanya, daidaiku ne Allah ya tseratar......." Ya ajiye yana sake kallon yannayin Saraki Ya dora da fadin" Dukan Hanyar da za'a bi dan a nuna masu wanene Ubangijinsu ba zata kai ta laluma da nasiha da wa'azi da ja a jiki ba....., Idan an kone masu a yanzu za'a kona zukatansu, idan har an kone masu a yanzu za'a tunzurasu ne, kuma ba'a isa a hanna su zuwa wani wajen su aikata wanda ya gimami wannan ba, ta yiwu masu halayar garin su bazu wani garin su ja ra'ayin masu jiran su ji amsa irin haka, Ba wai ina nuni cewa nasiha da kawo ayoyin Allah ne zai tseratar da dukannunsu ba, aa, wanin ko me ka nuna masa ya rigaya ya yi nisa...., Mu dai dama kwatantawa ne namu da yaki da abinda Allah ya halata mana mudin ranmu, idan a cikin dari ashirin suka gane mun ci riba ITIFAL..............................., Da so Samu na yi Ya ITIFAL mu bude masu magangannun da suka zo a cikin Alkur'ani, domin kuwa a cikin kaso d'aya na ukun Al ur'ani ana magana ne akan tauhidi ma'ana ka aita Allah, sannan ayoyi bila'adadi Allah ya yi magana akan shirka, idan muka duba Suratul Lukman aya ta 12 inda mahaifi yake wa dansa wasiyya cewa " "Mahallin sha'ir anan ranka shi da e shine shirka, munin shirkar yasa uban ya fara nusar da danshi da lamarinta har ya kirata da zalinci ne mai girma." Suratul Muhammad aya ta 32 tana tunasar damu cewa "Ya ku wad'anda sukayi imani ku yi da'a ga kuyi da'a ga manzonsa, sannan kada ku b'ata ayyukanku. A rayuwar dan adam babu abinda yake saurin ruguza aikinshi kamar shirka, zaka shekara dubu kana aikin lada, amma sakan d'aya ya wadatar ya bata duka wannan ayyukan indai shirka ce ka yi." Kara sadda kanshi yayi ya d'ora da" Akwai bukatar mu fara sanar dasu me ye shirka da illarta, dan daga cikinsu akwai wadda basu san muninta ba, kuma magana ce daga bakin fiyayyen halitta a hadisin Abu Huraira ruwayar Bukhari da Muslim cewa " *Lallai Allah yana kishi, sai dai kishin Allah shine ya ga bawansa na aikata abinda ya haramta masa*, a wani hadisin kuma yana magana ce cewa *Allah na matukar kishin ganin bawansa ya had'a shi da waninsa.*, ranka shi dade, shirkar nan tsabar muninta mai aikata ta ma Allah alkawarin wuta ya masa, kamar a Suratul Fathi aya ta 5 da ya ce *Zai azabtar da munafiki da munafika, na biyu sai ya ce da mushriki da mushrika, bayan shirka ne sannan aka kawo zina sannan Allah ya ce yana hushi kuma ya tsine musu albarka tare da alkwarin wutar masira.* , a suratul bayinat aya ta 5 ma Allah yace *Lallai wadannan kafiran daga ahlil kitabi da kuma mushrikai suna cikin wutar jahanna zasu dawwama a cikinta...*, sarkina, a ganina in dai girman matsalar ya kai haka, to dole sai da laluma za mu bisu da dabara har mu samu cimma nasara, dan bai kamata mu bari lamarin ya kai kamar yadda muka shina *a suratul Suratu Baqara aya ta 101 wanda suka tabbatar mana da lallai mai hada bautar Allah da wani to tabbas kafiri ne*." Sosai ya sake zuba masu ido, a hankali ya sauke ajiyar zuciya bai ce komai ba ya shige bayan motar ya zauna yana gyara zamansa irin zaman daram din nan ya sake waigowa ya zubawa jama'ar ido har suka tatara da jama'arsa suka fice gaba dayansu dafifin yara da manya na daga masu hannu ana masu byby da rakiyar motocinsu da dawakansu A hankali a hankali masarautar ta ringa hautsinewa, labarin barinsa garin ya idasa rikita garin Dogon dutsi, bama kamar dangin matar sarki da ita din kanta A rikice ta karasa dakinta ta dauki wayarta ta shiga kiran number auntynta, watau mata a wajen sarkin garin TANUT Hajia na dagawa ta shiga labarta mata abinda yake faruwa tana sheka kuka Itama hankalinta ya yi kololuwar tashi, domin a yaune ta ji ainahin maganar ta gaskiya, a da an sanar mata cewa matar ce ta tardo shi da lalata garin ya guje mata tsautsayi ya sauka a kanta har ta rasa numfashinta Rai bace, hankali tashe ta ce" Dama kin san abinda ya faru kennan kika yi sanyar da har UMUGHLUK ya san labarin? Yaya kika yarda uwar yarinyar ta fito ta zaga gari har ta fito magana ta fito duniya ya ji? Ke kin san baya tare da zalunci kuma ja tsoron uban wani yake yi ba, kina tunanin shi kawun nasa ya isa ya tankwasashi ne a kan gaskiyarsa? Bari ki ji, muma a nan a cikin tamu muke, domin magana ce boyayiya ke son fitowa saman ruwa amkar an zuba mai saman ruwa, maganar dake sirrin dakansa ce ke son fitowa fili, wace in tsoron da abinda Sarkin garina zai fanshi zaman lafiyarsa!, Ba zan ce maki babu maganar gannin Uban yara ba, ama ban maki alkawarin komai a kai ba, kar ki manta har yanzu Mahfuz bai gama kason da aka dibar masa ba, da ya isa da wani abin da ya hanna hakan!, Ki san hanyar da zaki fitar da danki idan ba zaki iya jure a kashe maki shi ba, ko ki san hanyar da zaki maye gawarsa da ta wani! Wannan shine shawarata a gareki , nima ta kaina nake!" Murya a raunane ta ce" Yanzu kina tunanin idan na masa hanya ya gudu ba zai gano nice na aikata haka ba? Idan ya gano kin san halinsa fa komai yana iya yanke min ba kunyar wani zai ji ba" Lebenta ta dantse da karfi tana jin ciwon lamarin yaron Tunani ta yi mai dan tsayi kadan , sannan ta ce" Zamu fara karkatawa wajen neman sulhu kan kar a kashe shi a barshi a suluru har wa'adinsa ya cika......, Ki sani mulkin UMUGHLUK ITIFAL takaitace ne! Idan lokacin hakan ya kai sai mu ci karanmu babu babaka!" Dakatar da shashekar kukanta ta yi a hankali ta ce" Kamar yaya takaitace ne?" Idannuwa Gimbiyar Tanut ta dago da dan sauri, sai kuma ta batar da maganar ta hanyar mikewa tana fadin" Ki share hawayenki zan kirayeki, ki fara neman mafita, nima zan buga ta nan, ga Bahija cen bata da lafiya ne zan tabo ki" Tsai ta yi da wayar a hannunta ta zubawa waje daya ido, ta tabata abinda ya kai bakin Gimbiya da yin wannan furuci abu ne ginane mai tushe, ta tabata Gimbiya ba zata yarda bakinta ya furta furucin da yake na karya ba, abinda ta fi ja ta tsaya a lamarin daya ne tak..... Shin menene boyeyen digadigin abinda aka boye a lamarin Zakin sarakai?, Basaraken da ya gaji sarauta ne aka yiwa furucin takaitaciyar sarauta ke gabansa yaro mai jinni a jika?, Shin tanada labarin wani abu zai sameshi ta sanadin mijinta ko kuma wata boyayiya take kasa a kan usulinsa? .....wannan furuci ya sakata manta abinda ya dace ace ta mike ta kamanta a matsayinta na uwa, watau taya yaronta rokon gafarar ubangijinsa da fatan hakan shine alkhairi a gareshi Sai ta bige da dogaro da maganar cewa yaronta zai fito ya rayu cikin isa da iza ya ci gaba da wulakantar da an mutane dan yanada DAMA!, Karshema zaman jiran kiran Hajiarta ta yi dan ta bata dama ta gama da sangartaciyar y'arta mai raini da raina na gaba da ita! __________________________________ A TANUT Da dan sauri Gimbiya ta karasa Tankamemen falon y'arta tana fadin" Fadime? Fadime? Shin bata yarda ta sha maganin bane?" FADIME mace ta hannun damarta, wace ke tare da ita tun shekarun tuwo, take bauta mata da anta ta juyo tana sauke ajiyar zuciya da sake rage tsayinta ta ce" Allah ya karra maki lafiya, tace ba zata sha maganin ba, shine nake jira idan ta farka ko zata yarda ta amsa?" Takalmin dake kafarta mai laushi ta cire ta haye saman gadon tana dora kafarta daya ta tankwashe ta saka hannayenta biyu ta yaye abin rufar ta miko hannunta da tsawa tsawa ta ce" Dan Allah bani ni, tun dazu na baki wannan dan aikin ki wani zo ki sakata a gaba bayan kin san dan kankin kanta ba sha zata yi ba? Tafi dan Allah ke kam kwata kwata bakida wani anfani a rayuwa sai shirme!" Jikinta na dan rawa ta rage tsayinta sosai ta mika mata kofin dake dauke da maganin sannan ta nemi afuwarta ta juya har tamkar zata kifa dan sauri Ina jira na ga an dago wata yar yarinya a bata abin nan, sai gani na yi an talafo wata gindimemiyar budurwa ana ta faman shafa gefe da gefen fuskarta ana tambayarta idan har jikinta ne ya yi kamari a kirayi docter? Ita kuwa tana langwabewa da ture maganin wanda kana ganni zaka fahimci tsabar tabara ce irin ta wanda ya samu dama ke damun wannan baiwar Allah mai sunna BAHIJA ya a wajen sarkin garin TANUT, wato ya mace daya kwal a wajen uwar gidansa sarautar mata ........................................................... Saurin da Fadime take bata zame a ko'ina ba sai a wajen ciyayin dake cen bangaren dawakai A hankali ta ringa amsa gaisuwar da bayin dake kasanta ke yi mata cikin girmamawa a matsayinta na baiwa mafi kusanci da uwar gidan sarki kuma mata a wajen