← Book details Zakin Sarakai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 87

Sashe 41

Zakin Sarakai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

amaa haka kawai tunda akaa ce an daura aurenku nske zumudin son ganninta, ko dan zamu karru ne a cikin duniyarka? Ko dan zan kara samun wata yar uwar ne bayan HUZNAH, sam ba wai ina sonta dan na kuntatawa Huznah bane, ko daya, hasalima HUZNAH ni babu abinda ta min, yannayin mu'amalarmu ne haka, wani lokacin har hira muke yi fa, ama da wata zata karu cikinmu sai nake jin farin ciki sosai, sai maganar da aka fada , na tabata bayin masarautarmu ba dai maganar su ringa kawo karya ba, wannan Umma bata samu galaba a kansu ta wannan fannin ba, du inda maganar nan ta fitoz da tushenta, tushsen nake son gani ni kuma' Har kofar dakinta ya rakata sannan ya koma ta hanyar da suka biyo bangarensa ya ci gaba da aikinsa yana sake rubuta hukunce hukunce ne na sata, da zina, uwa uba Luwadi .......................shara'ar dake gabansa mai zafi ce, kuma mai cakulewa ce, a dole Sheikh ya kawo masa su dan shi kadai ya isa ya tsaya ido cikin ido ya zartar kuma a bi koda ba'a sallah! A ranar HINDU bata zauna da yarta ba sai washe gari, tana tsakar yi mata nasiha Kira ya shigo a wayarsu Tana gannin yayarta ce ta tashi tana murmushi ta shige ciki dan su yi sirri FADIME a sanyaye ta ce" Hindu kin kaura ba?" HINDU ta yi shiru FADIME ta ce" Ki tataro ki dawo dakinki kin ji abinda na fada maki, kina nan ko bakya nan abinda Allah ya nufa zai samu yarki sai ya sameta, kar ki yi wasa da aurenki mana" HINDU ta gyara zama ta ce" Aunty ba wasa nake yi da auren ba, dama dan Habu baya nan ne, kuma kin ga jiya dai Indi cewa ta yi a cewa UMUGHLUK sai wani jikon zata je gaishe shi" Ai kuwa rikicewar da Fadime din ta yi har ta zarce ta HINDU, haka take salalami itama ta saka aka ba NADIRAH wayar, kamar zata fito ta wayar haka take yi, fadi take tana maimaitawa cewa Babansu ne fa, a kan me zata yi aiki kamar na yar kwaya? Tsaf suka karra sileta, ita kuma ta yi shiru, dan a ranta ayanawa take yi' Ba ku gane komai bama yaya da kanwarta gaskiya, ni ba zan fara kai kaina ba fa, yo ai ba haka ake yi ba'! Haka suka wuni sunna yan abubuwansu dan debe kewa, sai dai kowace zaman dakan ya fara isarta, domin ba sabawa suka yi ba gaba dayansu A haka har kwanaki biyun suka shige, a ranar na ukun ne sabuwar maganar zuwa bangarensa ta karra tashi, wannan karron kam ta ga da gasken gaske suke, Tun karfe goma aka shiryata akace cin abincin rana a bangarensa Kwata kwata sai ta ga abin nan ba wani tsari sai shirme Bata dai ce komai ba , haka ta zuba ido tana bin motsin kowa har lokacin ya yi aka rufa mata wata mahaukaciyar alkyabar da ita da kanta sai da ta ringa shafata, domin har ga Allah ba dai laushi daa kyau ba A nutse aka bude hanyar baya domin rana ne gatse gatse da nufin bi ta bayan da ita, Sun dauko tafia su hudu Umma sai karra gyarata take yi tana sake gyara mata rufarta ta ja ta tsaya A hankali ta nemi dukewa, hakan ya saka jakadiya tareta da sauri ana faman ambaton Allah da yi mata sannu Ido rintse ta kwashi barin jikin karya kab kab kab kamar da gaske Hankalin Umma tashe take talabota tana tambayar menene? Lafiya? Ama NADIRAH ta kasa fadin komai Hankali tashe Umma ta sake dagota tana girgizata ta ambaci sunnanta tana tambayarta menene? Muryarta na rawa ta furta" Umma, bayi nake son shiga, innalilahi zai bale" Har ga Allah Umma ta yarda, haka kuma da mahaukacin gudu ta saka aka juya da NADIRAH aka nufi ciki da ita hankali tashe aka nufi dakinta da ita Inna naa tambayar lafiya? Bayin ta shige bayan ta watso alkyabar ta ja ta rufe ta haye saman abin aikin ta ringa jan ruwan tana kakari kamar wace ke aikata aikin da ba jira A waje Umma da inna ke kai kawo ana tambayarta yaya da sauki? Tana buga gyaran murya Umma ta dubi Inna hankali tashe ta ce" Sai fa mun yi da gaske, kar aje kishiyar ke son cin mata, kina ga haduwa ta gagara bayan an daura aure ba yau ba?, Kar fa aje mun raina wayonta ita tana mana kallon shashashu, kar aje wankin hula ya kaimu dare, kar aje ta san me muke shiryawa tana neman yi mana sakiyar da ba ruwa, ina zuwa zan je na sanar masu abinda yake faruwa sannan na fita da kaina na kawo jikakun karya tambaya da kaikayi koma kan mashekiya, ko me ta aikata mata sai dai ya koma kanta walahi, wannan wace irin masifa ce, ki duba ki ga kwaliyar da yarinyar nan ta sha fa? Ai karya take idan takamarta bokaye ni a hanya na kwana dan ubanta!" Inna na tsaye bayan fitar Umma ta samu kanta da zaunawa tana kallon kofar bayi, haka kawai sai take jin damuwar rashin lafiyar da kuma rashin yarda idan har Indi bata da lafiyar ne, koda yake shi gudawa ai kawai zuwa yake yi kai tsaye, bara ta samo kuka ta bata ta sha sai ya tsaya, wannan abu dai kam itama bara idan ta bata kukar ta tofeta, idan har aka yiwa UMUGHLUK ITIBEL da NADIRAH faraku ai ita ta shiga uku, ko haduwa ba zasu yi ba kennan? Firgit ta mike ta fice itama ta rufo dakin ta tafi neman kuka a wajen kicin din bayi, ta tabata ba za'a rasa ba __________________________________ Kasancewar har sha biyun ta gota ya zamto shima ya sauko dan cin abincin Shigarsa ta sababin kaya ne kamar yadda ya saba, rawaninsa wanda aka rufe fuskarsa gaba daya ne Tun daga Auta har Huznah sun sha kwaliyar da sai da suka birge shi Sai dai mamakinsa gannin bai tardo harda yar mulkin a wajen ba Sakon da Umma ke sanar masa ya saka shi dora dubansa a kan Auta, wace yana kallonta ya hangi boyayiyar dariya a fuskarta Samun kansa ya yi da mamaki mai tsanani da kuma jin haushi hadi da son gaskatawa A kausashe ya ce" Karfe takwas na dare ya mata a falon nan, koda tana tafe ana tare abinda ke damunta ne!" Daga nan ya mike ya fice, domin bama zai ci abincin ba, ikon Allah shi za'a rainawa wayo? To ita me take takama da shi da har zata aikata haka?, Idan tunani take yi akoy maganar soyaya ko makamanciyarta da zara saka ya fuskanci me take nufi ta makaro!, Ba zai dauki rainin wayo ba sam!, Zara zo zai kuma fada mata gaba da gaba! Jikin Umma ya yi sanyi ainun, ba dan komai ba sai dan sanin da ta yi dole ne Nadirah ta zo koda ana tare mata gudawar kuwa, ita da ta so ta shigo kanta a sama? Ita da ta so idan ta zo sai hankalin kowa ya tashi? Akoy matsala Daga nan bangaren Nadirar ta koma dole, a lokacin Innar Nadirah ta dawo tuni ta tarar da Nadirah kwonce a dakinta tana rera wakar dandali tan kada kai, bayin ta shiga da sauri, ai kuwa bata ji alamu ko gannin alamu na abu mai doyi ya sauka ba, a lokacin ne ta yanke hukuncin lalle sai sun fuskanci junna ita da y'arta, sun yi magana ta fahimta Abinda Nadirar ta fada cewa ai ba aji ne ya sakata rushewa da kuka sai da Nadirar ta ringa rarafe tana bata hakuri da rike kafarta sannan ta saurareta, ta gama yanka mata kashedi ta fito Umma ta dawo Fuska da alhini Umma ta sanarwa Inna umarnin UMUGHLUK ITIBEL HINDU ta ce" In sha Allah zata kasance a wajen a lokacin, kar ki damu Umma" Da wannan Umma ta fice dan zuwa ta amso su karya tambayar nan dan ba zata yarda a cinma yarinyar ba! ( Uhum, hakane, wani lokacin makashin naka ke baka kariya kuma cikin kudurar ubangiji) _____________________________________ "Sannu, kar ki fadi mana" Muryar Umma ke fada kasa kasa tana karra shakar kanshin tutaran yarinyar domin ita ke rike da ita a jikinta, sai HINDU dake gefe tana rike da alkyabarta, domin sharadin NADIRAH sai dai idan da Innarta za'a je HINDU ta karra waigawa gabas da yamma, kudu da arewa, sai ta samu kanta da share hawaye tana karra wara idannuwanta tana kallo Tafkeken hotonsa dake makale, wanda rawaninsa mai shara shara ne ana gannin yannayin fuskarsa sosai ta zunawa ido, hakan ya saka ta ci tuntune da rigar Nadirar ta je ta gwarunma Nadirar Taga taga NADIRAH ta yi a dole ta kama Alkyabarta ta rike gam hankali tashe ta ce" annabi ka san da zuwanmu zamu rufto kasa!" Inna ta tareta raf tana fadin " Sannu Indi bamu kai kasam ba" Nadirah ta ja numfashi dan har ta rufe ido, sannan ta kama Alkyabar ta cire gaba daya tana jan numfashi ta kai dubanta wajen Umma zata yi magana Umma ta tareta da gagawa ta ce" Ya salam, Bahija sannu, baki ji ciwo ba?" Tsuru NADIRAH ta mata, sai kuma ta samu kanta da juyawa wajen da a shigowarsu take hangen kamar mutane Ido ta zuba masu itama, kamar yadda suka zuba mata, A hankali taa lumshe idannuwanta tana jin kanta na sara mata sanadiyar tino abinda ke boye Daga Auta kuwa, har HUZNAH idannuwansu tamkar zasu mana mata shi a jikinta hakane Fuskarta babu kwaliya ko diz a jiki, Dinkin dake jikinta doguwar riga ce ta leshi fari fal bashida ko digon wata kalar daya a jikinsa, haka kuma dinkin ya bi jikinta ya lafe a jikinta ya amshi jikinta har kirar jikinta Gashin kanta dama ba'a daura mata dan kwalin ba, alkyabar kawai ta rufa dan ita aka bari ta shirya ita kuma ta yi yadda ta ga ya dace da ita Kunnenta dan siririn dan kunne ne, hannayenta ba komai a jikinsu, sai sarkar dake kafarta a daure wace ana ganninta a bayane Mikewa suka yi dan karamata, da kuma yi mata sannu HUZNAH, jikinta har rawa rawa
Chapter 41 · 0% Book details