← Book details Zakin Sarakai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 80 OF 87

Sashe 80

Zakin Sarakai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

GAMA SHI FA *NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS ```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, al alaminmu ancinmu.``` *https://www.facebook.com/106494781436168/* *OUMOUGHLOUK ITIBEL* _(ZAKIN SARAKAI)_ _FREE BOOK_ *Na* *SAJIDA NIGER* 5 Idan baka iya kama barawo ba, shine zai kama ka Umma ta yi shiri cike da tabacin za'a yi tafiyar nan da ita bayan kamar awa biyu ta yi fita ta kai sau uku, ama shiru bata samu ganninsa ba, hasalima kofarsa bakin dakaru ne ta gani wa'inda ba zata ce ta taba sanninsu ba, sun nuna mata barci yake yi, a irin lokacin da tuni ya kusa karasawa garin TANUT ba tare da sanninta ba Yan magana sun ce ice da zafinsa ake dukansa a lokacin da yake tunanin yana tare da mutanensa na hannun dama a irin lokacin aka ainahin sace shin daga shi har iyalinsa , watau shi da matarsa da kuma yarsu mace cilo inda aka sheka su a duniyar barci aka yi doguwar tafia da su wace basu gane komai ba aka kai su boyayen ma'adani mai dauke da dakunna masu duhu da tsayi tamkar gidan yari, an wadatasu da dukkan abunda zasu iya bukata kama daga wajen kwonciya katifu biyu, abin rufa, buta , darduma, ruwa, abinci, sai dai ba'a zuba masu kayan shayi ba, shayi irin na bugaje, shayin da buzu na iya shiga halin kaka naka yi idan ya yi wuni daya tal bai sha shi ba, abinda ya fi kayan maye saurin rike zuciyar buzu, domin abu ne da ya rayu da shi tun yana karaminsa, ya zamto masa jinnin jikinsa zai fi gane ya wuni bai ci abinci ba da ya wuni bai sha shayi ba! A cikin dokar dajin suka tsaya , motoci ne irin Mitsubishi manyan nan masu baya bude na shiga sahara, a kalla sun kai su goma sha daya domin a wajen sun hadu ne da manyan ikon kasa wa'inda ya yi kiransu a hanya ya kuma sanar masu ga inda yake so su hadu, domin ko ba komai bafansa SARKI ne, koda garin da yake mulka dan karamin gari ne bstansa bat lokaci daya ba abu ne mai sauki ba bale garinsa ba karamin gari bane fit, dole sai an yi zaman nan dan su ganewa junna Kowane shi yake kallo, inda yake tsaye cikin shiga ta farin yadi kall, ya nada rawani na farin rawani kal, kafarsa sanye da takalmi baki sidik , irin takalmin nan mai yar siririyar igiya , hakan ya sa ake gannin fara kal din kafarsa da kuma wajen tsintsiyar hannunsa, Dinkin simple dinki ne ba gari da yar ciki ba, dinki ne irin sakaken nan ba mai lafewa a jiki ba sam, sai dai duda haka damatsunnansa a rike suke tak a jiki sun kama shi tak kakar zasu tsage Tunda ya tsaya fuskokin wa'inda ke laye yake bi da kallo, irin kallon nan na son karantar kowa abinda yake kan fuskarsa, domin ai labarin zuciya a tambayi fuska Sarkin yanka kuwa a tsate yake a gefensa, tsayuwarsa irin ta a mutun nan, shi kadai sai ka ji ya fitar da huci kamar bijimin sa , idannuwansa kuwa ba zaka so ka yi ido hudu da su ba a irin wannan lokacin A kan fuskar sarkin DOGON DUTSI ya sauke dubansa, sukaiwa junna kallo na kirki sannan ya dan sauke murmushi kadan kafin ya sake fuskantarsu a nutse ya ce" Ba zaku min tambayar dalilin dauko shi da na yi ba? Ko ba wannan ke damunku ba?" Elhaji Idriss ne ya sauke numfashi a nutse ya ce" Allah ya karra maka lafiya UMUGHLUK ITIBEL, dole hankalinmu zai tashi, wannan fadan cikin gida ne ko na waje? Munada hurumi a ciki ko bamu da shi?, Me yasa harda matarsa da yarsa? Kuma a ina ka boye su?" Me suka yi da tsanani har haka?" Da girmamawa, da kuma gannin girman Elhaji Idrisss a tausashe ya ce" Alhamdulilah, tabas wannan rikici ne da ya hade rigima biyu, ta cikin gida da kuma ta waje, kusan shekara hudu kennan da na kama takardun dukiya ta marigayi sarkin Agadaz, dukiya mai tarin yawan da aka nema aka rasa, har aka so yin rigima a kan hakan ama abin ya yi tuwo ya yi miya, aka zauna a haka nima na yi shiru na zuba ido, ba dan ban san adadin dukiyar ba, ba kuma dan ban san a ina da ina suke ba, sai dan na san ko waye yake rike da dukiyar nan zai falasa kansa wata rana, ko ya cita a hankali ko da garaje dukiya ce da bata boyuwa, dole wata rana sai ya falasa kansa da kansa, domin zinari ne na yankin rijiyar wuta ta gabas, wace take ta ainahin jinnin marigayi, ya gada take dauke da takardu har kwaya tara na nan Nijar da manya manyan kasashe masu fitar da Zinariya, wa'inda suka saka hannu cewa rijiyar nan zata zamto gado ne wa Namiji , idan sarki ya samu maza da yawa tasu ce, idan kuwa mata ne kadai da shi zata zamo ta talakawa ne!, A lokacin da aka zo rikicin rijiya da takardunta tun a lokacin da na sanarwa sarki cewa ba zan taba zaunar rijiya ba, ta talakawa ce!, Tatalin arzikin kasata ce, tun daga lokacin abubuwa suka ringa bilowa, karshe bayan rasuwarsa aka nemi takardu harda na gidan azurfa dake cikin kauyen Ingal ba'a samu ba! Daga wannan ranar na yi shiru da bakina, ama kuma na damu mutanena na daji na baza su du inda na san akoy dukiyata da ta talakawana na basu damar dora kiwo, noma da daba, ta yadda sako zai same ni a kan gaba!" Ya dakatar yana duba agogon hannunsa, ya juya wajen da su SHEIK ke tsaye, ya sake juyowa ya dora da fadin" Ya yi kokari sosai, domin ya dauki shekaru bai je ba, bai aika ba, sai dai mun fi shi juriya da hakurin jiranshi, tunda mu a wajenmu muke, kuma Allah ya ara mana aron rai da lafiya , Bai fara turawa ana masa bincike ba sai nan da shekaru hudu da suka shige, a lokacin yake dan bincikensa, har ya yi rashin wayon zuba mahaukatan karya jefi jefi suke rayuwa da mu dan su gane me muke ciki, a ciki akoy wannan wanda shine baban yaronsa na hannun dama, kuma shine wanda ya tsorata ya sake shi da wuri ya kama mu cikin hikima yake masa aiki yana zayane mana komai, duda ya iya takunsa, ba lale ka san cikinsa ba,........na kayade maku, mutuwar sarki ciwon ciki ne wanda kowa ya sanshi da shi, ama mutuwar marigayiya guba ce mai kumbura ciki, ita ta kashe uwata!" Ya idasa a kausashe yana kallon yadda suke zarro ido , wasunsu har sunna jan rawani baya sunna kallonsa Da tarin mamaki Kambori ya ce" UMUGHLUK, kar ka ce da mu Asarki nada wani abu a cikin hakan?, Idan haka ne ka fitar mana da maci amana mu sare kansa da hannayenmu, domin ba zamu taba bari irin haka ya wuce banza ba!" Daga gefensa , sarkin garin Dosso a tsanake ya ce" Bama wannan ba, yaya nake ji an ce da yarsu, a sanina yarsa mace daya ce jal, kuma ba ita bace ka aura kwananan? Ko ka kamata da wani mugun aiki ne?" Ajiyar zuciya ya sauke a nutse ya ce" ba ita suka aura min ba, wata suka bani a matsayin ita ce" Wannan abu shi ya karra girgiza masu zuciyoyinsu, domin dai babu wanda bai san abinda hakan yake nufi ba, tabas bayan kishirwar arziki , ta mulki ta shiga, idan kuma za'a bi tarihi dama mulkin haye ya yi masa , dan yanzu yana harin babar kujera ba mamaki, babu wanda mulki ya fi wahalarwa kamar wanda ya yi masa shige da karfi ko ya siya, Yawanci sun ajiye maganarsu ne kan ya yi yadda zai yi da shi da du wani mabiyin bayansa, watau koda hukuncin kisa ke kansa, ya aiwatar sunna tare da shi Kwaya biyu ne suka nema masa sasauci, sasauci a baki sai dai baban tashin hankali a zuci, domin sun sani da a kwacewa asarki sarautar nan gwara a kashe shi, sun nema masa sasaucin hukunci ne cewa idan har shi ya kashe sarauniya a kule shi a kaso cikin bayin da ya saka kaso na kulin rai da rai, yarsa kuwa idan bata da wani laifi ana iya sakinta, ita da mahaifiyarta, in kuwa suka tsaka tsandam wuka ta sha jinni kawai Da wannan suka rarabe da tsayuwar jejin, sannan ya sake kadaicewa da SHEIK Sosai Sheik ke karra tausarsa, ya san shirun nan nasa ba yana nufin baya jin ciwo bane, ba kuma yana nufin ya kyale bane, duda ya fara kai duka yana tsoron abinda ya boye a karkashin zuciyarsa Dan ajiyar zuciya ya sauke, a sanyaye ya ce" ban san ta yadda zan binciki HUZNAH ba, ina matukar jin kunyar sanarwa HUZNAH cewa a wajenta kadai nake ba namiji ba, haka kawai nake ji kamar nine ban yi mata adalci ba, sai nake ji kamar ni na yi sake wani abin ya sameta, idan har ta ji dacin hakan yaya zan rarashets?, Idan ta yi kukan hakan me zan ce mata?, Ina matukar jin kunyar amsar da zan iya bata " Da tarin tausayawa Sheik ke rarashinsa, yana karra nuna masa komai na duniya mukadari ne, in sha Allah itama ba zata dauki komai da zafi ba, kasantuwar abu a haka kuma Allah ya hukunta bata da yadda zata yi, fatana Alllah ya sa akoy maganin abin, domin idan babu maganin abin kam matar nan in har wannanma itace gaskiya tana da kin jin tsoron Allah, to ina zata kai hakin mutun ne Fisabililahi? _________________________________ A bangaren NADIRAH kuwa tana karasawa bangarenta ta tarar da Hindu da Auta a zaune rike da carbi sunna ja, hankalinsu a kan kofa kowane kana kallon fuskarsa zaka ga tsantsar tashin hankali a kan fuskar tasa A zabure Hindu ta mike tana kallonta, a rarabe ta ce" Yar indi yaya dai? Zo mana kar ki fadi" A sakalce ta karasa ta rungumu a jikin innarta, wace ta silale da ita saman kujera Muryarta a kurya ta ce" Auta taimaka min da ruwa , ama
Chapter 80 · 0% Book details