Sashe 8
Zainazain Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Maza ka gayamai komai yake Ciki ya Tattaro ya Dawo Gidanka ko Nan Gidan da Zama ban lamunci Zamansa awannan Gidan ba Tunda ba mata gareshi ba..!
Yafada Cikin Alamun ba Wasa yake ba Abba ya Jinjina kai yana Fadin"Hakane Alhaji Tsoho..Kai Haddir maza ka Tattaro kayanka Ka zabi Gidana ko Nan Gidan ka Dawo ka Zauna Zamanka achan baida wani amfani Tunda Kana da Wajen da zaka Zauna.."Hajiya Mama ta karbe da Fadin"In yana so ya samu sakewa..Yayi Aure..!
Fuska ba Walwala Haddir yace"Toh Abba Dama Abunda yasa na kama Chan Gidan naga yafi kusa da asibiti ne.."Alhaji Tsoho yace"Wannan Ba Hujja bace..Da zai saka ka Zauna kai kadai..Sai Mutane surika Munana maka Zato Tunda ina da Tabbacin ansan kana da Mu anan garin Zamanka achan bai Dace ba kayi yarda muka ce kawai ."Kai ya kada yana Fadin"Shikenan Weekend zan yi parking..Zan dawo nan daman Wannan Tsohon matar naka Tana So tana kaiwa kasuwa..!
Yafada yana Hararan Hajiya Mama Shewa ta saki Tana Fadin"Ja chan Me zan Dakai..?
Kaga Sabon Megida nan,Megidana akwai Cefane.."Tafada Tana Dafa Zain Dake gefenta Shima ya Dafata Harda Ma Haddir gwalo Abba yace"Hajiya mama Ayi ma Tsohon mu haka..?
Hajiya Mama tace"Me za"a Fasa..?
Shima Tawaye yake neman yayi min da Halimatu Kullum sai tazo Gidan nan kaga Sun Hada kai suna ta kus kus in kuma bata zo Zata kirashi a waya ko Aikomai da wannan kawomai wannan Kaga fa in batazo ba ya Dinga Damuna da Fadin Oho Aminatu yau Halimatu Shuru ko lafiya..?
Bari na Kirata..!
Abba na Dariya yace"Au Ramawa kikayi kenan kema kika kwace mata miji kenan..?
Hajiya mama Tace"Eh mana Taji In Da Dadi itama.."Alhaji Tsoho yace"Hoho Aminatu...Ina Laifin Halimatu kinsan Bakin Tsoho sai da Gishiri Gishiri kuma Kus kus Din Da kikace munayi labarin Iyayenta nake bata Ina gayamata kyawawan Halayansu da na sani Lokacin da muka Zauna dasu Suna Raye..."
Allah ya Jikan Umaru da Abdullahi da Duka Musulmab da Suka Rigamu gidan Gaskiya.."Gabadayansu suka amsa da Ameen sai kuma Jikinsu yayi sanyi Alhaji ya Cigaba da Fadin"Haske da Rahma yakai musu..Bayin Allah ne masu Zuciyar Zinare Na Sha Gayama Halimatu Ta Debo Wasu Daga Cikin Hallayan Mahaifiyarta Maryama.."Hajiya Mama tace"Ba Shakka...Allah ya Hadamu a Aljannah Dasu.."Gabadayansu suka amsa da Ameen Ameen kafin su Cigaba da Hiransu Jefi Jefi Abba bai Jima ba yayi musu sallama ya Tafi Zain kuma sai da ya Tsaya Suka Sha Furan da Hajiya Mama ta Damama Haddir Duk da yadda ya Dage kan bazai Sha ba Bayan sun gama suka Tafi Kitchen suka gaisa da Baba Tabawa Wata Yar Dattijuwa ne aiki take Gidan Alhaji Tsoho Tun Tana Matashiyarta Har Girma ya kamata an Riga da an zama Daya Dayake Baba Tabawa irin yan gudun Hijiran ne ba wasu Dangi ne Alhaji Tsoho ya Zame mata Tamkar Uba Duka su Zain Agabanta suka Taso Ita tayi Wahala dasu In Aka kawosu Hutu Gidan na Alhaji Tsoho.
Bayan sun Fito ne sukama Su Hajiya Mama Sallama suka Fito Atare Haddir na Kokarin Shiga Motarsa yana Fadin"Wai ina ka Tsaya Jiya Zainarka ta kirani Tana Tambayana ko muna Tare..?
Yana Sosa Gemunsa da Key din Motarsa yace"Na tsaya Cikin Asibiti ne Kuma Wayar tawa Tana Silent Shiyasa ban ji kiranta ba.."Kallon Sama da kasa Haddir yayi mai kafin ya Cije baki Cikin Tsarguwa Zain yace"Lafiya kake min wannan kallon..?
Ko zan maka karya ne alkali Hadiru..!
Yafada Lokaci Daya yana Dauke kai Mirmishi Haddir yayi kafin yace"Kai dai ka sani..Ka kama kanka ne ammh ni wani kallo nake maka..?
A koda yaushe bazan gaji da Fadamaka ba kaji Tsoron Allah..Ka kuma guji Ranar da Wata baraka zata Faru wacce Zata Zubar maka da kimarka Harda ta iyayenmu.."Yana Gama Fadar haka ya Bude Motarsa kiran Jeep ya bar Zain nan Tsaye yana Binsa da kallo Mganar Haddir din namai yawo a saman kansa yana Tsaye ya Fice Daga Haraban Gidan ya barsa ajiyar Zuciya ya Sauke kafin Shima ya Nufi Motarsa ya shiga ya Tasheta Shima da Gudu yabi bayan Haddir din.
Kusan Tare suka Shiga Cikin Asibitin..Kowa Bangaran Office Dinsa ya Nufa Saboda sun makara Sun san Fayels Din patient na chan na Jiransu da Uban Layi,illai Haddir yana Shiga Office ko zama bai gama yi ba yace First ya Shigo Shi kuwa Zain yana Gabda Shiga Office Dinsa Suka Hade da Dina ta Fito Daga Office Dinta kallo Kallo Sukayi ma Juna kafin Shi yayi Saurin Dauke kai ganin Tana Jifanshi da Irin kallon Data saba kashemai Jiki Dashi Fuska ya Hade kawai ya Tura kofar Office dinsa ya Shige yana Kiran Wata Nurse da Hannu Alaman ta Biyoshi.
Sai da ya Shige kana Dr.Dina ta Kada kai ta Murmusa tana Fadin"Kayi kuskure Dr.Zain in kana Tunanin zaka iya gujema Dina..Har Abada bazaka iya ba..Ban Fara sonka don na Daina ba kuma Ban Fara mu"amala Dakai don na Daina ba..Yanzu ma aka fara Wasan...!
Tafada tana wani Sakin Wani Shu"umin Mirmishi ta kada kai ta Wuce so take ta bar Cikin Asibitin Tunda Ta Duba patient 10 yau da Safe tace abarshi haka Sauran aturama Dr Imran Ita ZATA fita Ma"aikatan su Zakiya take son zuwa su Tattauna wasu Abubuwa sun kwana Biyu Basu hadu ba..!
*****
Fitowarsu kenan Daga Lecture Suna Gangarawa zasu Shiga Lap Duba wani Calculaton da aka basu Tafe suke suna Hira Sama sama Har suka Isa Libary Din Sai da suka samu Waje suka Zauna kana Halima ta Fito da Wayarta Tana Fadin"Kinga Laila kafin mu Fara Duba Assigment din nan Let me Call Firstlove Tukunnah na gayamai na Fito..!
Mirmishi Wacce aka Kira da Lailah Tayi,Itama Dim kamar Sa"ar Haliman ce sai dai Ita Fara ce Tas kuma kyakyawa ce,Kai ta kada Tana Fadin"Hmm kirashi Dama waya isa ya Hanaki Kiran Firstlove..'Halima bata Jita ba Domin tayi nesa da Ita Suna mgana da Dr.Zain tana mai Shagwaban Ta gaji,shi kuma yana Lallashinta Daga karshe yace in tagaji ta koma Gida Shima da wuri yau zai Tashi aiki nan dai suka Shiririce Suna Mgana Sai da Taji Shigowar Haddir da mganarsa kana Suka Datse kiran Ta koma Wajen Laila Tana Fadin.
"kawas afuwan..Na bata miki Lokaci.."Laila tayi Mirmishi Tana Fadin"Bakomai..ai na Saba Daukan Bata Lokaci indai akan Firstlove ne.."Dariya kawai Halima Tayi
Batayi mgana ba Laila ta kalleta Tana Fadin"Ni kuwa Halima in bazaki Damu ba zan so na baki Wata yar Shawara..!
Halima na Fito da Note Book Dinta Da Handout Lokaci Daya Tana Fadin"Wata Shawara..?
Ina Sauraranki Lailah..'Tafada Tana kallonta..'Laila ta gyara Zama Tana Fadin"Tunda muka Fara karatu a wannan makarantar muka Hadu Dake Halima muka kulla kawance Saboda Duka Abu Daya ya kawomu..Duk da Banta Aure ba ammh ina da Labaran Zamantakewar Aurarranki Da Dama Halima..Na Tabbata a Haduwata Dake zuwa yau zan Shaida Girman matsayin Soyayyah da Kauna Hade da yarda Da kike ma Mijinki Halima Kuma Hakan yana matukar Burgeni..ina jin Dama ace Nima na samu miji kamar naki Wanda zamu Dinga Gudanar da Rayuwarmu kamar yadda kuke gudanar da naku keda Firstlove dinki..!
Mirmishi Halima ta Saki kafin Tace"Bake kadai ba..Mutane Dadama Suna Fadin Irin Soyayyar Dake Tsakanina da Firstlove Tana Burgesu."Laila tace"Dole ne..Ammh Duk da Burgenin Datake Ina da yar Shawara gareki Halima..Kinga Da" Namiji Buhun kaya ne kuma Dan Hankaka ne gabansa Baki bayanshi Fari ina Tsoron yadda Kika gama Bashi Yardanki kada Watarana yaci Amanarki Zuciyarki ta kasa Dauka Har Abun yazo yayi affecting Dinki Halima..!
Tun kafin Ta karisa Halima ke Jefenta da wani kallo kafin tace"Bangane ba Laila..What Do U mean..!?
Kai tsaye Laila tace"Ina Nufin ki Rage Wannan Zafin so da yardan da kika bama Mijinki ban ce ki Daina yarda Dashi ba Duka No ki Rage karki manta Namiji ne kuma Likita Likitan ma na Mata Yana Harka da mata kala kala kinsan Zuciya bata da kashi Ina Tsoron kada Wani abu ya Faru kika sa Jurewa Zuciyarki Zata iya Tabuwa a yadda na Sanki da Komai kankanta Abu Damunki ya...!
"Don Allah Dakata Lailah..!
Bata karisa ba Halima ta Tareta a Fusace Shuru Laila Tayi Tana kallonta Ita kuma Halima ta Fara Mgana Cikin Bacin Rai Tana Fadin"Kin bani mamaki laila Wlh Ban Taba Zaton keda bakinki zaki zo da irin wannan Zargin ga Firstlove ba na Dauka kowani Kikaji yana Fada sai inda Karfinki ya kare adai yadda muke Dake ammh sai gashi keda kanki ki ke Fadan Haka..Toh bari na gayamiki Abunda baki sani ba Firstlove Bazai Taba Cin Amana ta ba Domin na Yarda Dashi Fiye da kaina Banda Uwa Bani da Uba..Iyayensa Sune iyayen Goyona Sun Rikeni Tamkar yar da suka Haifa Tun Ranar da na Zo Duniya Firstlove Shi ya Fara Daukana kafin Innata da Babana Goggo Halima da Bakinta Take Fadamin Taga Soyayyata a kwayan Idanuwan Firstlove Tun Ranar dana Zo Duniya..Laila inda Firstlove zai iya Cin Amanata da Tun Tuni yayi..Domin tun ina da Shekara 9 a Duniya ya Tafi London karatu Cikim Jajayen Fata da Turawa masu al"adu da Dabam Dabam...Ammh bai Sauyani ba Ya Jirani Har na Girma Shima Lokacin ya gama karatunsa Auran mu Ya Tabbata Baki Tunanin wanda ya Tsallake zukan Zukan mata Harda Turawa ya Dawo gareni baki kyautatamai zato laila..?
Tafada tana kallonta Ido Cikin Ido Ajiyar Zuciya Laaila ta saki kafin tace"Nifa Baki gane mganata ba Ha...'!
Nagane Duka Inda kika Dosa..So kike na Cire yardan da nayi ma Firstlove..Toh bari kiji na Yarda da Firstlove Aduk Duniya Shi na Fara yarda Dashi Tunda Ban yi Wayon sanin iyayena ba..Kuma ki sani Firstlove dina Bazai Taba Cin Amanata ba Har gaban Abada Saboda yafi kowa Sona da Sanin Raunina..!
Tana Gama Fadar Haka ta tashi ta Fara Tattara Takardunta Laila ta Mike tana Rikota ta Fizge Hannunta Tana Fadin"Stay Away From me Laila..Alaqata Dake bata yiyuba...Juz Leave me..!
Daga Haka ta kwashi Littafanta ta bar mata Wajen Laila ta Bita da Kallo Kafin ta kadai afili ta Furta..'Allah yasa Haka Halima..Rauninki na sani Shiyasa nake Tsausayinki Har acikin Raina ban kuma san Dalili ba ina Jin Wani abu acikin Raina mai kama da Tsoro..!
*Comments*
Share and Vote*
*Intelligent Writer"s asso*
*Janaftyshakira...*
*ZAINAZAIN..!*
_(Is a love Story and Betrayal)_
*Wattpad:Jamilaumar351*
*Mallakar:Janaftyshakira*
*BOOK 1*
*#SHEKARUN BAYA..*!