← Book details Zainazain Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 78

Sashe 44

Zainazain Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Suna zuwa Haddir ya kalli Zain wanda ke jingine Jikin motan Kallo Daya zakamai ka Fahimci baya Cikin Natsuwarsa,Cikin Tsausayawa yace"Bakaniken nan zamu bari anan..Zan bashi Key din Motar in ya gama gyaran motar zai Tukata zuwa Garejinsu Daga baya zan zo na karba.."Cikin Rashin Fahimta Zain yace"Bangane ba..?motar haya zamu samu Zuwa kanon..?

Bazai iya kallonsa ba Shiyasa ya Juya baya yana Fadin"Gida zamu koma..Na samu wayar Baban Kaduna kan cewa Alhaji Tsoho na neman mu dagaggawa.."Gum Zain yaji kamar an Bugamai Guduma asaman kansa Cikin Rashin Fahimta ya isa ga Haddir ya Juyo Da Fuskansa yana Fadin"Me kake son Fada Haddir..?

Cikin karaya Haddir yace"Banda...Tabbas ammh ina Bakincikin Sanar dakai Dina ta Rigamu...Ina Zargin mganar Cikin nan takai ga iyayenmu..!

Girgiza kai Zain ya Farayi kamar wani Zararre yana Fadin"Kai ina..?

Karya ne Wlh bata isa ba...Kila dai Kiran na Taron nan ne,kasan Alhaji Tsoho ya matsa fa.."Yafada Cike da kwarin Gwiwa,Cikin son yarda da Mganarsa Haddir ya Gyada kai yana Fadin"Allah yasa hakan.."Zain cikin karaya da Rauni yace'Ameen
Daga haka Haddir ya Fara Taran musu Mota sai dai basu samu ba Wajen Minti goma sai bakaniken yace su Jira gyaran bai da yawa yanzu zai gama,sai gashi Cikin Ikon Allah ko Minti Talatin baiyi ba ya gama gyaran Haddir ya Hau ya Bata wuta yaga Komai Daidai 5k ya bashi yace yakai ma ogansu su kuma ya basu 2k,Daganan suka Hau Mashin dinsu Su kuma su Haddir suka Hau tasu Motar suka Juya zuwa Gida Zuciyoyinsu Kowanne yana Saka Abubuwa Dadama.

Gudu Haddir yayi sosai Cikin Lokaci sai gasu sun iso Haraban Gidan Alhaji Tsoho Suna Fitowa Daga Motan su da Jeep din da su Kwamishina suka zo da ita suka ci karo Sai kuma Excort dinshi Guda Daya da Mamaki Haddir da Zain suka kalli Juna cikin alamun Tambaya,ganin basu da masaniya Dukkansu yasa suka Nufi Hanyar da zata Sadasu da Babban Falon Gidan na Alhaji Tsoho.

Haddir ne agaban Gaba Zain na Biye Dashi abaya cike da karfin Gwiwa koda suka ga Takalma akofar Falon Basu Tsinke ba sanin Duka iyayensu yau suna gidan na Alhaji Tsoho Shiyasa suka Shiga da karfin Gwiwansu Musamman ma Zain,gwara ma Haddir Tsoro ya Shiga Zuciyarsa.

Akusan Tare suka yi sallama akuma Tare Duka Jama"ar Falon suka Daga suna kallonsu Lokaci Daya suna Amsa Sallaman nasu Atare yadda Duka iyayen nasu suka Zuba musu ido ne yasa Jikin Haddir kawai yayi sanyi sai kaawai ya samu kansa da kwarema yan Falon kallo Daya bayan Daya zuciyarsa ta Tsaya Cak ne sanda yaci karo da kwamishina da Hajiya batula bai gama Mamaki ba sai da ya sauke ganinsa kan Dina da kawarta Zakiya suna kallonsa Cikin Wani yanayi ai sai Haddir yaji kamar an Dasashi lokaci Daya kuma Yaji kansa ya Sara wanda yasa ya Dafe kansa Lokaci Daya yana Kiran sunan Allah Cikin Rawan Zuciya da Rawan kafa
Zain kuwa Da zuciya Daya bai Fahimci Halin da Haddir ya Shiga Ko domin Shima bashi da Natsuwar ne,Wucesa yayi ganin ya Tsaya bai ma Lura da Su Dina ba Idanuwansa kawai iyayensa kadai suke nunamai acikin Falon kai Tsaye Alhaji Tsoho ya Nufa yana zuwa ya Zauna agefensa yana Fadin"Kai Tsohon Likitan nan ka cika Takura Miye kake ta kiranmu baka ya"......!

Sauran Kalaman Bakin nashi Sun makale ne sanda ya Dago zai Nuna su Baban kaduna kawai karaf Suka Hada ido Hudu Da Dina Wacce Daman Tunda ya Shigo Take nacin kallonsa Taga in ya ganta ya zaiyi aikuwa yana ganinta sai ya Fara Tunanin Gizon ta ne ya gane da Fari kafeta da ido yayi yana kallonta Cikin Bushewar Miyan Baki kafin ya waiga yana kallon Alhaji Tsoho irin kana kallon Abunda nake gani Sai dai kuma..?

Kawarta Zakiya Dake gefenta Dukkamsu suna Jifansa da wani manufukin Mirmishi Kamar wani wanda Wutar Lamtarki taja Haka ya Mike Jikinsa Ko"ina ba inda baya Rawa Idanuwansa ya Rufe Cikin Nuna ta yatsa yake Fadin"Dina..!

Kallonsa Tayi Ido Cikin Ido Kafin Tace"Na"am Zain..."Tafada tana wani karkatamai kai Idanuwansa gabadaya sun Rufe ya manta da Wadanda ke Falon ya fara Taku zuwa Gareta Kowani Taku kuma Kirjinsa na wani lugude kamar amafarki Yaji Muryan Alhaji Tsoho yana Fadin"Kai Zainullahi ina zaka..?

Maza dawo nan ka zauna..!

Yafada Cikin Kakkausan Murya,Cak ya Tsaya sai Lokacin kuma Ya Fara dawowa Cikin Hayyacinsa ya Lumshe Idanuwansa ya kara Budewa yana Bin Kowa Dake falon da kallo So yake ya Gani Da gaske ne Dina ya gani ko Gizon ta ne..?

Yakuwa kara ganin Gaskiyan Harda karin Kwamishina da Hajiya Batula,Gabadaya Falon Shi aka zuba ido ana kallonsa Idanuwansa ya Sauke kan Dina kyam kamar an Dasashi Wani Irin Hajijiya ce da wani Taurin Abu yake taso mai kamar zai kadashi Rufe ido yayi ya sake Budewa Still Dai gaskiya ne Tuni yaji Numfashinsa ya Tsaya Cak ya Daina aiki.

Cikin Bacin Rai Alhaji Tsoho ya kalli Zain yana Fada'Ko baka jina ne..?

Cewa nayi ka Dawo nan ka zauna.."zuwa Lokacin Tuni Jikin Su Umma ya gama yin Sanyi da Abunda zain yayi wannan ya nuna akwai wata akasa atsakaninsa,,Nene kuwa kai kawai ta Sadda Tana jin Duk Wata gabarta na Saki Haddir ne Daya ga Ran Alhaji Tsoho ya baci ga Zain kamar baya Cikin Hayyacinsa yasa ya Daga kafarsa Da yayi masa Nauyi ya isa ga Zain din ya Rikosa yana Fadin"Muje Alhaji Tsoho na Kira..!

Kamar wani karamin yaro ya Juya yana kallon Haddir lokaci Daya Yana Fadin"Kaga Abunda Idanuwana suke ganemin kuwa afalon nan Haddir..?

Cikin Wani irin kunya da Nadama Hade Tsausayi Haddir ya gyada mai kai yana Fadin"Eh nagani Zain..Yanzu ba Lokacin mgana bane muje ka amsa Kiran Alhaji Tsoho.."
Karyansa kuma ta karse yau..Haka Zain yake Fadi acikin Ransa Har suka isa Gaban Alhaji Tsoho wanda ke Binsu da kallo Cike da Nazari Cikin Dakiya Haddir ya Zaunar da Zain Kusa da kafafun Alhaji Tsoho Shima ya koma ya zauna Gefensa kansu suka maida kasa Haddir Nata Kiran Sunayen Allah ayayinda Zuciyar Zain Tana Daina ma Bugawa bakinsa kuwa Motsi yake ammh kuma baisan me yake Fada ba.

Gyaran Murya Alhaji Tsoho yayi kafin ya Daga Dayan Takardan Dake Hannunsa yana Fadin"Wani Likita ne ya baku wannan Shedar acikin asibitin Saulawa Spealist..?ya fada yana Kallon Dina Wacce Cikin Ladabi ba alamun Damuwa tace"Dr.Imran ne Ranka ya Dade.."Atare gaban Haddir da zain ya kara Bugawa kuma atare suka Dago suna bin Takardan Dake Hannun Alhaji Taoho Da kallo Sai dai Daga nan Basa Fahimtar komai Zain Dai kafe Dina kawai yayi da ido yana kallonta da Tambayar ni zaki ma Haka Don Kutumar Ubanki..?

Kai Tsaye Alhaji Tsoho ya kalli Haddir yana Fadin"Kai Hadiru kasan wani Dr.Imran a asibitinku..?

Cikin Sanyin murya ya Daga kai ba mgana Alhaji Tsoho yace"Toh Tashi..Kayi maza ka Dauki Mota kaje asibitin ka Taho min Dashi nan yanzu.."Daga shi Har zain sai da suka kara kallon Alhaji Tsoho aammh ganin yanayinsa yasa Basu kara marmarin kallonsa ba Da Sauri Haddir ya mike yana Fadin"Toh Insha Allahu.

Da Hanzari ya Fice Daga Falon Har yana Hada Hanya yana Fita Baban kaduna ya Kalli Alhaji Tsoho yana Fadin"Alhaji Tsoho zaman me meke haka ne..?

In zain ne gashi ya iso ka Tambayeshi ya gayamaka gaskiyan mgana Atashi wannan Taron mara amfani kowa ya kama gabashi.."Wani Mirmishi Takaichi kawai Alhaji Tsoho yayi kafin yace"Yaro Yaro
ne...Yaro man kaza ne.."
Yana Fadin Haka ya koma ya Gintse Ransa kawai yana Bin Zain da kallo Cikin Takaichi Da Bakinciki Wanda ke Fitowa Daga kasan Ransa Duk da bai da Wani Sheda kan Zain bai aikata wannan Fasadin ba ammh kuma alamun Rashin Gaskiya da Kamshin Gaskiya sun bayyana Garesa sai dai kuma Koda Hakan ta kasance yayi alkawarin kamanta gaskiya ga Duka Shashen Insha Allahu.

Har Haddir yaje asibiti ya Dauko Dr Imran Alhaji Tsoho bai kara mgana su Inna Rukayya ne ma ke Cecekuce,Dina kuwa da Zakiya Zukatansu kamar Farar takarda Saboda Fari,Zaim kuwa Tunda Haddir ya Tafi yana nan zaune inda yake Motsi mai karfi ma Bayayi kansa na kasa Baya ma Marmarin Dagowa saboda yadda Kowa na Falon ke jifansa da Wani irin kallo wanda ke kara Tsinkamai ya"yan Hanji.

Shigowar Haddir da Dr.Imran ne yasa Falon ya Dau Shuru gaban Alhaji Tsoho Suka Rusuna Dr Imran ya gaisheshi ya amsa Cikin kulawa kafin Dr.Imran yace"Ina cikin Office Dina Sai ga Dr.Haddir yazo ya sameni da cewa Ka umarceshi Dayazo ya Daukoni kana Nemana..Allah yasa Lafiya Ranka ya Dade..?

Alhaji Tsoho Ya muskuta yana Fadin"Eh hakane...Karbi nan.'ya fada yana Mikamai Takardan Dake Hannunsa wanda keda Tambarin asibitinsu wanda kuma Dr Imran din ya basu Sakamakon Cikin Dina ajiki Da Sauri ya Gani na wasu sakwanni kafin ya Dago yana kallon Alhaji Tsoho bai samu Zarafin mgana Alhaji Tsoho ya katseshi da Cewa"Ka gane wannan Takardan..?.

Dr Imran Dagowa yayi yana Bin Mutanen Falon da kallo sai alokacin Yaga Dina da Zakiya Cikin mamaki ya ke kallonsu da Neman karin Bayani Ido Kawai zakiya Ta kadamai Cikin Takaichi Inna Hannatu tayi Tsulum Tace"Kai Shashasha...Tambyarka akayi bawai an ce ka juya kana kallon wasu ba..!

Tafada Cike da Takaichi Cikin Wayancewa ya waiwayo yana kallon Alhaji Tsoho Lokaci Daya ya gyada kai yana Fadin"Eh Tabbas..Ni da kaina na bada ta
ta Shekaranjiya da yammah..'
Alhaji Tsoho yace"Kai kayi Test din..?

Nan ma kai ya Girgiza yana Fadin"A"a Bani keda alhakin wannan ba nidai Dina da kawarta Zakiya
gasunan sunzo sun Sameni kan Dina Bata da lafiya na Duba Toh Bisa Tambayoyin da nayi mata ne sai na Fahinci kamar Gwajin Ciki ne ya Dace da ita nan kuma take na Dibi Jininta na kai Lap dinmu na Basu suka Gwada kuma suka Fitar da wannan sakamakon.."
Yafada Cikin Fargaba da kuma Tunanin meyake faruwa..?

Kowa yaji Abunda ya Fada Cikin Hikima Alhaji Tsoho yace"Ka Tabbata wannan sakamakon na gaskiya ne..?
Chapter 44 · 0% Book details