← Book details Zainazain Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 78

Sashe 19

Zainazain Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nan sukayi ta ba Dadi Zain din ya Musa ma Haddir Zarginsa akaro na Farko yayi mai karya Ba Saboda komai ba Zain yana jin kunyar Haddir ya kara kamashi da laifin da yayi mai alkawarin ya Daina Uwa uba kuma ga Halima Wacce bata inda ta Rageshi,Auransu Duka Duka Wata Biyu ammh kuma Har ya Fara cin Amanarta..?

Koshi yana son ya yakice Dina acikin Rayuwarsa Tunda ba Sonta yake ba ya Dade da gayamata bazai iya Auranta ba,Su Rabu ammh Abu kamar Zanen kaddara Tunda ta Shigo Rayuwarsa ya kasa yakiceta.

Tun Zuwan Dina asibitin Dr.Imran ya kyalla ido ya ganta Ransa ya Biya Dama mayen mata ne,Tuni yake taya Nurses Din nan Wacce ta bata kai Shikenan Yayi Kokarin Tusa kansa ammh Dina Taki bashi Fuska Har Fitomata yayi da Maitarsa ammh ta Watsa mai kasa acikin Ido,Daya gane Zain take so Shi kuma sai yana Zugata da Cewa Zain baya sonta kowa ya Shaida Mace Daya yake so Itace Firstlove in yana Fadamata Haka ji Take kamar ta Mangareshi Ya gaji da Maitarsa bata kulashi ammh Duk da Haka bai Hakura ba Tsakaninta kuwa da Haddir gaisuwan Sama sama ne kawai na Wadanda suke aiki awaaje Daya ammh Ta Riga ta sani Tun Farko Bata Burge Haddir
Wani Lokacin Zain yana kaucema Haduwarsu da Dina ammh Ita ke Hillatansa Zuwa Gidanta Chan su lalace,Ko a Office Dinsa baiso suka Fara wannan Mu"amalan ba Ammh Dina Tayi ma Zain Farin sanin Da tasan Hanyoyin Datake kunnosa,Shiyasa baya iya kaucema Tarkonta Sunsha yin Fada kaca kaca kan Firstlove dinsa Daga baya kuma su koma Su Dinke Likitoci Dadama su Na Dora Musu Zargi ammh Rashin Shaida yasa kowa ya kauda kansa Tunda Zain din kwata kwata bai da Sakewa Saboda nan ba Wata kasa bace Gida ne kuma Duk Abunda zai yi Mara kyau zai iya Taba Mutumtakansa Data Gidansu Shiyasa yake Kokarin Kiyayewa
Bayan Auransu ne Halima Tayi Jamb Taci ita Da Zafeera suka Rubutu kuma Dukkansu sunci,Dukkansu ABU samaru Zaria suka samu ammh Zain yace Zainarsa bazata ba,Dole Zafera kadai Tatafi itama Din An Sauya mata BUK kano Tatafi Tana zaune gidan Inna Rukayyah Tare suka Fara karatu da yar Autatanta mai Suna Shema"u, Shi kuma Faruq Ya Tafi Kasar Ketare Wato Chicago inda ya Fara karatun Digree dinsa achan Ayayinda Shi kuma Zain ya Sauyama Halima makaranta Zuwa ATBU BAUCHI ta Fara karantar B.SC Mathematics Tana Shekaran Farko ne,Lokacin ya Siya Motar Hawa Ita kuma Abba Usman ya Siyar mata NATA Saboda Zirga zirgan Tafiya makaranta Tunda Zain yana zuwa Wajen AIKI bai zama ba lalle Tafiyansu tazo Daya ba,Shidai Zain ya bata Gudummuwar Siya mata Tsaleliyar Waya sai ta bama Zainab Tsohowar Tata wacce Abba Ya siya musu ita da Zafeera tun suna gida
Tun Zuwanta makaranta Suka Hadu da Laila Adam,Course Dinsu Daya,Kuma Sai Halinsu yazo Daya Tunda itama Lailan akwai kokari anan garin Bauchin take da zama ita da iyayenta Duk ba masu Hali bane Suna Da Rufin asiri,Bayan Zafeera Laila ce kadai Halima ta yarda Ta sake kawa da ita Tunda Zafeera Tana makaranta sai dai in sunyi Waya,Duk wanda ya zauna da Halima Dole yasan Waye Firstlove agereta,Laila Taje har gidan Halima Tasan Zain Shima yasanta Tunda Yana zuwa Daukanta Wani Lokacin in bata je da Motarta ba,Har gidan su Umma Taje,Tasha kuma Raka Halima Gidan Alhaji Tsohi suje su gaishesu Yarinyar tana Da Hankali Shiyasa Har Zain ya yarda Halimar Tayi kawance da Ita.

Halima Bata Taba ganin Dina ba Sai sau Daya Da Zain zai kaita makaranta Ranar Motarta ba Lafiya tana Wajen gyara sun Fito sai ya samu Kiran gaggawa Daga asibitin sai ya Fara Biyawa da Ita asibitin Har Cikin Office Dinsa awannan Ranar ne wasu Suga Firstlove dib Dr.Zain,Aranar zaina taga Dina Ta ganta Ido Cikin Ido Tunda batasan da zuwanta ba Ta Shiga Office din Zain din ne Ta ganta ganin Ta Tsaya Tana kallonta ne yasa Shi Zain din ya Gabatar da Halima ga Dina Itama Dinar ya gabatar da ita akan cewa abokiyar aikinsu ce Dr.Dina gaddafi Sherrif.

Hannu Dina Tabama Halima sukayi musabaha kowanne na Kallon kowa da Wani Tunani Dabam Ita Halima aganin Farko Taji Zuciyarta ta Fara rawa Akan Dina Haka kurum taji Matar bata kwantamata ba Duk Kokarinta na tayi mata Dariya kasawa Tayi sai yake,Shima Zain din bai yarda Zainar Tasa ta gano wani Abu ba,Ya Tattarata suka bar asibitin a Hanya da zai kaita Makaranta sai da Halimar tace ita Kuwa Taji Zuciyarta bai kwanta mata da Wannan Dinar ba,Da ta Fadi Haka yaji mamaki ammh sai ya Shanye mamakinsa yace mata Dama Haka Allah ke Abunsa ba kowa bane zakaji ya kwantamaka ba Ammh Dina Bata da matsala Daganan bai kara mgana ba itama Bata kara mai Zencen Wata Dina ba ammh Abun ya Tsaya mata arai Har Haddir ta Tambaya yace mata Karta Damu Juz kawai abokiyar aiki ne Shi ina zai yarda aji mutuwar sarki abakinsa ba Domin Har ga Allah Tsausayin Halimar yake ji Yana Tsoron Faruwar wani abu indai Sirrin Boye ya Fito Fili.
*******
Fitowa Tayi Daga Library Ranta a matukar bace da kalaman Laila agogon Fatan Dake Hannunta na kamfanin Gucci takai Duba Taga har pass 10 kuma sai 11am zasu Shiga Lectures Din Dr.Tafida ne Baya son Wasa ammh da ba Haka da gidan Umma zata wuce kawai.

Departement Dinsu ta koma ta Samu Waje ta zauna Ta Fito da Wayarta Tana latsawa Zafeera take son Ta kira sun kwana Biyu Basu yi mgana ba,gabadaya Walwalarta Ta Ragu akowani Dakika kalaman Laila gareta Suna Dawowa mata kuma Suna sanya mata Faduwar gaba da Wani Rauni wanda Ta Rasa Daga Ina yake Fitowa.

Ta kira Zafeera 2missedcalls bata Daga ba sai ta kyaleta Tana Tunanin kila itama Tana Class ne Tana kokarim maida Wayarta Cikin karamar Jakarta Laila ta kariso Wajenta bayan Ta gaji da nemanta Kafin ma Ta samu Zama Halima tayi Saurin Dagowa Lokaci Daya Tana Dakatar da ita Hannu.

"Wai bana ce miki ki kyaleni ba Laila..?

Don Allah ki barni Dazu najure kin Fadi maganganu Son Ranki Buh by now Zuciyata bazata iya Jure waba gwara ki Kyaleni kamar yadda nace Simple...!

Tafada Lokaci Daya Tana Mikewa Cikin Bacin Rai da Sauri Laila Tasha Gabanta Tana Fadin"Naji zan kyaleki Halima..Ammh plz ya kamata Ko Sau Daya ne kima mganata kyakyawan Fahimta ba Nufi...!

"Ya isa Laila..Sai yanzu na gano Inda kika Dosa Wato Kina son mijina,Shiyasa kika Fito da wannan Hanyar da Rashin Jituwa zai Fara Shiga Tsakaninmu saboda ki samu Wata Dama ko..?

Tafada tana Watsa mata wani kallo Waro Ido Laila Tayi kafin Tace"Wa...?

Innalillahi Wlh banzata ba Halima Banzata zaki min Wannan kallon ba..Ammh komai ya Faru ba laifinki bane ni naja..Allah ya baki Hakuri Insha Allahu haka bazata kara Faruwa ba kuma ina so ki sani yau ko Mutuwa kikayi bazan iya Cin Amanarki ba Ballatana Kina Raye Halima..!

Ta karishe Fada Idanuwanta na kawo kwallah kafin ta Juya Ta Fara Tafiya Halima da kalaman Laila suka kashe ma Jiki ta Daga Kafa Tana Tafiya ga Lailan Tana Fadin"Haka zalika kamar yadda Ko Da bana Raye bazaki iya Cin Amanata Haka ma Firstlove Ko Gawata bazai iya Cin Amana ba Laila Ballatana Da Rai na da lafiyata Bazan Taba yarda Dake ba..Domin Firstlove ya Fara Min Kauna ta gaskiya Tun ina Cikin Mahaifiyata..!

Cak Laila Ta tsaya ammh bata Waigo ba sai Halima ce Tasha Gabanta Tana Fadin"Nima am Sorry In mgana ta bata miki Rai I did Mean to hurt u..!

Tafada Tana Riko Hannuwanta Mirmishi Laila Ta saki kafin tace'Na Fahimceki Kawata..Samun Wannan kaunar ta Firstlove dinki gareki sai An Tona Irin Labaran da muka Sha karantawa ne English Novels Da Hausa Banta Tsammanin akwai Ira iransa a xahiri ba..!

"
Halima Ta saki wani kayattacen Mirmishi Tana Fadin"Gashi kin gani Wajen ZAINAZAIN..! laila ta Jinjina kai Tana Fadin"Kwarai kuwa na Shaida wannan kaunar Daga Allah ce.."Dariya suka Saki Lokaci daya kafin su Fara Tafiya Tare Hannayensu na Cikin na juna suna mgana Sama sama Wanda duk wanda ya gansu zai Fahimci Suna da kyakyawan alaqa akwancensu.

Cafteria suka je suka Sha Lemo da Snacks kafin su Wuce Class sai 1pm suka Fito Daga lectures Daganan Halima tayi ma Laila Tayi Zuwa Gidan Umma bata yi musu ba Ta Bita ammh Bayan ta Kira mamarta Ta gayamata Suna zuwa Gidan Umma su Saudart suka Fara Ihun Murnan ga Anty Halima ga Anty Halima Tun kafin ma Tagama Daidaita parking Dayake suna Haraban Gidan ne sai ga Zainab ta Fito suka Rumgume juna cikin Ladabi Take gaida Laila wacce Darajan Halima yasa Duka yaran ke Kiranta Anty Laila.

Bude Bayan Mota tayi ta Dauko Cake din suka Dunguma Cikin Gida Da Umma suka Fara cin karo Halima Tatafi gareta ta Rumgumeta Tana Fadin Tayi Kewarta Itama Rumgumetan Tayi Tana Fadin Itama Tayi kewarta Nene na gefe Tana Fadin Ayi dai mugani Umma tace anyi kuma Sun gani Laila na gefe Tana Dariya Cike da Sha"awan wannan ahalin Kafin Halima ta saki Umma Taje ta Rumgume Nene tana gaisheta ta Shafa kanta tana saka mata albarka Laila ta gaishesu suka amsa Cikin Sakin Fuska Suna Tambayanta karatu Daganan zainab Ta Shiga nuna ma Halima da Laila Vidio da sukayi ma Su Umma da Safe Lokacin da Zain yake yanka Cake sai da suka gama gani Halima tace kowa yazo suyi nasu Shagali Yanka Cake din akayi kowa yaci Halima Ta Diba Dayawa tace Na Alhaji Tsoho ne da Hajiya Mama su Umma nata Dariya Sallah sukayi sukaci Abinci kana Laila Tayi musu Sallama Tatafi Gida Saboda Mamarta zata Fita tace ta Dawo Da wuri Tunda kannenta Duk kanana ne suna Makaranta Gidan ba kowa.

Sai da Halima Tayi La"asar kana Ta bar gidan Shima Firstlove ya Kirata yace ta koma Gida Hakanan Daganan Gidan Alhaji Tsoho ta Biya ta gaishesu Shi da Hajiya Mama da Tabawa ta kuma basu nasu Cake din Hajiya Mama naci Tana Fadin"Shidai Zanullahi dan gata ne..Kowacce Shekara sai munci wannan Abun mai Dan karen Dadi da Sunan wai Bazday dinsa..!
Chapter 19 · 0% Book details