← Book details Zainazain Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 78

Sashe 53

Zainazain Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ka cutaar damu zain ka Cutar da zuciyar Uwa Wacce ta Sadaukar da komai saboda Kai kuma ka Cutar da zuciyar da Uwar data fi kowa sonka"
Haka Take ta Fada Tana kuka Wurjajam kukan Daya Dade aranta Bata samu Fitar Dashi ba,Ta Dade tana wannan kukan kafin ta Share Hawayenta,wanka Tayi kana ta Dauro alwala Jin ana Kiran sallar Mangariba Bayan ta Fito ta Sauya kaya Tayi Sallah,Sai ta Fita Zuwa Dakin Zaina ta Sameta Tana sallah Tana kuka Zainab Bata Dakin Fita kawai Tayi Daga Dakin Ta Leka Dakin Zareena nan Taga su Junior da Saudart da Jalal suka taso suna mata oyoyo kansu Ta Shafa Tana Dan sakin Mirmishi Saboda su yasa ta Shiga Cikin Dakin Tana kallon Zareena wacce ke Sanya ma Umma karama kaya Inaga wanka Tayi mata Zareenan ne ta Dago Tana gaida Umma ta amsa Cikin sanyin Murya kafin tace"Yaushe zaku koma ne..?

Itama Zareenan Cikin sanyinta Tace"Umma wata Daya zamu yi...Ammh Sati mai zuwa zan Je katsina Bikin Diyar kanwar Baban Jalal..Shima din ma yanzu muka gama waya Ranar Jumma"a zai zo ya Daukemu sai an gama Biki sai mu dawo kafin mu Wuce..''Kai Umma ta kada Tana Fadin"Ah akwai ma Sauran Lokaci Allah ya kaimu da rai da lafiya..,"Tafada Lokaci Daya Tana Dukawa tana ma Umma karama waasa da kallon Tsausayi Zareena tabi Umma Dashi Domin Taga alaman Tayi kuka ga Idanuwanta nan sun kumbura
Kafin ta samu Zarafin mgana Umma Ta Dago Tana Fadin"Ki daina Saka mata kayan Sanyin nan Haka zareena garin akwai zafi zafi kuma ki Rage wannan A.C kar ya Cutar da ita.."Mirmishi Zareena Tayi kafin Tace"Umma ai ta saba..Tun muna U.S Da A.C muke kwana Da Farko ma na Fara Fada Abbanta yace gwara na barta ta saba Tunda dashi zata Rayu..Da Farko ni ban saba ba Har nazo na saba Hakama Jalal Babansa Daman ya saba ya
kwana Cikin sanyi ya Tashi Cikin Sanyi..'Umma tace"Ni Daman Baku nake ji ba..Takwarata nake ji kar Sanyi ya kamata atoh.."
Zareena Tace"Itama ta saba Umma."Umma tace"Ta sabi me..?

Kudai yaran zamani masu Jegon yan gayu kawai.."Sai ga Zareena na Dariya itama Umman Dariyan Tayi Nene ce ta Dago Labulen Dakin Ta Shigo Tana Fadin"Dariyan me nake ta Jiyowa..?Umma ta kai Dubanta ga Nene Tana Fadin"Ni da Diyata ce..Kuma sai kowa yaji..?

Nene ta Tabe baki Tana Fadin"Naje Dakin ki ne Daman baki Ciki...Alhaji ne baya Jin Dadi Sai da yasha panadol.."Atare Umma da Zareena suka ce"Subhanallah..Allah ya sauwake..!Bari naje na Dubashi..'
Umma ta Nufi Hanyar Fita Zareena ta Dauki Umma karama ta mika ma Saudart Tana Fadin"Umma bari na biki na Duba Abba.."Umma batace komai ba Suka Rankaya suka Fita Harda Nene bayan ta tsaya ta gyara ma Saudart Rikon Umma karama sun Fito Falon kenan Sai ga Sadiq ya Fito Daga Dakinsa Kallonsa Nene Tayi ganin baida Walwala tace"Kaci Abinci..?

Kai kawai ya Girgiza mata yana Zama daya Daga Cikin kujerun Falon,Umma ta kalleshi ganin bai da wani walwala tace"Akwai abincin agidan ne..?

Nene tace"Eh Nace Zainab Ta shiga Kitchen ta Girka ko Macaroni Da kifi ne.."Kai kawai Umma Ta kada ta wuce zuwa Dakin Abba Nene ta mara mata Baya Zareena ce ta Tsaya Tana gayama Sadiq Abba baya jin Dadin Jin haka yasa ya mike Shima ya mara musu baya Shi da Zareena.

Ko da suka Shiga Sun iske Umma da Nene duk sun sakashi a Tsakiya,Suna Faman mai sannu Da kai kawai yake amsawa Domin Shi kadai yasan Halin da Zuciyarsa ke Ciki Shigowar Zareena da Sadiq ne yasa ya Bude Idanuwansa yana Kallonsu Gabansa suka Karisa Dukkansu suka Rankwafa suka gaisheshi suna mai Sannu Mirmishi Abba yayi yana Riko Hannun Sadiq lokaci Daya yana Fadin"Babana yaushe zaka koma ne..?ko dogon Hutu ka samu ne..?

Cikin Ladabi Sadiq yace"Gobe zan koma Abba..Dama na samu Break ne na leko ku sauran wattani kadan ne na kammallah sai Defence.."Abba ya Jinjina kai yana Fadin"Allah ya Taimaka..Allah ya tsaremin ku aduk inda kuke.."Ya fada Cikim karaya Dukkansu suka amsa da Ameen Harda Iyayen Kallonsa ya maida kan Zareena yana Fadin"Diyar fatima ina Amaryata na ganki ke Kadai..?

Zareena Tace"Tana Daki waje su Saudart Abba..Zan kawo maka ita sai ka ji sauki.."Kai ya kada yana Fadin"ki yi sauri ki koma kada Su Kada ita...Ina abokina Jalal ban ji Duriyansa ba..?

Zareena Tace"Duk suna chan Tare dasu Junior.."Abba yace"Ok..Ina megidanki..?

Kunsamu DogonHutu kenan..?

Kafin Zarreena Tayi mgana Umma tayi saurin cewa"Eh wajen Wata daya zasu yi..Sati dai mai zuwa tace Jawaad din zai zo ya Dauketa Su Tafi katsina Bikin Diyar yayar shi Mijin nata..'Abba ya Jinjina kai yana Fadin"Yayi kyau..Dukkanku Allah ya yi muku albarka Ina Zainab ina Halimatu har yanzu bata bar kukan ba ko..?

Cikin Tsausayawa Zareena Tace"Ameen Abba...Bata bari ba Abun dai yayi sauki ammh bata mgana Sai dai in ita da Umma ne.."Abba ya koma ya kwanta Yana Fadin"Fatima ki kula da ita..In Zazzabin nata yaki sauka kuje asibiti adubata..!

Umma tace"Taji sauki..Sai dai yawan kukan ne..Yanzu hakama Tana Sallah na sameta Tana kuka Zainab kuma Tana Kitchen.."Lumshe ido Abba yayi yana Fadin"Ina Tsoron wani Abu..Ina Tsoron Yarinyar nan takamu da wani Ciwo sanadin Yaron nan Basan da wani ido zan kalli ahalinta ba..!

Nene ta kada kai Tana Fadin"Sai Hakuri..Insha Allahu babu Abunda zai Faru....Zata warware Insha Allahu.."Mirmishin Takaichi Abba ya saki kafin yace"Allah yasa..Ku barni zan kwanta ko Ciwon kan zai sauka..!

Dukkansu suka mike suna mai Sannu Ya"yan ne kan gaba sai iyayen Sai da suka Fita kana Abba ya Juya yana Share kwallar Data Silalo mai ta Bayan Kunnuwansa,Dama Dalilin Daya sa yace su bashi waje kenan kar suga Rauninsa ammh Tabbas wannan Al"amarin ya Girgiza shi Shi Usman Ne za"a samu Daga Cikin ya"yansa wanda ya ijiye karuwa Har da Sakamakon Cikin Shege..?

Wannan Abun in ya Tuna sai yaji kunyar Duniya ta kamashi Ko Yan"uwansa ma Baya son Hada Ido da su saboda wannan Abun kunyar da ZAIN ya aikata.

Ya samu Barci sai Wajen 10pm na Dare ya Tashi yayi wanka Ciwin kan ya sauka sai dai Nauyin Kirjin Bayan yayi wanka yayi sallar Isha"i Umma ta kawomai abinci yaci Ita kuma Nene ta gyaramai Shinfidar,Mganin ya kara Sha ya koma ya kwanta Umma Ta Tafi Dakin zaina ta bar Nene zata kwana da Abba.

Dakyar da Lallashi Umma ta Lallashi Zaina taci macaronin nan Shima ba wani mai yawa ba ba Dadewa ta amayar Dashi Umma ta Fara Shiga Damuwa ganin kwana Daya Rak zaina Duk ta Fada kamar ba ita ba Idanuwana sun kumbura sun yi Luhu Luhu Sun kuma Fada Gabadaya Jikinta ba karfi saboda Rashin Cin Abinci,Ko Taci sai ta amayar dashi kuma taki yarda azo adubata ko kuma suje asibiti kada wata Cutar ta kamata.

Kamata Tayi suka Shiga Tiolet ta wanke mata baki kana ta Dawo da ita kan gado ta kwantar da ita Ta koma ta gyara Wajen Da tayi aman kana ta koma Kitchen ta Tsiyayo Ruwa a Fulas na zafi Ta Hada mata Tea Shima Din Sai da Tayi mata jan Ido kana Tasha kadan Kafin ta kauda kai Cikin Bacin Rai Umma ke kallonta Tana Fadin"Meyasa kike son kashe kanki Saboda wanda bai damu Dake ba..?

Ke sakaryan ina ne..?

Kalli yadda kika Rame Cikin kwana Daya..?

Kina so ki kashe kanki ne..?

Girgiza ma Umma kawai takeyi takasa mgana sai Hawaye Dakyar Tace"Umma Bazan iya cin komai bane..Ko naci sai nayi amai,Umma kirjina da Zuciyata Ko"ina Ciwo suke ni nafi son ma na Mutu Umma da in zauna wannan Dacin Da nake ji acikin Zuciyata yayii ajalina"Gam!

Umma ta make mata Baki Cikin Fushi Take fadin"Shi bai mutu saboda Abunda ya aikata ba ke zaki Mutu..?

Kul kar nakara jin wannan mganar Ki Fitar da Abunda ke Ranki ki Maida komai ba komai hakan bashi ne Karshen Rayuwarki ba Indai ina Numfashi sai Zain ya sake ki ki samu wani mai Nagartan ki aura Kicigaba da Rayuwarki Shi kuma yaje chan ya karata da Dadiron tasa da kuma Dan Shegen Da zata Haifa masa Tunda Haka ya zaba..!

Cikin Rauni da kuma wani Tsausayi Zaina tace"Umma kema baki yafe ma Firstlove ba..?

Hararanta Umma Tayi tana mika Kofin Shayin Take fadin"Bana son na kara jin wata mgana Daya Dangance sa..Karbi ki Shanyeshi Duka ki bani Kofin kafin na Saba miki.."Umma ta Fada Fuskarta ba alamun wasa Dole Zaina ta karba ta kafa kai Duk da Bakinta kamar Madaci Haka Takeji ammh Saboda Ran Umma ya baci yasa ta shanye ta mika ma Umma Kofin Ta karba Tana Fadin"Ko ke fa..?

Karki kwanta Tashi kisha Mgani naji kamar zazzabin ya Dawo..?

Da Toh kawai ta amsa Umma ta ballo mata panadol Ta mikamata Hade da Ruwa tasha Ta koma ta kwanta Tana Sauke Numfashi,Umma ta gyara mata kwanciya kana ta Fice zuwa Kitchen ta maida komai,Zareena ta kwanta Zainab ma Haka suna gama cin Abinci kowa ya nemi makwanci,Shiyasa ta koma Dakin Zaina din Ta Shimfida Bargo nan kasa Ta kwanta Bayan ta Rage Hasken Dakin Duk Zaina na kallonta Wacce ke ta Sharan kwallah bata so Kukanta ya Fito Umma Taji ta.

Washegari kuma Kafin Inna Hannatu ta wuce tazo ta Duba Abba Tunda Nene ta Kira Alhaji Tsoho Ta gayamai Abba bayajin Dadi yau ma bai fita aiki ba,Sai da Sadiq yaje yazo da Dr Imran Ya Dubashi Jininsa ne ya Hau yamai alluran barci Da kuma mganguna,Tunda Sadiq din yana ta Kiran Haddir bai Daga ba Sai daga baya ya Kirashi yace mai yana Gidan zain ne achan ya kwana Cikin Tsausayawa Sadiq yace"Ya Haddir ya Jikin Ya zain din..?
Chapter 53 · 0% Book details