← Book details Zainazain Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 78

Sashe 10

Zainazain Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dr.Saulawa Mutam ne nagari kuma Mai Daraja acikin Idanun Mutane da suka sansu su kuma San Labarinsa,Game da ma"aikatan Gidansa Shi mai Kirki game da Likitocin Dake aiki Dashi asibiti Mai kirki ne kama Daga ma"ikatan lafiya zuwa masu matsayin Aikin Share Share da goge goge da kuma Masu kula da Shige Da Fice Duka Sun Shaida Dr Saulawa mai Kima ne Haka game da patient dinsa zakayi mamakin ganin yadda yake Tafiyar dasu ba kyama ba wani Girman kai Zai koma Kamrsu Suma Ya Shiga Cikinsu Domin mema musu lafiya Shiyasa Lokacin kalilan indai Haukan naka bq Tuburan bane Dr Saulawa zai Taimaka wajen Dawowa Dakai Cikin Hayyacinsa awannan Fanni Shi kwararre ne kuma Haziki ne.

Dr.Saulawa yana da Wani Megadi Wanda yake gadin Gidansa Mai Suna Mallam Umar
Gada Wanda Dan asalinsa Haifaffan Garin Gada ne Dake Jahar ta Sokkoton Shehu,Talauci da kuma neman kudi ya barosa da Garinsa da ya"yansa zuwa Garin Bauchi yayi gadi a gidajen masu kudi Dadama da yan Siyasa bai ji Dadi ba Sai da Allah ya Hadashi da Likitan kwarai likitan Takalawa Wato Dr.Abubakar Bashir Saulawa Ya Bugeshi da Mota Lokacin yana Kokarin Komawa garinsu ne wajen iyalansa Abun ya Faru,Dr Saulawa ya Dinga Kula da Mallam Umar a asibitinsa Duk da bai wani ji Rauni ba Karaya ce da Gocewar kashi,Dashi da matarsa Hajiya Amina Wacce Mijinta da ya"yanta ke Kiranta Hajiya Mama Sunsha Dawainiya Dashi Bayan an sallameshi Dr.Saulawa da Matarsa Suka Dauki Mallam Umar har garin gada suka sadashi da Danginsa da Iyalansa.

Wannan Abun Da yayi ma Mallam Umar Shi ya karamai kima adanuwansa da kuma na Danginsa dana iyalansa Bakinsa ya Dinga Fadin Alherin Dakta Garesu,domin Da suka maidosa Gida bai barsu Haka ba sai da yayi musu Sha Tara na arziki balle ganinsu Cikin Halin Talauci da Wahalan Rayuwa Abun bai Tssya nan ba kowani Lokaci in Dr Saulawa ya samu lokaci zai zo ya Duba Jikin Mallam Umar kuma baya zuwa Hannu Rabbana kafin Mallam Umar ya warke yaga karammawa da kuma Karancin Irin na Likitan Mai Hangen nesa da Taimakon Takalawa ba Shi kadai ba yan"uwansa ma Suna yaban Hallin kirki irin na Dr Saulawa da matarsa.

Bayan Mallam Umar ya Warke sai Dr.Saulawa yazo ya zauna Dashi anan ne ya Fahimci ba wata kwakwaran Sa"ana da kuma Dalilin Daya kaishi Garin Bauchi Jin Haka yasa sai Dr Saulawa yace in bazai Damu ba yazo Gidansa ya Zauna Shida iyalansa Da matarsa Allah barshi sai ya Dinga Mishi gadi matarsa kuma ta Rika Shiga Tana Taimakama Amina Tunda Bai yi karatun Boko ba Ballatana ya Taimakamai ta wani Fannin.

Wannan Albishir din yafi komai yima Mallam Umar Dadi Yan"uwansa ma Sun Tayashi Murna,cikin Abunda bai fi Sati Daya ba Dr.Saulawa ya Turo Mota aka kwasheshi Shida Matarsa Atine da kuma Dansa kwara Daya Daya mallaka Abdullahi Zuwa Bauchi Gidan Dr.Saulawa aka kuma Saukesu a Shashin Boysquaters Inda Aka Jikasu da komai na Bukatan Rayuwa Mallam Umar da Matarsa Atine suna kuka suna ma Dr Saulawa Godiya na Irin karamcinsu garesu shi kuma yana Fadin karsu Damu.

Mallam Umar shi ya Cigaba da gadin Gidan Dr.Saulawa awanchan Lokacin bayan ya sallami megadinsa Dama Buzu ne, zai koma garinsu,Cikin Jin Dadi da kuma Cigaban Rayuwa ita kuma Atine ta zama yar gida Tunda Ta zama yar Dakin Hajiya Amina kusan a Shashensu Take wuni Abdullahi kuma anyi anyk a sakashi makaranta Boko yaki wai karatun allo yake so ganin Haka yasa mallam Umar ya Tattarasa ya maida gada inda chan aka kaishi argungu yana Makarantar allon Dayace Ita yake so.
********
*Bayan Shekaru Biyar..!*
Abubuwa Dadama sun Faru Cikin Gudun wannan Shekarun Ciki kuwa Harda kamallah Duka karatun Ya"yan Dr.Saulawa Duka Zaratan mazan nasu Wadanda Dukkansu suke da Qualification din Masters dinsu
Wato Bashir ne Babba wanda ya Samu aiki agarin kaduna A Refenaring,sai Usman Wanda Ke Bimasa Wanda Shi ya samu aiki a anan garin Bauchi a wata ma"ikata Inda Suke Wallafa Littafan karatun na makarantu Dabam Dabam a matsayin Manajansu sai Karamin su Aliyu Wanda Shine Lauya Mai zaman kansa.

Dukkansu sun yi Aure Sai Dai Aliyu ya Rigasu yin Aure da Matarsa Safiya,suna Zaune agarin Abuja,Sai Usman Wanda Dr.Saulawa ya Aurama Mata Biyu arana Daya Wato Fatima da Aisha kuma Dukkansu yan garin Bauchi ne Wadanda Dr.Saulawa yayi zaman Amana da iyayensu,kuma yaji yana Sha"awar Hada zumunci da ya"yansa da Farko Fatima ce ta Usman Aisha Ta Bashir ce wanda ko kafin Dr.Saulawa ya gabatar da ita ya Riga ya gabatar da matar da zai Aura Iklima Wacce itama yar Kaduna garin gwammace Koda Dr.Saulawa ya Kawo maganar Aisha sai Bashir din ya Nuna Ita Iklima din yake so sai ya kyaleshi Ganin ya Riga kuma ya Furtamai iyayen Ita Aisha sai ya Nemi Usman din Daya Hadasu Duka Biyun ya aura bai yi gaddama ba ya amince Dr.Saulawa ya Aura masa Fatima da Aisha Arana Daya Bashir kuma sai bayan Shakara Daya da wani Abu da Auran Usman kana yayi Auransa Tunda Daman Shi Duk yafi su akidan Boko ita kanta Ikliman yar Boko ce Tunda itama ma"ikaciyar gwamnatice.

Usman yana Zaune nan GRA inda ya Gina Gidansa kusa da iyayensa Tunda Shi kadai ne ke Zaune garin Bauchi sai yaga gwara ya zauna kusa da iyayensa Tunda Shi kanshi babu wasu Dangi Duk Sun kare ammh Har yau bai manta da garin katsina ba yana zuwa kuma Hannunsa na kaiwa nan yake Zaune Shi da Matansa Tamkar Tagwaye Wato Fatima da Aisha.

Ayayinda Bashir ke garim kaduna Shima ya mallaki gidan Kansa da Motar Hawa haka ma Matarsa nada Motarta Sai Aliyu Barrister kenan yana Zaune agarin Abuja Shida matarsa Safiya Suna Zaune a Maitama Abuja Shima Din ya mallaki gidan kanshi Da Motar Hawa Rayuwa Dai ta inga Su Rukayyah kuwa da Hannatu kowacce Tana Gidan Mijinta ta Haiyayyafa Suna kuma Cikin Jin Dadi sai wanda ya gani.

Dr.Abubakar Saulawa ya Samu Duka Cikar Burinsa Shiyasa Shekara na Zagayowa ya Tattara Duka iyalansa da matansu sukaje kasa mai Tsarki suka Sauke Farali,Shi dai Dr Saulawa da Hajiya mama Gida suka Dawo Ammh Su Bashir Kowanne kasar Dayake Muradi ya Wuce Shi da iyalansa Haka ma Su Rukayyah kowacce da Mijinta da ya"yanta Tun a Saudiya sukayi sallama da Junansu kowanne ya yada Zango a Inda ya Tsara zashi Su dai su Rukayyah da Hannatu da Mazajensu sun koma Gida da Wuri ammh Su Usman kam sai da Dr.Saulawa ya Dinga Musu waya yana Fadin Sun bar ayyukansu sun je wani kasa Sun Tare,Maza su Tarkato su Dawo wannan Dalilin yasa suka Tattaro Suka Dawo Kasar su ta Haihuwa kowanne na amsa Sunan Alhaji matansu ma na amsa Sunan Hajiya.

Duk acikinsu Matan Usman ne suka Fara samun Ciki Wato Fatima da Aisha kuma duk atare,Murnan wajen wannan Ahali ba"a mgana barin ma Dr.Saulawa Farinciki ya Cikashi zai Fara samun Jikoki,samuwar Cikinsu da Wata Biyar sai ga Wani albishir din Safiya ma Matar Barrister Aliyu itama ta Harbu Sai Farincikin ya ninku,Bashir dai Shuru Dama Shi yace Tsarin iyali zasu yi ba yanzu zasu Fara Haihuwa ba sai zuwa gaba koma sun Fara 3 Childeeen ya Ishesu.

Samuwar Cikin Fatima da Aisha Sai kuma Lalura ta karu gasu dama su kadai agidan ba yar aiki Tunda Tun Farko sun Nuna basu bukatar Wata yar aiki su Zasu Dinga aikinsu da kansu,sai kuma ga Samuwar Cikinsu Lokaci Daya kuma Dukkansu Suna Fama da lailayi sai Hankali Alhaji Usman ya Tashi kwarai yaje ma da Hajiya mama da Batun Samun mai Taimaka ma su Fatima kafin komai ya Daidaita ita kuma sai ta gayama Dr.Saulawa Batun Shi kuma sai yace Abun bana gaggawa bane gwara a tsaya a samu mai amana Tunda zata zauna da iyalansa ne.

Da wannan Mganar Alhaji Usman ya bar komai a Hannun Dr.Saulawa Da Hajiya Mama kwatsam Atine taji Hajiya Maman na Zencen sai tayi karaf tace In suna so ga Matar Dansu Abdullahi wanda yayi Aure Shekaru Uku da suka gabata ya Gaba Karatun allo ya koma Gada ya Fara Sa"anan sai da kayan Dinki Wanda Dr.Saulawan ne ya Tankamai Jali Tunda yaki Karatu kuma Har yau har gobe akwai amana Tsakaninsa da Mallam Umar da iyalansa Atine kuma ta zama kamar yar gida.

Wannan Mganar ta Atine Hajiya Mama ta kaima Dr.Saulawa Shi kuma yayi Na"am acewar Iyalan Mallam Umar Abun so ne Takalawa ne masu Wadatar Zucci da Dr.Saulawa ya Tuntubi Mallam Umar gada da mganar sai yaso yamusa saboda yace Kada Maryama Tayi Nesa da Mijinta Jin haka yasa Dr.Saulawa yace kada ya Damu Duka da Maryama da Abdullahin Zasu dawo nan gidan Usman da zama kamar yadda shi da atine suke zaume agidansa Dama yaji Usman Din na neman mai kula mai da Kifayen Dayake Kiwo Faduwa tazo Daidai da zama Mallam Umar Bai iya mgana ba,sai Godiya kamar yayi kuka na Karamcin Dr.Saulawa agaresu.

Koda Dr.Saulawa ya Tuntubi Usman da mganar bai yi gaddama ba Saboda Baba Atine kamar Wata Babba yaya Suka Dauketa Shi kanshi Mallam Umar ba"a Matsayin Megadi suke kallonsa ba Suna Kallonsa ne Kamar kanin Mahaifinsu Baba Umaru ma Suke Kiranshi Batare da bata Lokaci ba Dr Saulawa y
a Saka Mallam Umar ya Kiramai Abdullahi sukayi mgana Dayaji labari murna ta Cikashi Dama Tun bayan da yagama Almajirancinsa ya Dawo Bayan yayi Sauka ya Dinga Nadamar kin karatun Boko da yayi Tunda ya Fahimci yanzu Rayuwat bata Tafiya sai da Duka Fuka fukan Biyu gashi kuma Lokaci ya kuremai Dole dai Kanwar naki ya zauna chan Babban Gidansu a Gada ya Auri Wata yar"uwansa Maryama Bayan Dr.Saulawa ya Tankamai Jali ya Fara Sana"an kayan Miyan Jin wannan Rokon alfarman ta Dr Saulawa Sai Abdullahi yaji kamar an sakashi a aljannah ko kwana Uku basu yi ba ya Tattaro maryama Zuwa Bauchi bayan yayi sallama da Yan"uwansa ita kuma maryama Tayi sallama da yar"uwanta kwara Daya Tal aduniya wato Halima wacce ke Aure a nan garin Gada.
Chapter 10 · 0% Book details