← Book details Zainazain Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 78

Sashe 58

Zainazain Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Alhaji Tsoho yace"In ta Haihu ita kuma Bulala 80 za"ayi mata Tunda ita batayi Aure ba.."Hajiya mama Tayi Tagumi Tana Fadin"Ba wacce nake jin Tssusayinta Har Raina sai Yarinyarnan Halima Dazu mukayi mgana da Fatima Take Fadamin komai taci sai Ta Dawo dashi kwana Take kuka Ga Rashin Barci..'
Alhaji Tsoho ya kada kai yana Fadin"Nima Wlh Aminatu..Kamar kin Shiga Raina da Yarinyar nan marainiyar Allah nake kwana ina Tashi..Ina Fatan Allah yasa ya zame mata kaffara.."Gabadayansu suka amsa da Ameen,Kafin Alhaji Tsoho yace"Mganar da Hadiru yazo min da ita kenan kam in saka Baki Takoma Gidan Mijinta Shima yana chan kwance ba lafiya Hadirun ma ke Kwana chan yana Kula Dashi..".

Hajiya Mama tace"Oh ni Amina...Allah ya kyauta na gaba..Me kace kan mganar..?

Alhaji Tsoho ya sauke Numfashi yana Fadin"Me kuwa zan ce..?

Bazai yuyu Ta koma yanzu ba saboda Halin Datake Ciki Gwara ta zauna anan Uwarta na Kula da ita
Zuwa akara kwana Biyu ni dakaina zan saka Fatimar tazo Da ita nan na kara mata Nasiha Da Lallashinta Mganar Usman kuma Shima sai zuwa bayan an kwana Biyu zan mai Mgana kan ya Sausssauta Fushinsa Hakan bai da wani amfani Kai kuma Hadiru in ka koma Wajen Zainullahin in Jikinsa yayi sauki gobe ka kawomin shi nan ina son mgana Dashi.."
Haddir yace"Allah ya kaimu.."Daga Haka ya kalli Hajiya Mama yana Fadin"Me kuka Dafa ne Tsohuwa..?

Cikin Haushi Hajiya Mama tace"Uwarka Safiya ce Tsohuwa don kaniyarka.."Baki ya Rike yana Fadin"Me yayi zafi Kika sako Sunan uwata Gatse haka..?

Karkace kai Hajiya Mama Tayi Tana Fadin"Don ma Bance Aliyu Kai Tsaye ba..?

Baki ya kama yana Mikewa Lokaci Daya yana Fadin"Kirashi mana ai ke kika Haifi Abunki ni miye nawa..? duk Tsiyarki dai baki haifeni balle kice zaki Dakeni Ni kinga ma Tafiyama basai kin ga mutum bama ballatana ki gayamai mgana.."
Yafada yana Bayyana yadda yaji Haushin Kiran sunan Mamarsa Datayi,Alhaji Tsoho na Gefe yana Mirmishi Cikin Tura Haushi Hajiya mama Ta Rakashi Da Fadin"Kwarai na Haifeka kuwa..Tunda na Haifi Uban daya kawoka Duniya kaga kuwa bama Duka ba zanyi sakaka Cikin Daki nayi maka Dukan Tsiya sai na barka kwance.."Ko Tankata bai yi ba ya Fice yana Fadin"Sai kuma kiyi..Ji dai da wannan Rudadden Tsohon Mijin naki.."
Da karfi Tace"Bana ga Rudadde ba..Rudadde ya wuce Ubannanka Bashir ko Aliyu.."Yana Jinta Daga Falo kai ya Girgiza yana Fadin"Gaskiya Tsohon chan ne Daya ce Rigimarki su Baban kaduna suka kwaso.."Abayyane yayi mganar Dakinsa ya Shiga Wanka yayi ya Sauya kaya kana ya Fito Kitchen ya Shiga wajen Tabawa suka gaisa Cikin Sanyin Murya Take Fadin'Ya zainullahi yake ne Hadiru..?

Tura baki yayi yana Fadin"Kai Tabawa..Wai kema Hadirun nan Har dake.."Dariya Tayi Tana Fadin"Eh mana wannan Shine zamu kira namu na Mutan Da..Ko Bakin ku na yan zamani ne Hadiru..'Kai ya Rausayar yana Fadin"Ba wani kuna dai Batamin suna kuma ba kowa yaja ba sai Tsohin chan Da matarsa.."Tabawa Tayi Dariya kawai Haddir yace"Zain yana nan Lafiya..Bai dai jin Dadi ne yanzu ma Shi nazo samar ma wani Abu Allah yasa kinyi Tuwon nan naki mai Dadi Tabawa..'Cikin alhini tace"Allah Sarki..Allah bashi Lafiya Jarabawa ce Allah ya bashi ikon Cinyewa damu gabadaya..!

Haddir ya amsa da Ameen Kafin Tabawa tace"Akwai Tuwon Shinkafa Miyar Danyan kubewa Wanda nayi ma Alhaji Tsoho ne.."Da sauri Haddir yace"Alhamdulillah..Saka mana Cikin Kula nayi gaba Dashi Daman na Dade banci Tuwon ki ba Tabawa.."Tana Dariya tace"Na Dumaman Alhaji Tsoho ne fa ko nayi muku wani ne..?

Da Sauri Haddir yace"No..Samana wannan Tafiya zanyi na bar zain Shi kadai..Yaci yanzu banda Hadama yace harda wani Dumaman Safe..?

In yayi mgana gayamasa Manyan Jikokinsa na Bukata kin basu.."Tabawa na Dariya tace"Shikenan kuwa..!

Saka musu Tuwon Tayi Cikim kula Miyan ma Haka wacce Taji Kashin Rago da manshanu Dauka yayi ya Fice yana mata Godiya Ta Rakashi da Allah kiyaye Hanya da kuma sakon Gaisuwarsa ga Zain ko Dakin Alhaji Tsoho bai kara Lekawa ba Saboda yadda hajiya mama Ta gama bata mishi Rai abayan Motarsa ya Jera komai ka fin ya Shiga ya Tasheta ya Fice Daga Haraban Gidan Bayan Maigadi ya wangalemai get.

Yana Bisa Hanya Dadyn Abuja ya Kirashi sukayi mgana ya kara gayamai Halin da ake Ciki Daddyn Abuja ya Sauke Numfashi yana Fadin"Yanzu muka gama mgana Dashi ya Usman Din..Dama na sako mai nganar Zain din kashe wayarsa yayi ya Riga yayi Fushi Dashi ne sosai na kuma Kira Ya Bashir namai mganar Shima ya nuna Ma Ya Usman din yayi Daidai ne bazai saka baki ba..!

Haddir acikin Ransa yace"Daman ai wannan haka zai ce.."Haryanzu bai manta zafin marin Dayayi mai ba Cikin Damuwa yace"Daddy meye Abun yi Kenan..?

U hv to do Something fa..'Daddyn Abuja yace"Karka Damu...Muna ta Shiryan Shiryan Dawowa nan Bauchi Dukkanmu gabadaya Har sai an gama Bikin Kanwarka Hamdiya kafin mu koma Insha Allahu i will Tary may Best naga komai ya Daidata kaji ko..?

Ajiyar rai Haddir ya Sauke Kafin yace'"I Truth u Daddy...."Daddyn Abuja yace"Tanque Son..Ina zain din bani shi a waya nayi mgana Dashi..?Haddir yace"Yana Gidansa yanzu haka ina kan Hanyata ta zuwa ne naje na Karbomai Tuwo Gidan Alhaji Tsoho..'"Jinjina kai Daddyn Abuja yayi kafin yace"Alrigh in ka isa Call me Ina son nayi mgana Dashi.."Haddir yace"Ok Daddy..Ka gaida Mom..!

Daga Haka suka yanke Kiran Shi kuma Haddir ya Cigaba da Driving Dinsa Bai jima ba ya isa Gidan yaji Dadin ganin Zain yaji Sauki Har ya sake yin wanka ya Fito Falo Har ya Shiga Kitchen ya Dafa Ruwan Coffea,Haddir ya Nuna Jin Dadinsa Sosai ganin Zain din ya Taahi da kafarsa ba kamar kwana Biyu nan Dayake Wuni Kwance ba Tare sukaci Tuwon Suna santi kafin Haddir ya maida Sauran ya saka Cikin Fridge,Shima irin na Alhaji Tsoho zai yi Dumame kenan Bayan ya wanko Hannu ne ya Dawo ya Kira Dadyn Abuja yabama Zain sukayi mgana Sun Dade yana ta Fada Cikin Hikima da Salama yana kuma Nuna mai Kuskusaransa kana ya bashi Tabbacin zai zo Bauchi bazai koma ba sai komai ya Daidaita Zain nata Godiya yana kuka kafin Wayar nasu ta kare sai alokacin ne Haddir ke Fadamai Sakon Alhaji Tsoho Duk da Zain yaso yaji me ya Faru Dayaje Tahowa da Firstlove..?

Ammh sai yaki gayamai komai Illah cemai Da yayi Zareena da Nene na Gaisheshi Cikin mamaki yace"Ashe Har yanzu suna Sona..?

Dariya Haddir yayi yana Fadin"Ai ba"a sauya ka ba..Kanan nan amatsayin Yaya Daktan ka.."Sai da Zain ya Murmusa da kalaman Haddir Cikin Sanyin murya yace"Ya jikin Abba..?

Haddir yace"Yaji Sauki Shima.."Daga haka ya yanke mganar ya Dauko wayarsa ya Fara Latsawa Shi kuma Zain ya koma ya Jingina da Kujera ya Fada Zurfin Tunani yana so ya Tambayeshi Zaina kuma sai ya kasa Domin baya so yaji wani Labari mara Dadi akanta,Shiyasa yayi Shuru da bakinsa Ammh Abun nacin Ransa da Zuciyarsa..
*****
Washegari kuma Tun Wajen karfe 10am na Safe Zareena da Zainab da Little Umma da Jalal suka zo Gidan Zain sun iskeshi Shi kadai Haddir baya nan ya Fita Zuwa Cikin asibiti,Yaji Dadi da kuma mamakin ganinsu Domin bai taba tsammanin Wani Daga Ahalinsa zai zo Dubashi ba Karban Little Umma yayi yana Kallon Zareena yana Fadin"Ammh Abba bai san kun zo ba ko..?

Kai ta gyada mai Tana Fadin"Bai sani ba..Gidan Alhaji Tsoho nace zani..Umma ma bata sani ba Nene ce kadai ta sani tace na Gaisheka kwarai ita tabamu ma wannan Ferfesun Kayan Cikin Tace mu kawo maka.."Idanuwansa suka Ciko da kwallah yabi kulan Dake Hannun zainab da kallo kafin yace"Allah Sarki Neneta..Na Saka Zuciyarta Ta Raunana saboda ni..Allah na Tuba Allah ka yafemin.."Suma cikin Tsausayawa sukace Ameen Jalal ne ya Hau gadon yana Fadin"Uncle baka da lafiya ne..?

Kumatunsa ya Shafa yana Fadin'"Eh Sojan Jaawad...Ina Babanka.?

Zareena ne tace"Yana katsina ya samu Hutu ne...Daman kuma akwai Bikin Diyar yayarsa Jibi ma zai zo yaDaukemu mu Tafi Chan Family House dinsu sai an gama Biki zamu dawo insha Allahu.."Yana Mika mata little Umma yana Fadin"Allah ya kaimu ya kuma kaiku lafiya.."
Ta amsa da Ameen Shuru ya Biyo Baya Kafin ya Dago yana Fadin"Ya Firstlove take..?

Tabar yin kukan...?

Zareena tace"Tadai Sauki kam..Nadai jita dazu ita da Umma Tana ta yi mata Fada kamar zata Dageta kan Kukan Da takeyi..'Cikin karaya da wani Irin Soyayyarta Dake Cikin Zuciyarta yace"Bazan iya kwana ban je na ganta ba.."Da Sauri Zareena tace"Ya zakayi da Abba..?

Umma ma bazata barka ka ganta ba Domin Jiya marin Aboki Haddir ne kadai batayi ba kan yace yazo Tafiya da ita.."
Ido ya sakarmata yana Fadin"I know.."Yafada Cikin wata Murya Kamar yayi kuka kafin yace"Zan je koda zai Koreni ne..Zan je na Duka na Bashi Hakuri..Shi da Umma na kuma Dukama Firstlove na kuma Roketa Data Yafemim.."Zareena Tace"Shikenan ammh karka kaje kai Kadai..Ku Tafi Tare da Aboki Haddir.."
Kai ya gyada mata yana Fadin"Eh Tare zamu..Yanzu ma Shi nake jira zamu je gidan Alhaji Tsoho yace yana son ganina Ko bama Haka ba ni da kaina Zani Shima na Rokeshi Gafaran Abunda na aikata da kuma Kuncin dana sakasu Shi da Hajiya Mama..'Cikin Sanyin Murya Zareena tace"Ya kamata..Allah daidaita komai.."
Ya amsa da Ameen basu wani Dade ba suka wuce Zasu Biya School su kai Zainab Da Zareena Ta Fadamai haka ne ya Kalli Zainab yana Fadin"Zee Kun Fara Test ne...?

Kai ta Girgiza mai kafin tace"Bamu Fara ba mu..Ammh wasu Duk sun Fara Yaya Dakta ina Jin ma Harda su Anty Zaina Domin na Hadu da kawarta Anty Laila take cemin yanzu zasu Shiga Test ne.."
Cikin Karfin Gwiwa yace"Dole zan je na Roki Firstlove gafara..Na Dawo da ita Gida ta koma makaranta bazan yi Sanadiyar Ruguza Burinta nayin karatu mai Zurfi ba.
******
Su Zareena basu kai awa da Tafiya ba sai ga Haddir ya Dawo Daman Zain ya Riga ya Shirya Cikin Riga da wando na Wata Blue Din Shadda Fitowa kawai yayi suka Wuce,Suna Hanya ne Haddir ya juyo yana kallonsa yadda Duk yayi Zuru Zuru ga Kasumba Tayi mai yawa Cikin Damuwa yace"Ko zamu Biya Shagon aski ne ka Rage wannan Gashin..?
Chapter 58 · 0% Book details