← Book details Zainazain Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 73 OF 78

Sashe 73

Zainazain Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dakin Umma Su Zafeera suke Hamdiya kuma da gayyarta suna Dakin Nene Zaina sai da ta bari duk sun yi wanka sun yi Shirin kwanciya kana ta Zare Jiki ta Shiga Tiolet din,chan ta samu Damar yin kukanta ya Isheta da kuma Tunanin mafita Ta Dade kafin Ta yanke Shawara da kuma Hukunci Duk da Abun Da zata aikata bazai ma kowa Dadi ba ammh Shine mafitan Cikinta da kuma Auranta Uwa uba ta Gujema ganin Auran Firstlove dinta da Wata mace irin Dina...!
*Janafty...*
*ZAINAZAIN..!*
_(Is a love Story and Betrayal)_
*Wattpad:Jamilaumar351*
*Mallakar:Janaftyshakira*
*BOOK 1*
Sai da Ta Tabbatar da kowa yayi Barci kana tayi wanka ta Dauro alwala Ta Fito Daga cikin Bayin Sadaf Sadaf ta iske su Zafeera sun kwanta Duk sunyi Barci Alamun gajiya nan Taga Hamdiya Amarya Itama Ta baro chan Dakin tazo ne ta kwanta Saman Cafet barci ya kwasheta Saboda Gajiya.

A hankali Ta Dauki Hijabinta Ta Zura Bayan Tunda a Tiolet din Ta maido Doguwar Rigar Abayan Dake Jikinta,Ta shinfida Darduma Ta Tada sallah Bayan Ta Idar ta Dade Tana addu"a Lokaci Daya Taji Natsuwa ya sameta,na game da Abunda Take Shirin aikatawa,Batare da wani Dogon Tunani ba Ta Mike Tanayin komai ahankali Saboda Kar Zirga Zirganta ya Tada Wata Daga Cikinsu.

Side Drower din Umma Ta Bude ta Dauko Littafi da Biron Umma wanda Take Rubuta wasu Abubuwa Gudun mantuwa Komawa Tayi saman kujeran Dake kallon Kofa ta zauna ta Yagi Takardan Ta Dora saman Littafin kana Ta aza Biron zata Fara Rubutu sai kuma Wani Sanyi Jiki da kasala da kuma Tunanin anya Abunda zata aikata Daidaine..?

In tayi hakan Tayi ma Umma adalci.?

Ko Tayi ma Iyalan Alhaji Tsoho Adalci Wadanda suka Fifitata Fiye da ya"yansu..?

Toh ammh in fa Tana Son Cikin Jikinta da kuma Igiyar Auranta Dole sai Tayi haka Bata damu koma me zai Faru ba Ta Tabbata Watarana zai Wuce kamar bai Faru ba Hawaye Taji ya cika mata kwarmin Idanuwanta Har suna kwaranyowa da Sauri ta saka Hannu Ta Sharce Hawaye Cikin Juriya Ta Aza Hannunta Cikin kwarin Gwiwa ta Fara Rubutun.

Takai wajen Tsawon Mintina Talatin Tana Rubutun Tanayi Tana kuka,tana kuma yi Tana Tsayawa Domin wata zuciyar na sanyayamata Gwiwa ga aikata Abunda Ranta ya Rayamata ammh sai Tayi amfani da Zuciyar Dake Karfafa mata Gwiwan aikata Abunda Tayi Niyyah din har sai Da Ta kamallah Rubutun nata kana ta Ninke Takardam Tatashi Ta kaita Cikin kayan Umma ta sakata acikin Wardrope inda ma Hankalin wani bazai kai ba Umma kuma ta maida mata Littafnta da Bironta Inda ta Dauka Kana ta koma kan kujeran Da tatashi ta kwanta Kawai ba Domin Tana jin barci ba sai Domin bata da wata mafita sai na kwanciya.

Mganganun Dina da kawarta Zakiya nayi ta yi mata amsa kuwwa Gefe Daya ga Kudurin Umma,Abu Daya yafi Firgitata Rabata da Cikinta da Umma zatayi wanda Bata iya Jurewa ba Hannunta na Bisa Cikin Tana Hawaye Cikin Zuciyarta wani kunci ne,Domin Ta sani Dina Ta Rigata Daukan Kwan Haihuwan Firstlove acikin maranta kenan Gaskiya ne Ta Fita matsayi Tun Da gashi Komai ya Bayyana..?

Kuka Take ahankali kada wani ya Jita takai wajen Misalin karfe 3pm na Dare bata iya Barci ba Tana Ta kuka Da kuma Tunanin Makomar Rayuwarta da Abunda ke Cikinta In har ta Yanke wannan Hukuncin Datake Shirin yankewa.

Bata san sadda wani Barci mai Nauyi ya kwasheta ba Sai da Taji Zafeera na Tashinta kan cewa Tatashi har an gama sallah Ta mike akasalance Idanuwanta Duk sum Kumbura sai da ta Shiga Tiolet ta Dauro alwala Ta Fito kana Zafeera Ta Luura Da Kumburin Idanuwan Zaina Cikin Mamakinta Take Fadin"Ukti meya Kumbura miki ido Haka..?

Da Sauri Zaina Tace"Bakomai...Idona ne Jiya Da Daddare ya Dinga Ciwo shiyasa..'Cikin Tsausayawa Zafeera Tace"Ayyah..Sorry bari mu Tafi sai asiya mgani ki saka..wlh ya kumbura miki Fuska Sosai kamar wacce Tayi kuka.."Yake kawai Zaina Tayi ammh acikin Ranta Tana Fadin ai
kukan ne ma.

Bayan sun Idar da Sallah Zainab da Zafeera Suka Tafi Kitchen Neman Abun karyawa Dayake su Umma Duk chan suka kwana Harda Abba su kadai ne agidan Daman chan nan Zaasu zauna sai ana Gabda Daurin Aure zasu koma Chan Gidan Alhaji Tsohon Tunda ana Daura Auran zasu Tafi da Amarya kaduna.

Bayan sun gama Hada Breakfast
Din Zafeera ta Mika ma kawayen Hamdiya nasu ta kuma Dauki nasu zuwa Dakin Umma Zainab ce ta Dauki na Dina ta Shigar mata dashi Ko Da ta Shiga Tana Cikin Bargo Tana Barci Ijiye mata kawai Tayi ta Fice Dinar ma bata sani ba Ta koma Daki suka karya dasu Zafeera,Hamdiya kuma ta koma Wajen Kawayenta suka karya Tare kana Suka Fara wanka Suna Shiryawa.

Basu yi anko ba Kowa kayansa zai saka Zafeera da Zaina da Zainab Umma Tayi musu Atamfa Da Leshi Tun Shekaranjiya aka anso Daga Wajen Dinki ko Zaina dake gidan bata san da Dinkunan da Umma Tayi musu sai da suka Gani Ko kafin zuwa 10am na Safe sun gama Shiryawa Kowa yaci kwalliyansa ya Cakare Hamdiya Daya Daga Cikin kawayenta Tayi mata kwalliya Har Tayi ma Sauran kawayen dasu Zafeera Dama kunshi Da gyaran kai Daga Abuja Tayo Abunta.

Zafeera da Zainab anyi musu makeup dan daidai Ammh zaina Taki yarda ayi mata Dakyar ta tsaya aka Shafa mata Hodo akayi mata Dauri aka kuma saka mata man baki,Dukkansu ukun less Din suka saka mai Ruwan marun,Da Pick sunyi kyau sosai sai dai kayan yafi Cika Zainab da Zafeera Saboda ya kamasu ammh Zaina sai yayi mata Rakwa rakwa saboda Ta Rame kuma Inaga Measurement dinta na Baya Telan nasu yayi amfani Dashi.

An kawo musu Abinci Daga Gidan Alhaji Tsoho Shinkafa Friderice da Alala daman Drinks basu da mtsalanshi akwai agidan,Dukkansu Falo suka Fito Kowacce ta Cakare abunta suna Hira suna Dariya wasu kuma na gefe suna Hotuna irun su Zafeera Duk Rashin Son Kada Zaina Tayi Hoto sai ta matsa mata Zainab Ta Daukesu acikin Ran zaina Tana Tunanin kila wannan Hoton Shine Abunda Ukti zata Dinga kallo Tana Tunawa da ita.

Dina Bayan Tatashi Tayi wanka Ta Shirya Cikin Riga da wando na yan kanti Breakfast din Ta Tea kadai tasha Ta Tureshi Gefe Tashi Tayi ta Bude kofan Tana kallon Abunda ke Faruwa acikin Falon Daya Bayan Daya Take kare musu kallo su basu ma Lura da ita ba,Zaina Take kallo Zainab na Daukansu Hoto Ita Da Zafeera mamaki ya kamata na ganinta ko ajikinta Har da wani kashe Dauri kamar ta Fito Falon sai kuma Ta Fasa Ganin duka yara ne kuma Batason Hayaniya yasa ta Maida Kofarta Ta Rufe ta koma ta kwanta Domin Bata Gajiya Da Barci kamar Cikin Jikin nata Yana yawan sakata Kasala da Barci.
****
Bangaran Zain kuwa ya kwana da Gudurun yau ko ana ha maza ha mata ne sai ya Dauki Firstlove sun yi Nisa da garin Bauchi Bazasu Dawo ba sai Umma ta Sauya Ra"ayinta Tun safe suka Shirya Shida Haddir Tunda Daurin Auran 11am ne saboda angwaye Zasu wuce Da Amarya kaduna.

Dukkansu Shigar Farar Shadda sukayi Harda Babban Riga wanda Daddyn Abuja ne ya Dinga musu anko Dukkansu Harda Shi da Baban kaduna da Abba,Dukkansu kuma Harda Babban Riga sai suka saka Bakar Hula da Bakin Takalmi Booth,da agogon Fata baki na kamfanin Rado Dukkansu sunyi kyau Duk da Zain ya Rame ammh yayi kyau yayi Haske sai da Ramar Jikij kawai Kuma ita ta Shafi Zuciya ne.

Koda 10 tayi na safe suna Gidan Alhaji Tsoho ana ta Shirye Shiryen Daurin Auran da zai Gudana nan da Lokaci kadan Zuwa goma Da Rabi komai ya kamallah Haraban Gidan Alhaji Tsoho an gama Tsara komai an Malale ko"ina da Manyan Cafet sun Kawata Haraban Gidan Dayake Gidan Babba ne ammh Duk da haka wasu Motocin awaje aka Fakasu Musamman ma na Abokan ango da Tawagan yan"uwansa da abokan aikinsa Sojoji,Suma Abba ga nasu gayyar na Mutanensu Hakama Daddyn Abuja da Dangin Mama Safiya Suwa Shima Baban kaduna Daga Barayinsa ko"ina ya Cika da Mutane gaisawa kawai akeyi ana Farinciki In kaga zain bakinsa kamar gonar auduga Saboda yau ya gaida Abba kuma ya amsamai Har sunyi musabaha da juna Zain ya ji Farinciki har sai da yayi kwallah Zuwa Lokacin Da Time din Daurin auran ya kusa sai Alhaji Tsoho Ya Fito ya zauna Bisa Kujeransa Daidai Lokacin kuma su Zaina Motocin da suke je Daukansu suka ijiyesu Daga Wajen Gidan,Kanwar Mama Safiya ita taje tazo da Amarya da kawayenta Haddir ta saka ya kaita Sauran kuma Motocin abokan ango ne.

Da kafa suka Taka zuwa Cikin Gida zaina Kamar ta Harde haka Take ji Sun saka mayafansu pick Zafeera da Zainab sun saka jaka kowannensu ammh Zaina Mayafin akanta ta sakashi Ta Jashi Sama saboda kada aga Fuskarta Daga Kugunta kuma Takardan Data Rubutu ne matse awajen Lokaci Bayan Lokaci Tana kai Hannunta wajen kada Takardan Ta Fadi.

Zain Dake Haraban Gidan yaga Zaina Domin koda Ga Tafiyanta ya ganeta,Sake baki yayi yana kallonta Domin Rabom da ya ganta Cikin kwalliya Tun suna gidansu baki da Hanci ya saki yana kallonta Ita kuwa bata ma gansa ba kanta na kasa Har suka Shige daman Amaryance agaba Anty Gaje rike da ita sai Kawayenta sai su Daga baya Shiyasa har suka Shige ma basu wani Daga gansu ba ganin maza sunyi yawa aharaban Gidan..

Dakin Hajiya Mama suka yada zango su kuma su Zafeera suka Fice gaida su Umma,Umma ta Dinga Kolasu Tana sun yi kyau Kowa yaji Dadin ganin Zaina ahaka Har Hajiya mama sai da tace ko kefa Hali Dubu Mirmishi kadai Tayi mata Diyar wajen Anty Zareena ta karba Tana Jijjigatamata Ganin Tana kuka ita kuma Tana Shiryawa ne,Kowa ya ganta sai yayi mgana Ita Goggo Halima bata Fahimci komai ba Tunda ba wanda ya gayamata ammh Dai ta Fahimci Halimar ta Rame sosai kamar wacce Tayi Cuta Ammh dai Ta bar ma Ranta da kila Cikin ne ya sakata Rama Domin Taga Shigar Ciki awajen Halimar Taso Ta Tambayeta Zain Sai kuma Tayi Tunanin kila zai shigo bayan Angama Daurin Aure.
Chapter 73 · 0% Book details