Sashe 64
Zainazain Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kinga yadda Firstlove ya koma Ukti ya rame ya lalace Wlh Tallahi Ina Matukar Tsausayinsa acikin Raina.."
Baki Sake Zafeera Take kallon Zaina kafin ta Kada kai Tana Fadin"Alkawarin yaci Ubansa..Wlh in Kikaga Ruwan bai Dafa Kifin ba Don Ubansa sai dai in ba"a sakoshi Cikin Ruwa ba..Kuma Tunda kina so ki Koma Wajensa Koma Ukti Ammh ki sani Babu Ruwana In Kika Kirani Watarana Kina kukan Bakinciki zai kasheki Kina ji kina gani zai Auri Abokiyar watsewar tashi akoma ana Miki ganin Daya bayan Daya Gefe Daya kuma Dan gaba da fatihq na Gifta muku acikin Gida.."
Runtse Ido Zaina Tayi Tana Fadin"Haba Ukti..Kidaina aibata shi Haka karki manta Dan"uwanki ne fa.."Saboda Haushi Ko mgana Zafeera Bata mata ba ta Fice Daga Dakin Ta bar Zaina na Kiran Sunanta Kitchen Taje wajen Umma Ta kama mata aikin Abinci Sunayi suna Hira kan al"amarin Dayake Umma,Bata da wasu abokam Shawara sai ya"yanta Musamman ma Zafeera Tunda ita macece mai manyance da kuma Dattako kamar wata Tsohuwa.
Tare suka gama Girki kana Umma ta wuce Dakinta Domin Domin Tayi wanka Itama Zafeera sai ta koma Dakin Domin ta Dauro alwala Kai Hade da Gwiwa ta iske zaina kan Sallaya bayan Ta Idar da sallah kai kawai ta Jinjina Batayi matamgana ba ta Shige Tiolet ta Dauro alwala tazo Tayi sallah bayan ta Idar ne Umma ta kawo musu Abinci ta kuma sanar da Zafeera cewa Abba ya Shigo Daman yaje gaida Alhaji Tsoho ne Tace bari Tagama taje ta Gaisheshi Ganin Daga Umman Har Zafeera sun yi baanza da ita yasa ta sauko Ta Fara Tura abincin ko Rabi bata Ci ba Tatashi Zuwa Tiolet sai amai sai ta gama ta Fito ta Fada kan Gado Tana maida Numfashi Suka Bita da kallo kafin Zafeera tace"Anya Umma Ukti ba Ciiki gareta ba..?
Da Sauri Umma tace"Bar mata Fata Zafeera..Ni da nake so arabu Salin alim.."Kai Zafeera Ta gyada Tana Fadin"Kuma fa Hakane Umma...Zamansu ma ai ya Haramta Saboda zata cigaba da zarginsa Tana ganin sa da Abun gwara kowa ya nemi Daidai Dashi.."Umma tace"Shi nagani..."Zaina Tana Jinsu Lokacin da Zafeera tace ko Ciki gareta..?
Sai da gabanta ya amsa ta Fara Tunanin wajen wata na Uku kenan bata ga Al"adanta ba Da kuma yanayin Data samu kanta akwanakin nan Zuciyarta ce takara Tsinkewa Domin bako Tamtama Mganar Zafeera zata iya Tabbata Kunshe Bakinta Tayi kada Umma Taji kukanta kuma Ta Tabbatar ma kanta Umma Taasan Da Cikin nan da gaske sai ta kaita an Zubar mata Dashi Ita kuma bazata bari ba Domin Tana Son Cikinta kuma Tana Son Uban Cikin Tafi kowa sanin babban Burin firstlove aduniya Shine Yaga ta Haihu Bazata bari wannan Burin nashu ya tafi abanza ba Wata Zuciyarta tace mata Kin makara Domin Wata ta Rigaki Daukan kwayan Hallitan Haihuwansa a mahaifanta Tuna Haka yasa Duk wani Farincikinta ya gushe Kishi ya Rufe mata Ido sai kuka ammh kukan Zucci Sanin Daga Umma Har Zafeera Suna Jami"iya Daya ne kamata Tana kuka Dukkansu bada Sauki zasu mata ba.
Zafeera Taje ta gaida Abba ya Dinga Mata Fadan me ya Dawo Da ita suna Shirin Fara Jarabawa Tace gobe da safe zata koma kana ya kyaleta,Zain kuma Har kofar gidan yazo sai dai Megadi ya Tabbatar mai da Abba yana Gida Shi ya Hanashi Shiga ya Juya kan Motarsa Zuwa Gida wanda yayi mai Fadi babu Firstlove acikinsa Ba Laifi ya Rage damuwa saboda Asibiti Duba Marasa lafiya ma na Dauke mai Hankali ammh Tabbas ya gama Ramewa ya Fige da alamu dai yana Jin Ciwo ammh Bayaso ya kwanta ya Cigaba da Tsayuwa kan kafafunsa Domin in ya nuna Rauninsa Babu abunda zai Sauya.
******
Har suka kwana suka Tashi Daki Daya Zafeera bata sakar ma Zaina Fuska Duk da Tana Tsausayinta ammh kuma Ta bata Haushi yadda ta kasa mantawa da Ya Dakta da wani Abunda ya aikata gareta.
Bayan sun karya Zafeera ta Fara Shirin Tafiya ganin hakane yasa Zaina ta Fara kuka wannan Dalilin yasa Zafeera ta watsar da komai ta isa gareta ta Rumgumeta Tana ta lallashinta Da bata baki kan ta Cire Damuwa aranta ganin Zafeeran ta Sauko ne yasa tayi mata alkawarin zatayi Hakan Insha Allahu Zafeera taji Dadi ta Dinga Share mata Hawaye Cikin Shakuwa.
Abba kuma yana Gida bai Fita ba yau weekend Misalin 11am na Safe sai ga Kiran Alhaji Tsoho Bayan sun gaisa ne yake Shaidamai Tun safe sukayi waya da Kwamishina Baban Dina kan Yau Ita kanwar Mahaifiyar yarinyar Datazo Daga Sudan da mai Dakinsa zasu kawo ita Dinar kamar yadda ya Tsara saboda haka sun Taso Suna Hanya agayara mata masaukin da zata zauna Har Zuwa Lokacin da zata Haihu Adaura musu Aure tatare Gidan Mijinta Shikenan..
Abba yaji Kamar yayi kuka ammh kuma bai da yarda zai yi Tunda tun yana yaronsa baya Jayayyah da Alhaji Tsoho ballatana yanzu da Girma ya kamashi Waya ya Dauka ya Kira Nene da Umma Dukkansu yace su Zo Dakinsa su sameshi Kusan Tare suka Shigo kowacce Cikin mamakin wannan Kiran gaggawan sanin ma basu Dade da Fitowa Daga Dakin ba Umma kuma Dama nan ta kwana.
Cikin Kallonsu Dukkansu ya Isar musu da Sakon Alhaji Tsoho Dukkansu sun Ji wani Irin Barin ma Umma Nene ce ta Sauke Numfashi Tana Fadin"Umm..Sai dai Dakinsu da Halima ke Ciki yafi Girma,Dayan karami Kuma nan Zareena ke sauka In Tazo,Kaga kuma Sauran Dakunan na Sadiq ne da Faruq kaga ai bama Sauketa Dakunaansu ba Duk basa nan,Suna Zuwa mana Hutu kwatsam ne.."
Cikin Nazarin Mganarta Abba ya Sauke Numfashi Takaichi kafin yace"Shikenan agyara Dakin su Sa"adiya sai ta sauka aciki.."Cikin mamaki Umma tace"Ita kuma yar tawa taje ina..?
Karfa ku manta Dakinsu ne Tun suna yaransu har girmansu kawai rana tsaka sai asaka wata Najasa aciki kuma alhalin Zaina Tana zaune acikin Dakin..?
Umma Ta Fada Cikin Takaichi Nene ta kada kai Tana Fadin'Haba Umma ya kamata ki Daima aibata Wannan al"amarin da wani muguwar kalma Ko muna so ko bama so Cikin Jikinta Jinimu ne Tunda Danmu ya Digashi Kinga kuwa ya Kamata mu Cire komai mu Rumgume wannan kaddaran Tamu Hannu Biyu ammh naga ke kina Fifita Abunda kika Haifa kan Abunda Bake kika Haifa ba Umma.!
Ta fada Tana kallonta Cikin Hawaye Mirmishi Takaichi Umma Tayi Tana Fadin"Halima yata ce Halak Makak..Kamar uwa nake gareta ke nice ma Uwartata kuma Ubanta ban damu da me zaki ce ba ammh ina so Ki sani ni ba irin Matan da Domin Nasu yayi Laifi su kare su ki Nuna yayi Laifin Saboda Don yana nasu ako"ina ina Bayan gaskiya..Na Riga nagama mganata Anemar mata wajen zama ammh ba Dakin Ya"yana ba wlh..!
Tana Gama Fadin Haka ta Fice su Abba suka Bita da Kallo,Kallonsa Nene Tayi zatayi mgana ya Rigata da Fadin"Har kin Manta Fatima..? ki naka kenan ka so na wani..Tayi gaakiya uwar Sa"adiya take gareta Har Abada..Bari na Kira Alhaji Tsoho na gayamai.."Nene na Tsaye ya kira Alhaji Tsoho ya gayamai Abunda Umma tace Cikin Muryann Dattako yace"Me Halimar take Acikin Dakin Usmanu.. ?
Kace ma Fatima nace Injini Ta maida Halima Dakin Miijinta ita kuma Yarinyar ku sauketa nan Usmanu hakkinka ne ka kula da ita kaida Matanka Laifin wani baya Shafar wani mene ne laifin Abunda ke Cikinta..?babu Laifinsa na Iyayensa saboda haka kada ya karbi Hukuncin da ba nashi ba..!
Abba dai Toh kawai yace batare da ya kara yin wata mgana ba Nene
ma bai kara mata mgana Bayan Alhaji Yace In sun Kariso Hajiya mama zata kariso Dasu nan Gidan Damuwarsa yake so ya Boye Shiyasa ya Nufi Hanyar Tiolet yana Fadin"Kije ki saka ko Zainab ta gyara dakin nasu Sa"adiya Alhaji Tsoho ya bada Umarnin a sauketa anan.."Daga Haka ya Tura Kofar Tiolet din ya Shige ya maida Kofa ya Rufe.
Nene Fita Tayi zuwa Falo Ta samu Umma zaune Tana kallon Sunna Tv Ana Wa"azi ammh a zahirin gaskiya ba wa"azin Take kallo ba Hankalinta da Tunaninta na kan yadda Zuciyarta zata Juru zama da Dina acikin Gidanan da Suna wacce ke Dauke da Cikin Dan'ta kuma ba na Sunna ba Bakincikinta zai karu Kila har itama asameta da Hawan jini Daga sama kawai Taji Nene na Fadamata Umarnin Alhaji Tsoho na asauke Dina Dakin Su Zaina Umma ta Dago Tana kallonta Kafin tace"Toh in ko Hakane sai dai Zaina ta Dawo Dakina..Ban yarda Ta Hada wajen zama da Wannan Yarinyar ba Bazata ma sabu ba.."
Nene dai bata kara mgana ba ta Wuce zuwa Dakin nasu Zaina ta Iskesu Zainab da Zafeera ke Hiran karati zaina na Gefe Tana kallonsu bata dai mgana Ammh kuma Daga Dukkan alamu Hiran na Debe musu kewa Cikin Dakewa Nene ta Kalli Zainab Tana Fadin"Zainab ki gyara Dakin nan ki Share ko'ina ga Baki nam Daga kano..!
Zafeera ce tace"Baki kuma..!?
Ko Inna Rukkaya ce Nene..?
Kafin Nene Tayi mgana Umma ta Fado Dakin Tana Fadin"Ba Rukayyah bace...Yarinyar da Alhaji Tsoho yace zata Dawo nan ne suke Tafe yau..Kuma nan Dakin yace asauketa.."Dam!gaban Zaina ya Buga Har sai da ta mike zaune Dakyau Cikin yamutsa Fuska Zafeera tace"Dakin mu kuma Umma..?
Ukti kuma ta koma ina .?
Umma tace"Tashi ki Hada mata kayanta dana amfaninta..Dakina zata koma Kema in kinzo Hutu chan zaki Dinga Sauka Daga yau.."Tafada Fuska ba walwala,Zafeera ta Sauke Numfashi Tana Fadin"To Umma.."Daga haka Umma Ta Juya ta Fice Nenema tabi Bayanta Suna Fita Zainab tace"Har ga Allah bana son Dawowar yarinyar nan Gidanan..."
Zafeera Ta mike Tana kallon Zaina wacce ta kurama waje Daya Ido Zuciyarta na Suya Cikin Tsausayawa tace"Ukti Tashi mu koma Dakin Umma..Bari na Kwashe miki kayanki.."
Cikin karfin Hali Zaina tace"Bani ma da wasu kaya Dogayan Riguna guda 3 ne Hijabi da yan kayan kwalliya suma na Zainab ne Umma ta bani Duka kayana suna Lowcost..'Zafeera ta gyada kai kawai Ta Bude Wardrope ta kwaso mata kayan kana ta Tattara kayan Shafan gaban madubi,Dama zainab Dakin da Zaferea ke sauka ne nata Bata kwanan nan Dakin Kowa ya sani Dakin Zafeera da Zaina ne Tun abaya...