← Book details Zainazain Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 78

Sashe 50

Zainazain Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shi kanshi yayi kuka kan wannan lamarin Ballatana ita.
*Shakira..*
*ZAINAZAIN..!*
_(Is a love Story and Betrayal)_
*Wattpad:Jamilaumar351*
*Mallakar:Janaftyshakira*
*BOOK 1*
"Zain kuwa Tunda ya koma Gida ya Shiga Cikin Bedroom dinsu ya kulle kansa ya zauna akasa ya Hade kai da gwiwa ya Dinga Rafzan kuka Kukan Daya Dade baiyi kamarsa ba bama zai iya Tuna Rabonsa Daya Zubar da Hawaye ba Duk da ya kasance mai Taurin zuciya BA Abu bane karami bane zai saka kaga yana kuka ko Lokacin Suna yara Haddir yafishi Rauni ko Rashin Lafiya Zareena Take ya Shiga Tashin Hankali kenan Har kuka yana yi ammh bandashi iya wutar Rauninsa Sai dai idanuwansa su kada suyi Jajir Jijiyoyin kansa Su Tashi Radau kamar mai wani Cuta yau gashi Rana tazo Daya zauna Yana ta kuka Kukan Tsausayin kansa Dana kunyar Iyayensa uwa uba kuma kunyar Zainarsa da wani ido zai kalli Firstlove ya gayamata Duk wadananan Abubuwan sun Faru..?ya sani yanzu Lokaci ya Kuremai Karyansa kuma Tagama karewa.

Haka ya kwana cikin wannan Halin bai iya cin komai acikinsa ba Wayarsa kuma Rashin Chaji yasa Ta mutu,Ruwa Kadai yake sakama Cikinsa,Kafin safe wani Mugun zazzabi ya Rufeshi Ga Ciwon kai Dakyar ya iya Tashi yayi sallar asuba ya koma ya Kudundune kan gado yana Rawar Sanyi.
****
Dina na kwance kan Makeken Gadonta,Misalin karfe 9:30am na Safe Tun barcin Jiya bata Tashi ba Sallah ba sai Wajen 7am Tatashi Tayi ta itama Din Domin Hajiya Batula tazo ta matsa mata ne,Kasala Take ji da kuma Tsinkewar miyau Don ma Allah ya Taimaketa Cikin bai Mata Laulayi Sosai ba ballatana ta Wahala ko amai ba sosai Take yi ba sai Taji yunwa in Taci Abincin sai ta Dawo Dashi..

Hankalinta kwance Take Barcinta Ringing din wayarta Ya Tada ita Daga Barcin salama da Farincikin Datake yi Dagowa Tayi Lokaci Daya da karamin Tsaki Kafin ta Jawo wayar Dake gefenta Domin Dazu da asuba sunyi mgana da Ummi maimuna,Tana ganin Zakiya ce ke Kiran Ta Daga da Sauri Tana Fadin"Yanzu fa nake cewa in na Tashi zan kiraki..!

Dagachan Bangaran zakiya ta saki Dariyan Nishadi Tana Fadin"Kaga manya manyan mganin kanana...Mrs Zain Usman Abubakar saulawa Barka da safiya.."Mirmishin Jin Dadi Dina ta saki kafin tace"Barkanmu..Ya gajiyan Jiya... ?

Zakiya tace"Gajiya Tabi Jiki..ya Karfin Jikinki..?

Ki Dinga kula da kanki Dina Kinsan Ayanzu wannan cikin Shine fa makamin mu..'
Dina Ta yamutsa Fuska Tana Fadin"Wai yanzu haihuwansa zanyi..?

Allah ban Shirya Haihu yanzu ba zakiya.."Zakiya tace"Ya zama Dole kuwa Hajiya..Kina ganin ba Domin Cikin nan ba akwai wani uzurin da Danginsa zasu karba ne ballatana Har su Dubeki..?

Kima Dawo cikin Hayyacinki.."Dina Ta Kauda zencen da Fadin"Hmmm kawai..!

Zakiya Tace"Na kiraki ne na Gaya miki na cikama Dr.Imran alkawarinsa Daran Jiya Duka nashi ne Bai ma jima da Tafiya ba..Gaskiya zan Dan Raka da Gayen ya san Harka yafi Wadanan Tsoffanfin da Dama chan Basir da girma ya gama Cutar dasu.."Baki Dina ta saki Tana Fadin"Kai zakiya Don Allah ki bar wannan mganar...Ni da nake so kema ki Fidda wani ki aura Duka mu bar Rayuwa barikin nan.."Zakiya Tace"Wa zai yi Aure..?

Wai ni..?

A'a Wlh ko Baba yagaji da mganarsa ya kyaleni Ba yanzu zanyi Aure ba Dina Domin har yanzu ban samu Wanda yayi Daidai Dani ba nafi son na Auri Ustaz Wanda bai san komai ba na Auresa muyi ta Shan Soyayyarmu.."Dina ta Rike baki Tana Fadin"A ina zaki samu..?

Zakiya Tace"Acikin gari mana..Kina mamaki ne..?karki manta Bawa baya cire rai da Rahmar Ubangijinsa.."Dina Tace"Tsiya na Dake Sani..Ammh kina Take sanin naki.."Zakiya Tace"Mutane nawa ne acikin Duniyanan Suna sani kan Abu kuma Suke Takewa... ?

Ke duniyar nan fa cike da Mutane Dabam Dabam masu aikata Laifin ma sun fi kowa sani Ni kyale ni Nafi jin Dadin Rayuwata ahaka kin ganni nan Kedai Da kika ga zaki iya Auran Shikenan.."
Dina Tace"Allah ya Shirya.."Zakiya Tace"Ameen..."Har zakiyan Zata kashe wayarta Dina Tace"Wai ni ya matsayin Matarsa ne yanzu..?

Nifa tafi Tsayamin arai kuma Tayaya zan koma Gidansu da zama kina ganin ba mtsala..?

Zakiya Tace"Ai yanzu bai da Wata mata bayan ke..Agaban idanuwanki Kika ga Abunda ya Faru..Na Tabbata ko Waye zai saka baki bazata Saurareshi ba..wannan Firstlove din ya kare Daga Jiya Ina gayamiki..Mganar zuwa Gidansu kuma yayi Daidai..Kinga kin samu Hanyar kusanci da Zain kenan da Duka Ahalinsa Kuma Bashi da wani Ikon Wulakantaki Tunda kina Gaban Iyayensa ne Uwa uba kuma Alhaji Tsoho bazai bari wani ya Tozartaki ba..'
Dina Tace"Hakane....Da Farko ina Jin Tsoron Haduwa da Zain..Gabana nata Faduwa.."Zakiya Tace"Babu Abunda ya isa yayi miki..Yanzu ma Bata ke yake ba..Yana ta kansa ne ki Sharesa karma ki Kirashi In kin koma Gidansu Dole ku Hadu kuma Lokacin bashi da wata mafita.."Dina Ta gyada kai alamun gamsuwa Da sauri Zakiya tace"Sai mun sake mgana..!.

Daganan suka yanke Kiran Mika Dina Tayi kafin ta yaya Bargon Dake Jikinta ta Zuro Kafarta Waje Silafis Din Dake bakin Gadon Ta zura Ta Fada Tiolet Da Farko Tana Ciikin Damuwar Taya zata iya Rayuwa awani gidan da ba nasu ba..?

Ammh Mganganun Zakiya yasa Duk wani Fargaba ya Gushe mata.
*****
Zuwa Safiya sai zazzabin Jikin Zaina ya Ragu Taji Sauki Sosai Har Tatashi Da kanta Tayi wanka Ta Dauro alwala Tazo Tayi Sallah Umma adakin Ta kwana Tare da ita Dukkansu Suna Jere kan Darduma Bayan sun Idar da sallah Kowanne acikin Ransa Abubuwa Dadama yake sakawa.

Umma Azkar takeyi ammh Rabin Hankalinta baya Jikinta Tatafi Duniyar Tunani in Ta Tuna Abubuwan da suka Faru Jiya sai Taji Tsinkewar Zuciya da kuma Raunin Rai,gabadaya Abun ya Faru ne wanda basu Taba tsammani ba,Tunda Take bata Taba kawo ma Zain wannan Lalacewar ba Ta sani ita Ta Haifi Zain Kuma Soyayyar Uwa Da Danta na musamman ne Ammh ko afili Bata Taba Nuna wata alaman da za"a Fahimci Zain Danta bane bata Taba Damuwa da Sha"aninsa ba komai nashi Nene ne,Ita Halima itace yarta Domin Ita ta Riketa Tun tana karamarta har zuwa yau Tana Jin Dacin Damuwar Datake ciki Domin Wata Shakuwa ce tsakaninsu Kamar ta Uwar Data Haifi yarta da Cikinta ayanzu Tafi Dora Duka Laifin kan Zain ne ayayinda Gefe Daya kuma Take matukar Tsausayin Zaina,ayanzu ma Haka Ita Take Tunani Tana Tunanin wani Hali kuma zata Shiga agaba..?

Tana Tsausayinta Domin Tafi kowa sanin yadda zaina Tafi yarda da Zain Fiye da kowa aduniya Ta soshi Tun bata san kanta ba Tana Fatan Allah yasa Zuciyarta Tayi Juriya wajen Daukan wannan al"amarin.

Kallonta Ta maida kan Zainah Wacce ta Kurama Gabanta ido Ga Carbi a Hannunta Tana ja ammh bawai Tasan Abunda Take Fada bane Hawaye ne wasu na Koran wasu suke zubomata gani Take kamar a mafarki Abubuwan suka Faru in ta Runtse ido Da ta Bude kuma sai Ta Gasgasta Abunda ya Faru yau wai Firstlove ne yayi ma Wata Mace ciki ba Ita ba macen ma ba Wata mai Daraja ba karuwa wacce ya ijiye sunan zaman Dadiro Wannan Abun yafi komai yimata Ciwo da Nauyi akirjinta Ji Take kamar Zuciyarta Zata Fashe Tana Jin wani Zafi Zafi yana Fitowa Daga kasan Ranta,Tana jin aduniya kuma wa zata kara bama yardanta..?

Tunda wanda tafi kowa yarda dashi yau yaci amanarta Wanda yafi kowa saninta da sanin Rauninta yau yayi sanadiyar da Rauninta ya bayyanata Tanajin kamar ta Mutu ta Huta da wannan Bacikin Daya Ziyarceta Daga Jiya zuwa yau.

Umma ce ta Dafa Kafadarta Lokaci Daya Tana Fadin"Zaina..."Cikin wani yanayi na karaya da Tsausauyi Juyowa Tayi Tana kallonta Idanuwanta na Zubar da kwallah ganin Umma yasa Rauninta ya Karu kawai sai ta Fada Jikinta Tana sakin kukanta Umma ta Riketa Tana Lallashinta Itama kukan Zuccin Take ammh Tana Kokarin Dannesa Saboda kada Ta kara Raunamama Zainar zuciya.

Sai Da Tayi kukanta ya isheta kana ta Dakata,Umma ta Dago ta Tana Share mata Hawaye Cikin Sigar Lallashi Take fadin"Kinga baki da lafiya ki Daina wannan kukan kinji ko..?

Jikin ki da zazzabi har yanzu kada ya kara Daukan zafi.."Tana kallon Umma da Rinannun Idanuwanta Tace"Umma Don Allah a zamana da ya zain akwai Abunda na Rageshi Dashi ne..?Ko kuwa akwai wani Abunda nake mai wanda baya Burgeshi ne..?ko kuwa Daman chan Baya sona ne Umma alfarman na Tashi agabanki yasa ya Aureni..?meyasa Firstlove zai min Haka..?Umma Meyasa bai ce min yana son ya kara Aure ba..?

Wlh bazan Hanashi ba Zan barshi ya kara aure indai zai Cigaba da zama Dani a matsayin matarsa,Da kuma Kare kansa da aikata zina...!

Ta karishe Fada Cikin wani Gunjin kuka Tana Sulalewa Jikin Umma ita kanta Umman kukan Take Cikin Zuciyarta dago da Fuskarta Umma Tayi Tana Girgiza mata kai Lokaci Daya Tana Fadin"A' a Diyata ki Daina kuka..Bari kuka.."Take Fada Tana Share mata Hawaye Cikin Wani irin Dacin Zuciya Zaina Tacigaba da Fadin"Umma Dadiro fa Firstlove...Dadiro ya ijiye har yayi mata ciki..?

Zuciyata Tana zafi kamar zan mutu Ina jin kamar bazan kara Rayuwa ba..Bani da kowa Umma mahaifana Duka sun Rasu wazan Tunkara wa zai Tsayamin ga wannan Jarabawan Rayuwan Data Fadamin Umma bani da kowa.."
Take Fada Tana kuka kamar Ranta zai Fita,Umma Tayi mata Kuri Tana kallonta,Cikin bayyana Bacin Ranta ta saka Duka Hannuwanta Ta Tallabi Fuskar Zaina Tana Fadin"Dago ki kalleni nan Halima..!

Tafada Cikim kakkausan Murya jin Umma ta ambaci Sunanta yasa Zaina Ta Dago da Jajayen Idanuwanta da suka kumbura Tana Binta da kallo Cikin Nuna kauna da Tsausayi Take fadin"Tunda kika taso na Taba nuna miki wani bambamcin Da zaki ji cewa bani na Haifeki ba..?

Ta Fada Tana kallonta Girgiza kai Zaina Tayi Hawaye suna kwararan mata Umma ta Cije baki Kafin ta Cigaba da Fadin"Toh meyasa kike Tunanin baki da kowa..?

Kalleni nan Halima kina da kowa ni Fatima nice Uwarki Abban su kuma Shine Ubanki Har gobe,Kidaina Tunanin baki da wanda zai Shiga Lamarinki Ni nan zan iya Shige miki gaba akomai Wlh Na Daukeki Tun baki Cika Shekara Biyu ba aduniya Halima Na Rike Tamkar Diyar Data tsaga Jinina ta Fito Keda Zafeera da zareena Ban Taba Jin bani na Haifeku ba ina muku kallon Shakikan ya"ya ne Saboda Haka ki Sani Bazan Taba bari Acuci Rayuwarki ba..Zan Tsaya miki Tsayin Daka Har sai Zainullahi YA SAKE KI..!
Chapter 50 · 0% Book details