← Book details Zainazain Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 74 OF 78

Sashe 74

Zainazain Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Karfe 11:10am aka Daura Auran Hamdiya Aliyu Abubakar Bashir Saulawa da Angonta Hafeez Muhammad Ikra,Daurin Auran da Shedu suka Tabbatar Dashi,Wan Baban Ango Shine Waliyin Hafeez Shi kuma Baban Kaduna ya zama Waliyin Amarya Masha Allahu su Alhaji Tsoho Suna Daga Cikin wadanda suka Shaida Daurin Auran ya samu Hallartan Manyan Mutane kama Daga Lauyoyi masu zaman kansu Abokan aikin Dadyn Abuja Da Tsoffofin abokan Alhaji Tsoho Da ya"yansu wasu Tsoffin Likitoci wasu kuma sun Taka wani mukami agwammati,Sai Abokan aikin Abba Dana Baban Kaduna Dangin Mama Safiya da wasu Daga katsina,Abokan Angon Shi kanshi Da kuma Tawagar Iyayensa da Yan"uwansa,Zuwa abokan aikin su Zain da kuma Makota Da abokan arzuka Hardasu Dr.Imran da kuma Dr.peter Sun Hallaci Daurin Auran Bayan an Gudanar da Daurin auran aka Fara Fito da abinci da Lemuka ana ta Rabawa kowa yana zaune kan Cafet yana cin Abinsa da Naman kaza ga Ruwansa agefe ana Korawa da Lemu Haraban Gidan Alhaji Tsoho kamar wani Restaurant Haka ya koma.

Daga cikin Gida Kuma ana Ta Shiryen Shiryen Tafiya da Amarya Nasihu Dama Tuni iyayenta sun mata su Umma dai ke karawa Da Hajiya Mama Alhaji Tsoho Daman Tun Daran Da suka iso yayi Mata nata Sosai,Kuka kawai Hamdiya Take ganin Da gaske Tafiya da ita fa Za'ayi Adaidai Lokacin kuma Zaina ta mika ma Zareena Yarta Ta koma Dakin Hajiya Mama Jakar Zafeera na Hannunta Ta bata ajiya Suna Chan Dakin Alhaji Tsoho suna Hadama Hamdiya kayanta.

Ba kowa adakin sanda ta Shigo Duk suna Falo ana Tsaye Masu Shirin Tafiya masu Rakiya ma na Tsaye Baban kaduna da Abba Sun Shigo Har gida suna Fadan su Shirya 12 suka ce zasu Mika Hajiya mama Ta Tsara masu Tafiya Kaduna Tace Umma zata Tafi da Mom lklima da Inna Hannatu da Inna Rukayyah sai Dangin Mama Safiya kanwarta Da Diyar wan babansu Sai Ya"yan yan"uwansu yan mata Daga Barayin nan kuma Hajiya Mama tace Zafeera da Zainab da Shema da maryama duk zasu Tafi Asma"u ma da Zareena suma Duk Dasu za"a je Hajiya mama tace Goggo Halima ma Da matar Danta zasu Tafi Da Farko tace bazata ba Hajiya mama tace sai Taje Umma na jin da ita za"a Tafi Ta kuduri Niyya da Zaina zata Tafi Sai ta Fara Nemanta ammh bata ganta ba Zafeera tace kila tana Dakin Hajiya Mama Umma Ta taka Kafa zata Bita Hajiya Mama ta kirata kan da ita da Mom Iklima da kanwar Mama Safiya zasu kai Hamdiya Tayi sallama da Alhaji Tsoho da kuma Iyayenta wannan Dalilin yasa Bata koma Dakin ba suka Dunguma zuwa Haraban Gidan Kaya kuma Tuni wasu an Fara sakawa cikin Mota kuma Daman an je Tuni anyi jere chan kaduna wannan aikin Mom iklima ce.

Zaina sai da Ta Tabbatar duk sun Ragu afalon kana Ta Tashi Daga Kofar Dakin Hajiya Mama inda Ta Labe Jakar Zafeera ta Bude Ta Taga kudi 3k sai ta Dauki 2k ta bar mata Sauran Lokaci Daya kuma ta saka Takardan Data Makale a kugunta Cikin Jakar Ta ijiye mata nan Gefen gadon Ta warware Daurin kanta Ta Rike kallabin Ahannunta Ta saka mayafinta Ta Yane kanta Ta zazzagoshi yarda bamai ganeta kuka Take kuka mai Cinrai hawayenta na Zuba Tana Sharewa Sikat din yadan mata yawa sai Tajashi sama Sai da ta Leka Daga Falon Taga duk ba wanda ya santa yawancin Dangib Mama Safiya ce Sadaf Sadaf Ta Fito Tana waige zata Fice Daga Falon Taji Muryan Hajiya Mama Da ta Fito Daga Dakin Alhaji Tsoho Tana Fadin"Ke waye nan zai Fita..?

Dam!gaban Zaina ya Fadi tayi Saurin Share hawayenta kana ta Juyo Tana Fadin"Nice Hajiya mama..Zani waje naga Tafiya Amarya ne muyi sallama.."Hajiya Mama Da taci wani Ubansu Leshi Ta kariso Tana Fadin"Au Halima ce..?

Eh gwara haka Kinga ke bai kamata ki Tafi ba gwara ki zauna in Uwar taki sun kaita sun Dawo sai ansan yadda za"ayi ki koma Gidan Mijinki.."
Cikin Sanyin Murya Zaina Tace"Toh Hajiya Ma..ma.."Ta Fada Muryanta na rawa ganin haka yasa ta Dafa kanta tana Fadin"Karki damu kinji ko..Ga Nene ai ba da ita za"a Tafi ba saboda kada abar gidan ba kowa ga Amanar yarinyar nan a Hannunsu Kiyi hakuri gobe zasu Dawo Dukkansu.."Tafada Cikin Sigar lallashi tana ganin kamar zaina ta Damu ne za"a Barta ita kadai Saurin kwakwalo Mirmishi Tayi kafin tace"Bari naje muyi sallama.."Hajiya Mama tace"Hanzarta.."Ko gama Rufe baki bata yi ba ta Fice har tana Tuntube sai da Hajiya Maman ta Bita da kallon mamakin ganin kamar tana Sauri kuma bata Cikin Natsuwarta.

Girgiza kawai Tayi ta koma Ciki,Achan Haraban Gidan kuwa Zaina na Fita ta Tsaya Daga Gefe,Tana Hango Hamdiya Durkushe gaban Alhaji Tsoho Da Abba Da Babban kaduna da Daddyn Abuja su Umma na Tsaye Daga Chan gefe kuma Tuni wasu ma Daga Tawagan anko sun Fara mikawa su Zafeera kuwa suna jikin wata Jeep Daga gani ita zasu Shiga Daman sun Taho Da kayansu Tun Daga Gida wajen ya cika da jama"a Shiyasa wani ma bazai gane wani ba an cika maza da mata Kamar an ce Ta kara Daga kai ta Hango Firstlove yana ma Zafeera mgana Bata san me ta gayamai ba Taga ya Nufi Wajen su Umma Kara Lafewa Tayi jikin Fulawan Dake Haraban Gidan tana kara Rufe Fuskarta Tana gani ya Rankwafa yana gaida Goggo Halima ta amsa Tana Shafa kanshi bakinta har kunni Daga gani albaeka Take sakamai Zuwa chan kuma ya mike ya Nufi Hanyar Shiga Falon gidan Sai Zaina ta kara Boye kanta Tana Danne kukanta ganin Firstlove ya Tada mata Duka wani Mikin Dake Zuciyarta,Wani irin Sonsa da kuma Raunin Rasa sa ya Bayyana Gareta Tana kallonsa har ya Shige Cikin jikinta ta Dafa Lokaci Daya wasu hawaye na Zubomata afili ta Furta"Nasan zakaji Ba Dadi in kaji irin Hukuncin dana yanke..Kada kadamu nayi hakane saboda Tseratar da Cikin ka da kuma Aurena Dake hannunka..da kuma kauce ma ganin wata Ta haifa maka D'a ko ya' ba ni ba da kuma kaucema ganin Wata a matsayin matarka..Ammh zan Dawo In da Rabo kuma nayi maka alkaawarin Kula maka da kaina da Abunda ke Cikina Insha Allahu.".

Kuka Ta fashe dashi kamar Wacce aka Duka Har sai da Ta Duke jin kamar Motsi ne Daga Bayanta yasa ta waiga Tana Toshe bakinta kada wani ya jiyota,Ido ta zaro Tana kallon Zain Daya Fito kamar yana neman wani abu Jikinta ya Fara Rawa Ta Tabbatar da ita yake nema ya kamata tayi ta Fice Daga Gidan nan kafin komai ya kwace mata,Tana ganin ya Nufi Wajen Zafeera Tayi Zuruf ta Fito Daga maboyarta Ta Bayan Mutane ta Dinga Bi Tana ta kare Jikinta kada Zainab ko Zafeera ko Umma wani gane kayan Jikinta ya Kirata,Allah ya Taimake ta har ta kusa barin Haraban Gidan bata Hadu da wani idon sani ba Tana Gabda Fita ne suka kusa cin karo da Haddir ya Shigo yana waya ganin Hankalinsa yayi gaba ne yasa sau Daya ta Waigo ganinsa yasa ta Juya da Sauri Ta na gyara Gyalanta Shi kuma sai da yace mata Tayi hakuri kana ya koma yana kallonta ganin yadda take wani Sauri kamar zata Tashi sama mamaki ya kamashi Ko dai Barauniya ce..?

Ammh kuma kamar Dazu Da suka je gidan Abba yaga kamar wasu da kayan nan Dayake shi bamai wannan luran bane yasa kawai ya Cigaba da wayarsa ya Juya ya Nufi Haraban Gidan.

Hankalin Zaina bai kwanta ba sai da Taga Ta Fita Daga Haraban Gidan Alhaji Tsoho kana ta Dago Ta kalli Gidan Ta kara kallo Hawaye na Zuba acikin Idanuwanta kafin Ta Furta"Umma ki yafemin..Abba ka yafemin...Goggo Halima kema ki yafemin...Firstlove da Ukti kuma ku yafemin.."Kafin ta Fashe da wani kuka mai cin rai adaidai kuma Lokacin ne Motar Zakiya Wacce Dina ke Ciki ta Faka nan kusa da Zainar bata ma Lura dasu ba Tana kallon Gidan Tana kuka sai Da Taji muryan Dina wanda ko Mafarki Tajita zata ganeta kana ta waigo Gabanta ya yanke ya Fadi Data gansu Saurin Juyawa Tayi Tana Rufe Fuskarta Lokaci Daya kuma Tana Tsallakawa Daga chan Dayan Hannu Da kallo suka Bita Dukkansu atamfa Riga da Sikat suka saka ammh fa kayan sun kamasu Zakiya ta Zubo attch din nan Dina dai bata saka ba ammh Itama gashinta waje ga wani mayafi kamar basu basu saka ba.

Ta gefen ido Taga suna kallonta yasa ta Fara Tafiya da Sauri Da Sauri kamar wacce Zata Fadi Hannunta daya Damke da Sikat dinta da kudin Dake hannunta Ganin haka yasa Zakiya tace"Ita wannan fa..?

Tana sauri kamar wata mara gaskiya..!

Hankalin Dina naga Haraban Gidan Take Fadin"Miye naki..?

Kila barayin nan ne da suke zuwa Sata wajen Biki..Tagama Diban Rabonta Zata kara gaba.."
Ta Fada Tana kallon Bayan Zaina wacce ta Fara musu Nisa Cikin Wani yanayi kafin ta Kauda kai Zakiya ce Tace"Umh...Lalle ana Shagali kalli fa da Yadda Gidan ya cika da manyan Motoci kalli yadda Gidan ya cika fa Shine ke din acuceki sai ace ki zauna agida ke kadai.."Dina Ta saki Dariya Tana Fadin"Kyalesu...Ai na bar musu megadin gidansu yayi musu gadin gidansu..Nima sai nazo aci bikin dani nima ai na zama yar Dangi.."
Zakiya Tace"Kwarai...Kuma ai mu ai abun kunya gaba muka bashi ba Baya ba..Kuma Tunda Dansu ya bari ya Shiga Tarkonmu sai Hakuri.."Dariya suka kara sakawa harda Tafawa Kafin Zakiya ta kashe Motarta su Fara Taku zuwa Cikin Haraban Gidan Daman Zakiya ce Tazo Gidan Taga Dina ita kadai duk sun watse sun barta Shine ta zugata kan ta Shirya Suma sai sunje Bikin Dama Dina nason Fita Ta gaji da zama waje Daya nan da nan ta Shirya suka bar Gidan,Megadi kadai suka bari agidan Hatta su Saudart Tun Jiya suna Gidan Alhaji Tsoho.

Achan Haraban Gidan Alhaji Tsoho Kuwa Zain ne ke Ta neman Zaina bai ganta kuma Da Farko Zafeera ya Tambaya tace mai Tana Dakin Hajiya mama ya Shiga Ciki kuma Hajiya Mama tace yanzu ta Fita Tace zatayi sallama da Amarya Har wajen Yaje bai ganta ba Haddir ya gansa yana ta Neme neme yasa ya Tambayeshi wayake nema yace mai Firsrlove Haddir yace yaje wajen su Zafeera kila suna Tare.
Chapter 74 · 0% Book details