← Book details Zainazain Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 78

Sashe 47

Zainazain Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Babu..Kada ka kara kokarin zuwa Kusa da Zuciyar da Ka Riga ka Bata Rauni Zainullahi...Ka kiyaye Fushina akanka."Daga haka kawai ta Wuce Cikin kuka ta Rufama Zaina Baya,Haka zain ya Duke kawai yana kuka Hawaye na Zuba Alhaji Tsoho na kallo yama kasa mgana Baban kaduna ne ya mike afusace ya isa ga Haddir ya Mikar Dashi Tsaye Sai ji kayi Shima ya bashi Fayau Fayau har guda Biyu Sai da Shima ya Duka Cikin kunar rai yace"Kaima ka bada Gudummuwa wajen Faruwan komai..Meya hana Tun Farkon Wannan Lalacewar ta zain baka Kirani Ko Ni Ko Aliyu ka sanar mana ba In bazaka iya Fadama Usman ba..Don Ubanka ...?

Dagajin yadda yake mgana zaka Fahimci Yadda Ransa ya baci Hajiya Mama na Sharban Hawaye Tana Fadin"Bafa Hadiru bane Abun Duka ga Abun Duka chan...Kai Zainullahi Ka cucemu ka cucu kanka Wlh.."Waje ya Fara Daukan mgana Inna Hannatu da Idanuwanta suka kala sukayi Jajir ta kalli zain Tana Fadin"Baka Fara kuka ba Zain yanzu zaka Fara Tunda kasa iyayenka kuka da Bakincikinka..'Sadiq kuwa Tuni ya Fice yana kuka ganin yayansa Cikin Wannan Halin Zareenaa ma kuka take kamar Ranta zai Fita Haddir kuwa Kasa ya Duka yana kuka yana Fadin"Don Allah kumin aikin Gafara..Nasan zaka ga laifina ammh ban Boye wannan mganar Saboda komai ba sai saboda Rufamana Dan"uwana asiri..Kuma Har ga Allah bansan Har Dawowarmi suna Tare da Dina ba Tunda Tun muna London yayi min alkawrin Dainawa kwata kwata..Ku yarda Dani Wlh Allah bansan komai ba yadda kukaji komai nima Haka naji.."Ya karishe Fada yana Rike Kafafuwan Baban Kaduna wanda ya Fizge yana Fadin"Rufemin baki Shashenshan banza..Ai gashi nan garin Rufamai asiri ka barshi ya saka kansa Cikin Bala'i da mu kanmu iyayanku Dukkansu sai kunci Ubanku kunjima na Rantse..".

Ganin Abun na neman yayi yawa ne yasa Alhaji Tsoho ya Dakatar yana Fadin"Bashir koma ka zauma..Yanzu ba Lokacin wannan bane...Mu zauna mu samu mafita Tunda mai aukuwa ta auku..'Da haka kowa ya koma ya zauna Alhaji Tsoho ya gyara zama yana Fadin"duba da Duka Abubuwan da suka Fara Da Shaidan gani da ido dana ji da kuma amsan ZAIN na cewa ya yarda Cikin nan nashi ne..Toh zanyi ma Abun Duban Fahimta na Farko bazamu bari mu kara aikata wani kuskuran ba..Mganar azubar da ciki bata Taso ba Dole Yarinyar nan zata Haifi Abunda ke Cikinta..!

Baban Kaduna yace"Ta haifa fa kace Alhaji Tsoho..?

Ammh dai ba"ana
ba ko..?

Ina zamu kai wannan Abun kunyar..?

Cikin Mirmishin Takaichi Alhaji Tsoho yace"Anan kuwa..Kuma agidan Iyayen Zainullahi zata Haifa Abunda ke Cikinta.."Kowa Alhaji Tsoho ya zubama Ido Harda Dina da Zakiya Cikin Dattako ya kalli kwamishina yana Fadin"Kwamishina kamin afuwa zanyi maka wani karambani..Abun nan ya Riga ya Faru bamu da yarda zamu sai dai Fatan Allah ya kyauta na gaba..Naji Dadin yadda ka nuna min kai Mutumin kwarai ne wajen Dauko wannan yarinyar ka kawota nan naji Dadi..Nima zan yi amfani da wannan Damar Mu Taru mu Rufama Juna asiri kai dan Siyasa ne Fasuwan wannan mganar matsala ne ga Kimarka,Saboda Haka na yanke Shawaran Yarinyar Wajen naka zata Dawo Nan Bauchi da zama agidan Mahaifin Zainullahi karkashin Kulawa iyayansa Mata Nene da Umman Zareena zasu kula da ita Har ta sauka Lafiya Daganan ta samu tsarki da zasu iya yin auree Bayan haka ni Dakaina in ina Raye zan Daura Auran yarinyar nan da Zainullahi in kuma bana Raye ga ya"yana nan insha Allahu zasu Cikamin wannar Wasiyar Tawa.."Gabadaya Falon sai D'au Shuru Dina kuwa Tun sadda Alhaji Tsoro ya Furta kalmar Aureta Runtse ido tayi Tana jin kamar tatashi Ta Taka Rawa ita bata ma Damu da Cikin jikinta da akace sai ta Haife ba,Domin Soyayyar Zain yasa Take matukar son Cikin Jikinta,ita kuwa zakiya a kunne ta mata rada.

"Finale MRS ZAINULLAHI USMAN SAULAWA.!

Mirmishi Dina ta mata Tana kallon Zakiya kamar ta Goyata su Baban kaduna kuwa basu ma iya mgana ba sanin In Alhaji Tsoho ya yanke Hukunci Shikenan Zain kuwa Kallon Alhaji Tsoho yake cikin Wani yanayin ya zakamin Haka Abba kuwa Kansa na kasa Ko Dagowa bai yi ba,Ballatana ma agane wani Hali yakeciki.

Kwamishina kuwa saboda Murna Har kasa ya Duka yana ma Alhaji Tsoho Godiya Alhaji Tsoho yace"Bakomai..Kada ka Damu..Abunda ya Hadamu bamai Dadi bane..Ammh da yardan Allah zai zama mai Dadi Watarana Ina kuma Fatan Allah ya Shiryama Zuru"a Gabadaya.."Yadinga amsawa da Ameen kafin yace"Ina so zan koma da ita zuwa Sati mai zuwa Sboda zuwan kanwar mahaifiyarta Daga sudan..Zan zaunar da ita na gayamata komai Tunda ya zama Dole tasani kamar uwa Take gareta..Allah barshi bayan Haka ni Dakaina zan kawota wajenka Ranka ya Dade.."Alhaji Tsoho yace"bakomai..Allah ya nuna mana.."
Agogo Fatan Dake hannunsa Kwamishina ya Duba 3pm na Rana ta wuce da Sauri ya Mike yana Fadin"Subhanallah munja Lokaci..Ko Sallar azahar bamu yi ba..Zamu wuce yanzu Alhaji..Nagode kwarai Daka Fahimceni Allah ya kara Kiyayewa.."Alhaji Tsoho ya amsa da Ameen yana Fadin"Dukkamu
mun Shiga Rudani bamu san Lokaci ya Tafi haka ba..Allah ya Tsare yakai ku gida lafiya..!

Da Ameen ya amsa Bayan ya Bashi Hanmu sunyi Musabaha Haka yabi su Baban kaduna suma yayi musu musabaha suka karba Fuska ba Fara Abba ne ba"agane wani yanayi yake Ciki Mikewa Hajiya Batula tayi Dasu zakiya,Hajiya batula nayi musu sallama suka amsa Fuska ba Walwala Mama Safiya ce ma ta Amsa da Allah bamu alheri su Nene kuwa ko kallo Kowacce da Abunda Take Sakawa.

Dina kuwa Zuciyarta Kamar Farar Takarda Saboda Haske Ta gaban Zain tazo ta wuce Tana Fadin.."Ka bar kuka..In ka Rasa Wata matarka..Ga wata nan kuma Uwar ya"yanka ce Insha Allahu.."Tafada a Hankali kasa kasa ba wanda zai jita sai Zain din Wanda ya Dago yana kallonta Cikin Wani irin Tsana da Bakinciki yake Jifanta da wani matsiyancin kallo Mirmishi ta sakamar Lokaci Daya Da gamai Gira kafin ta wuce Zakiya ta mara mai Baya Tana mai kallon Sorry For u Self Dr Zain.

Sai da suka gama Fita kafin Alhaji Tsoho ya yunkura ya mike yana Dogara sandanshi yace"Sallar azahar ta Kubucemana Kowa yaje ya gabatar..Mu Dawo aci Abinci Ayi addu"a kowa yaje ya Huta.."Daga haka ya Fara Dingisawa zuwa Dakinsa Su Baban Kaduna suka Bishi da kallo Har ya Shige,Baban kaduna ne ya Mike Tsaye sai Daddyn Abuja wanda ya saka Hannu ya Mikar da Abba suka fice Batare da sun ma kowa mgana ba Suna Fita Haddir ya mike yabi Bayansu Sai Hajiya mama Tabi bayan Mijinta,Sai Zaneera da Hamdiya suka Shige Dakin Hajiya Mama Daganan sai Inna Rukayyah da Inna Hamnatu da su Mama safiya suka Mike suka Nufi ciki Ko kallon Zain dake zaune Dirshan ba wacce Tayi Laila kuwa kawar Zaina Tun Saddan Zaina ta Shiga ciki Tana kuka ta mike ta Fice Daga Gidan Ta Nufi Gida Tana kuka da mamakin Halin Namiji Damam Abunda Take jiyema zaina kenan Tuni.

Nene ce kadai Ta Rage afalon sai Share kwallah Take ganin haka yasa zain ya Rarrafa gareta Zai Tabata Tayi Saurin Janye kafarta ta mike Tana Juyamai Baya cikin Fitan Hayyaci Da Muryan kuka Yace"Nenee...!

Bata ma Jira cewarsa ba ta wuce Ciki Itama Tana Sharan kwallah Da kallo ya Bita Yana Jin Tsiyayan Hawaye lalle kuwa yau yayi Nadamar aikata Zina gashi Dalilinta Mutane Biyun da basu Taba gujemai ba Sun gujeshi yau wato Fitstlove da Nenensa Duniya Abun Tsoro ne.

Nan ya Durkushe yana kuka Shikadai kamar zai Shide Yana cikin kukan yaji an Dafa kafadansa yana waigowa zatonsa Nene sai gaya Tabawa ce bai san sadda ya Rike hannunta ba ya kara saka kuka yana Fadin"Tabawa na Cucu kaina...Dalilin Biyema zuciya da Shedan yau Firstlove taki Dubana Nene ma haka Umma kuma Ta Daga Hannu ta mareni Wanda Tunda ta Haifeni bata Taba Koda Dungurina ba sai yau.."...

Yafada yana kuka Kansa Take Shafawa Tana kuka Lokaci Daya Tana Fadin"Kayi Hakuri...Jarabawa ce..Allah ya baka Ikon Binta..Zasu sauko Dukkansu kuma zasu yafe maka Bacin Rai ne yanzu.."Kuka kawai yake Kamar karamin Yaro kafin ya mike Zumbur yana Fadin"Ina jin kunya..Ina Jin kunyar kara Haduwa da wani Ahalina ayanzu Tabawa..".

Daga haka kawai ya saki Hannunta ya Fice kamar walkiya yana zuwa Haraban Gidan yaga su Abba na Sallah sunyi Jami"i ne Dadyn Abuja ke Bada Sallar Haddir ma na Cikin Sahu Hango Key din Motar Haddir yayi agabansa yasa ya karisa da Sauri ya Dauka Duka suna kallonsa ba Halin mgana Tunda suna sallah suna Ji ya shiga Motar Haddir ya Fice Daga Gidan da Gudun Kamar zai Tashi sama.
*Shakira...*
*ZAINAZAIN..!*
_(Is a love Story and Betrayal)_
*Wattpad:Jamilaumar351*
*Mallakar:Janaftyshakira*
*BOOK 1*
"Zain na Fita Daga Gidan Alhaji Tsoho Sai ya rasa Duka Natsuwarsa Tuki yake ammh ba
Cikin Hayyacinsa ba Kuka yake kukan Nadama da Danasanin Abunda ya aikata yau gashi ya Girbi Abunda ya Shuka.

Iyayensa Da Duka Danginsa yau ba wanda ya kalleshi Matarsa yau Ta shiga wani Hali Saboda Shi Daman irin wannan Ranar yake ta Tsoron gashi yau tazo mai acikin yanayin da bai kamata ba, Tafe yake yama Rasa ina Zashi ayau ya Tabbatar da kansa Duk Abunda zaka aikata kada ka kaucema Umranin Allah In baka Kauce ba kowani Hali zaka Shiga zakaga Allah ya baka Mafita in kuma ka Kauce ma Umarnin Allah Zaka Dade kana Yadda kaga Dama Ranar da Allah yayi Niyar kamaka bazakaji Da Dadi ba Kashima sai yafika Daraja kuma Haka Rayuwarka zata Shiga kilaWakalan Bakinciki Da Damuwa na Har Abada.

Yana Tafe yana kuka Lokaci Daya kuma yana Tuki Haka ya Dinga Zagaye Titunan garin Bauchi Yarasa Ina zashi..?

Wajen wa zai Nufa.?

Allah kawai ke Tsarewa ammh Wajen Sau Biyu yana Buga ma Mutane Mota Saboda baya Cikin Natsuwarsa,Daya gaji ne yasa ya samu Wani masallaci ya shiga yayi sallar Azahar da La"asar nam ya zauna Cikin Masallacin yana ta Rokon Allah Gafara ga Cikinsa na Jin yunwa ammh kwata kwata Bakinsa bayajin Zai iya saka wani Abu.
Chapter 47 · 0% Book details