← Book details Zainazain Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 76 OF 78

Sashe 76

Zainazain Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin Raunin Murya yace"Baba zan karbo Takardan ne..Na Tabbata Firstlove ta Rubuta shi.."Baban Kaduna ya Jashi Ya zaunar Dashi Saman kujera yana Fadin"Zauna..kai Hadiru karbo Takardan chan muga kome ke Ciki.."
Yafada yana kallon Haddir Ba yadda Zain ya iya Dole ya koma ya zauna yana Sharan Zufa Lokaci Daya Yana Sakin Numfashi Sama Sama Abba na kallonsa Cike da Tsausayawa Haddir ya Taka gaban Zainab ya karbo Takardan ya kawo gaban Baban Kaduna Cikin Umarni Alhaji Tsoho yace"Kai Hadiru Warwareta ka karanta Kowa yaji..Tashafi kowa Tunda ta Shafi Fatima da Usman dashi kanshi Zainullahin da kuma Goggonta Halima ka karanta Kowa yaji.."
Cikin Bin Umarni Haddir ya warware Takardan sai ga Dogon Rubutun Zaina ya Bayyana Cikin Budewar murya yadda Kowa zai ji ya Fara karantawa Yayinda Falon ya Dau Shuru kowa na Sauraransa Hatta kuwa da Umma Dake kuka Amarya Hamdiya na Gefen Mom iklima Tuni Ta bar kuka Ta koma Jajanta wannan lamarin yayinda Dina da Zakiya suka saka kunni suna son suji wani sako wannan Takardan Take Dauke dashi
_Assalama irin Ta Addinin Musulunci Assalamu Alaikum Warahamatullahi Ta"ala Wabarakatuhu,Nasan
zaku yi mamakin ganin wannan Sakon nawa ammh kuma ya zama Dole Kuma Ina da Tabbacin Lokacin da zaku ga Sakon nan na Riga nayi Nisa da Garin Bauchi,Shiyasa nace Sakon kai Tsaye ga Umma ne Da Abba sai kuma Firstlove,Alhaji Tsoho da Goggo Halima kafin nace komai zan Fara da Neman afuwanku Bisa wannan Hukuncin Dana yanke batare da nayi Shawara da kowa ba..Nasan Cewa Wannan Abunda na aikata bazai muku Dadi ba in kuka nemi kuka Raasa kuma kuka Fahimci Cewa na Bar ku ne,Da Farko zan Fara da Baki Hakuri Umma Don Allah ki yafemin Ba"a son Raina na Tafi na barki ba kuma ba Niyyata Na Bijerema Umarnin ki ba ko na saba miki ba..!ko na Watsa Miki kasa a ido ba..!

Umma Tun ina Jaririyata na Rasa Duka iyayena kika Tallafeni kika zama Uwa gareni kika Fifitani sama da ya"yan da kika Haifa,Da ace mata da yawa zasu koyi da irin Halinki da sun Dace kin kasace Uwa Tagari mai maida D'an wani nata kin Soni Da Zuciya Daya kin Fifitani kan Abunda kika Haifa Saboda kina So ki inganta Rayuwata kin Kuntatama Abunda kika Haifa saboda ni Umma Sai dai ni na kasa Miki Hallaci bazan iya juran Rabani da Firstlove ba da zaki yi ba Umma Ina sonshi ina kaunarsa Shine Raunina Shi na sani Shine komai nawa Umma Shine Duniyata Zuciyata bazata iya Daukan abubuwa Biyu alokaci Daya ba..Umma ban yanke Shawaran yin nesa daku ba sai da naga kin Fahimci ina da Shigar Cikin Firstlove ajikina Wanda Duk da banje asibiti an Dubani ba ammh Duka alamomin masu Suna Bayyana ciki Gareni Nayi kokarin Na Sirrinta Abun kada ki sani sai dai hakan bai Faru ba, kin gano ina da ciki kuma Kin Fadamin zaki Zubar dashi Saboda Kina son Cigabana baza ki barni na Cigaba da Zama da Firsrlove ba Umma ina son Cikina naji ina kaunarsa Kuma nayi alkawarin zan kare lafiyarsa Muddin Raina Koda wajen Haihuwarsa zan Rasa Raina Na yarda na amince na Haifama Firstlove Wani Abu Daga Tsatsona Daga karshe Umma ina mai neman Gafaranki Don Allah ki yafemim kuma ina Rokon alfarman da ki yafema Firstlove koda wannan ne alfarma ta Karshe da zaki man Ummata..Sai Abba Kaima Zan Roke Gafara Domin kaima Uba ne gareni ka Rikeni Tsakani ga Allah ka Hadani da ya"yanka ka Inganta Rayuwata alhalin ni ba Kowan kowa bace Face Diyar Maryamai mai aiki da Abdullahi megadi ammh baku Duba wannan ba ka Rikeni kabani Dukkan gata Ina matukar Gode maka ka cika Uba nagari Abba ka yafemin Don Allah Kuma ka yafemin Firstlove Abun da ya faru Bawa baya wuce kaddaransa,Abba bazan cigaba da zama ina ganin kana Fushi da Firstlove ba Kana hanashi shiga gidanka ba Duk Saboda ni ba..Shiyasa naga Tafiya ta itace Mafita kaima Don Allah ka yafema Firstlove Na Tabbata Nadamarsa ta Gaskiya ce bazai kara aikata makamancin haka ba,Sai Kai Firstlove Mijina Abun alfaharina Bangona Majingina komai zaka min aduniyan nan na Riga nayafe maka Duniya da Lahira,Kayi Rayuwa cikin Jajayen Fata kaga mata kala kala Wadanda suka fini komai da komai ammh kace sai ni din nan Kamin komai aduniya ka nuna min kauna Ka soni Ka kaunace ni kuwa dame zam saka maka.?

Zuciyata tayi Rauni Lokacin da Naga Wata amatsayin Wacce kake Rabamana na Rayuwa da ita naji Dama na iya Fincike sonka acikin Raina sai dai ina Bani ke Sarrfa Zuciyata ba naji na kasa sai ma karin kaunarka da Tsausayinka dakeCin Raina akullim ina kwana kuka ne ba Saboda komai ba sai saboda Tsausayina da Tsausayin kanka bazan Juri Raunin Rasa ka ba kuma bazan Juri Raunin wata ta sameka ba kuma Bazan juri Raunin Rasa Cikin Jikina ba Shiyasa na zabi na Tafi waje mai Nisa Zuwa Lokacin da komai zai Daidaita ka sani na yafe maka Nima ka yafemin Tare damin alfarman Barin Igiyar Auranka akaina Koda bazamu sake Haduwa ba...Nayi maka alkawarin kula da kaina da Abunda ke Cikina In har muna da Rabon Haduwa Shikenan in kuma ta yanke sai da nace Sai Wata rana..!

Alhaji Tsoho Dattojon arziiki kuma Wanda ya Tara Zuru"a ta kwarai Babu Abunda zan ce maka kai da Zuru"anka sai Godiya Allah ya saka muku da alheri,Kamin Nasiha na ki Jin mganarka nasan zakaji zafin wannan Hukuncin Dana yanke ammh kuma Shine daidai awajena Katayani Bama goggo Halima Hakuri kuma Don Allah komai zataji kan Firstlove kada Tayi Tir Dashi Ta Dubi mganar da Fuskan Basira,dangina da yan"uwa na Gada da kuma Ukti,Faruq,Anty Zareena da kowa da kowa nasan bazaku ji Dadi Ba Dake zainab Ammh don Allah ku yafemin ku sani Duk inda zani zanyi matukar kewarku..Kada kusha Wahalan nema na nayi Nisa Na Tafi bansan Inda zani ba ammh kuma In da Rabo zan Dawo Insha Allahu Zuwa wani Lokaci in kuma ba Rabon ganawarmu sai nace Allah ya Hada Fuskokinmu a Darussalam..masallam_!

Gabadaya Falon ya Dauki wani irin Shuru kafin kuma ya Kaure da Salallami da kuma Koke koke Umma kasa ta Durkushe Tana Fadin"Innalillahi...Wayyo Ni Fatima me na aikata..?

Nayi sanadiyar Yata ta bar gida ina zata..!

Wlh koda na Rantse zan Raba wannan auran Daga Baya nayi Nadama har cikin Raina kuma nayi Niyyar maida ta Gidan Mijinta na yarda zanyi kaffara Saboda haka,Kuma mgana Ciki Wlh harga Allah Shine Shaidata Ba Har raina na Fada ba gatse nayi mata ganin tana kuka ashe ashe ita Ta Dauka Da gaske ne.."Ta karishe Fada Cikin Kuka Hajiya mama na Sharan kwallah Tana Fadin"Kinga Abunda kika aikata Ko Fatima..?

Dama na gaya miki Abunda Hakuri bai bamu ba Wlh a kasasin bazai bamu Ba gashi yarinyar Tabar gida yanzu wani Hali zata Fada bamu sani ba.."
Abba kansa kawai ya Dafe Yana Salallami Baban kaduna ma Haka su Mama Safiya Kowa dai afalon Sai salati ke tashi Zafeera da Zainab kuwa sai kuka Suke Dina ce kadai Take Farinciki Sosai Zuciyarta Kamar farar Takarda,Alhaji Tsoho kai ya Sadda kasa yana Kiran Sunan Allah,Goggo Halima kuwa Da ta Shiga Rudi Da kuma Rashin Gane ina aka Dosa ta kalli Hajiya Mama Tana Fadin"Hajiya mama me ya Faru ne..?

Halima Tayi gangancin me ya Faru da zafi da zata yanke irin wannan Hukuncin Tana yarinya karama ga Danyan Ciki Tare da ita kai Innalillahi.."
Hajiya Mama Ta girgiza kai Cikin Sharan Hawaye Tana Fadin"Bari kawai Halima Mganar mai Tsayi ce sai mun zauna.."Hajiya Mama bata gama Rufe bakinta ba Zain ya Mike Tsaye da karfi sai Lokacin ya samu Damar mikewa,Tun Sadda Haddir yake karanta Takardan Gabadaya Muryan Zaina ke mai yawo a kunnuwansa gabbansa sun saki Kafafunsa sun gaza Daukansa bai Kara Shiga wani irin Rudewa ba sai da ya fahinci Zaina Ta tafi Ta barshi Sannan kuma Tana Dauke da Cikinsa ajikinta Tundaga Lokacin bai kara Fahimtar komai ba Domin Jinsa Da ganinsa ne ya Dauke alokacin sai yanzu yaji kamar ya Dawo Cikin Duniyar.

Gabadaya aka Zubamai Ido ana kallonsa ganinsa yana Nuna Hannu yana so yayi mgana ya kasa Runtse ido yayi wasu Zafafan Hawaye suka zubomai Cikin Rawan murya kamar mai In ina yace"First...L..O..v..e...Ta..tafi...Ta..barni.Kuma..Ta...na...Da...Cikii...naaaa...!bai ida karisa mgarsa ba Kawai ya Sulale ya Fadi nan da Karfi sai kaji Tim nan da nan Idanuwansa suka kafe ba Numfashi Cikin Tashin Hankali su Abba dasu Daddyn da Baban Kaduna da Haddir suka Rufu kansa Cikin Rudewa da wani Tashin Hankali Haddir da Baban kaduna Suka Tallafeshi suna Kiran Sunansa ammh ko Motsi Abba Dake gefe ya Rikice Hakama Su Umma sai kuka ya kara Tashi Dina Dake gefe ganin Zain baya Motsi ya Tada hankalinta Ta nufi Wajenshi Tana Zuwa Ta ture Haddir Dake Rike da kansa Baki ya saki yana kallonta Cikin Tashin hankali ta Rike Hannunsa Tana Fadin"Na Shiga uku plz zain don"t do this to me..Kada ka Tafi ka barni da Cikinka.In ita bata Sonka ni ina Sonka Zan zauna dakai nayi maka Duk Abund
a take maka Don Allah ka tashi.."Sai kuma ta saka kuka Galala kowa ke kallonta sai Lokacin ma Su Umma suka ganta Cike da mamaki Wadanda basu san Labarin Dina ba suka saki baki Cikin mamaki irin su Goggo Halima.

Kowa ya kasa mata Mgana Sai Baban Kaduna ne ya Fizge Hannun Zain din yana Fadin"Ke miye haka..?

Wannan wani
Rashin Hankali ne..?

Baki ganin Halin Dayake ciki..?

Ya Fada Cikin Takaichi kamar ya maketa Kuka ta kara sakamai Zatayi mgana Zakiya tazo Ta jata Tana Fadin"Kuyi Hakuri Don Allah..Ta saka Control din kanta ne Da Halin Dayake Ciki ne.."Inna Hannatu Dake Gefe ta Lailayo Ashar Tana Fadin"Kaza kazan Halin Data ke ciki..

Duk son data kemai Takai mahaifansa ne..?

Nace baga uwarsa nan da Ubansa ba Me kika ga sunyi..?
Chapter 76 · 0% Book details