← Book details Zainazain Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 78

Sashe 24

Zainazain Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dr.Dina kuwa na Fita Daga Office Din Zain Hanyar barin Cikin aaibitin Ta Nufa Tana Tafe Tana Sharban Hawayen da ta kaasa Hanasu Zubowa,Allah ya Taimaketa bata Hadu da wani Likita ba sai dai Nurses da Metro wadanda ke mata kallon Ko lafiya wasu kuma suka Fara Gulman cewa Dama ai ita ke Bin Dr zain ammh Shi kallo bata Isheshi ba,Ahaka dai ta kai kanta Haraban Ajiyan Motoci Ta Bude Motarta ta Shiga Tayi mata Key idanuwanta Har Rufewa suka Farayi saboda kuka da Bacin Rai Da gudu ta yi Riverse ta Saki Hon aka Wangalemata Get tafice da Gudu Daga Cikin asibitin kamar azata Tashi sama Kai Tsaye Hanyar kano ta Dauka Domin Haka Kurum taji Tana Bukatar Zuwa Gida ko Zataji Sanyi Ko taje wajen zakiya mganar Duk Dayane Wlh zain yana so yayi mata Wulakanci kuma Wlh karyansa,Tana Tsausayamai bataso komai ya kwacemai ammh zai Fusata tayi Abunda batayi Niyyah ba,Haka tayi ta Sharara gudu kamar zata tashi sama.
*****
Yau da Halima Tatashi Daga School Sun gama Lecture da Wuri Wajen 12pm ta Fito Daga Cikim makaranta Sai da ta Shiga Motarta ta Kira Zain Bayan ya Dauka sun yi gaisuwan da suka saba da Tambayan lafiya juna ta tambayeshi Tana so Taje Gidansu Laila Ta Duba Mamarta Bata da lafiya Dazu sukayi mgana da Lailar ganin batazo School ba yasa ta Kirata nan take Shaida mata Mamarta bata ji Dadi ba Batare da wani Tunani ba Zain yace Taje ammh Ta Tuka kanta a Hankali ta kuma kula da Kanta ta kuma Dawo da Wuri Domin Shima Bayan Sallar Jumma"a zai Dawo Gida Da Haka suka Rabu.

Laila Suna zaune a anguwan yakubu Wanka ne,Koda Taje Jikim Mamar na Laila da Sauki Tunda Har an Cire mata karin Ruwan Da aka saka mata nan Halima Ta gaisheta da Jiki ta amsa Cikin Sakin Fuska Tana Tambayanta megidanta Daganan Dakin Laila suka Shigo Suna Hira Halima na Fadama Laila Karatun da sukayi a makaranta yau bata wani Jima ba ta mata Sallama ta Tafi da alkawarin gobe zata Dawo ganin yau din Bata Riko ma Mamar Lailan komai ba.

Har Wajen Mota Laila ta Rakata Sukayi sallama Daganan Gida ta Koma Tayi wanka ta Shiga Kitchen Tayi Tuwon Shinkafa Miyar agun da Tok Fish Saboda Alhaji Tsoho da Kuma Abba ta Riga ta saba Tunda sukayi Aure Da Zain Duk Jumma"a bata Fashi Sai tayi musu wannan Tuwon Takai musu,Tana kamallahwa ta Saka a kololi guda Biyu Daya na Gidan Alhaji Tsoho Daya na Gida ne,na Abba kenan Sauran kuma ta Zuba ma
Tanimu megadi nashi Sauran kuma ta Saka Cikin Wata karamar kula nata Dana Zain kenan Dama Tun Da Tadawo Zobo Ta Fara Hadawa ta saka a Fridge saboda yayi sanyi.

Sai dai ta Gyara Kitchen din kana ta Koma Cikin Bedroom Ta Shiga Dama bayan ta Dawo Sai Taga Jinin al"ada yazo mata Tana Cikin Toilet tana Wanka Zain ya Shigo Gidan Bayan ya Shigo Dakin Jinta Tana wanka yasa Shima ya kwabe yabi ta Chan Bayi sai ta ganshi kawai ya Shigo Bata damu ba sanin Dama Yawanci Tare suke wanka nan suka Hadu sukayi wanka bayan an Sha Shafe Shafen Juna kafin su Fito Tare suka Shirya kansu Ita Shigar abaya Tayi Domin Halima Tana son Abaya Sosai Shiyasa Zain ya Cikamata Wardrope dinta dasu Shi kuma wani yadi ya saka mai Santsi Falo Suka Fita suka baje sukayi Dinner kana sukayi Shirin Fita Zain shi ya Dauki Duka Kololin Tuwon Ita kuma ta Dauko na Miya Sai Wani katon Jug da Zobo na Abba ne Alhaji Tsoho baya Chan Zobo,sai da suka kai komai Cikin Booth din Motar Halimar kana ta Koma ta Daukoma Tanimu megadi nashi haka ya Duka Har kasa yana mata Godiya da Kirarin Gimbiya agidan Dakta.

Shidai Zain gabam Motar ya kame Saboda yace mata a Motarta Zasu Fita ita zata Tukasu ganin ta Biyema Surutun Tanimu ne yasa ya Fara latsa mata Hon da Sauri ta Sallameshi bayan tace ya Bude mata get da Gudu ya wuce Yana Fadin"Angama Uwargidan Dakta..Amaryama kuma Insha Allahu Daga ke ba kari gimbiya agidan Dakta..!

Yafada yana yar Dariya Mirmishi kawai ta saki ta Juya ta Shiga Motar kallonta ZAIN yayi yana Fadin"Meyasa kike Biyema Shirmen Tanimu ne..?

Shifa baya gajiya ko kwana zaku yi kuna Mgana..!

Mirmishi ta Saki Lokaci Daya Tana ma Motar key Ta tasheta tayi Kwana ta Saki Hon kafin ta Sulala ta Fice Daga Gidan Tanimu na Faman Daga mushi Hannu Shi kuwa Fadi yake"Kai Tirr...Ga Gimbiyar Dakta..Tana Tuka Daktan da kanshi Allah bar kauna Kaji..!

Sai da ta Daidata Tafiya kan Titi kana ta Saki yar Dariya Tana Fadin"Allah Tanimu na Tuna min da wani Idi akusa da gidan Goggo Halima Dake gada..Surutunsu da komai nasu Iri Daya ne.."Zain na Latsa wayarsa yace"Kidaina dai Biyemai Zainata..Karki manta ke Matar Dr.Zain ce..!

Mirmishi Ta Saki kafin tace"Insha Allahi Zain Dina..!

Hannunta Datake Driving yakai ma Kiss Yana Fadin"Nagode zainata..!

Hira suka Fara sama sama Cikin Hiran ne Halima ta Kalli Zain Tana Fadin"Firstlove wai yaushe Zamu je Gada ne..?

Ina son ganin Goggo Halima bansani ba ko lafiya kwana Biyu ina ta Kiran Layinta bana samu..!

Kansa ya Shafa yana Fadin"Ki bari ku samu Hutu mana..Nima Kinga bani da Lokaci ko Weekend ne ina Shiga asibiti.." bata som mai musu yasa Tace"Shikenan Allah ya kaimu.." shi kuma ganin kamar ta Damu yasa yace"Karki damu ba komai..Tunda baki sameta ba ki kira Layin Isuhu mana kiji ko Lafiya..?

Da Sauri tace"Kash nako manta da Kiran Ya Isuhu bari mu Daawo zan Kirasa naji ko lafiya..?

Kai kawai ya gyada mata yana Cigaba da Latsa wayarsa ahaka har suka kai Gra Gidan Abba suka Fara Zuwa Sun ci sa"a kuma yana Gida Tana Shigowa da Kololi Bayanta kuma zain ne da kulan miya da Jug Din Zobo Nene Tace"Mungode Allah Da zuwanki Halima Domin ga Abbanki nan Duk Abincin da muka gama Jeramai yaki Taba komai yana Jiran Tuwonki..!

Zain da Halima suka saki Mirmishi Abba kuwa yana Zaune kan Daya Cikin Kujerun Falon ya Sauko kasa yana Fadin"Allah yayi miki Albarka Diyata..Bani nan Kigani Hannuna Dama Tun dazu na wankeshi ke nake jira..'Gabadaya suka sakamai Dariya Har Umma data Fito Daga Kitchen nan Halima ta Baje komai Bayan Taje Kitchen ta Dauko Filet da Cokali ta Zubama Abba Kin karban Cokalin yayi yana Fadin"Bar ni na saka Hannuna Dashi Annabin Rahma ke Cin Abinci..!

Umma na Gefe Tace"Ba Tayi ne Abba..?

Kai ya girgiza mata yana kai Lomar Tuwo yana Fadin"A"a fa kuci Abincin ku yau na yafe..Wannan Tuwon Har Dumamen Gobe..'" Su zain Suna ta Dariya nan aka zauna ana ta Hira Halima ta Tambayi su Saudarta Nene tace suna gidan Alhaji Tsoho.

Basu bar Gidan ba sai Bayan Sallar La"asar suka isa Gidan Alhaji Tsoho Shima chan Hajiya Mama Nata Fama Dashi yakin Cin komai yana Jiran Tuwon Halima Suna zuwa Hajiya mama tace"Nikam Halima wani Boka kika kai Sunan Mijina ya kamashi haka..?

Aka saka Dariya Alhaji Tsoho nacin Tuwonsa yana Fadin"Ba Boka ba Mallam..Yin Allah ne Ko Hali Dubu..?

Halima ta Daga kai Tana Fadin"Gayamata dai Tsoho..Kyaleta Kishi Take dani..!

Hajiya Mama tace"Nima ai na Rama Domin Zainullahi yanzu Nawa ne.."Halima na Dariya Tace"Wane ke..?Mata ma Dadama sun gwada sun kasa ai Ba wacce ta Isa ne Ni da Firatlove Takalmin kaza kenan.."Zain yace"Kin Fadi gaskiya Zainata.." hararansa Hajiya Mama Tayi Tana Fadin"Au bayanta kabi.." yana Dariya Yace"Toh yana iya Hajja mama..?

Ki dau na Annabawa kawai..!

Gabadayansu Dariya suka saka Nan suka kai Dare har sallar mangariba nan sukayi suna Shirin Tafiya ne sai ga Haddir da kaya yayo parking din kayansa ya dawo gidan Alhaji Tsoho Zain sai Dariya yakai mai yana Fadin"Wanda Yaja da Likitan kwakwalwa zai ga ba Daidai ba..!

Alhaji Tsoho na Zaune yana Sakacen Hakorinsa Daya gama Cin Nama yana Fadin"Kwarai Matukar ina Raye Idanuwana na kan Jikokina Musamman ma Kai da Hadiru...'Haddir bai Tankashi ba Fuskarsa ba Walwala ganin Haka yasa Hajiya Mama da Tabawa suka Rika Tayashi kwasan kayansa Zuwa Bedroom Din Dake kusa dana Alhaji Tsoho Tana Fadin ta Sauya Miji ga Hadiru Yaro Sammari ga kyau ga Kudi me zatayi Da Ragowan Halima.

Sai Dariya ake Zuwan Haddir yasa suka Kara Shantakewa sai Wajen karfe 9pm suka koma Gida,Zain yana Cike da
Bukatarta Ganin Tana Fashin Sallah yasa ta Lallabashi ta mai Dubarin Datake mai in Tana Cikin Jinin Al"ada har ya samu ya gamsu suka kamkame juna Har Barci mai Nauyi mai Dadi ya kwashesu.
*Shakira..*
*ZAINAZAIN..!*
_(Is a love Story and Betrayal)_
*Wattpad:Jamilaumar351*
*Mallakar:Janaftyshakira*
*BOOK 1*
*KANO...*
_Area:Sabuwar kofa..!_
"Kwance Take Kan mamaken Royal Bed wanda yaji Shinfudun Alfarman,Misalin karfe 10:46am na safe na Ranar Lahadin karshen mako.

Motsawa Tayi Ta leko Da kanta cikin katon bargon Datake ciki Lokacin Da Taji Karar Wayarta Dake saman Side Drower din Gadon,Hannu ta zira tana wani yamutsa Fuska Lokaci Daya Ta Jawo Wayar nata ganin Sunan Zakiya Ya bayyana baro baro saman Sreen Din Wayar nata yasa Ta Daga Cikim kasala Tana Fadin
"Zakiya yane...!

Dagachan Bangaran Zakiya Tace"Kina ina ne nazo naga gidanki a kulle..?

Ko kina Cikin asibitin ne..?

Wani Hamma Dina Ta tattaro ta sakarma Zakiya Tana gyara zaman Blanket din Data Rufu Dashi Take Fadin"Ina anguwar Sabuwar Kofa...!

Cikin Mamaki Zakiya Tace"Kano..?

Dakai Dina Ta mata amfani Wajen bata amsa Kafin Tace"Eh ina Kano..Tun Ranar Friday na Taho.." Zakiya Ta gyara Tsayuwarta Jikin Bakar Motar kirar prado Tace"Ke kuwa me kika je yi kano Haka da gaggawa ba Labari..?

Karamin Tsaki Dina Taja Lokaci Daya Tana yamutsa Fuska Kafin ta Yunkura ta Mike zaune ta Jinkina Bayanta da Jikin Gadon Lokaci Daya Tana Fadin"Hmm Bari kawai Zakiya Wai ni Zain ya kora Daga Office Dinsa..."
Cikin Zaro Ido Zakiya Tace"Kora kuma..? cikin Takaichi Dina Tace"Wlh Korar kare yayi min Ranar friday Dana Shiga Cikin Asibiti,Abunda ya bani Tsoro Shine wani kallon Tsana Danaga Yana Bina Dashi Abun ya bani Tsoro Sosai...!
Chapter 24 · 0% Book details