← Book details Zainazain Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 78

Sashe 32

Zainazain Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kafin wayewar gari Labarin Ciwon Alhaji Tsoho yakai kunnan Duka ya"yansa Dalilin Dayasa Zafeera ta Fasa Tafiya kenan Zain ma yana Gida Nene ta Kirashi ta Shaidamai Hankali Tashe Shida Zainarsa suka Nufi asibitin,Hakama Abba Da su Umma da Nene da Zainab da Zafeera su Saudat suna makaranta Kafin karfe goman Safe Hatta Baban Kaduna da Dadyn Abuja sun iso Inna Rukayyah ce ta Kira tace tana Hanya Inna Hannatu kuma ta biyo Jirgi Itama Duka Hankalinsu ya Tashi Lokaci Daya Hatta su Zareena Dake Kasar U.S Haddir ya Kira Jawaad ya Fadamai sai Kira Zareena take tana Tambayan Jikin na Alhaji Tsoho.

Dina Bata sani ba sai da Ta Shigo Cikin Asibitin Taga yadda Asibitin ya Cika ga yalwar Motoci a parking Space,Ta faka Motarta kenan tana Shirin Fitowa Misalin 12pm na Rana sai ga Motar Haddir ta Shigo Cikin Asibitin Inda ya Dauko Inma Hannatu Daga Filin Jirgi ita da Autarta Maryama,Agaban idon Dina suka Firfito Daga Motan zuwa Cikin asibitin Gabanta ya Fadi Domin Taga Tsantsan kama da Zain din akan Fuskar matar sai ta Fara Tunanim ko mahaifiyarsa ne..?

Cikin asibitin ta Shiga sai kuwa suka ci karo da Dr Aisha ita ta Tambaya take Fadamata Mai asibitin aka kawo ba lafiya Kakan Zain da Haddir Dr Saulawa Ido Dina ta kwalalo Tana Fadin"Kai don Allah Tun yaushe..?

Dr Aisha tace"Tun Cikin Dare..Su Dr Imran sukayi Attempting Dinsa ammh yanzu da Sauki Tun safe Jikokinsa da ya"yansa suka Cika asbitin nan.."Dina tace"Allah sarki Allah bashi lafiya.."Dr Aisha tace Ameen harzata wuce Dr Aisha tace Mata"Ki shiga ki Dubashi mana Yana Family Side Dinsu.."Kai kawai Dina ta kada mata Jikinta asanyaye ta wuce Office dinta tana Jin wani Sanyin Jiki Taya zata Hadu da Ahalin Zain bayan kuma suna kam Shirya wani Abu..?

Haka ta isa office dinta sukuku har ta zauna bata da Natsuwa patient din ma sama sama take Dubasu Duka duka goma ta Duba ta kira wata Nurse tace ta kwashe Sauran Folder din ta kaima Dr Aisha batajin Dadin Jikinta ita kuma ta maida kanta ta jingina da kujera ta Dauko Wayarta ta Doka ma Zakiya Kira Don Ta bata mafita.
*Janafty...*
*ZAINAZAIN..!*
_(Is a love Story and Betrayal)_
*Wattpad:Jamilaumar351*
*Mallakar:Janaftyshakira*
*BOOK 1*
"Koda ta Kira Zakiya ta gayamata Abunda ke Faruwa karamar Dariya Zakiya tayi kafin Tace"Sai me..?

Kema Dangin ki ne nan da Lokaci kadan zaki zama Daya Daga Cikinsu So ya kamata ku Hadu Duk yana Cikin plan dinmu ne..!

Dina Ta saki Numfashi Tana Fadin"Zan iya kuwa Zakiya..?ina jin wani iri zuciyata tana Rawa Taya zan Fara Tunkararsu yanzu..?

Zakiya tace"Karki Damu ki Jira zuwa nan da 3pm zan tashi Daga office zan biyo nan asibitin zan Rakaki sai muje mu gaida inlaws dinki.."Ta karishe Fada Cikin Dariyan Shakiyanci kashe wayarta kawai Dina tayi tana maida Numfashi Har acikin Ranta tana jin Wani iri bayan Haddir da Zaina adagin Zain bata taba Haduwa da kowa ba Zuciyarta na Rawa Tun yanzu kafin ma su san Ita din Wacece a wajen Zain.

Haka kuwa akayi Misalin 3pm na Rana sai ga Zakiya tazo Cikin Asibitin Lokacin Har Dina ta koma Gida tayi wanka ta Sauya Shiga Zuwa Wata Abaya mai Ruwan Coffea,Ta yane kanta da Vail din Abayan wacce ta Bayyana Suran Jikinta,Kafarta sanye Cikin Wani Damdamalin Takalmi Fuskarta ba kwalliya ammh Sanin Dina mai kyau ce ko Batayi kwalliya ba kyanta yana Haskawa Ita kuma Zakiya Doguwar Atamfa ce ke jikinta wacce ta kamata sosai Daga mazaunanta,Kanta ba Dankwali Sai da ta yafa wani Vail a Kanta zuwa Saman Kafadarta Takalmin kafarta ma mai Tsini Ne sai wani Glass Data Toshe Fuskarta,Hannunta Dauke Da karamar Jaka lokaci Daya kuma Tana Kada key din Motarta akallon Farko in kayi musu sai ka kara Domin Sun amsa Sunansu na Mata masu aji da Baiwar iya Taku da isa da kuma Haiba Iya Sarrafa Jikinsu.

Zakiya Tayi ta kara ma Dina karfin Gwiwa Tunda ita ta Sare,kuma ganin Kowa nata zuwa gaishe da Alhaji Tsohon zakiya ta nuna mata in bataje Ba, Zain bazai ji Dadi ba Da wadanan kalaman Ta kara jan Ra"ayinta Ta jata suka Nufi Family Side na Cikin Asibitin.

Duk wanda ke asibitin Dr.Saulawa ya san da wannan Shashin,Shashi ne wanda Dr.Saulawa tun yana da karfinsa yasa aka samar Dashi Saboda iyalansa da yan"uwa da abokan arzuka nan ake Attempting Dinsu har su samu lafiya Shashi ne mai matukar Girma da kawatuwa,Koda yaushe Cikin Gyarashi ake da Sauyamai Fasali,Duka iyalansa ba Wanda bai da Fayel acikin asibitin Saboda Halin Rayuwa Dr.Saulawa da kansa yayi ma Shashin Lakabi da Fanmiy Side.

Daki na Mussmman Mai dan Girma ne Alhaji Tsohon ke Ciki Kofar tana Rufe ne ammh Kana jin Hayaniyar mutane kadan Kadan Daga Ciki Zakiya ce tayi Knooking Din kofar kafin ta Tura ta Fara Shiga da karamar Sallama Hannunta jaye da Hannun Dina Wacce Take jin Wani irin Faduwar gaba kamar ta arce ta gudu,Suna Shigowa Dakin Gabadaya kallo ya Dawo Garesu Sai da suka kariso Tsakiyar Dakin zakiya Taja ta Tsaya Itama Dinar sai ta Tsaya cak,wanda yaji kayan alfarma kamar ba asibiti ba kama Daga Cafet,Kayan kallo kujeru Da kuma Abun Sanyaya Daki A.C,Fridge, Sai gadon Mara lafiya Dake gefe chan Shima din Wani Tsararra ne,Wanda ba Daya yake da Sauran gadajen Dake Cikin Asibitin ba Daga gani na Musamman ne kamar yadda Barayin Ko Shashin yake na Musamman.

Baban Kaduna da Daddyn Abuja sai Abba Usman Suna zaune kan kujeran Dake Gefe,Yayinda mai kallonsu kuma Mom Iklima da Mama Safiya sai Nene ke zaune akai,Daga gefe kuma kan Wata Farar kujera Inna Rukayyah ce zaune,Daga Saman Cafet din kuma Umma ce da Inna Hannatu,Daga saman Gadon da Alhaji Tsoho ke Kishigide Bayan an karamai Filo abayansa kuma Hajiya Mama ce ke zaune gefensa Itama Daga gefenta Zain ne zaune ya yada Kafadarsa Bisa Kafadarta Suna mgana kasa Kasa Daga Tsaye kuma Haddir ne Wanda ya coge Hankalinsa kaco kan yana kan Wayarsa ne,Daga tsakarwajen kuma ga manya manya kololi nan Baje na Abinci sai manya manya Ledoji na kayan Marmari,Daga yanayinsi zaka Fahimci Tabbas Ahalin ya Cika Ahali kuma Ahali ne na Girma Da Dattako.

Da yin Sallamarsu Dama Wajen yayi Tsit duk da Farko Hira na Tashi Sama sama,Gabadaya ido Suka zuba musu suna kallonsu Sama sama da kasa Duk da Baki sun Ta shigowa wasu ba saninsu sukayi ba wasu Likitoci Asibitin ne wasu kuma Nurses ne da Sauran Harda ma"aikatan Asibitin Ba"a barsu abaya ba,ganin Sun Coke ne sun kasa karisowa yasa Inna Hannatu ta Washe bakinta mai Dauke da Hakorin makka Tana Musu Maraba sai Lokacin Dina ta iya Dago kanta ta Kare ma Jama"ar Dakin Kallo Daidai Lokacin da Zain ya Dago kansa Daga Kafadar Hajiya Mama suka Hada Ido Hudu Da Dina.

Wani irin yanke gabansa yayi ya Fadi Lokaci Daya ya zaro Ido yana kallonta ita kuma sai ta lamgwabe mai kai ta wani Rausayar da idanuwanta,Zakiya ce ta Damke hannunta Lokaci Daya tana Sakin Mirmishi ganin Gabadaya idanuwansu yana kansu ne,Zain kuma da Sauri ya kauda kai yana kokarin Daidaita
Natsuwarsa Haddir ne ya Dago kansa ya Sauke su kan Su Dina da mamaki yake kare musu kallo bai samu Zarafin mgana ba Yaji Alhaji Tsoho Dake Kishingide Cikin Wata Farar Jallabiya Muryansa ta Dan Shake alamun Mura yace"Maraba sannunku da zuwa..Ke Hannatu ku basu Wajen zama mana.."
Yafada yana kallon Inna Hannatu dake Zaune kasa,Bata mike ba illah kafanta Data jaye Tana Fadin"Ai maraban nake musu Alhaji Tsoho Sannun ku da zuwa ga waje ku zauna Duka iyayan naku sun zaune kujerun.."
Tafada Tana yar Dariya Da Sauri Zakiya Tace"La bakomai..Dama munzo Duba mai Jiki ne.."Tafada tana jan Dina zuwa Gaban Gadon Alhaji Tsoho Cikin ladabi Ta Rankwafa ta gaisheshi da Alhaji Tsoho da Jiki ya amsa Ganin haka yasa itama Dina Tayi hakan ya amsa Cikin Sakin Fuska yana ta saka musu albarka Zain dai Gabadaya bai da Natsuwa Hajiya Mama dake gefensa Tace"Kai kuma lafiyarka sai Hada Zufa kake Kamar wanda yake jin kashi..!

Tafada Tana kallonsa Dariya ta Kubcema Haddir ya saketa har yana Dukawa yana kallon Zain wanda ya Hade rai yana wani Hura Hanci Cikin Son Basarwa yace"Ina Ruwanki kedai ji da wannan Tsohon Mijin naki gawa taki Rami kawai.."Haddir sai Dariya yake Hajiya Mama na Tayashi Dina kuwa sai nacin kallonsa Take yaki yarda su Hada Ido Zakiya kuwa kowa awajen take karema kallo su Baban kaduna dai suna ma Hirnsu ne haka ma su Nene Gwara ma Inna Hannatu da Umma hankalinsu na kansu Suna Nazaratansu.

Alhaji Tsoho ne yayi gyaran Murya yana Fadin"Yau kuma Aminatu Keda Megidan naki ake jin kanku..?

Haddir yayi Saurin Fadin"Tsoho Daman ai Megidan na Bugi ne..Nine kadai Megidan gaskiya.."Hararansa Hajiya mama tayi Lokaci Daya Tana maida Hankalinta kan Zain wanda ya Fito da wayarsa yana Dannawa ji yake kamar Ahalinsa sun san Abunda yake aikatawa Shiyasa ya kasa Sukuni Sai Hada Zufa yakeDafoshi Tayi Tana Fadin"Kaji Juyo gareni Megidana Zainullahi kyale Hadiru ni kam Bani son Shi baya Cefene."Saurin Ture hannunta yayi yana Fadin"Jeki na Sakeki..Ko ki koma wajen Tsohon Mijinki ko kuma ki koma Ma Haddir din."kwabe baki Tayi Tana Fadin"Au ni zaka watsa ma kasa a ido..?

Fuska ya Hade yana Fadin"An watsan wa ya ja.."Yafada yana matsawa kusa da ita nesa kadan Haddir da Alhaji Tsoho suna ta musu Dariya Dina dai da Zakiya suna Tsaye suna kallon Tsabar Shakuwa Tsskanin Jikoki da kakaninsu,Alhaji Tsoho ne ya an kare dasu,Dasauri ya kallesu yana Fadin"Af..Kunga mun Sha"afa da Baki..Sannunnku an gode ko..?

Ammh Daga ina kuke ne...?

Yafada Cikin Muryan Tsufa Lokaci Daya yana gyara zaman Farin Gilashin Idonsa Zakiya ce ta Murmusa bata samu Zarafin mgana ba Haddir yace"Wannan
anan asibitin Take aiki...Wannan kuma ina jin kawarta ce Domin ba'anan take aiki ba"Yafada yana kallonsu Zakiya Tayi yake kafin Tace"Eh ni Kawarta ce.."Tafada tana wani kallon Haddir din Kasa kasa yana Lura da ita ammh sai ya basar da ita,Alhaji Tsoho yace"Allah Sarki Sannunku fa Nagode Allah yayi albarka.."Sukace Ameen Cikin Dattakonsa ya kallesu yana Fadin"Duk wanda yazo gaisheni Ko daga ina ne baya Tafiya sai na san Sunanshi ko Sunanta.!
Chapter 32 · 0% Book details