← Book details Zainazain Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 65 OF 78

Sashe 65

Zainazain Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hannunta Zafeera ta Riko Har Dakin Umma ta Saka mata kayan sawan Cikin Wardrope kayan Shafan kuma ta Saka mata Kan madubi,Ta koma ta zauna Gefen Zaina wacce Tayi Tagumi kawai Haka itama Zafeeran Tayi Tagumin ganin haka yasa Zaina ta kalleta Cikin Sanyin murya Tana Fadin"Ya naga kin zauna..?

Kin fasa Tafiyar ne..?

Zafeera ta Sauke Taguminta Tana Fadin"Ina zani na barki Cikin wannan Ukti..?

Ni kaina da bani bace Mijina ya aikata wannan Lamarin ina jin Dacin Dawowar yarinyar nan Gidanan Baki ji Zuciyata ba.."Mirmishin Dayafi kuka Ciwo Zaina ta saki Batayi mgana ba Daman ance Hawaye Samun waje sukayi In Bala"i yayi bala"i kukan ma nemansa kake ka Rasa.
*****
Karfe 12pm da wani Abu na Rana Su Hajiya Maimuna da Hajiya Batula da Dina suna Zaune falon Gidan Alhaji Tsoho Tabawa ta Cika gabansu da kayan Ciye Ciye da Shaye Shaye,Hajiya mama na gefe zaune ta Fito suka gaisa da Hajiya Maimuna da Hajiya Batula ba Shakka kam Hajiya Maimuna ko Hausanta baya Fita Da ka ganta kasan Daga Chan ta Fito Dina kuwa Tana Gefe Ta lafe kan Kujera Tana latsa wayarta Taci Wata Doguwar Riga baka Wacce ta Dan kamata kadan sai Tayi Rolling din da bakin gyalen Abayar Ta kara Kiba Da Fari Daga gani Cikin ya karbeta Hajiya mama sai kallonta Take Tana mamaki Dakyar Ta iya Daga baki ta gaida Hajiya Mama Shima sai da Hajiya Maimu tayi mata mgana.

Bayan sun Sha Ruwa ne Hajiya Mama Tayi musu Jagora Dakin Alhaji Tsoho suka shiga suka gaisa sai alokacin Hajiya Maimu Ta kara ganin Kimarsa Sosai Take kuka Tana ta Godiya,Alhaji Tsoho yace Karta damu bakomai Kallon Hajiya mama yayi yana Fadin"Aminatu Ki Rakasu chan Gidan Usmanan Suga inda zata zauna.."
Kai Hajiya Mama ta gyada cikinn alamun gamsuwa.

Kallonsa ya koma kan Dina wacce Take ta kare ma Dakin kallo Tana wani Tabe baki yace"Zaki zauna Gidan Iyayen Zainullahi kamar yadda na Fada Daga Farko..Ina so kin san wani Abu zaki zaman neman gafaran Allah ne da kuma Jiran Wa"adin Haihuwan Cikin ki in kika Haihu ni kuma a Tabbatar da Tsarkin ki zan Daura miki Aure da Zanullahi ammh kuma baya Nufin zaki kara Wata Hulda Makamciyar wacce kukayi da juna abaya matukar kuna so ku Hallasta Auran naku."
Kai su Hajiya Batula ke gyadawa alamun gamsuwa Dina kuwa kai ta Sadda kasa Tana Fadin"insha Allahu Alhaji..Nagode.."Kai ya gyada kafin ya sallamesu Sukayi sallama kan cewa Dagachan zasu koma Domin ba kwana zasu yi ba.

Da Farko Motar da suka zo da ita wata katuwar Jeep Hajiya mama Zata Shiga sai ga Haddir ya Dawo Daga asibiti Hajiya Mama na ganinshi tace su bari Shi zai kaita sai su bisu abaya Ko Gidan Bata bari ya Shiga ba Ta gayamai Abunda ke Faruwa Kallon Kallon sukayi tsakaninsa Da Dina kafin ya Dauke kansa Motar ya koma Hajiya mama ta Shiga yayi Riverse ya Fice Daga Gidan Suma suka Shiga Mota suka Rufa musu baya.

Suna Zuwa Afalo suka iske Nene da Zainab,Umma kuma tana Dakinta ne Nene ce ta Mike tana musu Maraba Direbansu kuma yana ta Shigo da Uban akwatina kamar za"a Bude Shago kusan Rabin kayanta Dina ta kwaso,Mamaki ya kama Nene da Haddir Zainab kuwa Dinar take kare ma kallo ganin tana ta wani Bin Falon nasu da kallo Tana wani yamutsan Fuska acikin Zucityar zainab tace"Kan Uba wannann ai yar Bariki ce.."
Saman kujerun Falon suka yada Zango suka Fara gaisawa da Nene Sai ta Umarci Zainab Data Kawo musu Ruwa da abinci Hajiya Batula tace Bazasu Sha ba sun Sha Daga Gidan Alhaji Tsoho.

Hajiya Mama dai suna Zuwa Dakin Umma ta Shiga Tunda ta Tamnaya akace Tana Ciki Zuwa Tayi tace ta Fito ba yadda Umma ta iya Dole tabi Bayan Hajiya Mama hakama Zafeera sukabar Zaina ita kadai Cikin Tsinkewar Zuciya.

Sun kawo Falon Daidai Lokacin da Hajiya Maimu ke fadin"Nice kanwar mahaifiyarta Daga Sudan Sunana Hajiya maimuna kece Mahaifiyarsa..?

Nene na Shirin Tayi mgana Umma Tayi Saurin Fadin"Eh itace sannunku da zuwa.."Dagowa tayi Tana kallon Umma kana suka gaisa Nene kuwa bata samu ma bakin mgana ba Hajiya maimu Tace"Mahaifinsa baya nan ne..?

Nene Tace"Eh yadan Fita ne.."Hajiya maimu tace"Allah sarki..Mun fa Gode Allah ya saka da alheri Sai Hakuru Duk da Abun ba Dadi ammh Tunda an samu Fahimtar juna Shikenan ga Dina nan mum kawo muku ku Dauketa Tamkar yarku Don Allah kada ku saka mata Ido Duk Abunda ya kamata Don Allah akwaba mata Da na kowa ne mugu ne sai Mai shi..'Tafada kamar Tayi kwallah Nene kadai ta amsa da insha Allahu Umma da Zafeera Dinar suke kare ma kallo ganin ko ajikinta Sai ma Latsan waya Data keyi.

Hajiya Mama ce ta Kalli Nene Tana Fadin"Nene ku kaita masauki mana.."Mikewa Nene tayi Tana Fadin"Toh Hajiya mama..Na Dauka zasu ci abinci ne.."Hajiya mama tace"Akai musu cikin Dakin.."Da sauri Hajiya Batula tace"Mun gode Wlh..Muna kan Hanya ne yau zamu koma.."
Hajiya Mama tace"Ayyah ba laifi.."Nene ce kan gaba Suka Bita abaya Bayan Hajiya Batula ta kalli Dinar tana Fadin"Taso mana Dina.."Mikewa tayi Tana gyara zaman karamar jakar Hannnunta kafin tace"Kayana fa nan zan barsu Uwata.."
Yadda ta Fadi Uwata din gatsal ne ya bama su Umma mamaki Hajiya Batula tace"Za"a Shiga dasu mana.."Da Sauri Hajiya Mama tace"jeki za"a Shiga Dasu.."Bata da yarda zatayi haka tabi Bayansu Zuwa Cikin Dakin suna Shiga Hajiya Mama ta kalli Zainab Tana Fadin"Ke zainab dake da Zafeera kuja akwatimam nam kubisu dashi.."
Dukkansu basu so ba suna Tura baki suna komai suka ja su suka Shigar mata dasu wajem akwatina Shida fa,Koda suka Shiga sun iske Suna ta mata Fada da Nasiha Nene daman Tuni ta Fice Dukkansu Falo Kowa ya Dawo ya zauna su Zafeera da zainab sun Buga Tagumi Umma Tayi Zugudi Nene ma Haka Haddir na Gefe zaune yana Latsa wayarsa Zain ya Tura ma sakon Zuwansu Dina sai shi kuma yamai sakon Abba na gida..?

Yace mai A,'a cikin Sauri yace gashi nan zuwa.

Hajiya mama ta kalli su Umma Tana Fadin"Ina Baban nasu yaje ne..?

Nene tace"Bai fadamana ba..Yadai ce zai fita Direban ya Daukesa kila Office yaje ko akwai wani Abu ya taso.."Hajiya mama batace komai ba sanin Ta sani Kawai dai yana Gujema Haduwa dasu Hajiya batula ne yana Jin kunyar a nunashi matsayin Mahaifin Zain Ita kuwa Dina ko ajikinta yadda kasan Cikin dam Sunna ne bana Shege ba.

Su Hajiya Batula ma basu Jima ba suka Fito zasu Tafi,Su Umma suka Mike suna musu sallama Ba wacce ta Rakasu waje sai Nene Hajiya maimun Tana ta Godiya da kuma Rokonsu alfaram suyi Hakuri Tanayi Tana Sharan kwallah Nene taji Tsausayinta Sosai Hajiya Batula kuwa Batace komai ba sanin dai Dina ba yar Goyo bace ako"ina sai Ta Nuna bata da Tarbiya.

Motarsu na Barin Gidan na Abba na Shigowa kilama sun Hadu a Hanya Yana Shigowa Falon yagansu Tsaye Cirko Cirko Ganin Hajiya mama ya Tabbattar da koma Miye Cikin Ladabi ya gaisheta Ta amsa Tana Kallon su Umma Lokaci Daya Tana Fadin"Wai ina yarintar nan Halima ne..?

Tunda muka Shigo ban ganta ba..!

Umma tace"Tana Dakina..Chan nace ta koma Tunda Dakin nasu ya zama na zaman wata.."
Hajiya mama tace"Hakane..Ammh itama Alhaji yace Ki maida ta Gidan Mijinta zai fi zamanta anan Fatima..Sai fa hakuri Abunda ya Faru ya Riga ya Faru in muka sa Hakuri komai zai wuce ne.."
Da Sauri Umma Ta Mike Tana Fadin"A"a Hajiya Mama..Wannan karon ba Gaddama ko Jayayyah da Umarnin Alhaji Tsoho zanyi ba...Na Riga na yanke Shawaram Raba Auran ZAINULLAHI DA ZAINA..!!

DAM!DAM...! gaban ZAINA dake make Daga Kofar Dakin Umma Tana Jin Abunda ke Faruwa afalon sannan kuma Haka Gaban Zaina yayi wannan Bugawar Lokacin da yake sawo kansa Falon Nene,Abba,Hajiya Mama,Haddir,Zainab sai da suka Gwalo ido suna kallon Umma Banda Zafeera wacce ta Kada ido alamun Daidai kenan.

Kowa ya kasa mgana ba Illah Umma Data Cigaba da Fadin"Dama Lokaci kawai nake jira kuma yayi Lokacin..Saboda Haka ya kawomin Takardan Sakin Halimatu Bazan bari Ta kara zama dashi ba Ballatana Har Cin Amanarsa ya kasheta Lokacinta baiyi ba..!

Tafada Tana kauda kai Daga kallon Da Abba da Hajiya mama ke mata Muryan Zain suka ji wanda ba wanda yaga Shigorwarsa Falon Cikin Rauni kamar Cikin Muryan kuka yace..'
"UMMAAA....!
*Shakira...*
*ZAINAZAIN..!*
_(Is a love Story and Betrayal)_
*Wattpad:Jamilaumar351*
*Mallakar:Janaftyshakira*
*BOOK 1*
"Gabadayansu suka Juya inda sukaji Tashin Muryan Zain din Yanayin da suka ganshi Dukkansu sai da ya basu Tsausayi Hatta kuwa da Abba Dayake Fushi Dashi.

Durkushe yake kan gwiyoyinsa Daga Kofar Falon Domin Tun Lokacin da Umma ta Furta Rabashi da Firstlove yaji kafafunsa sun Gaza Daukansa Gabadaya Nan ya zube Bisa Gwiwoyinsa Idanuwansa sun kala Sun Jajir Cikin Wata irin Murya mai Cike da Rauni yake Fadin"Ummaa..!

Don Allah..!

Don Darajan Ma"iki ki yanke min kowani Hukunci Ammh banda Wannan bazan iya ba...Wlh kikace na Rabu da Fisttlove na Tabbata Ranar da na Saketa Nima Ranar zaki Rasani na Har Abada..!

Yafada yana Sakarmata Idanuwansa Cikin Tabbatar da mganarsa Cikin Wani Irin Rauni da Tsausayi uwa kan D'anta Umma Taji kuka ya kwace mata ammh sai ta kauda kai da Sauri Cikin Daga Murya tace"Karya kake...Karya Kake Zainullahi...Baka son Halima da kana Sonta da baka aikata Abunda ka aikata ba,kaji ma Rantsuwan Dan Musulmi Wlh Tallahi Sai ka saketa Domin Har Abada bazata Cigaba da zama Dakai ba.."
Ba zain kadai ba Hatta Abba wannan karon sai da ya kara sakarma da Umma Ido Saboda Jin yadda ta karfafa Rantsuwarta Haddir ya Zaro Ido Cikin Tashin Hankali yana kallon Zain wanda yayi zaman yan Bori akasa Zaina kuwa Dake make kuka ya kwace mata In zata Fito ta Fadi gaskiya koda wannan Al"amarin ya Faru Kaunar Dake tsakaninta da Firstlove bata ma Girgiza ba Tana Jin in ta Rabu Dashi bazata iya kara son wani Da Namiji ba acikin Rayuwarta,Lokacin da Umma ke Fadin bazata koma Gidansa ba Ta Dauka Daga baya in Komai ya lafa zata ssuko ammh Yau kam ta kara Tabbatar ma da kanta Cewa da Gaske Umma take zata raba Auranta da Firstlove wanda Allah ne ya kulla wannan kaunar Junan Tun tana Cikin Uwa Gareta Maryama.
Chapter 65 · 0% Book details