Sashe 49
Zainazain Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Mama Safiya tace"Hakane kam Hajiya Mama..Bawa bai isa yaGujema Kaddaran Allah ba,..Allah ya kara Shiryamana Zuru"a Nima yanzu Da kika Shigo Su Nene nake ta ba Baki kan suyi Hakuri kada Fushinsu yayi yawa in yayi yawa Zasu saka Zain din ya kara Shiga Wani Hali Uwa uba ga Yarinyar nan Abun Tsausayi Wlh.."
Hajiya Mama Ta jinjina kai Tana Fadin"Allah Miki albarka Safiya...Naji Dadin mganarki Fatima da Aisha Don Allah ku bar wannan kukan..Ke kuma Zareena Ji da yarinyar nan Sai kukanta nake ji Tun dazu ku kuma kuzo mu tafi yana Jiranku.."Daga haka ta Fice Daga Dakin Inna Rukayyah da Inna Hannatu suka Rufa mata Bayan Sun iske Alhaji Tsoho nata Lallashin Ya"yansa da Nasihu Sai gashi Lokaci Daya Sun Warware sun kuma ji Damuwarsu ta Ragu Suma Su Inna Rukayyah suka nemi Waje suka zauna suna Sauraransu Cikin Mganar Alhaji Tsoho ya kallesu Yana Fadin"Kun gano Inda muka Kuskure kan wannan Al"amarin..?
Gabadayansu kai suka Girgizamai alaman A'a Cikin Hikima Yacigaba da Fadin"Kuskuran mu kadan ne .Bazan ce Saboda mun kai ya"yanmu kasashen Ketare karatu ne ya Jawo mana wannan Abun ba A"a Abun ba Haka yake ba Duk da wasu Dalilin Haka Suna Lalacewar ammh Hakan ba zai zama Hujja ba Tunda Nima nayi wayon Kashashen Ketaren kuma Wlh Allah ban yi wannan Lalacewar ba Kuma gaku kunyi kuma har yau wani Abu mai kama Da haka bai Faru ba..Nayi Tunanin Sakacinmu da kuma Rashin Bibiyar ya"yanmu akan lokaci Ko kuma nace Rashin Saka Ido Inda ace muna Kokarin Saka ido Sosai koda basa gabanmu Achan Kasar da suke mu Samu wani mai amana wanda zai Dinga Kula da Shige da Ficen ya"yanmu na Tabbata in da Muna Haka zamu samu labarin wani Abun kafin ya Girmama kun gane Abunda nake nufi..?
Gabadayansu suka ce'Hakane Tabbas..Alhaji Tsoho.."Mirmishi yayi Cikin Jin Dadi yana Fadin"Yauwa..Tunda mun gano haka Sai muyi Kokarin Kiyayewa Yanzu akwai Ragowan Yaranmu da Basa gabanmu Bana jin Ta zafeera Tana Gaban Rukayyah ne kuma nasan ita da Shitu bazasuyi Sakaci Da Tarbiyansu ba.."
Da Sauri Inna Rukayyah Tace"Insha Allahu Alhaji Tsoho muna iya bakin Kokarinmu.."Alhaji Tsoho yace"Yauwa sai Abubakar karami ko..?
Yana ma wata kasa ce .?Da Sauri Daddyn Abuja yace"Shi yana Cyprus ne Alhaji ammh ya kusa kamallawa.."Alhaji Tsoho ya gyada kai yana Fadin"Masha Allah...Sai mai sunan Manya Umaru Faruq shima yana Chicago ko..?
Baban Kaduna ya gyada kai yana Fadin"Hakane..!
Alhaji Tsoho yace"Allah ya tsare su..Dukkansu zamu saka musu ido.."Baban kaduna ya Jinjina kai yana Fadin"Insha Allahu Alhaji Tsoho.."Kallonsu yayi Dukkansu yana Fadin'"Mganar Hamdiya kuma inda yafi Sauki za"a Daura auran.."
Daddyn Abuja ya Kada baki yace"Nan za"a Daura Alhaji Tsoho.."Jin haka yasa Kowa yayi Na"ama Da mganar,Alhaji Tsoho yace"Sai Mganar Zafeera Zan bata Lokaci Zuwa bayan Bikin Hamdiya in bata kawo wani ba zan bama yaro nan Ahmed Dama.."Kowa yayi Na"am Da mganar nan sukaci ba Da Tattaunawa,Kafin Alhaji Tsoho ya Hada kan ya"yansa sukaci Abinci Suka koshi suka Sha Ruwa Su Inna Rukayyah kuma suka koma Dakin Hajiya Mama Kowacce Tana hada Kayanta Gobe zasu wuce.
Sai Gabda Mangariba Zaina ta Farka Daga Barci Tana kuma Tashi Da kuka ta tashi kamar yadda Ta kwanta Dashi,Mganar Duniyan bata Tanka kowa ssi Umma da ita kadai Take mgana Dakyar ta Lallasheta Ta Rakata Tiolet tayi alwala tazo Tayi Sallolin Dake kanta azaune Tana Sallah Tana kuka Domin kamar Magiji Haka Abun ke Dawo mata.
Abunci kuma Umma Tayi Tayi ammh Taki ci Zareena Ta kalli Zaina Tana Fadin"Kici Abinci Zaina..Don Allah.."Tana kallon Cikin Idanuwan Zareena Sai Hawaye ta kasa Mgana ganin Haka yasa Handiya Taje ta Kira Hajiya Mama tazo Tana ta Fada kan Zaina Taci Abinci ammh Sai Taki ci sai da Tayi mata jan Ido kana Ta yarda Ta karbi Abincin Daga Hannun Umma ta Tusa Ko Loma Goms Batayi ba Zuciyarta Ta Fara Tashi sai Amai Tun Tanayi da karfinta Har ta kasa Umma da Mama safiya suka Riketa ganin Bata da karfin Jiki yadda Take kuka ne Tana Hawaye yasa Tsausayinta ya kara Shiga Ransu Ruwa aka kawo Umma ta wanke mata baki Hamdiya kuma ta Tsaftace Wajen kafin kace me Jikinta ya Sake Daukan zafi Ta kwanta Jikin Umma Tana Rawan Sanyi.
Abba ne ya aiko kan su Umma su Fito su Tafi Gida,Dole Nene da Umma suka Mike Kowacce Fuska akode,Hajiya Mama Tace Umma ta Kwantar da Zaina kan Gadonta su Tafi sai dai me Tana Mikar da ita ta makalkaleta Cikin kuka da Rauni Karo na Farko Datayi mgana..
"Umma...Zan...Zan biki..!
Tafada Cikin Fitar kwallah gabadayansu da kallo suka Bita Lokaci Daya Ta maida kanta Jikin Umma Tana Sauke Numfashi Ganin haka yasa Hajiya Mama taje ta gayama Alhaji Tsoho Halin Da Ake ciki Cikin Nazari yace"Barta su Tafi da ita..Taje gidan ta Huta na wani Lokaci Shima ai zainullahin baya cikin Natsuwarsa yanzu haka zuwa gaba in komai ya Daidaita za"a samu Masahala.."Da haka Taje tace Umma su Tafi da Zainar gida Inji Alhaji Tsoho.
su Mama Safiya da Mom Iklima suka Taya Umma Kama zaina suka Rakasu har Haraban Gidan Inda Direban Abba ke jiransu,Zareena ma Ta Goya yarta Tabi su Umma,Su Baban Kaduna Duk suna Waje nan sukayi sallama Kowane ba Farinciki ammh Da Sauki ba kamar Dazu ba,Abba ya kalli Umma yana Fadin"Fatima Har yanzu Jikin Halimar..?
Kai Umma Ta Dagamai Tana Jin Taruwan kwallah Saman Goshinta ya Taba wanda yasa Ta Bude Kodaddin Idanuwanta Tana kallonsa Cikin Tsausayawa Yake Fadin"Sannu Halima..Sannu kinji ko..?
Nima Hakurin zan baki Allah ya kiyaye kawai.."Yake Fada haka su Baban Kaduna Sallama sukayi Suka Shiga Mota Nene dai ba Baki sai dai kaga Tayi Shuru Kawai Tana kallon Mutane Abun ya Daketa Sosai..
Koda su Umma suka Koma Gida sun iske Sadiq ya koma Labari kuma Tuni yakaima Zainab Tunda Sadiq daya Dawo yake Fadamata itama taci kuka bata ma Kara Jin Wani kukam ba sai Da Taga Shigowarsu Umma haka Tazo ta Rumgume Nene Tana kuka Gefe Daya kuma Tana kallon Umma Dake Rike da Zaina wacce ke Kuka kasa kasa.....
Dakinsu Ita da Zafeera Umma ta kaita ita da Zafeera da Nene Abba kuma ya wuce Dakinsa,Kwantar da ita sukayi suna Mata sannu Jin Jikinta yayi zafi Zareena ce ta Dago Tana Fadin"Umma ko zan kira Aboki Haddir ne yazo ya Dubata..?
Wannan zazzabin yayi yawa ajikinta..!
Numfashi Umma ta Sauke Tana Fadin"Kirashi in zaki sameshi.."Tafada Tana kallon zaina wacce ke kara Shiga Cikin Bargo Tana Kudundune kanta Jin za"a Kira Haddir yasa ta Dago kanta da Idanuwanta da suka Kumbura Tace"A"a Umma..Kada ki kira kowa..Ki bani panadol kawai .Domin wannan Ciwon Da nake ji acikin Kirjina Bashi da mgani Har Abada..!
Tafada wasu Tagwayen Hawaye na Zubomata kafin ta koma ta kwanta Tana maida Numfashi Umma Ta Dade Tana kallonta Batayi mgana ba Nene ta kada kai Tana Fadin"Dole azo adubaki Sa"adiya Dare muke gudu..Dama ba mganin Damuwarki zai baki ba, na lafiyarki ce Domin Damuwa ko Mu bamu da mganin Tamu sai Hakuri kawai.."
Zareena Ta Ijiye Jakar Zaina Wacce Ta tattaro mata Daga Gidan Alhaji Tsoho nan Gefen Gado Jakarta ta Dauko Tana Laluban wayarta Cikin karamar Jakarta Take fadin"Kuma Nene Zazzabin yayi yawa fa..!
Hannu Umma Ta Dagama Zareena Tana Fadin"Kyaleta Zareena Ayi mata Abunda take so..Ina Jin Tsausayinta Fiye da yarda nake jin Tsausayin kaina Bari nayi sallahr Mangariba nazo na Taimaka mata tayi sallah Tayi wanka sai na Bata mganin Ta kwanta.."Ba suyi mata gaddama ba Suka Fice Daga Dakin Umma dai Kofar Tiolet ta Tura ta Shiga ta Dauro alwala Tayi sallah Ta Tada Zaina wacce Zazzabin ya karayin zafi Ta kaita Tiolet Ta Taimaka mata tayi wanka Tazo Ta Taimaka mata ta zura mata wata Doguwar Riga Umma Ta kasa Daina Jin wani iri game da Kukan da zaina keyi ta kasa ma Lallashinta,Dakyar ta sakata Tayi sallah azaunr kamar ta Kife
Fita Tayi zuwa Kitchen ta Iske Zainab na Hada Fruit Salad shi ta Diba Ta kai ma zaina Dakyar ta iya Bata tayi Cokali Biyar ta kauda kai Allah yasa batayi Aman ba wannan karon Ta Balla mata panadol Ta bata tasha Ta koma ta kwanta Fadi Take"Umma Rufamin Bargo..Sanyi..Sanyi.."Hakoranta na Haduwa Rufamata Tayi Tana Tofa mata addu"a bata barta ba sai Da taga kamar makyarkyatan ya Ragu kamar zatayi Barci kana ta Fita Zuwa nata Dakin Tayi wanka Lokacin ana Kiran Sallar Isha"i Tayi Kan sallayar ta zauna kawai Domin Gabadaya Gidan yau ba Dadi Nene ma na Dakinta Haka ma Abba Zareena ma Tana Dakin Datake sauka ita da Jalal Zainab Kuma dasu Saudat suna Falo duk da su Yara ne basusan Komai ba Sun Fahinci gidan Ba kamar yadda yake ba Sadiq ma yana Dakinsa bakajin Motsin kowa.
Babu Wanda ma ya Nemi Wani Abu Zainab ce Tayi Tunanin Hada Fruit salat Saboda Ruwa Ruwa ne zai yi Dadin sha Toh banda Wanda Umma ta bama zaina Ko Kitchen din ba wanda ya kallah Zareena ko Tana Dakin Datake sauka Bayan tayi Wanka Tayi sallah Ta Kira Haddir Sai da tayi mai Kira Biyu ya Dauka Sama sama suka gaisa Take Tambayanshi yana ina..?
Yace mata yana cikin asibiti..Cikin Jimami tace ina zain Ya bata amsa da bai sani ba Tunda ya Fita da Mota Dazu bai kara ganinsa ba,Kuka ne yaci karfinta ta yanke kiran Shi kanshi Haddir kukan yake Tun Dazu yazo cikin asibitin ya kulle kanshi Cikin Office dinsa yana ta kuka Kukan Tsausayin Iyayensu da Zain din Shi kansa da kuma Uwa Uba Zaina wacce Yake Tunanin wani Hali Take ciki yanzu..?