← Book details Zainazain Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 78

Sashe 56

Zainazain Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bai mata mgana ba Jin kamar Abba na Shirin Fitowa Daga Tiolet Da Sauri Nene ta wuce Gaba Tana Fadin"Biyo
ni muje Dakina Hadiru..Alhaji ya Riga yayi Fushi Da Zain kuma Fushin da bamu Taba ganin yayi kamarsa da wani ba.."
Ba Musu ya mara mata Baya zuwa Dakinta suna Shiga Ta Rufo Kofar Tana Fadin"Hadiru ba dai wani Cutar ne ta kama min D"ana bako..?

Haddir ya Girgiza kai yana Fadin"A"a Bata kama
shi ba ammh in ya Cigaba da saka Damuwa zata iya kamashi Har tamai illah.."
Salallami Nene ta Fara kafin ta zauna Gefen gado Tana Fadin"Oh ni Aisha..Ina zan saka Raina Wlh Hadiru Tun Shekaran Jiya Rabona da samun Barci mai Dadi agidanam Hankalina na wajen yaron nan babu Kowa awajensa bamai Sauraransa sai kai Ba Domin Alhaji yana mana iyaka ba Da Tuni naje naga Halin Dayake Ciki.."
Haddir ya gyara Tsayuwa yana Fadin"Haka sadiq ke Fadamana yanzu Daya Biya kafin yanzu mu Fito Tare nakai shi Tasha ya Hau Motan Zaria,Zain din ne ma ya matsa bayan yaji Sauki kan zai zo gida da na Hanashi yaki Hanuwa Shine Sadiq yake Fadin Abunda Abba yace..Abun bai yi Dadi ba Nene Kinsan Fushin Iyaye kan ya"yansu fa Ba kyau sam.."Nene na Sharan kwallah Take fadin "Na sani Hadiru ya zanyi..?

Wlh ni kam bana Fushi da zain sai dai in na ganshi zan mai Fata fata na Nuna mai Bacin raina kan Daukan Tarbiyan da ban Taba mai Shi ba..Ya na iya Alhaji yayi Fushi sosai wanda kuma sauko Dashi kan wannan Fushin sai Alhaji Tsoho kuma Shi din na Tabbata ba zai saka baki yanzu ba kuma Fushin Alhaji Duk da Yarinyar nan Halima ita ke kara Sakashi Jin Takaichin Zain Wlh Domin Kuka fa Take kwana yi Ta Wuni Yi Tunda Abun nan ya Faru.."
Haddir yace"Ai da wuya ma Alhaji Tsoho yace wani Abu yanzu..Mganar ma Zainar
Duk da ita ta kawoni Nene,Ku saka Baki ta koma Gidan Mijinta Wlh Zain yana Bukatarta Sosai kuma Abu ya Riga ya Faru ai sai Hakuri Bawa bai isa ya kaucema Kaddaransa ba.."
Nene tace"Hakane...ammh kam banajin Hakan zai yuyu gaskiya..'Haddir yace"Saboda mene Nene..?

Nene tace"Saboda Ba wanda zai ce Dole Sai Halima ta koma Gidanta..Alhaji kuma bazai yi mgana ba Alhaji Tsoho kuma yasan Tana nan gidan ammh bai ce komai ba Uwarta ce kuma Bazata Yarda Ta baka ita ba.."
Cikin Sauri yace"Wai Umma..?

Nene tace"Eh..."Haddir ya Sauke ajiyar rai yana Fadin"Bari naje nayi mata mgana in tayarda ta bani ita shikenan Abba da Alhaji Tsohi basu da yarda Zasu yi indai sukaji Ta koma Wajen Mijinta ai ba wanda ya isa ya Raba Tsakaninsu sai Allah Nene.."
Nene Ta Mike Tana Fadin"Kwarai mganarka Haka Take muje Dakin Halimar Umman Tata tana Chan Tunda Ita ke kwana da ita.."Daga haka ya Fita itama tabi Bayansa Sun Fito Falo kenan suka ci karo da Zareena Tana Zaune afalo Tana bama Takwaran Umma Nono Jalal na Gefenta yana Game acikin Tap dinsa,Ganin Haddir yasa Ta saki baki Tana Fadin"Aboki Hadiru Tazuru kuma kanina Yaushe kazo gidanan..?

Tafada Tana yar dariya Ba laifi Itama Ta Fara sakewa ba kamar Jiya ba Tunda Har tayi wanka Zataje gidan Alhaji Tsoho ne Hararanta yayi yana Fadin"Ni sa"anki ne wai Abokiya Zareena..?

Kin Raina ni ko..?

Cikin Shakiyanci Tace"ji wannan yaron..?

Ban girmeka bane nifa yayarka ce ko kaki ko kaso.."Haddir yace"Wata Hudun da kika bani Shine kin Girmeni..?Ki sake Tunani yarinya akwai malaman da suka ce komai kankantar Namiji shine Shugaba akan mace saboda Haka ki Dawo Cikin Hayyacinki Maza Bisa kanki yarinya.."Yafada yana Kashe mata Ido Daya Bata rai Zafeera Tayi Tana Fadin"Da aurena da ya"yana kake cemin yarinya..?

Yace"Au Ai harta wanda ya ijiyeki Engnear Jawaad din yaro ne..."Duka Zafeera Takaima ya kauce yana Dariya Nene ta Tayasu Sai ga Jalal ya Saka Dariya ashe Tun dazu yana Kallonsu kumatunsa Haddir ya Kama yana Fadin"Ai gaskiya na Fada ko Son..?

Da sauri yace"Is Truth Uncle.."Dariya ta kama Haddir har Sai da ya Bashi Hannu yana Fadin"Dat my Son Plz Give a Five.."Yako bashi Hannu suka Kashe Zareena tacika kamar ta Fashe Nene sai Dariya Takeyi Haddir da Jalal na Tayasu.

Kukan Little Umma ne ya katse Zareena ta koma ta zauna Ta Cigaba da Bata Nono Tana Fadin"Ka samu sa"a ne Aboki Zaim baya nan Da shi zai Taremun Tunda kafini baki.."Ambaton sunan Zain Da Tayi ya Dauke duka walwalansu Cikin Damuwa Haddir yace"Yana Gida ba Lafiya Abokiya Zareena.."
Cikin Damuwa Itama Zareenan tace"Ayyah..Allah ya bashi lafiya..Zan je na Dubashi ammh Nene Kada Abba yaji labari.."Nene tace"Wa..?

Ba wanda zai ji kinji na Rantse Miki anjuma kije ki Dubamanashi Don Allah kice ya kwantar da Hankalinsa Nenensa na Tare dashi komai zai Wuce.."
Zareena Tace"Insha Allahu...Zan Tafi Gidan Alhaji Tsoho na kai mai mai Sunan Umma Shi da Hajiya Mama da Tabawa Daganan sai na Biya na Dubashi..Allah sarki wannan Kaddaran bata kyauta mana ba sam Nene..'"Haddir yace"Uhm...Bari dai na ga Umma kam mganar Zaina.."
Zareena Ta kalleshi Tana Fadin"Tab...Anya kuwa..?

Da kun bari zuwa akwana Biyu Lokacin Abun ya saketa.."Haddir ya kama Tafiya Zuwa Dakin Su Zaina yana Fadin"A"a Barin zuwa Wani Lokacin ta wannan bangaran abun kara Tabarbarewa zai yi..Zain na Bukatarta ahalin Dayake Ciki.."Zareena Tace"Allah yasa ku dace..'
Nene Tace"Ameen Ameen..."Daganan Itama ta mara ma Haddir Baya zuwa Dakin Da zaina Take,Haddir ne kan Gaba ya Tura Kofar ya Shiga Nene na Binsa abaya Da Umma suka ci karo ta Riko Zaina sun Fito daga Tiolet kamar Wanka Ta Taimaka mata Tayi da alwala Tunda dai Wasu masallatan Har sun Fara Kiran Sallar mngariba.

Atare Umma da Zaina suka kai Dubansu kan Haddir da Nene Cikin mamaki Umma ke binsu da kallo har suka kariso Cikin Dakin,Haddir ne ya Fara gaisheta Cikin ladabinsa Lokaci Daya yana karema Zaina kallo ganin Tayi wani Fari fayaut kamar bata da jini ajiki kuma Ta Rame bakinta ya Bushe akallon Farko sai yaga kamar Tayi wani Danye Danye kamar wata mai Shigar Sabon Ciki Ita kuma Sau Daya Ta kalleshi kawai ta kauda kai kan Gado Umma ta zaunar da Ita Tana Fadin"Zauna ki Huta kafin ki shafa mai ki saka kaya sai kiyi sallah kici Abinci ko..?

Kallon Umma kawai Tayi batare Da Tayimgana ba Umma ta maida Hankalinta kan Haddir tana amsa gaisuwansa Nene ta kalli Zaina Tana Fadin"Sannu Halima Ya Karjin Jikin..?

Bata amsa ba illah kanta Data maida kasa Daman bata saka Rai zata amsata ba Domin Tunda Abun nan ya Faru Bazata ce taji mganar Zaina ba ko sau Daya ba sai dai in da Ummanta,Umma ce ta kalli Nene Tana Fadin"jikin nata da Sauki ba zazzabi sai dai Rashin karfin Jiki Shi kuma wannan Rashin Cin Abinci ne Tunda ko Taci sai ta amayar dashi..?

Nene tace"Toh yanaga Idanuwanta sun kumbura ne bata bar kukan bane..?

Umma ta Rausayar Dakai Tana Kokarin Daukan man Vaseline saman Madubin Dake dakin Tace"Bata bari ba..Kuma Harda ma da Rashin barci Da Rana tana samu tayi kadan ammh Da Daddare bata barci Kwana Take kuka.."
Umma Ta Fada Fuskarta na Sauyawa Haddir ne ya sauke Numfashi yana Fadin"Allah ya Sauwake ya kamata Taga Likita Gaskiya.."Umma tace"Bata so..Bazata asibiti ba tace..Ni kuma bana som matsamata Na kyaleta Ko Taje asibiti Basu da mganin Damuwarta Hadiru.."
Haddir yace"Hakane Umma..Ammh Kuka ma da Amai Da Rashin barci ai Wata Cutan ne na Dabam ko..?Umma batayi mgana ba illah mika ma Zaina Man Data Dauko mata Datayi wacce ke sanye da Hijabi Dogo na wajen zainab ne Umma ta Dauko mata Karba Tayi Ita kuma Umma tace"Ki shafa.."
Haddir ne yaga Umma na Shirin Shiga Tiolet yace da Sauri"Umma wajenki fa nazo.."Dakatawa Umma Tayi Ta waigo Tana kallonshi kafin tace"Wajena kuma..?

Allah sa lafiya..?

Haddir yana kallon Zaina wacce Ta Dago Tana kallonsa da Rinannun Idanuwanta yace"Lafiya lau..Dama mganar Zaina ce Umma"
Umma Ta Juyowa Gabadaya Tana Fadin"Ina Jinka.."Tafada Tana kallon Nene wacce ta marairaice mata Tun Daganan Ta gano Inda suka Dosa Sai dai bara Ta katse musu Hanzari ba gwara Taji Daga bakinsu lalle zasu ga Fushinta nan take kuwa.

Idanuwan Umma sun ma Haddir kaifi ya kasa mgana sai da ya Sunkuyar dakai kana ya iya Fadin"Dama..Dama..Umma mganar Komawar Zaina Gidan Mijinta ne kinga Zain yanachan kwance ba lafiya kuma Yana Bukatarta ayanzu gaskiya.."
Har ya gama mganarsa Umma na Jifansa da wani kallo na lalle nema kun Raina mutane Zaina kuwa Tun mganar Haddir Taji Dan Jinin Jikinta ya Daina Gudu Bata Sha"awar kara ganin Ya zain ma Ita acikin Idanuwanta ammh akasan Ranta Tsausayinsa Sonsa Sun Hanata Sukuni Kamar Daga sama Taji Umma na Fadin"Ok Shi ya aiko ka kenan...?

Shine kuma Da zaka zo Fada ka Dauko Uwarsa kuka zo Tare ko..?

Nene tace"Eh yazo yagamin komai..Nace yazo muje mu Taru mu Roke ki Umman Zareena Hannunka fa baya Taba Zama Cuta gareka,Bamu da yarda zamu yi da wannan kaddaran kuma Hana Zain matarsa kamar kara Tabarbara komai ne,ki barta ta koma Gidan Mijinta Suyi Jinyan Juna Ya bata Hakuri sai Kiga komai ya Daidaita.."
Umma Ta Tsuke Fuska Tana Fadin"lalle nema..Wato yanzu ne Take da kima da Daraja acikin Idanuwansa ko..?

To kaje ka Fadamai Wlh Tallahi kunji Rantsuwan Musulmai yata bazata Je ko"ina ba.."
Daga Haddir Har Nene kasa Mgana sukayi jin Umma ta Rantse,Cikin Jan karamin Tsaki Umma tace"Ina Dadiron nashi ko nace karuwan nashi Da bai Kirata tazo Tayi Jinyarsa ba Ko nace Uwar Shegen nashi..?

Sai yata Zata Dinga Wahala kansa ko..?

Hadiru ka Fita idona karka kara Zuwarmin da wannan mganar Banzan Daga kai har Uwarsa Wacce bazata ga Illah Da Abun Tir din da D'anta ya aikata ba.."
Tafada Cikin Bacin rai Da Sauri Haddir ya Rankwafa yana Fadin"Don Allah Umma..Ko Sau Daya ki bani Dama nayi mgana Da zaina kila ita ta Fahimceni.."Kamar Umma zata mareshi Haka ta taso mai Tana Fadin"Anki abaka Daman..?

Nace an ki abaka daman..?
Chapter 56 · 0% Book details