← Book details Zainazain Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 78

Sashe 15

Zainazain Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Itama Din Tafiyarsu ba Dadewa Ta Tatattara zuwa Zaria Inda Ta Fara Karatunta na Aikin Jarida Wato Mass Com,a nan cikin ABU zaria Cike da kewar yan"uwanta Wanda suka Riga suka zama Jikin jikin Juna,Hakuri kawai Take Tinda Daman ko ba Karatu akwai Aure wanda Dole zai Rabasu.

Sai bayan Tafiyarsu Su Umma Da Nene suka Fahimci Yadda Shakuwa tayi mugun Shiga Jikin Halima Domin kwana Take kuka Tana Kiran Sunan zain Dalilin Haka sai da tayi zazzabi Harda kwanciya a asibiti Da aka Sallamota Sai ta koma Shuru Shuru bata Mgana sai dai ka ganta ta zauna Tayi Tagumi Kawai Chan kuma sai ta Fara kuka Sai a Hankali a Hankali Ganin Zafeera da Faruq suna Kokarin Janta ajiki Saboda ta Saki Jikinta da Ita kanta Umma da Abba Wadanda basa Son ganin Damuwarta Da akayi Hutun Makarantar Wannan Shine karo na Farko Da taje Gada Tayi musu Sati biyu ta Dawo,Domin Lokacin da Zain yana nan Baya barinta Taje ko"ina in ma Abba ya matsa Dakyar yake yarda Suje da ita tayi kwana Daya Su Dawo Goggo Halima Ta gaji da Mitan ta Zura ido Ammh Bayan Tafiyar Zain sai Alhaji Tsoho yace Taje chan Tayi musu Hutu Saboda yan"uwa su ganta Koda Taje Din bata wani Sake ba Duk da tasan Sune Dangin Mahaifanta ammh kuma Rashin Zain a gareta Tamkar wani Gibi ne na Rayuwarta.
******
Rayuwar Haddir da Zain a Jami"ar Oxford Universty London Tasha Bambam Domin Dama ko Ahalayya da na yau da kullum Suna da Bambamci Haddir Mutum ne mai Mugun Zuciya Kuma So Silent gashi bai Cika Shiga Shirgin mutane ba,In ka ganshi ya Sake to da Dan"uwansa Zain ne,Duk da ba Abu Daya Suke karanta ba,Shi Zain yana Bangaran Gyneacologist ne,ayayinda Haddir yake Bangaran Paediatric ne,ammh yanzu Suna Hade ne sai Tafiya Tayi Tafiya ne kowane Bangare zai Ware kanshi.

Tun Zuwansu Makarantar Basu Dade ba Sunan Zain Usman Abubakar Saulawa yayi Fice Saboda Zamowarsa Guru a bangaran Kokari Shi kanshi Haddir ya sani bai kama kafarsa ba Dalilin Haka sai ya Sanu Tarin Masoya da abokai kana kuma gashi Handome Matashin yaro mai Kokari,nan da nan ya Shiga Ran maza da mata kafin kace me Zain ya Shiga Click na mata da Maza ba Adadi Tunda Gaskiya Haddir yafishi irin wannan kamewar Ammh Shi Zain yana son Rayuwa da Jin Dadi.

Tun Farko Sai da Haddir yamai mgana kan ya maida Hankali ga Abunda yakai su Ammh Zain bai Ji ba,sai ma yayi Biris da Mganar Haddir din yana Ganin ai yana ganin Karatunsa bazai Hanashi Jin Dadin Rayuwa ba,Ganin Haka yasa Haddir ya Fita Batunshi Saboda karatunsu ba Koda yaushe suke samun Kiran Gida ba Sai bayan Wasu Satittuka Dama Shi Zain Ba da wanda yake waya sai Halima Waya Dakeki..? kina cin kaza..?

Kin yi kuka..?

Umma na baki madara..?

Tambayoyi Dai gasunan sai Ta Rasa wanda zata amsa mai ma aciki Dama Shi yana Kiran Gida ne saboda ita Domin Duk Duniya bayan Iyayensa Itace agabansa kuma aransa.

Ko achan London zaku yi mamakin yadda Sunan Halima yayi Fice Sau Tarin Abokan Zain Turawan Suna mai lakabi da ZAINAZAIN ne kuma yana Jin Dadi Baya jin kunyar yace musu matarsa ce da zai Aura da zarar ya gama karatu ya koma Gida Shi Ba mutum bane mai ijiye Sirri A"a indai ya Hadu da kai ko na Wuni Daya ne Dole ka Shaida Wacece Firstlove a Wajen Zain.

Ba Dina Bace Sanadiyar Fara Lalacewar Zain ba Ita Dina Daga Baya tazo makarantar Domin Zain na gabanta da Shekara Daya sai akaci Sa"a kuma Duka Course Daya zasu karanta,Zain yana da Sakewa da Mutane Both Mata da Maza Sabanin Haddir Dake da kamewa da kuma Daraja Mutumtanka Gidansu da kuma Tarin Nasihun Iyayansu har ma Gargadin Alhaji Tsoho Garesu na su Tsarkake Zuciyarsu Suji Tsoron Allah Suyi Abunda ya kaisu ammh Zain ya watsar da Wannan Farkon Abun da ya Fara kaishi ga Kusanta ZINA shine Biye ma Matan Turawa Wadanda muke da Bambamcin al"ada dasu da kuma addini.

Tun Zuwan Zain makarantan Yayi yanmata da Kawaye mata Wadanda bai san iyakarsu ba In suka ce Suna sonsa baya Taka musu Burki Saboda Shedan ya saka Mishi Sha"awarsu Banda Son su Saboda So Daya ne Tak kuma Zainarsa yake ma Wannan Son Da wannan Abun yasa ya kan kyale su Tabashi Har ma Suyi Hugging Dinshi Su kuma yi Kissing Dinsa baya Damuwa Tunda ya gani a nan Duk Normal ne.

Dalilin Fara aikata Zinarsa Ta Farko Suna Shekara Na Biyu a Landon ne Wata Kawarsa Gloria,Baturiyace yar kasan London din ce itama karatu ya kawota makaranta Tun ganin Farko Da Tayi ma Zain ya Shiga Ranta Ta Dinga Neman kusanci Dashi Dayake bashi da Wuyar Sakewa Nan da nan ya Saki Jiki Da Ita suka Shaku suka zama kawaye suna Fita yawo Tare da Zuwa Wurare Dadama Kwatsam Ranar ta gayyaceshi Gidanta Cin Abincin Dare Wato Dinner Daya nemi Haddir yazo suje yace bazashi ba sai yayi Fushi ya Tafi shi kadai Ashe ta Shiryama Ranar Mganin karfin Sha"awa ta sakama Zain a Alemi yasha Domin ya Biya mata Bukatunta Tunda Tayi kokarin Hakan ta kasance ammh kuma Shi Zain din yana kwace ma Hakan.

Ranar Zain yayi Zina da Gloria kuma Abun Takaichi ma Bashi ne ya Fara saninta ba Ranar agidanta ya kwana Bayan komai ya Lafa yashiga Nadaman Abunda ya Faru yana kuka yayi mata Kaca kaca suka Rabu koda ya koma Gidan da iyayensu suka kama Musu Shida Haddir baya Cikin Natsuwar,Dama bai da Rike Abun Aranshi yana komawa ya kwashe komai ya Gayama Haddir Suka zauna sukaci kukansu Tare ammh Haddir yayi ta ma Zain Fada kuma yayi mai alkawarin Rufe wannan Sirrin ba Wanda zai Ji Bayan Shi Zain din yamai alkawarin zai Guji Faruwan haka.

Kamar Gaske Zain ya Fitar da kansa Cikin Wani Shashancin makaranta ya koma ya maida Hankalinsa kan karatunsa sai dai kuma Waasa Farin Girki Tunda Gloria ta Dandanamai kamar ta Jona mai Bala'i sai ya kasa Sukuni yayi yayi ya Danne Abun ya kasa Bayan Faruwar Haka da wattani kadan Zain ya Koma Ruwa Harka da Mata kaca Kaca Duk wacce ta saki kanta zai Taya kuma yayi Abunda yaga Dama da ita Tun Yana Boyema Haddir har Abun ya Bayyana ya sani Ranar ya kwana Cikin Bakincikin Halin da Dan"uwansa ya saka kansa Yayi mai Fadan da Nasihan ammh Duk Abanza Sai ya koma mai addu"an Shariya Abu Daya ne yamai Dadi ganin bai wasa da karatunsa ba kusan yana Jerin masu Tafiya da manyan point aset dinsu.

Addu"an da Haddir ya keta mai da kuma Nasihan Dayake ta mai a kullum yasa Kuma Abun yayi sauki Zain din ya Rage Neman matansa Ba kamar baya ba Duk da yana yi ammh ba Sosai Haddir nata jin Dadin sai dai kwatsam Suna Shekara ta uku a London har kuma Lokacin basu je gida ba Sai da Abba yazo Dubasu Shida Alhaji Tsoho da Dadyn Abuja Wanda suka Rako Alhaji Tsohon wani Asibitin aka Dubashi bayan Tafiyarsu ya Fara Fama da Kafa Da sukazo Haka Zain ya Dinga Rokon Kar Haddir ya Fada musu Halin Da yake ciki Shi kuwa mai zai kaishi Fadan wannan Abun..?

Ya gwammace koma me zai Faru ya Faru ammh Zai Rufama Amininsa Kuma Dan"uwansa asiri Ahaka suka zo suka gansu suka koma Batare da sun Fahimci Zain din ya Chanza Daga yadda suka Shanshi ba.

A Daidai Tsskanin ne kuma Dina Gaddafi Sheerif ta Shigo Rayuwar Zain wanda ta kara Tabarbara komai Daga Tarbiyansa Gabadaya.

Dina Gaddafi Sheerif Haifaffiyar Garin Jahar Kanon Dabo ce Mahaifinta Gaddafi Shareef Dan garin Bama ne Dake Maidugurin Nageria,Mahaifiyarta kuma Sarah Balarabiyar Sudan ce Auran Soyayyah suka yi da mahaifinta Wanda ya kasance Dan Siyasa ne,Tun bayan Auransa da Sarah suka Fara samun Matsala kan Rashin Kulawa ga iyalansa Yafi maida Hankali kan Harkokinsa na Siyasa Suna Haka har Allah ya basu Dina Ita kadai kwara Daya Allah ya basu Shiyasa ta tashi Cikin Gatan Duniya ta kowani Bangare.

Abunda yasa Ta kara Sangarce Shine Rasuwa Mahaifiyarta Sara Tana da Shekara goma aduniya Dangin Mahaifiyarta Sun so su Dauketa Su maidata Sudan su Riketa Tunda Rikon Diya Mace sai mace ammh Alhaji Gaddadi Shaeerif ya Hana Adauketa Saboda yadda Gabadaya ya maida Soyayyar Sarah ga Dina din Dole suka Bar mai Ita Ba Domin Ransu yaso ba Sai Domin Tsausayinshi na Ganin Rasuwar Sarah din Ta Tabashi Sosai.

Da farko kamar zai iya kula da Ita sai kuma ya gaza Saboda ya kara Shiga Harkan Siyansa Sosai,Sai ya Dauko mata mai Reno ya kawo Gidan Tana kula da ita Tunda Wani Lokacin Tafiya Tana Kamashi Wannan Dalilin Shine Dalilin Dayasa Dina Tatashi bata Da Tarbiya Ga kuma Sangarta Datayi mata yawa Tatashi ba"a gaban Uwa ba Ba kwaba Uba kuma bai da Cikakken Lokacinta Ballatana ya Tsaya Tsayin Daka Wajen bata Tarbiya Sai Rayuwarta Tatashi Sai Abunda Dina Taga Dama Take yi kuma Duk Abunda Tayi Niyya Shi take aikatawa bamai ce mata Domin komai Ko Chan Sudan bata Cika zuwa ba sai dai su suzo su ganta Ko su Suna Cikin Takaichi da bakincikin Yarda Dina Ta sangarce Ta kuma Tashi ba Wata Tarbiya Tare da ita.

Duka Karatunta Har zuwa matakin secondary a Frine Collage Tayi Dake garin kano Sai kuma alokacin Alhaji gaddafi ya kara Aure,da Wata Mata Itama Ta taba Aure Mijinta ya Rasu Sai dai bata Taba Haihuwa ba mai Suna Hajiya Batula,itama yar nan garin kanom ce kanwar Wani abokin Siyarsa ne ya bashi ita ya Aura Saboda Suna samun suka Wajen abokan Siyarsasu kan Rashin Auren na Alhaji Gaddafi.
Chapter 15 · 0% Book details