← Book details Zainazain Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 78

Sashe 31

Zainazain Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Koda suka koma Gida Zain bai iya Daga ma Zaina kafa ba Sai ya ta Tabbatar da ya samu Natsuwa kana suka Shiga wanka Bayan sun Fito ne ya Shirya ya koma asibiti saboda ya samu Kiran Dr Aisha Ita kuma ta Zage ta Shiga Kitchen Domin Farantamana Mijinta Abun alfaharinta.
******
Kwanci Tashi babu Wuya awajen Allah gashi Har Su zaina sun cinye Hutunsu Dayake Hutun bamai yawa bane sosai iyaka Sati Hudu ne Ma"ana One Month kenan,Zafeera ma Tana ta Shirin komawa Ana gobe zata koma Tazo Gidan Zaina ta mata Wuni Tazo kenan ba Dadewa sai ga Laila itama ta iso Daman Tana Jin Labarin Ukti Zafeera wajen Zaina ammh bata Taba ganinta
ido da ido ba sai dai ahoto Itama Zafeera Tana Jin Labarin kawar Zaina ta makaranta Laila sai Ranar suka Hade nan fa sukayi ta shan Hira Suna Dariya Dukkansu Ukun Tare suka Shiga Kitchen sukayi Girki Sukaci,Zain bai dawo Da Wuri ba,sai wajen biyar na yammh Lokacin Laila ma na Shirin Tafiya ne,Yayi mamakin ganinsu bayan sun gaisa yana ta Musu Tsiyan ashe sune suka zo suka saka Firstlove dinsa yau kwata kwata ta manta Dashi,Laila na karewa Zafeera dai Sai Mirmishi Sanin Ko da suka Taso Kai da kai Tare da Zaina Yaya Dakta bai Cika sakar mata Fuska ba Shiyasa itama Take jan kankantar ta da matsayinta awajen Matarsa.

Ciki ya Shiga Zainar ta Bishi Ta Taimakamai yayi wanka ya Sauya kaya Ta zubo mai abinci yaci kana ya sake Fita zuwa gidan Alhaji Tsoho,Domin yace ya kwana Biyu bai lekasa ba Daganan zai biya ya gaida Matan Abba Nene da Umma Bayan Fitansa ne laila Tayi ta ma Zaina Tsiyar ko sun samu karuwa ne Taga tayi wani Kiba ne Ta kara Cika kamar ba Ita ba Zafeera kuma Tana gefe Tana kare ma Zainar kallo Itama Tana Shaida Kibar Dataga Tayi ammh Tasan koma miye In Ta fasu zasuji.

Kusan Tare da Laila da Zafeera suka Fita Zafeera da Motar Umma tazo sai ta Rage ma Laila Hanya Ta kaita Har gida kana ta Wuce Gida,Tana zuwa gida taci karo da Ya Haddir ya kawo Zainab Daga Kaduna yake ya je Gaida Maman Wani Abokinsa sai ya Biya shine Baban kaduna ya Hadosa da Zainab sama Sama suka gaisa da zafeera daman Ita bata cika sakarmai Fuska ba tace ya cika Girman kai yaya Dakta ya fishi Sakin Fuska shima kallon Wata mai Girma kai yake mata Shi kuma bata sanshi ba Haka yake yafi Zain Miskilanci da Shariya.
*****
Misalin karfe 8:30pm na Dare Zakiya ne zaune kan Daya Daga Cikin Kujerun Falon Da suka yi Ma Falon Dina kwanya itama Dina Tana zaune kan kujeran Dake kallon Wacce Zakiyan ke kai Dukkansu kananan kofuna ne a Hannunsu cike da madaran Hollandian suna Sha Suna Taba Hira,Yau din zakiya ce takawo ma Dina Ziyara Shima din ba Dadewa zatayi ba wani Alhajinta take Jira zai zo Gidan Dina ya Dauketa.

Sai da ta Hadiye Abunda ta kurba kana ta Tsurama Dina ido Tana Nazarartanta Ganin haka yasa Dina tace"Yane..?irin wannan kallo sai kace kin ga wani Tsohom kwartonki.."Dariya Zakiya ta saka kafin tace"Tsohon Kwarto ai ya gama aiki Dina...Rabani bana Harka da Duk Abunda ya zama Tsoho nafison Harkan da Abunda yake sabo ko banza zan Mori Quality dinsa kafin ya Tsufa.."Dukkansu Dariyar suka saka Cikin Nishadi kafin su Tsaigata Zakiya ce ta ijiye Kofin Dake Hannunta kan Center Table Din Dake Tsakiyar Falon Tana Fadin.

"In lissafina ya cika Daidai mun Riga mun Dana Tarkonmu Tun 3weeks da suka gabata.."Tafada Tana kallon Dina Mikewa Dina Tayi Dauke da Kofin Hannunta Tana Fadin"Eh mana..Kin manta ke ma ai sabuwar alluran taki Satinta uku dana Rakaki akayi miki ko..?

Zakiya tace"Hakane..Toh sai ki Dage ba Daga Kafa mu samu Zomon mu ya Shiga Tarko..In ya Shiga Duka Burikanki zasu zama gaskiya ayayinda Zaki mallaki Zain mallaka na Har Abada..'
Kai Tsaye Dina Tace"in kuma plan din mu ya Kuskure fa..?

Wani munafukin Mirmishi Zakiya ta saki kafin tace"Kin Rasa Zain har Abada Dina..In nace Har Abada ina Nufin har Abada bazaki Taba mallakansa a matsayin Miji ba kuma kila nan da Lokaci kadan ma Tarayyar Dake tsakaninku ta Wargaje gabadaya kedashi sai dai Hange Daga Nesa.."Ta karishe Fada Tana kallon Dina Ido Cikin Ido.

"Bai isa ba..Bazai Taba yuyuba ya zama Dole na mallakesa ko yana so ko baya so.."ta fada Cikin zafin Rai dana zuciya Zakiya Ta mike tana Taku Daya Bayan Daya Zuwa ga Dina Lokaci Daya tana Dafa kadarta Tana Fadin"Shiyasa nace in baki son Hakan ta kasance sai kin dage sosai Kin kuma Danne wannan bakin Kishin acikin Ranki in ba Haka ba Duk sanda kikace zaki Rika bayyana Abunda ke Ranki Game da matarsa zaki lalatamana plan ne Domin zai gujeki kuma ni bana son Haka nafison ku kasance Tare har sai Hakanmu ya cimma Ruwa.."
Tafada Tana kallon Dina wacce ta sadda kansa Tana wani Tunani kafin ta Dago Tana Sakin ajiyar rai lokaci Daya Tana Fadin"zan yi kokarina..Ammh Wlh baki ji yadda na Tsani Diyar megadin nan ba in ya ambaci Firstlove ji nake kamar naje gidanta na Burma mata wuka in kuma ya ambaci Zainarsa din nan kamar na Kashe kaina nake ji.."Zakiya ta Kara Dora Hannunta saman kafadarta ta Hannun Hagu ta Girgiza da karfi Tana Fadin"Ki Daure kada ki lalatamana plan Dina na gayamiki.."
Dina tace"Insha Allahu muke da Nasara..."Zakiya tace"Ina saka Ran haka..."Ta fada tana wani Mele baki Kallonta Dina Tayi Tana Fadin"in plan din mu ya Tafi Daidai me kike ganin zai Biyo Baya..?

Sakin Kafadunta Zakiya tayi kafin Ta Sheke da wata Dariya irin na mugunta sai da tayi ya isheta kana ta Dakata Tana Fadin"Ke yanzu baki Hasoso mezai Faru gaba ba..?

Ta fada Tana kallon Dina wacce ta sakar mata ido Tana kallonta lokaci Daya Tana girgixa mata kai alaman Bata sani ba Cikin Tafa Hannu Zakiya take Fadin"Ya kamata ki Hasaso wani Abu mana Dina Har kin manta Tare Dani DaKe muka biya kudi muka samu Labarin Tarihin Zain Tundaga Tushe..?ashe har kin manta..?

Da Sauri Dina Tace"Ban manta wannan ba meyasa kika ce haka awannan gabar..?

Zakiya tace"Dalilai Da Dama mana..Bala"i ne zai Faru Lokacin da muka Fasa kwan...Za"ayi Kitimurmura fa,Ahali zasu Girgiza fa Kimarsu zata Raunana ba kadan ba,kinga wannan Matar nashi Dayake ji da ita kamar ransa..?hmm wannan Firstlove din da Zaina na zain ko.?

Duka zasu kare Plan din mu zai saka Soyayyarasa ta Rikide ta koma Tsantasan Tsanarsa acikin Ranta Yan"uwansa da iyayensa zasu Daina yarda dashi kilama har Iyayensa Su kama Fushi Dashi Fushi mai Muni ma kuwa,..!"
Ta karishe Fada tana wani kallon Sama kamar tana ganin Abun na Faruwa agabanta ne.

Dina ta saki Mirmishi Tana Fadin"Naji Duk wannan ta ina nawa Burin zai cika..?

Zakiya ta Dago kanta Tana kallon Dina Ido Cikin Ido kafin tace"Ta wannan Hanyar...Karki manta Sunan Kakansa Dr.Abubakar Bashir Usman Saulawa ya zaga garin Bauchi dama kewayanta Wajen Kimarsa da Dattakonsa da Son Talakawansa Na Biyu kuma Mutum ne mai Daraja wanda Al"umma ke ganin Darajansa Karki manta mai bamu labarin ya gayamana Duk Cikin Jikokinsa yafi son Zain da Haddir kuma yana kimantasu acikin Idanuwansa ya kike ganin in wannan Labarin ya Sameshi Da Shaida mai karfi..?

Zai so wannan kimar nashi ta Zube..?

Bazai Taba yarda ya Rasa Dattakonsa ba Dole mafita Daya ne Zasu bi koda Zain din yana so ko baya so Saboda Lokacin ba Mganarsa za"a Tsaya Saurara ba Domin bashi da wata Kima alokacin..'
Kai tsaye Dina Tace"Wata mafita ce..?

Ta fada tana Kallon Zakiya da neman karin Bayani ta Bude baki zata yi mgana kenan Wayarta dake Cikin karamar Jakarta ta Dauki Kiran Neman agaji Hannu ta kada mata Tana Fadin"Kin cinye lokacinki Alhajina ya iso.."Tafada tana Karisawa kusa da Jakar nata ta Dauka ta Zageta ta Dauko Wayar nata Har Kiran ya katse Tana ganin mai Kiran Ta Dago Tana kallon Dina Wacce ta Sakar mata Ido Tana Jiran amsanta Dariya ta saka Tana Fadin"Sorry kawata Lokacinki ya kare...Ammh ki bani Bashi zan baki amsa in muka Hadu.."
Bata bari Dina ta samu Zarafin mgana ba ta kama Hanyar barin Falon Daidai Lokacin Da wayarta ta Sake daukan Neman agaji Ta Daga Ta kara akunne lokaci Daya ta waigo Tana kallon Dina Tana Fadin"Zan bar Motata awajenki Zan dawo na Dauka..."
Daga haka ta Bude kofa ta Fice Cikin yanga da Takun Yanmatan Zamani Wadanda suka san kan Duniya Dina Ta rakata da kallo mai kama da Takaichi kafin ta koma kan kujera ta zauna Tana Dafe kanta.
******
Washegari iyalan Dr.Saulawa suka Tashi da alhinin Rashin Lafiya Alhaji Tsoho Wanda Mura da Zazzabi ya Sarkeshi Cikin Dare Numfashinsa ma baya Fita sama sama kamar zai Sheka Dalilin haka yasa Haddir Da Hajiya Mama suka Rankaya Dashi Zuwa Asibitin Dayake mallakinsa Wato Saulawa specialist Hop,wajen Misalin uku na Dare,Dr.Imran Haddir ya Kira Tunda Shi ke kusa da asibitin Kafin su iso ya iso Cikin asibi
tin Tare dashi Da Dr.Peter suka bashi Taimakon gaggawa Har Numfashinsa ya Dawo ya Daidaita ashe majina ce ta Tushemai Kirji yasa baya iya Numfashi,Duk da Dare ne alokacin ammmh akwai Nurses masu Duty din Dare suna ta kai da kawo ganin Dr.Saulawa da kansa aka kawo ba lafiya.

Daki na Mussaman aka kaishi Wanda Dama Dakunan na Family ne in wata mtasala ta Faru,Sai wajen asuba kana Haddir ya samu natsuwa ganin Alhaji ya samu Barci Hajiya mama Tasha kuka Haddir nata Mata Tsiyan Shima kanshi ya Shiga Rudu nan ya barta ta Shiga Toilet ta Dauro alwala Domin ana ta Kiran Sallar asuba Shima Fita yayi zuwa masallacin Cikin asibitin Yayi alwala yayi Sallah sai da aka idar kana ya Tuna da Abba da Sauri ya Fito da waya ya Kirashi ya gayamai Abunda ke Faruwa Hankalinsa ya Tashi Dama lokacin Dawowarsa masalaci kenan Su Nene suna tsaye Sun Firfito Jin Salatinsa sai da Ya gama wayar kana yake gaya musu Suma Duk Sun Rude sanin sudai Basu Taba ganin Alhaji Tsoho yayi ciwon Daya kwantar Dashi Haka ba.
Chapter 31 · 0% Book details