← Book details Zainazain Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 78

Sashe 45

Zainazain Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kai Tsaye Dr.Imran yace"Wlh Allah kenan..Wannan Sakamakon Gaskiya ne..In ma baku yarda ba sai akoma asibitin akara gwadawa a gani"Alhaji Tsoho ya Dagamai Hannu yana Fadin"A'a Ba Bukata ai ka Rantse..In ma karya ka Fada kai da Allah..Mungode..Kai Hadiru bama Abubakar Key din Motarka ya maidashi..'
Ajiyar rai ya Sauke yana Fadin"Nagode Ranka ya Dade.."Daga haka ya mike yana Tafiya yana waiwayansu su Dina kamar zai Fadi Dina kai t kauda zakiya kuma Fari kawai ta mai ido alamun zamu gamu,Yana Fita Sadiq Daya karbi Key din Mota hannun Hadir yabi bayansa Ya Daukesa ya maidasa Har suka isa Dr.Imran kansa na Kulle ya Tufka ya warware ammh yakasa gano Bakin zare yaso ya Tambayi Sadiq
sai dai Rashin Samun Fuska yasa Ya kama Bakinsa..

Dr Imran na Fita zakiya ta Fito da wayarta Tana ma Dina Rada Tana Fadin"Yanzu Wasan zai Fara Daukan Dadi..Bari na Karisa Dayan aikimn."Mirmishi Tayi mata Cikim Kwarewa Ta Shiga Wsop dinta bayan ta Bude Data Ta Lalubo Lambar Zaina wacce Dina Ta Sato mata awayar Zain Tunda Wayarsa bata da matakan Tsaro,wasu Bad pics Take Turamata wanda Dina ta Daukesu ita da Zain cikin yanayi mara Dadin kallo Wajen guda Goma ta Tura mata Sai da Ta Tabbatar daya Shiga kana ta Fita Taje Bangaran Sakoninta ta Lalubo lambarta ta Tura mata sako Kamar haka...!
*Kina Bukatar sanin wani Abu game da wanda kika bama Amanarki Da Duka yardanki..?

Toh in dai kin Ci karo da Sakon nan ki Bude Data dinki ki Shiga Wsop zaki ga na Tura Miki da sako..!*
Na Farko kenan na Biyu kuma sai Tace *Nasan zaki Shiga Rudu da Dimautuwa ko..?Kina kuma neman Karin Bayani..?

Toh zaki sameshi Cikakke Harda ma wadanda baki sani ba..Kiyi Hanzari Kizo gidan Kakanin Mijinki zaki samu Duka Amsoshinki yanzu yanzu...*
Tana Gama Tura mata da Ta Tabbatar da ya shiga sai ta Kashe wayar Dama Sabon Layi ta Siya Kuma saboda wannan amfanin Tana gamawa ta Taka Kafar Dina Tana Fadin"All D Plan Done..Sai Abu Daya kawai ya Rage Tabbatar da Auranki da zain.."Tafada tana wani Juya ido Dina batayi mgana ba ammh Ranta kamar Farar Takardan Saboda murna
bangaran Alhaji Tsoho kuwa Dr Imran na Fita Alhaji Tsoho ya Juya yana kallon Kwamishina yana Fadin"Kayi Hakuri fa...Bawai don ban yarda da Abunda Kazo min Dashi bane..A"a ko Daya sai Domim kada mu zama Wasu Mutanen da Marabansu da Dabbobi kadan ne..Ko miye ya Tunkaromu mu Maida Hankalinmu mu Bincika in mun Gano Gaskiya kada mu Fusata..Mu Natsu mu yanke Hukunci Yadda ya Dace.."Kwamishina na jinjina kai yake Fadin"Hakane...Tabbas na yaba da Hikimarka.."Yafada yana jinjina ma Kaifin Basiran Alhaji Tsoho.

Kai Tsaye Alhaji Tsoho ya kalli Dina yana Fadin"Diyata...Wani Shaida gareki da zai Tabbatar mana Da cewa Zainullahi ne Uban Cikin Jikinki..?

Yafada yana kallonta kai ta Dukar kasa ganin Falon kallo ya Dawo kanta Zain kuwa Tunda Yaji Abunda Alhaji Tsoho yace kansa ya kara kasa kamar wanda zai Kifa Saboda Tashin Hankali,Zakiya ce ta Rike Hannun Dina tana Daga mata kai Shiya Bata kwarin Gwiwan Dagowa ta Fara mgana"Saboda Shine kadai Saurayina..Kuma Tunda Nake Shine kadai Namijin Danake irin wannan Mu"amalan Dashi.."
Dam...Gaban Kowa ya Fadi,Kowa sai ya saki baki yana kallon Dina Alhaji Tsoho ya Cije Abunda yake ji acikin Ransa yana Fadin"Ai bamu san haka ba Diyata..?

Cikin Dakiya da Rawan Murya Dina Tace"Shi ya sani..Shi yasan komai...Yafi Kowa sanin Bayanshi bana Mu"amala da kowani Namiji..Tabbas Zain yasan wannan Cikin Dake Jikina ba Shakka Shine Ubansa..!

Tafada Idanuwanta na Cika da kwallah Gabadaya sai Falon ya koma Shuru Alhaji Tsoho ya Kalli Zain Cikin Kakkausan Murya yace"ZAinullahi...Kai Zainullahi..'Yafada yana Zungurinsa da Sandan Hannunsa Firgigit Zain ya Dago kansa Idanuwansa da suka Kada suka yi Jajir ya juyema Alhaji Tsoho Cikin Bacin Rai da kuma Lalama yace"Kaji Abunda Ta Fada..?

Kallonsa ya maida kan Dina Sukayi Kallon kallo na wasu Mintina kafin ya Janye idanuwansa Cikin Rawan Murya da Datsewar Harshe yace"Ehhh...Amm..."Hannu kawai Alhaji Tsoho ya Dagamai yana Fadin"Ba Ammh na Tambayeka ba..So nake nace Gaskiya ne Abunda Ta Fada da wanda na gani arubuce Cikin Dake Jikinta Na ka ne..?

Yafada yana Tsaresa da ido kamar yadda Kowa ya Tsareshi Da Ido Zuciyoyi na Bugawa,Kowa na Jiran yaji mai Zain zai ce shi kuma Ji yayi kamar kasa ya Bude ya Shige Ciki Wata irin Nadama da Danasani ne suka Lullubeshi,Jikinsa ya kama Rawa Zuciyarsa ta Fara Bugawa haka Yake kallon Duka iyayensa suna kallonsa Cikin son kada wannan Zaton ya Tabbata ammh Ina Bakin alkami ya Riga ya Bushe Haddir ya Kallah wanda ya Gyada mai kai alamun ka Fada kawai zain yau din Ranar Da nake Juyemaka ne Tazo.

Kansa ya maida kasa yana Jin Tahowar kwallah ganin Irin yadda Abba ke kallonsa da Alhaji Tsoho Cikin Nuna mishi Mun fa baka yarda Cikin Rawan Murya Dana Zuciya ya Bude Baki Cikin Kuka yace"Ehhjhhh...!Alhaji Tsoho Ba Shakka Cikin Dake Jikin Dina nawa ne..Ni nayi mata Shiii...Ta Fadi gaskiya Dani kadai take Mu"amala Gaskiya ne..!

Yafada yana Rufe Fuskansa da Tafukan Hannayensa yana sakin wani marayan kuka Kamar karamin yaro,Gabdaya Falon sai ya Rude da Salati da Salallami da kalaman Zain Dina da Zakiya kuwa Hannu suka Damke suna Sakin Numfashi Umma da Nene kuwa sai kuka Haka Zareena dasu Hamdiya Hajiya Mama da Inna Rukkaya Fadi Suke Hasbunallahi wani"imal wakil.

Baban Kaduna da Daddyn Abuja Hulunan kansu suka Cire sun
a Fifita cikin wani yanayi Abba kuwa kansa na kasa yana jiin Jikinsa Gabadaya yayi sanyi Alhaji Tsoho kuwa Sunan Allah kawai yake ta Kira,Duk da ya Zargi hakan zata Faru ammh Ya bama Zain Duka yardansa.

Daga Chan Bakin Falon sukaji Kara Da kuka Lokaci Daya da Fadin
"Innalillahi Wa'inna Illaihiraju"un....Lahaula walakuwatu Illahbilahi..."Zaina Take Fada Tana Daafe da Kirjinta Wanda yake Barazan nan Fashewa da jin kalaman Mijinta Abun kaunarta wanda tafi Kowa yarda Dashi Duk Duniya.

Hannu ta Daga Tana Nuna Zain Cikin Wani Fargici Shi kuma Tunda yaji kara da Mganarta ya Dago kansa Lokaci Daya ya Mike Zumbur Duka idanuwansa suna Waje
Laila Ke Riketa da Ita Itama kanta Cikin Rudin Take da Jin wannan mganar kafin Tayi wani Yunkuri Zaina ta Sulale kasa asume Bakinta na wani karkafa kamar Wata mai aljanu.

Ai Da wani Gudu kamar walkiya Zain ya Taka ya Nufi Zaina,Gabadaya Su Inna Rukayyah da su Umma suka mike afirgice suka nufeta.

Cikin Wata irin Murya mai amo Cike da kuka Zain yake fadin.

"FIRSTLOVE....".
*Janafty...*
*ZAINAZAIN..!*
_(Is a love Story and Betrayal)_
*Wattpad:Jamilaumar351*
*Mallakar:Janaftyshakira*
*BOOK 1*
"Shi ya Fara isa gareta da wani Gudu kamar zai kifa,Laila ce Ta tareta sanda zata Fadi Sakamakon Ta Rinjayeta sai Dukkansu suka Zube kasa Tare,Laila kuka ta Fashe dashi Tana Jijjiga zaina Lokaci Daya da Kiran sunanta kafin Zain ya kariso wajen gwiwa Biyu ya Duka agaban Zaina ya Ciccibi kanta ya aza Bisa Cinyarsa yana Kiran sunanta Cikin wani yanayi haka ma su Umma da suka Karisowa kowa ya Shiga mamakin ganinta da Abunda ya Faru Tunda basu san sadda tazo Gidan ba Balle har taji wannan al"amarin da kowa yasan Bazai mata Dadi ba.

Laila ce ke kuka Tana Jijjiga Hannun Zainar Tana Fadin"Na Shiga uku Halima ki Tashi Don Allah..Wlh da nasan Abunda zai Faru kenan da ban yarda na kawo ki nan da kika ce ba..Allah na Tuba.."Take Fada Tana kuka kamar An Tambayeta ta Cigaba Da Fadin'"Ni bansan me ya sameta ba Tun Dazu muka gama Abunda zamuyi muka samu Waje muka Zauna muna Hira Tana ta cewa na Tashi mu Tafi nace mata mu kara Zama na wani Lokaci Ni bansan meyafaru sai dai kawai naga kamar An Turo mata sako a wayarta ta Ciro wayarta Ta Duba Daganan ne sai ta Rikice ta Fara kuka Tana Dafe Kirjinta Nayi Ta Tambayanta Ko wani abu ya Faru ne taki min mgana,Sai cewa kawai Da Tayi na Rakota nan Gidan bata ma iya Tafiya na Rikota muka Fito Daga Cikin Makaranta muka Hau adaidaita zuwa nan..".

Ta Karishe Fada Cikin kuka Kamar wata karamar yarinya ba wanda ma yabi ta kanta ganin sun Rude ne sun Rasa yadda zasuyi yasa Haddir ya Shiga Kitchen da Sauri ya Dauko Ruwa mai sanyi yana Zuwa Ya sheka ma Zaina afuska Lokaci Daya ta saki Ajiyar rai Numfashinta ya Fara Tafiya Da Sauri Sauri,Zain Rumgumeta yayi yana Sauke Numfashi Lokaci Daya yake Fadin Alhamdulillah.

Dina kuwa da ZAkiya Juna suka kallah kafin Dina ta Dagama Zakiya Hannu Alamun Jinjina ita kuma Sai ta Daga mata kai Cikin Jin Dadin yabonta,Ganin Numfashin zaina ya Dawo yasa sai kowa ya fara komawa Wajen zamansa Aka bar Umma da Nene da Zareena kan Zaina wacce ke Rumgume Jikin zain,Sai Laila Dake gefe Rakube Cikin Alhini Da Damuwar Wannan Al"amarin Dayake Shirin Faruwa da kawarta ko ma Tace yake kan Faruwa.

Ahankali Take Bude Lumsansun Idanuwanta,Kafin Ta Fara Gani Dishi Dishi ahankali kuma ganin nata ya washe,Fes ta Saukesu kan Zain wanda ke Rike da ita Kura mai ido Tayi na wani Lokaci kamar kiftawan Ido Abubuwa suka Dinga dawo mata Tun Daga Hotunan da aka Turomata na Mijinta da wata karuwa Suna Halin Sirrarantan Juna Har zuwa Tambayar Alhaji Tsoho da kalaman Zain Tuni Idanuwanta suka Rufe Zuciyarta Ta fara wani Tsalle tana Bugawa Da karfin Bala"i ta Saki kawai ta Fashe da kuka Lokaci Daya tana Jaye Jikinta Daga na Zain Shima cikin Raunin Zuciya ya kara matsota yana Mika mata Hannu zai kamata Da wani Karfi Zaina ta Tattaro Jarumtar ta Tashi Tsaye Duk da Jirin Datake gani Idanuwanta na Zubda kwallah Tana kallon Zain ammh Ta kasa Furta ko kalma Daya.

Shima Mikewan yayi Yana Kokarin Nufarta Da Sauri Ta Fada Jikin Umma tana Sakin Wani marayan kuka wanda Duk wanda yaji wannan kukan zai san kukan ne Dayake Fitowa Daga karkashin Zuciyarta Rumgumeta Umma Tayi Itama Tana Kukan mai Hawaye,Gabadaya Falon Jikin kowa yayi sanyi Kowa kaga Fuskar ba Annuri kuma Cikin Tashin Hankali Masu kuka kuma natayi...
Chapter 45 · 0% Book details