← Book details Zainazain Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 78 OF 78

Sashe 78

Zainazain Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Direban Dake gaba yana Driving ya waigo yana Fadin Lafiya nan kwadastan ya kwashe komai ya gayamai Direban daman Dan Shaye Shaye ne yace"Bari na Tsayamu Sauketa..Karya Take Yanzu haka irin yan iska nan ne Masu Zuwa bariki bada kafar Dama ba.."Kwasdastan yace.." Daga ganinta kuwa oga."Yafada yana kallon Zaina wacce ta Dukar dakai Tana Hawaye Gabadaya hankalin yan Motan ya koma kanta kowa sai Tofa albarkacin bakinsu suke Tun alokacin
Zaina Taji ta Fara Nadaman Wannan Fitowar Datayi ganin Direban na shirin Tsayawa ne yasa wani Dake zaune agaba Tun Dazu bai ce komai ba ya ciro 300 ya mika ma Kwadastan ta baya yana Fadin gashi nan ya cikamata Suje Allah ya kaisu lafiya Sai Lokacin Kwandastan da Direba suka yi Shuru ya karbi kudin yace Zaina ta kawo na Hannunta ta mikamai sai Hararanta yake maida kanta Tayi kasa kawai Tana Hawaye Lokaci Daya Tana Share Hawayenta da Gefen Damkwalinta.

Cikin Ikon Allah Wajen 3:00pm na Rana suka isa kano Saboda Rashin Mutumcin Direban Nan ko Tasha bai kai Zaina ba ya Sauketa nan Bakin Hanya Da yan Motan suka mai mgana yace Shi haka kurum bai yarda da ita ba Tunda dai an zo kanon Shikenan Zaina Taji ta Muzanta Sosai ko Tsayaawa ma Batayi ba Ta Juya ta Fara Tafiya yan Motan suka Bita da kallo wasu na Fadin gaskiyan Diraben ne Suma basu yarda da Zaina ba kamar wata mara gaskiya nan dai suka wuce suka Barta Tana ta Tafiya akasan Abakin Titi Motoci nata wucewa da Adaidaita Tafe take kawai Tana kuka da Nadaman Fitowarta Tana Tunanin ko Ta koma gida ne..?

Ammh ina Taga kudin Mota..?

Ina zata..?

Wa zata Nufa..?

Inda ma take bata ma sani ba Kuka kawai take Tana Sharan kwallah kamar an ce ta Juya sai ga Wata golf da sauri ta saka hannu ta tsaidata ta Faka agabanta Sai taja ta Tsaya Direba ne amotan sai wani a agefensa sai Wata Mace abayan Motan ita kadai ta Hakimce,Dukowa Direban yayi yana Fadin"Hajiya ina Zuwa..?

Da Kamar bazatayi mgana Ganin Abunda wanchan Direban yayi mata ammh sai tace"Za...Zaria zani.."Da Sauri yace"Ikon Allah muma ma chan muka Nufa..Hajiya Don Allah bari na kara Mutum Daya.."Daga Bayan tace"Bakomai.."
Ya Bude Ma Zaina gaban Motan yana Fadin"Kai bawan Allah gyara mata..Ta zauna ke Shigo.."Zaina tayi kwalkwal kafin tace"Ammh sai dai ka Taimaka min bani da kudin Mota.."Wani sakaran kallo Shima ya Bita dashi kafin yace"Allah ko..?

Daman har yanzu akwai masu wannan Taimakon..?

Gaskiya kiyi Hakuri ni Sana"a na Fito ba Taimako..".

Da Sauri Zaina Tace"Don Allah ka Taimakamin.."Ta Fada Tana Hawaye karamin Tsaki yaja kafin ya Taka Motarsa yana Fadin"Kiyi hakuri kila mai Taimakon yazo.."Yana Shirin Tafiya ne Matar Dake Baya wacce ke Kallon Abunda ya Faru Tace"Ka Dauketa..zan Biya.."Da Sauri ya juyo yana Fadin"Zaki Biya fa Hajiya..?

Ta gyada kai Cikin Washe baki yace"Shikenan Hajiya..Ke Shigo ki godema Allah hajiya ta Biya miki.."Jin haka yasa Zaina ta Sauke ajiyan zuciya ta kama Murfin Motan ta Shiga Tana Sauke Numfashi Idanuwaanta duk sun kumbura saboda kuka Sai da Ta Daidaita zamanta Tana matsawa Domin Taga kafadanta na Gogan Namijin Dake kusa da ita sai da suka Fara Tafiya kana ta waiga Bayanta Tana Fadin"Nagode Haji...!

Mganarta ta makale ne Ganin Wacce Direban ya ke kira da Hajiya Wata kyakyawan Farar mace ce mai kyau Gata Fara ga Dogon Hanci da Tsukikin baki,Tana Sanye cikin Shigar Doguwar Rigar material Buba wacce Taji Stone work Kayan Jikinta masu Tsada ne haka kunnuwanta da Hannayenta duka Sanye da Zinare,ta saka wani Jan Vail Ta yane kanta Dashi Kamar yadda Takalmin kafarta yake ja haka Jakarta ma Dake gefenta Ja ce mai Tsada Dogon Hancinta yana Sanye da Hudun Hanci,Kallo Farko in kayi mata zaka Fahinci Tana da Zubi Da Fulani,Sannan kuma karamar yarinya ce mai akallah Shekaru 25 aduniya Tana Zaune Cikin Mota ta Hakimce Kamar Wata Sarauniya.

Kara Waro Idonta Tayi Tana kallon Zaina Bayan ta Kauda Idanuwanta Daga Taba wayarta Cikin Basarwa ta kalli Zaina wacce ta saki baki da Hanci Tana kallonta Haka kurum Taji Matar ta Burgeta Cikin Sanyin Murya Tace"Bakomai..karki damu..!

Tafada Lokaci Daya Tana Cigaba da latsa wayarta Cikin Sanyin Jiki Zaina ta Daina kallonta ammh Lokaci Bayan Lokaci Tana kallonta Ta madubi kuma In Matar ta Dago suna Hada ido,Haka kurum taji Matar kawai ta Burgeta Ganin Farko Da Tayi mata Haka suke Tafiya Zaina na kallonta ta Madubi Itama in Ta Dago sai Su Hada ido Ganin haka yasa in sun Hada ido sai ta sakar mata Mirmishi Domin bata san Dalilin Yarinyar ba na yawan Nacin kallonta
Shida Saura na yammah suka iso Zaria ta Sabon gari suka Shiga Wajen Bayan gidan iya ya Sauke wannan Namijin sai itama Ta Hajiyar tace ya Sauketa nan Fakawa yayi ta Bude Mota ta Fito Tana Bude Jakarta bandir din yan Dubu Dubu Ta Fito Dashi ta zari Guda 15 ta bama Direban ya karba yana Ta Godiya,Wucewa kawai Tayi Tana wani irin Taku Lokaci Daya Tana Tsaida mai Adaidaita Baki zaina ta saki tana kallon Mace iya mace wacce ta mallaki komai na ajikin Mata,Direban ne ya katseta da Fadin"Ke wai ina zaki Sauka ne..!?

Da Sauri Zaina Tace"Nan zan sauka.."Kallon Mamaki yayi mata kafin yace"toh ki sauka mana ko kina Jiran sai nace ki Sauka.ne..?."Batama Tsaya Jinsa ba Ta Bude Murfin Mota Ta Fita Tana Kallon Kyakyawan matanan ta Tsaida Adaidaita ta Shiga Direban bai bi ta kanta ba ya Wuce yana Murnan ya samu kudi a asama.

Tsaye Zaina Tayi Tana kallo Matarnan Adaidaitan Data Hau ya Fara Tafiya kamar Wacce ta santa sai Taji in ta Bari Tatafi Zata Rasa Madafa,Kuka ta Farayi Tana Bin kasuwar da kallo Kowa sai Harkan gabansa kawai yake ba Ruwan wani ma Da ita bata Taba Zuwa Zaria ba sai yau Tana Cikin wannan Halin Taji an Dafa kafadanta da Sauri Ta Waigo Sai kawai Taga Kyakyawan Hajiyanan Ganinta yasa ta Sauke Numfashi Ta saki Mirmishi.

Cikim mamaki Tace"Lafiya..?

Na shiga adaidaita mai Adaidaitan yace min ga wata chan tana kallonmu Tana kuka ko Tare muke..?

Sai da nace ya Tsaya na Fito na ganki lafiya..?

Ina ne Gidanku..?

Wata anguwa zaki..?

Duka Ta Jero mata Tambayoyin Cikim kulawa,Da Sauri Zaina Tace"Bansan ko"ina ba..Bansan ina zani ba.."Cikin mamakinta Tace"Topha..Wajen wa to kika zo..?

Sai Zaina ta Fara Hawaye Tana Fadin"Bakowa.."Shuru Tayi Tana kallonta kafin Tace"Shikenan bar kukanan ki gayamin me sunanki kuma Daga Ina kike..?

Zaina Tace"Sunana Halima..Daga Bauchi nake.."Haka kurum Taji bata son Ta gayamata karya Cikin Kallonta sama da kasa matar tace"Bazan matsa naji me ya Fito Dake Daga Gida ba...ina ganinki naji kin bani Tsausayi kuma zan iya Taimakonki ammh Zan Fada Miki gaskiya Domin Ita ke Rike Dani har yau har gobe..Ni sunana AISHA FARIDA mutane Suna kira da SHOLLY
ni ba yar garin Nan bace Yar Gombace ammh na Zama yar Zaria Domin nafi Shekara Hudu acikinta kuma ni ba Zaune nake gaban Iyayena ba Zaman kaina nake in kin amince zan Tafi Dake gidan Dana ke zaune Gidan Uwar Dakina ce Dake nan anguwan gwado Gidan UWAR MATA..!

Zaina Taji gabanta ya Fadi ta kalli matar sai kuma Taji ta Natsu da ita Cikin Ranta Tana Tunanin ina ta Barta Tatafi ina Zata Cikin Sauri Tace"Shikenan zan Biki nagode Anty Farida.."Mirmishi Aisha Farida Tayi mata kafin tace"Ok...Shikenan muje gida Sa"adiya kiyi wanka kiyi sallah kici Abinci ki Huta ko Domin naga Duk kin gaji.."
Murna Ta kama Zaina Ta fara Hawaye Tana Fadin"Nagode Sosai..Nagode.."Aisha Farida tace"Karki damu.."Daga haka Taja Hannunta Zuwa Cikin Napen Din Tana Fadin"Muje mallam...!
*Tammat Bihamdulillah...*
_Alhamdulillah nan na kawo karshen wannan Labarin ZAINAZAIN kashi na Daya kamar yadda na Fada muku Labarin yana da Shashe Biyu ne mun gama Shashe na Daya zamu shiga Shashi na Biyu,Tabbas Zainzain kashi Na Daya yazo akyauta ne kamar yadda kuka gani sai dai kuma ku sani Kashi na Biyu na wannan Labarin IS NOT FOR FREE..!,Na Tabbata indai Soyayyar da na gani ne Dalilin Rubuta wannan Labarin Ko nawa na saka kudin Labarin nan zaku Siyeshi har ku ninkasa ma Nasan da yawanku Masoyan Amana ne Kama Daga Wsop Zuwa Wattpad Na Tabbata Zaku yi TuruRuruwa wajen Siyan Kashi na Biyun wannan Labarin Kodomin ganin Yadda Zata kaya Ga Zaina ta bar Gida ta Fada Hannu Aisha Farida Sholly kuma Sholly Zaman kanta Take agidan Uwar Dakinta Uwar mata yaya Rayuwar Zaina Zata kasance atsakiyar karuwai..?

Yaya Rayuwar Zain zata kasance ba Zaina..?

Yaya Dina.?

Shin Tana Haihuwa..?

Xata samu Nasaram auran zain da samun Soyayyarsa..?

Yaya Duka Ahalin Zain Zasu ji da wannan Salon al"amarin Daya Faru dasu..?

Wacece Aisha Farida..?

Yaya Rayuwar Zakiya da Dina Zata kasance Daga karshe..?

Shin Zaina Zata Haifi Cikin Jikinta ko kuwa..?

Zata koma Ma Firstlove ko Rabuwarsu kenan..?

Duka wadanan amsoshin Suna Cikin ZAINAZAIN kashi na Biyu ne Wanda zaku sameshi Cikin Farashi mai Sauki da yardan Allah.._
*ZAINZAIN PART 2 KUDIN KARATUNSA
250 NE KACHAL GA MASU AMFANI DA BANKI ZAKU TURA SHEDAR BIYANKU TA WANNAN ASUSUN BANKIN 0552179550 JAMILA UMAR GT BANK SAI ATURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR 09069067488,KAI TSAYE MUTUM ZAI TSINCI KANSA A PAID GROUP,MASU TURO KATIN WAYA KUMA ZASU BIYA
300 NE KACHAL INDA ZASU TURO HOTON KATINSU TA WANNAN LAMBAR 09069067488,KAI TSAYE ZASU TSINCI KANSU A PAID GROUP DIN DA ZAMU FARA POSTING DIN ZAINAZAINA KASHI NA BIYU MUTANENMU NA NIGER KUMA ZASU TUNTUBI WANNAN LAMBAR WAYAR +22794775574 SAI KUNZO ALLAH YA BAKU IKON SIYA AMEEN...*
*01/07/2021*
*Janafty....*
SummaryInformation
DocumentSummaryInformation
WpsCustomData
TECNO LD7
WPS Office
Normal
Times New Roman
Times New Roman
Calibri
Calibri
!%),.:;>?]}
$([{
20c6358e6e5047728eee02d9fd4e7215
Chapter 78 · 0% Book details