← Book details Zainazain Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 78

Sashe 54

Zainazain Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Haddir ya Sauke Numfashi yana kallon Zain dake kwance yana Barci yace"Da sauki zamu ce Sadiq gashi kwance yana Barci.."
yanzu ya gama amayar da Tea din Da Haddir ya Hadamai yasha..Alluran barci ya sake mai ya kara Doramai Drip,Zazzabin da Ciwon kan ya sauka Jiya ammh Zuwa safiya kuma Sai ya Dawo,ba Domin Haddir gidan ya kwana ba baisan wani Hali zain zai Shiga ba yama ki yarda suje asibiti ne da Chan zai kaisa abashi gado adinga Kula Dashi Tunani yake Allah yasa wannan Damuwar da zain ya saka ma Ranshi bazai haifarmai da Hawan Jini ba
Cikin Tsauyawa Sadiq yace"Allah ya bashi lafiya..In zan wuce zan Biyo na Dubasa Daman kiran da nayi maka Don kazo ka Duba Abba Shima ya kwana Jikin ba Dadi ganin ban sameka ba sai Alhaji Tsoho yace naje asibiti na Dauko Dr Imran har ma yazo ya Dubashi yamai alluran Barci ya samu barci.."Cikin Damuwa Haddir yace"Innalillah meke damunsa..?

Cikim Damuwa Sadiq dake Haraban gidansu bayan ya rako Su Inna Hannatu ne Direban Abba ya Dauketa zuwa Filin Jirgi Dagachan zai wuce da Zainab makaranta Tare da ita suka Tafi yace"Yace Jininsa ne ya Hau sosai ya Haddir..!

Cikin Salati Haddir yace"Subnallah yanzu ya Jikin nashi..?

Sadiq ya numfasa yana Fadin"Da sauki har ya samu barci ma.."Haddir yace"Allah kara lafiya zan shigo zuwa anjuma na Dubashi in Jikin nashi yayi sauki Ina Halima..?

Sadiq yace"Itama fa Tana kwance ba Lafiya ya Haddir.."Haddir kansa kawai ya Shafa yana Fadin"shikenan Allah ya bata lafiya.."Daga haka suka yanke Kiran Dafe kai kawai Haddir yayi yana kallon Zain Wani Irin Abu yake ji a kaasan Ransa zai iya Rantsuwa cewa Zain ne sanadin Hawan Jinin Abba Kaicho Dama irin wannan Abun yake ta Jiyema Zain Tun Suna makaranta ammh yayi kunun Uwar Shegu Da mganarsa sai yanzu da komai ya baci ne zai koma yana Nadama Gashi ya saka kowa Cikin Damuwa Iyayensa na Fushi Dashi haka Zakalika ma Matarsa Kuma Tana cikin wani Hali Saboda shi Yana Fatan Allah ya yayyafa ma Abun Ruwan Sanyi.

Yana Tare da Zain ko"ina Baya zuwa ko Salla agidan yake yinta Daya Farka Shi zai Taimakamai yayi alwala yayi sallah yaci Abinci wanda Haddir din ke Fita ya Siyomai,Har zuwa Wajen bayan La"asar dai jikin na Zain yayi sauki Zuwan Sadiq ne wanda zai koma zaria Jikin ya kara Rikicewa Domin ya Fadamai Zaina na chan kwance kwana Take kuka Bata ci bata Sha Umma kadai take ma mgana,In ba ita ba sai dai ka gaji Dayi mata mgana bazata Tanka ka ba sai kuka Shima da zai Tafi ya Shiga inda Take ya Duka Har kan gadon Da take kwance Yana Mata mgana Tare da kalaman Lallashi gareta ammh Zaina sai kuka kawai take,Yayi kokarin yaga Tayi mgana ammh Taki cemai komai Umma tace ya Tashi ya Tafi kawai bazata mai mgana ba ya Fita da Tsausayin Zaina acikin Ranshi Zain yaji Hankalinsa ya Tashi Kwarai ya Fara Kokarin Tashi Dama Haddir ya Ciremai karin Ruwan Da cewa zai je GRA ya Duba Firstlove dinsa.

Haddir na Kokarin Hanasa Da cewa"Ina zaka kana Cikin wannan Halin..?

Shima Abba ba lafiya gareshi ba yau sai da Dr Imran yaje ya Dubashi Jininsa ne ya Hau.."Cak Zain ya Dakata Daga Sanya kayan dayake kokarin yi ya waiwayo yana kallon Haddir Lokaci Daya yana Fadin"Jininsa ne ya hau..?

Ya Fada da Sigar Tambaya Cikin Muryan Ciwo da mamaki Kai Haddir ya kada yana Fadin"Kwarai da gaske...Na sani kuma kaima ka sani Kana da Nasaba da Hawan Jinin Abba In haka ne kuwa zuwan Ka gida yanzu ba alheri bane..Wlh Zain ko Alhaji Tsoho Dake matukar kaunar ka bai zo so ganinka yanzu ba Gwara ka Jira zuwa nan da Kwanaki kadan in Abun ya sake su sai ka Tunkaresu ammh yanzu akwai matsala Domin Sai Ciwon Abba ya kara Tashi in ya ganka..!

Ya Fada yana kauda kai Saboda Bayason kallon Zain din balle har ya Fahinmci wani Hali yake Ciki Kuma baya so ya Furta masa Abunda ya Faru tsakanin Dadyn Abuja da Abba Jiya Shi kuwa Zain gabadaya Jikinsa sai ya kama Rawa wani Jiri na neman Gadashi ya Rike Jikin Wardrope yana Fadin"Firstlove fa Haddir..?

Bazani naga Halin Data ke Ciki ba..?

Nafi kowa sanin Halin Zaina bazata ci Komai ba Kuka zatayi Tayi har wani Cuta ta kamata Tana da Rauni indai akaina ne sosai...Ya kamata naje na lallasheta.."
Ya Fada kamar yayi kuka Haddir ya kalleshi Cikin Jin Haushi yana Fadin"U are not Serious..Kana Tsammanin akwai Wata mgana da zaka gayamata ne ayanzu ta Saurareka..?

Ka riga ka gama Zubar da Duka Kimarka da Soyayya da yardan dake tsakaninku..Da kake Fadin Kasanta Tana da Rauni akan ka Meyasa kasan da Haka Tun Farko baka Daina Abunda watarana In Taji Raunin nata zai bayyana ba..?

Yafada Cikin Bakinciki Da Takaichin Zain din Wanda kawai ya Sunkuyar dakai bai kara mgana ba Rigar hannunsa ya Zura na wani Farin yadi ko hula bai saka ba Duk yayi wani Busu Busu dashi ya Nufi Haddir yana Fadin"Aramin key din Motarka..?

Haddir ya nuna mai Gaban Dressing Mirror din Dakin yana Fadin"Ga Key din Taka Motar chan yau da Safe dana Shiga Cikin asibiti na Taho maka da ita.."Da sauri ya nufi wajen ya Dauka Yana Sauri kamar baya Cikin Natsuwarsa yana Shirin Barin Bedroom din yaji Muryan Sadiq yana Fadin"Kar kaje gida ayanzu Yaya Zain..!

Ya Fada yana mikewa Haddir na Gefe yana kallonsa Zain ya Juyo Cikin Cije baki Da alamun Rashin lafiya yace"Kai Sadiq meka sani..?

Baka san komai game da Dacin Da nake ji acikin Raina ba Dole zan je na Roki Abba dasu Umma gafara na kuma Dauko matata mu Dawo Gida na Tabbata ita mai yafiya ne gareni.."
Daga Haka ya Juya zai Fita Sai kawai yaji Sadiq yace"Ko kaje Ba wanda zai maka mgana Ballatana ya Saurareka..In ma Abba ya bari ka Shiga Gidan kenan..!

Yafada Cikin Wani yanayi Atare Zuciyar Zain Data Haddir ta amsa da Dam!

Haddir ya Waro Ido yana kallon Sadiq shi kuma Zain da wani Sauri ya waigo yana kallon Sadiq Cikin Rashin Hayyaci kafin yace"Ban...Ga...ne ba..!

Ya Fada muryansa na Rawa...

Kada kai Sadiq yayi yana Fadin"Eh...Jiya nan Abba ya gama Tara su Umma da Nene yace bai yarje musu In kazo Gidan suyi maka mgana ba ballatana Har su Saurarekaba Daga karshe yace harta Anty Zareena na bai yarje mata ba kuma Umarni ne ba Shawara ba Daga Karshe yace Shi da kanshi zai gayamaka kada ka karo Tako mai Gida Tunda ba Da kudinka ya Siya Gidan ba..!
*Shakira..*
*ZAINAZAIN..!*
_(Is a love Story and Betrayal)_
*Wattpad:Jamilaumar351*
*Mallakar:Janaftyshakira*
*BOOK 1*
"Ba Zain kadai ya kad'u da jin Mganar Sadiq ba Hatta Haddir Shima sai da ya nuna Kad'uwarsa a Zahiri,Zain kuwa K'asa kasa Daukansa Tayi Domin Wani irin Jiri ne ya kwasheshi ya Tafi luu zai Fadi Atare Dukkansu Sadiq da ya watsar da Jakar Hannunsa ya Nufeshi Sai dai Haddir ya Rigashi isa Gareshi Tunda Shi yafi kusa Dashi Cikin Ikon Allah ya Tallafeshi ya Fado Jikinsa Cikin Fitan Hayyaci yake Fadin"Abba...Ne Abba ne yace kada na kara Shigomai gida .?

Yafada wasu zafafan Hawaye suna Biyo Duka kuncinsa Atare Sadiq da Haddir suka Rikosa Zuwa Bakin gado ganin yadda Duka Jikinsa ke Rawa suna Zaunar Dashi Haddir ya kalli Sadiq yana Fadin"Jeka Kitchen ka Dauko Goron Ruwa mai sanyi a cikin Fridge..ka Hado da karamin kofi plz.."
Jin Haka yasa ya Fita Da Sauri ba"a dau wani Lokaci ba ya Dawo da Ruwa a Hannunsa Da karamin Kofi ya mikama Haddir Shi kuma ya karba ya Tsiyaya Ruwan Fin Rabi acikin Kofin ya Mikama Zain yana Fadin"Karbi kasha..Zuciyarka Zatayi sanyi ta kuma Daina Bugawa Da Sauri Da Sauri.."Idanuwansa da Suka Sauya kala ya Watsama Haddir Dake mikamai Kofin Ruwan Cikin Bugun Zuciya da wata murya Cikin yanke Tsammani yake Fadin"Taya kake Tunanin zan iya Shan Ruwa ya Tsirgamin Haddir..?Kanaji fa Abba Da kanshi yace kada kowa ya Saurareni kuma Shima zai Fadamin kada na kara Takamai zuwa Gida..?

Kaichona Haddir Wlh ban Taba jin na Tsani kaina ba Irin Jiya yau kuma kalaman Abba Gareni sun kara karyamin Duk wani Sauran kwarin Gwiwata yanzu ina zan saka kaina Duka iyayena da yan"uwana Suna Fushi Dani kuma suna kallona a mutumin da bai da wata kima..? taya zan kara samun Damar da Duka Ahalina zasu yarda dani..?Ga Firstlove itama Zata barni saboda wannan Bakin Fentin da na Saka ma kaina Allah na Tuba Allah ka yafemin Astagafurullah...!

Yake Fada Cikin Kuka Lokaci Daya yana saka Fuskarsa Cikin Tafukan Hannayensa yana wani kuka mai cin rai Harda Sheshsheka kamar zai Shida,Sadiq baya ya koma Shima yana Sharan kwallah Domin Zuciyarsa bazata iya Juran ganin Jajirtatacen Yayansa na irin wannan kukan,ba Haddir kuwa kansa kawai ya Dukar yana Sauraran Duka maganganun Zain din Shima Ya gaji da kukan zuccin Da yake yine,Dagowa yayi yana kallon ZAIN Din kafin ya sake mikamai Kofin Ruwan yana Fadin'"Duk naji...Karbi dai kasha Ruwan ko bakomai zai Saka ka Natsuwa..!
Chapter 54 · 0% Book details