← Book details Zainazain Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 77 OF 78

Sashe 77

Zainazain Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai ke karan kada Miya Matsa ki bamu Waje Maras kunya"Sumi Sumi Zakiya Taja Dina Dake kuka suka koma Gefe Zakiya Ta kalli Dina Cikin Takaichi Tana Fadin"Ki Natsu Dillah..Kina da mtsala wani Lokacin.."Dole Dina Ta natsu ammh hankalinta na wajen Zain wanda Daddyn Abuja yace aje asibiti Alhaji Tsoho ya Dakatar dasu yaje su kawo Ruwan zamzam Hajiya mama ta kawo yayi addu"a ciki ya bama Baban kaduna yace su Shafamai afuska Cikin Ikon Allah yana Shafamai sai gashi Ya sauke ajiyar Zuciya Kafin kuma ya Fara Bude Idanuwansa.

Ganinsa Akan Cinyar Haddir gasu Baban kaduna sun zagayesa Gefe Daya gasu Umma komai ya Dawo mai Zumbur ya Mike su Abba na Rikoshi Yayi Saurin Cire Baban Rigan jikinsa yana Fadin"Ku sakeni naje na Nemota..Wlh bazan iya Rayuwa bata ba...Bazan iya ba"Yake Fada kamar wanda ya Zare Baban kaduna da Haddir ke Rikesa Abba kuwa Da Daddyn Abuja kwalla suke dama sune masu Raunin ganin yaki yarda ya zauna yasa Alhaji Tsoho ya Daga baki ya Kirashi Sunansa.

"Zainullahi...kai Zainullah yaka nan."Jin Alhaji Tsoho na Kiransa yasa ya Dakata da Neman Fitan Dayake ya Zubamai Ido yana Hawaye Cikin kuka yake Fadin"Alhaji Tsoho kagani ko..?

Zainata Tatafi ta barni sai da nace ku bani matata aka ki bani..Ku barni na Taje na Nemota.."Alhaji Tsoho ya kalli Haddir yana Fadin"Hadiru zaunar Dashi.."Haddir ya zaunar Dashi Kan Kujera Dakyar sai Sambatu yake,Kana Alhaji Tsoho ya kalli su Umma da Nene dasu Zafeera Dake kuka yace"Kuyi hakuri kubar kukanan..Aminatu Tafi Da Goggo Halima Dakinki ki gayamata komai Ya kamata tasani yanzu.."Ba musu goggo Halima Tabi bayan Hajiya Mama Daman Ta kosa Taji me ya Faru Ga kuma Tashin Hankalin Data ke ciki na Takardan Zaina,Suna Tafiya Alhaji Tsoho ya juya yana kallon su Mama safiya Lokaci Daya yana Fadin"Hannatu da Rukayyah da Wasu Cikin yan"uwanki su Dauki Hamdiya Zuwa Dakinta Saboda kunga suna Waje suna Jiranku ba Dadi..Ku Tafi ku kaita Dakinta Allah basu zaman Lafiya.."
Suka amsa da Ameen Jiki a sanyaye kafin Alhaji Tsoho ya Juya Ya kalli Haddir yana Fadin"Kai kuma Hadiru ka kara Komawa ka Dudduba Hanya da kuma Tasha..In Allah yasa batayi Nisa ba Shikenan in kuma Tayi Allah ya Tsareta aduk Inda zata je...Kaddaran Data Fadamana kenan sai Hakuri.."Haddir ya gyada kai yana Fadin"To Alhaji Tsoho.."Ya mike kenen Zain Shima ya mike yana Fadin"mu tafi Tare Haddir..!

Da Sauri Alhaji Tsoho yace"A"a Koma ka zauna..Ina zaka Cikin wannan Halin..?

Cikin Karaya da Muryan kuka Zain yace"Taya Zakacemin na zauna alhalin Matata Ta bace ba"a ganta ba..?

Bazan zauna ba din sai naje Wlh.."Yafada Harda Rantsuwa Cikin Fada,Alhaji Tsoho ya kada kai yana Fadin"Kai Bashir kamasa ya zauna..Ba inda zaka nace Zainullahi.."
Zain zai kara mgana Baban kaduna ya Hanashi Da Fadin"Kaga koma ka zauna Jiri fa kake gani koma ka zauna.."Zain ya koma ya zauna yana Fadin"Baba Firstlove ce Fa tace wai Tatafi..?

Ina zata..?

Kuma fa Tace Tana da Ciki Baba Bata da inda zata Baba kabarni naje na Nemota.."Abba ya kauda kai yana Sharan kwallah Daddyn Abuja ne ya Dafa kafadarsa yana Fadin"Karka damu za"a ganta da ikon Allah.."
Shuru kawai Zain yayi ya maida Fuskansa Kan Tafukan Hannuwansa yana Rera Siririn kuka,Haddir yamike zai Tafi Zafeera Ta Mike Tana Sharan kwallah Tace"Zan bisu Alhaji Tsoho.."Da Sauri Umma ta mike Tana Fadin"Nima zani.."Da Sauri Alhaji Tsoho yace"A"a ke Fatima ki zauna..Kai Hadiru ku Tafi da Zafeera.."Kuka Umma Ta saka Zareena ta Riketa Tana Lallashinta.

Haddir da Zafeera suka Fice da Sauri Suna Fita Yan Kai Amarya suka Fara Fita Zuciyoyi ba Dadi ba wanda yabi Takan Dina Da Zakiya inna Rukayyah da Inna Hannatu sai Dangin Mama Safiya,da Mom iklima Suka Tafi da Hamdiya Kawayenta Tun dazu wasu abokan ango suka yi gaba Dasu Inna Halima kuma Tana Dakin Hajiya Mama tana ta Sharan kwallah Bayan Hajiya Mama ta gayamai komai Tana Fadin"Wauta ne ke Damun Halima in banda Sarkaci Data saka kafa Tatafi ina zata..?Tana da Inda yafi nan ne..?

Allah Sarki Hajiya Fatima kin cika uwa Nagari.."Take Fada Tana kuka Hajiya Mama na bata baki Su Umma na Falo suma suna nasu Kukan Domin Zain banda kuka da sambatu ba abunda yake,Jin kiran salla yasa Alhaji Tsoho yace kowa yaje yayi sallah Su Umma suka koma Ciki su Abba suka Fita Zuwa sallah Harda Zain din wanda Baban kaduna yake Rike Dashi Gabadaya baya gani Sosai In ya sakesa zai iya Fadi Sambatun ambaton Firstlove kadai yake gwanin Tsausayi da kuka, Mama Safiya kuma Sauran yan"uwanta suka Fara Shirin Tafiya Alhaji Tsoho Dakinsa ya koma Cikin Damuwa Domin yayi sallah.

Dakyar Umma Tayi sallah sai kuka Take Tana Rokon Goggo Halima Kan ta yafemata itace Sillan komai ita kuma Goggo Halima na basu hakuri Nene da zainab har sun Share Hawayensu Kowa kagani Cikin Damuwa Mama Safiya sai Fadi Take Allah ya bayyana wannan yarinyar,Dina kuwa da zakiya ba wanda yasan Fitansu Sai dai aka ga basu Ashe Zakiya ce Taja Dina suka bar Gidan ganin Tana kuka Tana neman kara ja musu Abun mgana Gidanta ta kaita Tana Mata Fadan meyasa Ta cika Mtaala ne..?

Yadda yau gidan Ya Rikice Daman gashi ana Jin Haushinta sai ace itace ma Sanadiyar Tafiyar ma Halimar.

Bangaran su Haddir kuwa haka suka Dawo ba wani Labari mai Dadi Wannan Labarin ya sa sai da Zain ya kara Suma Cikin Daukewar Numfashi Hankula suka kara Tashi an Daukesa Zuwa asibinsu Kenan Ita ma Umma ta Suma sai da aka sakamata Ruwa Gida ya Rikice ko abinci ba wanda yabi ta kai Dangin Mama Safiya ganin ba Lafiya suka yi sallama suka wuce bayan Sunyi Fatan Allah ya bayyana Halima.

Zain ya Shiga Doguwar Suma ne Dakyar aka Daidaita Numfashinsa aka sakamai Oxygen su Dr.Imran ne sukayi Attending dinsa Domin Dr.Haddir ya kaasa Tabuka komai Saboda Tashin Hankali Daki na musamman aka kai Zain Su Abba Duk suna asibitin Tare da Zain harda Zafeera kowanne kagani Hankali atashe acikin Zukatansu kuma Rauni ne Da kuma Fatan Allah bayyana Halima Abba kuma Yaji Tsausayin Zain dayasani da Tuni ya yafemai inda yasan haka zai Faru Daya saka baki Umma ta bashi Matarsa da Duk haka bai Faru ba addu"a kawai yake Allah Tada kafada Baban Kaduna kuma wani Abokinsa ya Kira Dake aiki nan Gidan Tv na garin Bauchi Ya gayamai Bacewar Halima Bashi da Hotonra Haddir ya saka ya Turamai Hotonta da kayan Dake Jikinta da kuma Cikakken Sunanta,Shima bai da Hoton nata awayar Zain dake Hannunsa ya Cira ya Turamai da Cikakken Bayanin Zaina din ko Allah yasa za"a dace yadai ce yanzu zai saka Duka Cigiyan In da Rabo za"a dace ko kuma wani yazo yabada Bayanin ya ganta.
****
Bangaran Zaina kuwa Tana Ta Tafiya sai da Taga tayi Nisa da GRA kana ta Tsaya Tana Haki Domin ta Dade batayi Tafiyar kasa haka ba,waige waige ta Farayi saI kuma Lokacin Tunanin ina ta Nufa yazo mata Tana Tunanin Bayan Gada da kano Bata Taba zuwa ko"ina ba sai ko Lagos kuma yanzu bai kamata Taje ko Daya Daga Ciki ba Tana wannan Tunanin ne Taji mai adaidaitan Daya Tsaya gabanta yana Fadin"Hajiya Tafiya ne..?

Kallonsa Tayi Sai kuma ta Juya Bayanta Tana tsoron kada ayi Saurin ganin Takardan nan abiyo Sawunta Sai kawai Taji bakinta ya Furta"Tasha zaka kaini inda zan samu Motar barin garin nan.."Bai damu da yanayinta ba Yace ta Shigo ya kaita da Sauri ta Shiga yaja suka Tafi,Tun acikin adaidaitan TaFara Kuka Tanayi tana Sharan kwallah basu Dauki Lokaci ba sai gasu Cikin Tasha Suna Zuwa mai Adaidaitan yace"Gamu Tasha Hajiya ina zaki ne Hada..?

Cikin Muryan data Shake da kuka Zaina tace"Ina zani kuma..?

Nima bansani ba.."Da sauri mai adaidaitan ya waigo Yana kallonta kafin yace"Topha..Baki sani ba kuma..?

Cikin Sharan kwallah Zaina Tace"Eh ammh nan Motocin ina ne..?

Mai adaidaitan yace"Motocin Lodin Bauchi Zuwa Fambeguwa da garuruwan Dake wajen har Zaria sai kuma na Bauchi Zuwa Zaria da kuma ta Zuwa kano.."
Cikin Wani Sanyi Zaina Tace"Zaria..? zaria ta kaduna State.."?

Mai adaidaitan Cikin mamaki yace"Kwarai Hajiya.."Zaina na kara Kallon Kudin Hannunta Tace"Bari na Hau ta Zarian.."Da sauri mai adaidaitan ya Fito yana Fadin"To muje na sama miki Motar.."Jin haka yasa ta Fito Tana Bin Tashar da kallo Tunda Take bata Taba zuwa tasha ba yau ga Dalili ya kawota Dankwakinta Ta warware ta kara Nanndawa aka Ta Rufe Fuskarta Dakyau Tabi mai Adaidaitan zuwa wajen da Motocin ke fake suna zuwa wani Dan Union
mai adaidatan yayi mao mgana Shi kuma yace mai Motar zaria Ko me yaceme.?sai ya juyo ga Zaina yana Fadin"Kinji yace Ba Motar da Zata Zaria Direct sai dai ki Hau Ta kano in kinje chan zaki samu ta Zarian Direct.."
Zaina Bata da Zabi Sai kawai Tace"Shikenan.."Mai adaidaitan Ta kallah Tana Tambayanshi Kudinsa yace"Dari uku ne.."Dubu Dayan ta Dauka Ta bashi ya Fasa ya bata Chanji yana mata Allah ya kiyaye Hanya tace Ameen ta Wuce Tabi Bayan Dan Union din yana Fadin ko Tana da kaya ne..?

Tagirgiza kai kawai Har wajen Mota sukaje Kiran Sharron Ta kusa Cika Sauran Mutum Biyu Ta Cika akace ta Shiga ta zauna Ta Shiga Ta zauna Tana jin wani Hawaye na cika idanuwanta Tana Shiga sai ga Wani yazo Ya Shiga Ba Jimawa kawai suka Tashi Sun Fara Tafiya kenan kwandasta yace kowa ya Hado kudin Mota Cikin kasala lokaci Daya Tana kara Rufe fuskata tace"Nawa ne kudin Motan..?

Cikin Sauri kwandastan yace"Dubu Biyu ne Hajiya
kudin Motanki zuwa Kano."Waro Ido Zaina Tayi Gabanta na Faduwa Lokaci Daya tana kara kallon Kudin Hannunta Dubu Daya da Dari bakwai,kallon Kwadastan tayi Shima yana kallonta yace"Yadai Hajiya..?

Cikin In ina Zaina tace"Don...Allah...ka..min hakuri...Kudina bai kai ba Dubu Daya da Dari bakwai gareni na zata iyakarsa 1500 ne.."Cikin kallon Sannu ko Kwandastan ya Bita Dashi kafin yace"Lalle nema kaji wata yar rainin wayau oga..?
Chapter 77 · 0% Book details