← Book details Zainazain Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 78

Sashe 37

Zainazain Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zakiya Dagachan Bangaran ta Saki Wata Dariya kafin tace"Daman ai nasan haka zai Faru..Saboda Abun bai zata bane ya Faru...Karki Damu Normal ne Tsarin na Tafiya Dai Dai yadda muka Tsara.."Dina Tana Sauke Numfashi Tana Fadin"Kinji Abunda yace..Ya zamu yi namu Tsarin Goben..?

Zakiya tace"Karfe 7am na Safe yace...Mu kuma zamu Tafi karfe 6am ne na safe in Juransa Sammako mu Atafe muka kwana..Karki manta ki zama Cikin Shirin In kika batamana Lokaci zai iya Riskanmu kuma kinga Faruwar hakan kamar Batamana Shirin mu ne.."Da Sauri Dina Tace"Karki Damu zan yi kamar yadda kika ce..!

Daga haka suka yanke Kiran Dariya kawai Zakiya ke kwasa Lokacin Data ke maimaita Mgangamun Zain Data gama Nada cikin wayarta Cikin Kada kafa ta Furta"Waya gaya Maka Borno Gabas Take Zain...Wlh sai na Tabbata kaji kunyar Duniya gaban Duka Ahalinka Sakarai kawai.."
******
Zain Allah ne kadai yakai Shi Gida Lafiya Domin yana Cikin Tashin Hankali da Dimuwa da Firgita Haka yaje gida ba Cikin Natsuwarasa ba Da Zaina ta ganshi ahaka sai da ta Tsorata Ta Fara Tambayanshi Lafiya yama kasa mata mgana ganin Hankalinta ya tashi ne yasa yamata karyan cewa Sun Rasa Patient din Dayaje Dubawa ne Allah Sarki Baiwar Allah harda kukanta Shi kuwa Zain Abunda ke Damunsa Dabam yana Tunanin yadda komai zai Tafi ne Batare da wani matsala ba.

Tun adaran ya Fadama Zaina tafiya ta kamashi Zuwa Gombe kuma zata Dauki Tsawon kwana Uku zuwa Hudu bata kawo komai acikin Ranta ba tamai Addu"an Fatan alheri Harda Hadamai kayan Tafiya Shi kuwa yana zaune ya Zafga Tagumi kawai yana Ta Zufa,Natsuwa kwata kwata bai da ita Duk zaina ta Damu ganinsa Cikin wannan Halin,Ammh sAbun da ya bata mamaki ansha Samun irin wannan Case din a asibiti bata taba ganin Firstlove ya Shiga irin wannan Halin ba sai yau ammh sai ta Danganta da kila yau Matar ta bashi Tsausayi ne Haka Dai Ta gama Hadamai kayan Dakyar ta lallasheshi ya Shiga wamka ita kuma Barci yaci Idonta koda ya Fito Tayi Barci sai yaji Dadin haka,Zama Dirshan Zain yayi barci ko Barawo ya kasa Saceshi Zaina kawai yake kallo yana jin kwallah na Cika kwarmin Idanuwansa lokaci Daya yana mai Kaico da Rayuwarsa daya Kasa Barin Abunda Allah ya Haneshi gashi yau Dalilin Bijirema Allah ya saka kanshi Cikin Wani Bala"i wanda Fitar dashi sai Allah
Da Zaina taso ta Farka sai ya kwanta ya Rufe ido kamar yana Barci,sai kuma yaga ta koma Farkawanta na uku ne ta tashi ta Bude ido ganin Wuta kau ga kuma Shi Zain din ya kwanta Ko Towel din daya fito wanka Dashi bai Cire ba saboda Zullumi da Fargaba,Ganin haka yasa ta Sauko Daga kan gadom tana Fadin"Allah Sarki Fistlove Daga gani ya gaji..Ji ko Towel bai Cire ballatana ya saka kayan Barci.."
Wardrope ta Bude ta Daukomai Boxers dinsa tazo a Hankali ta Warware Towel din ta Zuramai wando Tana yi tana Lura kada ta Tadashi,Har tagama sakamai ta gyaramai kwanciya ta Rufeshi da Blanket ta sakarmai Kiss a goshi Lokaci Daya tana Shafa Fuskarsa kafin ta Dauki Towel din ta Bude Tiolet ta Shiga Idanuwansa da suka Kala sukayi ja ya Bude ya bita da kallo Sai ya kara jin Nadamar Abubuwan da yayi ta aikatawa Tun Suna London sai kuma yau ya kara yarda Da kalaman Haddir ya kuma yarda Masoyinshi ne Ace bai yi ma Matarsa ta Sunna Ciki ba sai karuwa..?

Dama haka Allah ke lamarinsa Kodomin yanu mana mana Ishara mu Bayinsa,Yana Jin Motsin zata Fito ya sake lambo kamar mai barci yana Jinta ta kashe Wutar dakin ta kunna Dumlight,Ta hayo Gadon kan Kirjinsa ta yada Zango Ta Ja bargo Ta Rufesu Gabadaya Shi kuwa Zain kasa Rungumeta yayi Domin haka kurum yau yaji yana jin kunyar Tabata Haka kurum zuciyarsa ke wani Rawa ga Zunubun aikata Zina ga kuma Girman Zunubin Kashe Rai Lalle yana Cikin Bala'i
Yadda yaga Safe haka yaga Dare,Sai gabda Asuba ne barci ya Kwaaheshi,Sai dai yaji ana sallame Salla Ita kanta Zainar ta makara Haka ya tashi Jikinsa Duk ya Mutu,Agurguje yayi wanka yayi sallah kana ya Shirya yana yi yana Duba agogo Fatan Dake Hannunsa Zaina na Kitchen Tana Hadamai Breakfast ya Bitachan yace mata zai Wuce Duk iya Kokarinta na Ya tsaya ya karya kasawa yayi ganin 7 din Daya ce ta Kusa haka ta Rakashi har Bakin Mota Har Motarsa Ta gama Ficewa Daga gidan Tana Tsaye Tana kallonsa Haka kurum Take jin wani Sanyi Jiki da Faduwar gaba haka kuma Take ganin yau kamar Firstlove din nata baya cikin Natsuwarsa Haka dai ta koma Cikin Gida Sukuku ta karisa aikinta ta Fada wanka Domin itama tana Da Shiga Sch 8am na safe.

Koda zain ya fita Daga Gida kai Tsaye Gidan Dina ya tsaya Ammh Abun mamaki har ya kusa Mintina goma yana Mata Knooking Shuru bata zo ta Budemai ba ganin haka yasa ya koma Mota ya Dauko wayarsa ya Shiga Kiranta Abun Da yakara saka Zuciyarsa Bugawa Fat Fat Shine wayarnata Tana Kasheni,kamar zararrare haka ya Fito Daga Mota ya koma Jikin Kofar yana Bugawa Lokaci Daya da Kiran sunan Dina yayinda kuma Hannu Daya yake ta Gwada Layinta.

Neagbours dinta ne wani Namiji Dama Gidajen irin ajere suke Kamar Estate ne yaji Bugun kofan yayi yawa ya Fito yana Tambayan Zain ko lafiya Shine ya karisa suka gaisa yana Tambayarsa Dina Shi kuma ya bashi amsa da Bata nan Domin yana Dawowa Daga sallar Asuba Yaci karo da ita ta Fito Daga gidanta da akwati a Hannunta wata Mota ta Dauketa Sun Fita da Gudu,kafin ma ya gama Zain bayani Numfashinsa ya tsaya Cak kamar wanda aka Dauke ma ji da gani Shidai yana gama gayamai ya wuce ya koma cikin Gidansa ya maida kofa.

Zain kuwa wani Irin Juyawa ce ta Daukesa sai gashi a kasa yana Haki,Idanuwansa sum koma Jajir cikin wani yanayi yake Tunanin toh ina Dina Taje..?

Wata zuciyar tace gidanku mana zataje ta Tona maka asiri..?

Wani irin Rugurugu yaji a tsakar kansa kamar Rugugin Hadari Kamar an Tsikareshi haka ya Tashi yana Layi ya nufi Mota yana Fadin"Bazan bari ki Tozartani ba Dina..Bazan barki ba."
Haka yake Fada kamar wani Zararre haka ya Tashi Motar ya Fita Daga Haraban wajen kamar zai Tashi Sama shi kadai kawai yake Fadin"Karki mun haka Dina..A"a don Allah karki Mim haka..!

Haka yake ta Fada kamar wani Wanda yayi gamo ko ya zauce..!
*Tanque so much Dearests..Allah ya bar kauna da Zumunci ZAINAZAIN BAND 1&2*
*Shakira..*
*ZAINAZAIN..!*
_(Is a love Story and Betrayal)_
*Wattpad:Jamilaumar351*
*Mallakar:Janaftyshakira*
*BOOK 1*
_Budaddiyar wasika Daga Zainullahi Usman Abubakar Saulawa Mijin Halimatu Abdullahi Gada zuwa ga Tarin Masoyansa da makiyansa,yace na Fada muku Mussaman yan Group din ZAINAZAIN BAND 1&2, da kuma yan Group din Janaf Novella 1&2,da Sauran Group din da suke masa One love Rokon alfarma yake Don Allah don Annabi ku Taimakamai ku Koma bayansa ko zai samu wannan Bala"in Dake Tunkaroshi Da sauki a samu masu Rokar masa Firstlove Da kuma masu bama su Alhaji Tsoho baki Domin adaidai wannan Gabar dai ya Sare Ya riga ya Shiga kogin Nadama..Yace na gaya muku yana Godiya ga masu Zaginsa da Tsine masa albarka da wadanda ke Jin Dadin Faruwar haka da kuma Fans dinsa masu Jin ba Badi Dukkanku yace na ce muku yana Muku One love.._
"Zain yana Fita Daga Gidan Dina GRA ya wuce kai Tsaye yana Tafe yana manganganu Shi Kadai kamar wanda ya Fita Daga Cikin Hayyacinsa.

Hon ya Dinga Zubama Megadi agigice kafin ya wangalemai get ya Sulalo da Motarsa Cikin Gidansu ko gama parking bai yi ba ya Bude Murfin Mota ya Fice da Sauri Gudu Gudu Sauri Sauri Zuwa Kofar da zata sadashi Da asalin Cikin Babban Falon Gidansu.

Abba na Tsaye a tsakar Falo yana gyara zaman Hulan kansa Nene na gefensa Dauke da karamar Jakar briefcase Dinsa Umma ma na Tsaye Dayan gefen,ayayinda suka sakashi a Tsakiya kenan Sai Zainab Dake gefe Itama Cikin Shirinta na kamala Domin har ta samu Gurbin Karatu a Jami"ar ATBU bauchi Ta Fara zuwa Aji Daya 7:30am na safe Take da aji Shiyasa Abba zai kaita tunda Ma"aikatansu na Gaban Jam"ar ne,Tunda har yanzu Motar da Abba ya Siya mata bata iso ba.

Sallama Abba yake da su Umma ya mika Hannu zai karbi Jakarsa Zain ya Fado Falo kamar Daga sama Gefe Daya kuma yana ta waige waige kamar wani mara gaskiya Gabadaya iyayan nashi Suka sakarmai Ido Suna kallonsa Cikin mamakin ganinsa Bashi da Natsuwa kwata kwata atare Dashi.

Cikin Mamaki Abba ya kalleshi yana Fadin"Kai Zain lafiyar ka kuwa..?

Ka Shigo gida kamar a Firgice..?

Yafada yana sake karantarsa Shi kuwa Sai da yagama Dube Dubensa bai ga alaman Dina Tazo Gidan ba kana ya Saki Ajiyar Zuciya ya kalli Su Abba yana Fadin'Bakomai Abba...Dama...Dama..!

Nene ta katseshi Da Fadin"Dama me..?

Yarona Lafiya kuwa..?

Ko wani abu ya Faru Da Zaina ne... ?

Da sauri ya Girgiza kai yana Fadin"A"a Nene....Dama Dama zan Wuce asibiti ne shine nace Bari na biyo na gaisheku Komai lafiya Da yardan Allah.."Ya karishe Fada yana Faman goge Zufar Dake Tsatsafomai Daga saman Goshinsa Gabadayansa in ka kalleshi baida wata Natsuwa.

Ido Suka zubamai suna kallonsa kawai Cikin mamakinsa kafin Abba yace"Kai zain yaka nan..Daga ganinka baka Cikin Natsuwarka Meya faru..?

Kada kai kawai yayi yana Fadin"Bakomai Abba Allah kuwa..Na Wuce asibiti.."Daga Haka bai basu Zarafin mgana ba kawai ya juya ya Fita a gaggauce kamar zai Tashi sama Dukkansu suka Bisa da kallon Mamaki har ya Fice Umma ta kalli Nene Tana Fadin'"Nene yaronki ba lafiya fa..?
Chapter 37 · 0% Book details