← Book details Zainazain Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 78

Sashe 13

Zainazain Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin Ikon Allah ana Kokarin Saka ahannu akan Takardan da za"ayi ma Maryama aiki Allah ya Sauketa Lafiya Inda ta Samu Haihuwar yarta Mace mai kama da Ita sak,sai Kuma Duhun mahaifinta Data Debo Saboda Maryama Faraace Sosai Sabani
Abdullahi Dayake bakin Fata Sai da aka gama gyarata ita da Abunda ta Haifa kana Nurse Ta Fito da Jinjiran a Hannunta Da Halima ta Faracin karo Zata mikamata Zain yayi azamar Mika Mata Hannu yana Fadin Ta bashi matarshi Tsaye Tayi tana kallonsa Cikin Mirmishi Dr.Saulawa yace ta mikamai Tako mikamai ya karba kamar zai Fadi Halima ta tareshi suka koma Suka Zauna kowa ya Kura mishi ido ana kallon yadda ya kurama Jinjiran ido yana kallonta da wani Mirmishi Kafin ya Dago yana kallon Abbansa Cikin Yarinya yace"Abba me sunanta...?

Kafin Alhaji Usman ya bada Amsa Abdullahi ya bashi amsa da Fadin"Maryama Ta gayamin in ta Haifi mace Sunan Yaya Halima Take son asakamata Saboda Haka Alhaji Dakta kayi mata Huduba da HALIMATUS SA"ADIYA..!

Gabadaya Murna Ta kama Halima wacce ya"yanta ke Kiranta Goggo Halima Cikin Jin Dadi Take fadin"Masha Allah..Allah ya Raya Halimatu.."Zain kawai akaji yace"Ba Sunanta Halima ba Abba..Ni Matata irin Sunana gareta..!?

Cikin mamaki Nene tace"Irin Sunanka Da'n Nene..?

Wani Suna kenan..?

Cikin Kura ma Jinjiran ido yace"Tunda Sunana ZAIN ita kuma Sunanta ZAINAH daga yau ba Halima ba...Kunga Zainazain kenan..!gabadaya al"ajabi da Mamaki ya kama kowa Dr.Saulawa yana kallon Zain da wani Farinciki acikin Ransa kafin ya Dafa kansa yana Fadin"Allah ya maka albarka...Karka Damu Sunanta Halima ammh Kai mijinta me kuma ka zaba mata Suna ai Shikenan kowa ya Shaida Sunan Matar Zain Zainah ko..?

Yafada yana kallonshi Washe baki yayi yana Daga sai Abun ya basu Dariya Dakyar Dr.Saulawa ya iya karbanta Suka Dunguma Dakin da aka maida Maryama Suka Iske ta Farfado agabanta yayi ma Jinjiran Huduba da Halima ya Dago Yana Fadin"Allah ya Raya Halimatus Sa"adiya..!

Karaf Zain yace"Ba Sunanta Halima ba Sunanta Zainah nace muku..!Maryama ke neman karin Bayani Nene ta Koramata yadda akayi Dariya Tayi Tana Fadin"Gaskiya ne Yarona..Sunan da aka Zabamata yayi Daidai da..Sunanka ina Fatan ko bayan Raina zaku Tabbatar da Halima amatsayin matar Zain..?

Tafada Tana Tsare Duka yan Dakin da Ido Kowa sai yaji Abun Wani iri Baba Abdullahi ne yayi Mirmishi yana Fadin"Kema yarintar Zain din zaki mana..?

Kai ta girgiza Tana Fadin"Ba yarinya bace..Ku kalli Idanuwansa Tsabar gaskiyansa yake Fada..Nidai Nayi alkawarin Tun Kafin Ta Fito Duniya na Bama Zain ita amatsayim Mata Har Abada Ko Bayan Raina Abdullahi ka Tayani Sauke nauyin Dana Dauka..!

Kowa adakin Sai da Jikinsa yayi Sanyi Dr.Saulawa ne yace"Karki Damu Maryama...Insha Allahu da kanki zaki Hada Hannun Zain da Halima amatsayin ma"aurata."Wani Sanssayar Miemishi Tayi kafin tace"Allah yasa Ina Fatan Haka.."Daga Haka bata kara cewa komai Suma ba wanda ya kara mgana sai aka koma Raba Rigima Tsakanin Zain da Zareena Inda Take Rigiman sai ta Dauki Halima karama ammh Zain ya Dafe gadon da Maryama ke kai yace bamai Taba mai Mata Tun Abun nashi na basu Dariya Har suka zo suka Tabbatar ma kansu zain Da gaske Acikin Ran Dr.Saulawa kuma yana Ta auna Abubuwa afili ya Furta Haka Allah ke al"amarinshi Daman.

Kwana Daya Maryama Tayi a asibiti Aka sallamota ta koma Gida aka cigaba da karban yan Barka Gabadaya Kulawanta ya koma Karkashin Nene da Umman zareena Duk da suma Suna Fama da kansu Goggo Halima Sai dai kallo Domin ko Tace su barshi Sai suce sai sunyi ai maryama Tamkar kanwa Take garesu Hakama Hajiya Mama Tana iya bakin Kokarinta,Zain kuwa ansha Fama Dashi Domin Tunda akayi Haihuwan sai Ansha Fama Dashi yake zuwa makaranta sai ya Fara kukan Sai dai ya Tafi da ita da Dubara yake Tafiya yana Dawowa kuwa Shashen Maryama yake yada Zango Daga ma Karshe chan ya koma da kwana Saboda Zaina Ba Wanda ya Damu da Hakan Domin Kowa yana ganin Maryama da Mijinta yanzu Suna Cikin Ahalin Dr.Saulawa Tsudum.

Dr.Saulawa da ya"yansa sun ma Maryama kara Sosai Da Abun arziki Sai wanda ya gani Musamman ma Alhaji Usman da Matansa Sunfi kowa Rawan gani Haka da yan Gada suka zo Suna suka koma da Fadan Irin Dimbin karamci da Dattako irin na Iyalan Dr.Saulawa Goggo Halima ma Bayan Suna Ta koma Itama da Sha Tara na arziki Tana Ta Godiya Aka bar Maryama da yarta Halimatu Sa'adiya wacce Taji Tudu Biyu Sunan Goggo Halima kuma Sunan Baba Atine na gaskiya.

Kwanci Tashi ba Wuya awajen Allah Zaina nada Wata Shida Aduniya Nene ta Haifi Yarta mace Wacce taci sunan ZAFEERA bayan Haihuwanta da Kwana Hamsin Ita kuma Umman Zareena ta Sauka Wannan karon ma Namiji ta samu Yaci Sunan Mallam Umar suna Kiransa Faruq,kamar dai yadda Tsarin yake Nene uwar Maza Taja Nata itama Umman zareena Uwar mata taja nata Tunda Lokacin Zareena ta Girma Suna Cikin Shekaru na Goma da Haihuwa sai Tattalin ya koma kan Zafeera Yadda kukasan kwai haka Umman Zareena ke ji da Zafira kamar Tsoka Daya amiya Zain kuwa da karfi Da yaji ya zama Dan Shashen Maryama Saboda zainarsa Reno kuwa Tare sukeyi da Maryama Tun baya Iya Daukanta Har sai da ya iya Haka zai zauna yana ta mata wasa Tun Kafin ta isa Cin Abinci Zain ya Fara bata kayan zaki Ko Iyayen nashi na Fada Maryama Ta kanyi Mirmishi Tace su kyaleshi Mutum da matarsa Saboda Hakama Ta Riga ta ganeshi Da Taji muryansa zata Fara wuntsila kafa Tana Babban Dariya irin na Jarirai yana Daukanta kuma Shikenan Haka zasu yi ta Rigima da Zareena kan sai ya bata ta Dauketa In Kuma akaci Sa"a ya bata Zareena na Daukanta sai ta Fara kuka Sai Zain ya Fara Dariya Haddir dai yana Gefe Shi baima Cika cewa zai Dauka ba Ganin yadda Zain din ya mamaye komai Sai dai yayi tama Zareena Dariya ita kuma Taji Haushi Ta Fara kuka Maryama Ce mai Raba Fada ta kuma Shiga Ciki Tayi alkalanci.

Shekaran Halima Daya da Wattani Maryama ta kara samun Ciki Sai dai kuma yazo da matsala Tunda Tayi ta Ciwo sai da akaje asibiti nan aka gano Tana da Cancer Mahaifa Hankakula Suka Tashi barin ma Abdullahi,Ammh Dr.Saulawa da Alhaji Bashir sukayi Tsaye sai da akayi mata aiki taji Sauki Bayan an Fitar da wanchan Cikin,Dalilin wannan Ciwon sai Dawainiyar Halima Ya koma Hannun Umman Zareena Tunda Allah ya Doramata kaunar Yarinya Ta Hadasu ita da Zafeera Tana Rainonsu Tare Zain na Tayata Domin Dakyar ma ya bari Umman Zareenan ke Daukan Halimar har ta goyata Ganin Mama Maryaman Bata da Lafiya ne Shiyasa.

Bayan Taji Sauki ma Hakan bata Chanza Zani ba sai dai in Tana kuka akaita Maryama Ta bata Nono a maida mata Ita,Cikin ikon Allah ba Dadewa Maryama ta Sake samun Wani Cikin Wannan karon Da Sauki Abun Sun dai koma asibitin anyi Gwaje gwaje aka Tabbatar da Maryama zata iya Haihuwa ba Matsala Da haka tacigaba da Rainon Cikinta Gefe Daya kuma Dawainiyar Halima yana Hannun Umman zareena Cikinta na Shiga wata na Shida Ta Yayeta Ta Damkama Umman Zareena Ita,wacce ake ma Lakabi da mai Rainon Yan Biyu Sakamakon Zafeera akwai Girman Jiki Har ta kamo Zaina a Girma Ita har ta Fara Takawa Halima din ce Take Ta Rarrafe.

Acikin Wannan yanayin ne Wani al"amari ya Faru wanda iyalan Dr.Saulawa suka kasa mantawa Dashi Shine Wata Ranar Asabar da Misalin karfe 2:00pm na Dare yan Fashi Suka Shigo Gidan Alhaji Bashir da Manyan makamai Lokacin da Suka shigo Gidan Abdullahi ya Tashi gaban get ya Shiga Gidan Wajen Maryama Dama Hakan yake yi sai asuba kuma yake Dawowa,Duka ya Kulle get Din Haurowa sukayi suka Shigo kamar Wasa Dama Tunda ya Shiga Ciki bai kwanta ba,Alwala ya Dauro ya Fara Sallar Nafila yakai Raka"a na Biyu yaji motsin Takun Kafafu Da Sauri ya Sallame ya Dauki Fitilansa da Sandansa zai Fita Sai maryama ta Farka ganin zai Fita yasa Ta Tambayeshi sai yace mata yana Zuwa ya Fita da Sauri Yana Fita kawai yaci karo da Wani katon Mutim Cikin bakaken kaya ya Haskeshi da Fitila yana Tambayan waye Kafin ma yaji wani Abu Daga Bayansa yaji an sakarmai Harshashi aciki nan Take ya Fadi matattace Jin wannan karan Harbin Shi ya Rikita Maryama Ta Fito Da Gudu Ga Ciki Tana kuka Itama nan Take wani ya sakarmata Harshashi aciki Itama Ta Fadi ba Rai.

Innalillahi Wa"inna illairaju"un wannan ahali Sun ga Tashin Hankali kwarai yan Fashi Sun Shiga Har Shashen Alhaji Usman basu dai kashe kowa ba ammh Sun Karbi kudaden Daya Dawo Dasu Daga Tafiya yana Shirin Washegari zai kai Banki,sai kuma Dan kunnayen Zinaren su Nene da wasu kudaden Dake Hannunsu Sukayi ma Alhaji Usman Dukan Tsiya sai da ya Suma kana suka Tafi Su Nene suka Rude sai kuka Ga su Zain Suma kukan suke Zaina da Zafeera kuwa sai kuka Suke na Tashin Hankali Umman Zareena ita Tayi Hausan Kiran Wayar Dr.Saulawa ta Na kuka Tana gayamai Halin daSuke Ciki Cikin Tashin Hankali Shida Hajiya Mama suka Nufo Gidan Domin Daman Kaf an anguwan ba wanda bai ji karan Harbi Biyun Da sukayi ba.

Abun Tsausayi Suna Zuwa Gidan suka ga Get a wangale Hankalinsu ya Tashi ai basu Rude ba sai da suka ga gawan Maryama da Abdullahi kwance afarfajiyan Gidan cikin Jini Sai Zuciyoyi Suka Raunana Idanuwa Suka Zubda Kwallah Su Nene sun Rude matuka ga Halin da Suke Ciki ga mutuwar Maryama da Mijinta Sun Rasa Ina zasu Tare Hawayensu ne,Wanda ke zuba ba kama Hannun Yaro ganin Alhaji Usman baya Cikin Hankalinsa ne yasa aka Tattarashi Zuwa asibiti Dr.Saulauwa ya Kira yan Sanda suka zo Suna Ta Binciken gawan su Maryama Abun gwanin Ban Tsausayi Hajiya mama Kuwa Ta Rude sai kuka Take tsakanin ita dasu Nene an Rasa mai bama wani Hakuri.
Chapter 13 · 0% Book details