Sashe 42
Zainazain Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Karfe 7am na safe Zain ya samu Kiran Alhaji Tsoho inda yake gayamai ya Tabbatar da Shi da Halima sun zo Taron da zai Gudana agidanshi Cikin Hadiyan Miyau yace zasu zo ammh Zaina sai Ta Shiga makaranta zata kai Assigment ne kuma lacran yace Individual yake Bukata Shi kuma sai yayi mai karyar zai Shiga Cikin Asibiti Ya Duba patient ya gama Dasu zai zo Shidai Alhaji Jadaddamai yake ya gansu awajen kana suka yanke Kiran Tunda lokacin komai nashi yake Sukuku Zaina ta taimakamai yayi wanka ya Shirya itama ta Shirya Tunda Shi zata Bi Motarta ta lalace tana wajen gyara,Breakfast ma Dakyar ya yarda Ta Turamai Fadama yake bayajin Cin komai har ta Fara Tunanin ko Bashi da lafiya ne yace mata Kada ta Damu Lafiyansa kalau.
Suna Mota zai kaita makaranta Kiran Haddir ya Shigo Wayarsa Dama ajiyan sun Rabu kan kada Zain ya Kirashi shi zai kirashi Da kanshi da Sauri ya Daga Kiran Shi kuma Haddir yace mai yana Cikin asibiti yazo ya Sameshi da Rawan Jiki ya amsa mai gudu gudu ya karisa da ita Cikin Makaranta ya ijiyeta Abunda ya bata mamaki ganinsa a gaggauce yau ko bakin Department dinsu bai kaita ba ya ijiyeta wai yana Sauri ne har ya bace ma ganinta Tana Binsa da kallo Haka kurun Take jin Tsinkewar Zuciya Jakarta ta saba ta Fara Takawa da Kafa Zuwa Department dinsu ammh Cikin Zuciyarta sam ba Natsuwa Tana Jinta kamar ba ita ba.
Aguje ya Shiga Cikin asibitin yana Faka Motarsa sai ga Haddir ya Fito Daga Cikin Asibitin yana gyara zaman Suit din Dake Jikinsa Motarsa kawai ya Nufa yana Fadin"Shiga muje...Ya kamata muje mu dawo kan Lokaci Kafin Alhaji Tsoho ya Farga Damu.."Zain najin haka yaDauko wayarsa Ya zare key din Motarsa ya Rufeta kana ya Zagayo ya Shiga ta Haddir wanda yana Shiga ya Tasheta suka Bar Cikin asibitin Hanyar kano Suka Dauka Lokaci Daya Haddir na Fadin"Ka sameta..?
Zain na Dafe kansa yace"Ban sameta ba..Tun da muka Rabu nake Kiran wayarta..Amsan Daya ne
akashe take.."Haddir yayi karamin Tsaki yana Fadin"Kashe wayar ma wani Tsarinta ne..Nidai Fatana Allah yasa in mun isa kanon mu sameta agida Komai zai zo da Sauki In muka sameta.."Jin jina kai kawai Zain yake yama kasa Mgana Daka ganshi zaka Fahinci ya Riga yayi Laushi da Rauni.
******
Abunda su Zain basu sani ba Lokacin da suka Dauki Hanyar kano Lokacin Tuni Babban Jeep din Kwamishina Ta Tsufa kan Hanyar zuwa Bauchi Tun safe,Dagashi Sai Hajiya Batula sai Dina Su Waleed Da Waleeda agida aka barsu Tare da Zulai,Sai a Gaba Direbansa da Escort dinsa Guda Daya Sai Zakiya Dake Motarta ita ke gaban Bisa Tsarin ita zata musu Jagora zuwa Gidansu Zain din
*10:00am...*
*Falom Alhaji Tsoho..*
Falon Alhaji Tsoho cike yake da ya"yansa da Matansu da Kuma Wasu Daga Cikin Jikokinsu irin su Hamdiya da kuma Sadiq babba,Baban Kaduna,Dadyn Abuja,Abba suna zaune waje Daya asaman Cafet din Daya mamaye Falon na Alhaji Tsoho Gefe kuma chan Umma ce da Mama Safiya sai Mom Iklima da Nene Daga yammah kuma Inna Rukayya ce da Inna Hannatu Chan kuma Daga Farko Sadiq ne Zaune Sai Zareena Dake gefensa Ita Da Jaririyarta Jalal yana gida Wajen Zainab suna ta wasa dasu Junior,Daga gefen Alhaji Tsoho kuwa Hajiya Mama ce da Hamdiya Dukkansu suma zaune saman Cafet din Sai Alhaji Tsoho kadai Dake saman kujeransa yadan Mike kafa saboda Ciwo Sandar sa na Gefensa yana Bin kowa da Kallo.
Kafin afara Taron sai da yace a Kiramai Zain da Haddir sai dai kuma anyi Rashin Sa"a Suna Daji Lokacin Motarsu ta lalace musu Shiyasa akayi ta Kiransu ba"a samu ba,Ran Alhaji Tsoho ya baci Domin Dukkansu sai da ya Sheda musu Duk Taron da suke Gudanawa basa samun Hallata wannan kuma yana Sha"awarsu a wajen ko bakomai Su din Ababen alfaharinsu ne.
Ganin yadda ya Damu ne Baban Kaduna yace"Alhaji Tsoho kayi Hakuri...Kila suna Cikin asibiti ne Wani Uzuri ya Rikesa ammh ka kwantar da Hankalinka kafin mu Tashi zaka gansu.."Da wannan kalaman Zuciyar Alhaji Tsoho Tayi sanyi ya Umarci Dadyn Abuja ya Bude Taro da Addu"a Haka kuwa akayi bayan ya Bude Taro da addu"an Alhaji Tsoho ya Fara Jawabinsa kamar ko yaushe Nasiha ne da kuma Tunatarwa kan su Hada kansu kana ya gangaro kan su Rike aman junansu dana Matansu su kuma yi Adalci A tsakaninsu Ya"yansu kana ya Gangaro Riko Da Zumuncin Dake tsakaninsu su zama Tsintsiya Daya madaurinsu Daya ko Da watarana Baya Raye Wata Baraka bazata Bullo a tsakaninsu ba,sai ya gangaro kan mganar Auran Hamdiya ya kuma Yi mgana da Kakkausan Murya kan Zafeera game da Mai sonta Barrister Ahmed yace tunda asan Nagartan yaro bai kamata azauna ana Biye mata Kamata yayi iyayenta Maza Baban Kaduna da Daddyn Abuja suyi wani Abu akai shi in yayi wata mgana ya"yansu zasu ga kamar yana matsa musu ne,Sai kuma yayi mgana kan Haddir da zamansa Har yanzu bai yi Aure ba kuma sun saka Ido Sunki cewa komai.
Baban Kaduna ne ya Fara mgana Bayan Alhaji Tsoho ya gama Jawabinsa ya Dora da mai Alkawarin zasu kiyaye wannan zumunci kana Daga karshe yace"Game da mganar Zafeera Da Haddir...Ka bamu Lokaci Alhaji Tsoho kafin Taro nagama zakaci Labari mai Dadi.."Daddyn Abuja yace"Insha Allahu.."Shima Abba ya Tofa albarkacin Bakinsa haka ma su Inna Hannatu Daganan kuma sai suka karkata kan Bikin Hamdiya Dake gabansu sun yanke Shawaran anan Bauchi Za"a Daura Dauran da Bikin Gabadaya Tunda Kaduna Hamdiya zata zauna wani Navy zata Aura,Inna Hannatu ce ta Fara kawo mganar azo nan ayi Bikin Sai Baban Kaduna yace Shu bai ga Fa"idar haka ba gwara atsaya chan ayi wannan mganar tajawo cuceku cikin Falon Matansu dai sunyi Shuru Tunda wannan ba Fagensu bane,Alhaji Tsoho na zaune yana kallonsu bai kuma katsesu ba.
Ana Cikin Haka ne sai ga Sallamar Megadi Daga bakin Falon Sadiq ne ma yaji Sallaman ya amsa ya tashi ya Leka nan Megadin ke Shaidamai agayama Alhaji Tsoho Yana da Bako yace ace mai kwamishinan Ilimi ne Alhaji Gaddafi Sheerif.
Mamaki ya kama Sadiq sai dai kuma Bai yi mamaki ba sanin Kakansa ai ba Boyayyan Mutum bane,Komawa yayi Cikin Falon Har Gaban Alhaji Tsoho ya Duka ya gayamai Shuru Alhaji Tsoho yayi yana Nanata Sunan kwamishina Kafin ya kada kai yace yamai Jagora ya Shigo,yana Fita Alhaji Tsoho ya yi gyaran Murya yana kallon ya"yansa Lokaci Daya yana Fadin"Ku Saurara..Yanzu Abubakar yazo ya gayamin ina da Bako awaje..Kwamishinan kudi na Jahar kano.."
Gabadayansu Da mamaki a Fuskarsu Suke kallon Mahaifin Nasu kai ya Jinjina musu yana Fadin"nace amai iso...Ku Mata ku Tashi ku Shiga ciki har muji damai yazo.."Ba gaddama suka mimmike zuwa Cikin Falon Hajiya Mama,Suna Shiga ba Dadewa Sai ga Sadiq ya Shigo da Sallama Bayansa Kwamishina Alhaji Gaddafi Sheerif ne Yaci Riga da wando na Shadda Harda Babban Riga Bayansa kuma Hajiya Batula ne Cikin Shigar alfarma sai Excort Dinsa wanda Kwamishina yabama Izinin Komawa waje Gabadaya su Abba mikewa sukayi na alamun Girmamawa Kafin suma gama mamaki sai ga Zakiya ta sawo kanta Falon Dina na Binta Abaya Cikin Shigar Abaya ta Nannade mayafin Bisa kanta.
Gabadaya kallo kallo kawai ake ma Juna Alhaji Tsoho ya yanke Shurun da yima Kwamishina Maraba Har gabansa ya karisa ya mikama sa Hannu sukayi musabaha Lokaci Daya da gaisaawa Gefensa nan kasa Kwamishina ya zauna ayayinda Hajiya Batula dasu Zakiya suka yada Zamansu kan Kujerun Dake Falon suna kallon Ko"ina suma su Abba komawa sukayi suka zauna Sadiq ma bai Fita Shima ya samu Waje ya zauna.
Alhaji Tsoho ne ya kalli Kwamishina yana Fadin'Naji mamaki da aka sanar dani Kai ne Bako ne..Ina Fatan lafiya.?
Kwamishina ya gyara zama yana Fadin"Eh Toh Lafiya ba lafiya ba..Kamar yadda ka sani Sunana Alhaji Gaddafi Sheerif Wannan kuma Matata ce Hajiya Batula sai Yata Dina da kawarta Zakiya.."Yafada Yana nuna Kowa da Hannunsa Alhaji Tsoho Dasu Abba suma suka Bisu da kallo.
Gyada kai Alhaji Tsoho yayi yana Fadin"Masha Allah...Sannunku da zuwa.."Hajiya Batula ce kadai ta amsa Dina da Zakiya kansu suka maida kasa,kara gaisuwa akayi Suma su Abba Suka yi Hannu Da Kwamishina aka gaisa Cikin Girmamawa.
Alhaji Tsoho ya Kalli Sadiq yana Fadin"Abubakar Shiga ciki kace Tabawa Ta kawo kayan Motsa Baki da Ruwa.."Da Sauri kwamishina yace"A"a Akoshe miki Mungode.."Alhaji Tsoho yace"Ayi haka..?
Annabi ya koyamana Girmama Bakon mu..".
Kwamishina yace"Hakane..Ammh kafin nan bari mu fara gabatar da Abunda keTafe Damu..Dina Dago kanki.."Yafada yana kallon Dina Wacce kanta ke kasa da Sauri ta Dago Kanta Tana Fadin"Na"am Daddy..."Kai Tsaye ya kalli Alhaji Tsoho yana Fadin"Ka ganeta..?
Alhaji Tsoho ya kalli Dina da Zakiya Sosai Gashi yana so kamar ya ganesu ammh kuma sai ya rasa ina ya sansu Su Abba ma kallonsu suke sudai Tabbas sun Shaidasu,Alhaji Tsoho ya Juya yana kallon Kwamishina Lokaci Daya yana Fadin"Kayi Hakuri..Kasan Jikin Tsufa Kila ko na Taba ganinsu yanzu na mantasu gaskiya.."
Kafin kwamishina yace Wani Abu Baban Kaduna ya kalli Alhaji Tsoho yana Fadin"Alhaji Tsoho Ka manta ne,Sune wadanda suka zo gaida kai Lokacin da ka kwanta asibiti,Har Haddir yake Fada maka Ita wannan Din Tana aiki a asibitinmu Dayan kuma Kawarta ce..."
Ya karishe Fada yana Nuna su Mirmishi Alhaji Tsoho yayi yana Fadin"Anyi Haka kuwa...Na Sha"afa kwarai har ma suka Fadamin Sunayensu,Gashi Har sunayen nasu ma ya Shigemun.."Yafada yana Yar Dariya Kwamishina ya Kalleshi yana Fadin"Wannan ce Yar Tawa Sunanta Dina...Sai kawarta Zakiya..'
Alhaji Tsoho yace"Ba Shakka Sun Fadamin Sunayensu..Masha Allah Sannunku da zuwa..."Suka amsa da yauwa kafin Alhaji Tsoho ya maida Hankalinsa kan Kwamishina wanda ya gyara zama yana Fadin"Dama Abunda ke Tafe dani Abu ne mai muhimmanci Ganin Dukkanmu ba yara bane Naga kafin Komai ya Biyo baya yakamata nazo na sameku mu Tattauna na Sanar Daku Abunda Dan'ku ya aikata ma yata in ma kunsani Toh ku kara sani in ma baku sani ba Na sanar daku..!
Yafada yana kallon Fuskokin su Abba da su Baban Kaduna,Suma Kallonsa suke Cikin Rashin Fahimta Baban Kaduna ne ya Bude baki yana Fadin"Wani irin Abunda Dan'mu ya aikata..?
Wani.."
"Bashir..."Yaji Alhaji Tsoho ya Kira sunansa ya Dago yana kallonsa Cikin Umarni yace"Karka kara mgana sai na baka Umarni.."Kai ya Jinjina yana Fadin"Shikenan.!