← Book details Zainazain Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 68 OF 78

Sashe 68

Zainazain Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nene da kanta ta kaima Dina nata Farantin Dinner ammh Tana ganin Tuwo tace ita kam Batajin Tuwo sai Dai adafa mata Maroconi da Kifi Nene batayi kasa agwiwa ba ta saka Zainab na Tura baki Tana komai ta Dafa mata sai da aka gama tace Bata ma son kamshinsa Fura Take so Tashi Nene ta Fita ta bama Direban Abba sako Yaje ya amso mata kana ta Karba Tasha Umma bata man san Wainar da aka Toyaba sai da Safe Zainab ke basu Labarin Abunda ya Faru domin agabanta komai ya Faru mamaki ya kama Umma Tana Mamakin Nene wani Lokacin Datake Daukan irin wannan Iskancin.

Tun Safe Zafeera tayi Shirin Komawa kano Motar haya zata Bi,Tagama sallama da Kowa Har Abba ma ya sallameta Direban Abba ya Dauketa Zuwa Tasha Bayan tace ma Zaina sai Bikin Hamdiya zata dawo Da zata Tafi suka sarke Hannun Juna Zaina Harda Hawaye.

Ganin Abba ya Fito Cikin Shirin Office Zainab yake kwalama Kira Ta Fito su ijiyeta makaranta Tana da Test da Safanan,Sai ga Nene ta Fito Daga Dakinta Tayi Wankanta ta Shirya Cikin sakin Fuska Ta gaida Abba ya amsa yana kallonta,Daganan Dakin da aka Sauki Dina ta Shiga ta isketa Cikin Bargo Tana Sharan Barci Domin Ko sallar asuba ma batayi ba.

Tashin Tayi Tatashi Tana wani Tura baki Cikin Lallabi Nana tace Tatashi ta sa sauya kaya tazo
Ta gaisa da Abba zai Fita Tunda Jiya basu Hadu ba kamar tace bazata jeba sai wata Zuciya
ta kwabeta da Cewa Mahaifin Zain fa wanda ya Haifan miki Abun Sonki kuma ko Banza Taga Nene na kula da ita ba kamar Umma da Sauran kannen zain din ba
Tashi Tayi Cikim kasala ta Fata Tiolet tayi Brush ta Dauro alwala tazo tacr bari Tayi sallah Nene ta cika da mamakin karfe 8am na safe dan Musulmi ke sallah Lalle Duniya Sallar ma nata Yar faki ce Tayi kuma da Wani mayafi ta Nade jikinta kan Kayan Barcin Dake Jikinta Riga da Wando masu kauri,Nene taso ta sauya kaya ammh Dina taki Tama yi gaba ta bar Nene na Binta da kallon Mamaki.

Abba na Shirin Barin Falon Zainab na Binshi abaya da Jakar Briecafe dinsa,Umma na Falon itama
Yaji Muryan Dina na gaisheshi Ya waigo yana kallonta Cikin mamakinta ganinta Tsaye sama da kasa ya kalleta kana ya iya ganeta Cikin Sauri ya amsa mata bai ma Tsaya Sauraran Nene dake mai wani Bayani ba yace sai ya Dawo Zainab ta Rufamai baya Umma kuma ta kada kai ta koma Dakinta Ta gani Zaina Ta Fito Daga Wanka Nene kuma Tayi Tsuru kawai Dina kuma Mika Ta saki kafin Ta Tabe baki ta koma Cikin Dakin Har Cikin Ranta Tana Jin Haushin Yadda Nene ta Takura mata ta katse mata Barcinta mai Dadi kan Gadon Ta koma bayan ta Cire Mayafin Data yane kanta Dashi Ta koma ta kara Lafewa bisa filon.
*Ina godiya da Sharhinku Both Wsop da wattpad..Keep it Up*
*Janafty..*
*ZAINAZAIN..!*
_(Is a love Story and Betrayal)_
*Wattpad:Jamilaumar351*
*Mallakar:Janaftyshakira*
*BOOK 1*
"Ranar dai Nene Tayi ta Wahala da Bukatun Dina wani Lokacin ma har da iskanci acikin Lamarinta ammh bata nunawa saboda Ita babba ce kuma Bazaka Biye ma Mara Tarbiya ba Ballatana sanin ya kamata ba.

Sai wajen 10am tatashi tayi wanka Breakfast din da Nene ta kawo mata bata ci ba Doya da kwai ne sai Tea da Dankali Tace bataci wai amai yake sakata Don Tsirfa waina Fulawa tace zataci Haka Nan Nene ta Fita ta Soya mata ta kawo mata ko kunya kuma ta karba ta Tsakura kadan Tabar kwanukan nan ta Tsallake ta koma kan gado Ta Fara Dannan waya Kayanta kuwa nan Gegen gado Ta Zubesu Data Bude akwatin zata Dauki Kayan da zata saka Ta saba agida komai zulai ke mata Shiyasa ta Tsallake ta bar komai haka Kila Tana Jiran Nene ko Umma su gyara mata ne Tunda Zafeera dai ta kara gaba Zainab kuma ta Shiga makaranta.

Zaina kuma Tana Dakin Umma ko Lekowa Falo batayi ba Umma ce kadai ke Zirga Zirga Tsakanin Falo da Kitchen,Misalin karfe 12pm na rana Umma Ta gama Miyar agushinta Sai Taji kanta na Sara mata sai ta bar ma Nene Tuka Tuwon Shinkafan Tace zata Daki tasha mgani ta kwanta,Nene ta mata Allah ya kara lafiya ta karbi aikin Tana Zuwa Daki ta iske zaina ta Tsiri aikin Saka mata goggun kayanta da Jiya mai wanki da guga ya kawo Cikin Wardrope taji Dadin Ganinta ta saki Jikinta Yau watarana zaina bata kuka Sannu da aiki zaina tayi ma Umma itama Tayi mata,Wayar Umma ce tayi kara Zaina na kusa da ita ta Miko mata Tana Fadin Zafeera ce.

Bayan Umma ta Dauka sun gaisa tace mata ta isa Tun dazu..Yanzu ma tana Cikin makaranta Fatan Nasara Umma Tayi mata kana suka yanke Kiran Tiolet Umma Ta Shiga Tayi wanka kana ta aiki Zaina Zuwa Kitchen ta Dauko mata Ruwa Ta sha mgani Ta kwanta,Bayan Zaina ta gama Jera ma Umma kayanta Cikin Wardrope dinta sai ta Rage mata Karfin A.C ganin ta Fara barci ganin kar zamanta ya Dameta sai ta saka wani bakin Vail Samam bakar abayan Dake Jikinta,Jiki ba kwari ta Fita Zuwa Falo wanda Tun Zuwanta Gidan batace ga Ranar da Ta fita ta zauna afalo ba.

Sai da ta Leka Bataji Motsin kowa ba Kana ta Fito Falo Tana kallon Kofar dakin da aka Sauki Dina Shuru kamar ba kowa agidan,Su saudart suna makaranta adofane ta zauna kan Daya Daga Cikin Kujerun falon Tana Raba ido Bata so Dina ta Fito Ta ganta ba saboda komai ba Sai Domin kauce ma Haduwarsu,domin Zuciyarta bazata iya Juran ganinta Dauke da Cikin Firstlove ba.

Cikinta ta kura ma Ido Tana Jin wani Shaukin Sonsa na kara Shigarta Da Tsausayin kanta Dana Firstlove wanda Tana da Tabbacin in Umma ta san da wannan Cikin bazata barshi ba ita kuma mai yunkurin Rabata Dashi Sai inda karfinta ya kare.!

Bata ji Shigowarsa ba ballatana Sallamansa ba Tadai ji kawai Kofofin Hancinta na Shako mata kamshin Turaransa wanda ko Mutuwa Tayi aka Dawo da ita zata iya Shaida mai irin wannan Kamshin Cikin Mamaki Ta Dago kanta Karaf kuwa Idanuwanta suka Sarke Cikin Nashi yana Tsaye agabanta Sanye da wasu Ubansu Ameriacan Suit Masu kalan Ruwan Toka ya matse Wuyansa da Nektie,mai Ruwan Toka kafarsa Tana sanye da bakin Takalmi Booth Hannunsa kuma Sanye da agogon Fata na kamfanin Rado Akallo Farko in kayi zaka ji kana marmarin kara kallonsa Saboda yanayin kyawunsa da Haiba sai dai in ka kura mai ido zaka Fahimci Baya Cikin Cikakkiyar natsuwarsa,Ya Rame Wuyansa ya Fito Haka ma Fuskarsa sai idanuwana da karan Hanci Kasumba ta Cikamai Fuska wanda abaya Saje ne kawai Zagaye da karamin Bakinsa Sabanin yanzu da ba gyara sai duk ya zama wani iri gashi nan ne.

Yau tun Safe ya samu Kiran Gaggawa Daga asibiti,Wata mata ce zata Haihu kuma Jini ya yanke mata ya isa ko Fara Duba patient din bai ba Allah yayi mata Rasuwa ita da Abunda ke Cikinta Domin ta Rasa Jini Sosai Abun ya Tabashi Sosai Haka ya koma Office dinsa ya zauna Sukuku Dama Jiya kwana yayi bai yi Barci ba,Sallah yayi bayan ya Idar ya koma Tuban ma Allah gefe Daya ga Zullimin nganar Umma da Abun ya kwana aranshi,Kawai yaji ba wacce yake son gani Sai Firstlove agogon Dake Hannunsa ya Duba ya Tabbatar da yanzu Abba ya Tsufa awajen aiki,Ya yanke Shawaran zuwa yau ko ta Halin kaka sai yaga Matarsa ko da Umma zata Dakeshi ne.

Shine yana Shigowa Falon kamar almara yaci karo da Zaina Zaune afalo ta kurama Cikinta ido,Farinciki yaje ji ko me bai sani ba kawai Ido ya Zuba Mata yadda itana ta sakar mai nata Idanuwan Hannuwansa na Cikin aljihun wandon Dake Jikinsa,kallonta yake da wani Managadisu Tare da Sonta da kaunarta kallon Ban Hakuri karki barni kallon Sha"awa kewa da kuma Muradi ita kuma Idanuwanta ne suka Tara kwallah kallon meyasa ka Cutar damu..?kallon Tsausayinsa kallon Soyayyarsa da kaunarsa kallon Girma kima Tare da wani kewa wanda Bata Taba Tsammanin zai yi Faruwa da ita ba.

Hannunta kawai Taji ya kama ya Mikar da ita tsaye Kur tamai da ido Tana kallonsa bai Tsaya Bata samu zarafin mgana ba Taga ya Fara janta suna Tafiya yana Rike da hannunta,Ganin sun Nufi Dakin Umma yasa ta Kwalalo ido Waje Cikin Tsoro da Rawan Jiki Tace"Umm..Umma...!

"Shiiii..." Ya Fada ba tare da ya Waigo ba sai ya sauya akalarsa zuwa Dakin Nene kamar wata Rakuma da akala haka Take Binsa Nene Dake Kitchen Taji kamar Motsi ta Fito kenan Taga Zain Rike da Hannun Zaina sun Shige Dakinta baki ta Rike acikin Ranta kuma sai Taji Dadi Cikin Sanda ta leka Dakin Umma Ta ganta kwance Tana Barci da Sauri ta Fito Tana Fadin"Haba...Naji Dadi ya samu Lokaci da zai gana da Matarsa..Haba Duk kin wani Takura ma yaro kin Hanashi kwanciyar hankali.."Tafada Tana kyafci Lokaci Daya Da komawa Cikin Kitchen din Ta Cigaba da Abunda Take yi.

Suna Shiga Dakin Nene Ya Saki Hannun Zaina ya Murza ma Kofar key Cikin Rashin Fahinta zaina ke kallonsa kafin ma ta samu Zarafin mgana Taji sa ya Fado Jikinta Cikin wani Irin Rumguma mai karfi ya Rumgumeta Saura kadan ta Fadi Dakyar ta iya Daidaita kanta Bayanta ta saka Hannu Ta Dafa Gefen gadon Nene...

Irin yadda ya sakata acikin Kirjinsa ya bata Tsoro,Matseta yayi ya Kamkame kawai Taji yana Sakin Numfashi Sama sama Kamar wanda zai Shide,kansa yake Tusawa Cikin Wuyanta Yana kara kamkameta kamar zai maidata Cikin Jikinsa,Tana Jinsa Kuma ta Fahimci Komai ban Hakuri da yarensa Numfashinta Take son Fizga ganin ya matse mata Wuya Yasa ta Fara mutsun mutsun Kwace kanta ammh yaki Sakinta sai ma kara Riketa Da yayi kam kam kamar wani zai kwace masa ita..

Ganin Ta kasa kwace kanta ne yasa ta Rabu Dashi kawai ammh Zuwa Lokacin Itama Rauninta ya bayyana Hawayenta kadai ke Zuba daga kwaryan Idanuwanta,Sai da suka Shafe wajen Mintina Goma ahaka kana ya Saussauta Rikon Da yayi mata Kafin kuma ya saketa lokaci Daya yana kallonta yadda Hawayenta ke Zuba Shima kukan Zuccin yake Domin Idanuwansa sun kala Sun Jajir kamar gawarshin Wuta.
Chapter 68 · 0% Book details