← Book details Zainazain Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 78

Sashe 33

Zainazain Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zakiya ta Murmusa kafin Tace"ni Sunana Zakiya Nuhu Daga Jahar kano.."Tafada tana kallon Dina Wacce take nacin kallon Zain Shi kuma yaki kallonta Cikin Sadda kai Tace"Dina Gaddafi Sheerif Nima Daga Kano.."Alhaji Tsoho ya kalleta Sosai bama Shi kadai ba Hatta su Baban kaduna sai da suka Dago Suna kallonta kafin Alhaji Tsoho ya samu Zarafin mgana Baban Kaduna yace"Gaddafi Sheerif Dai da muka sani kwamishinan kudi na Jahar kano.."
Haddir ne ya gyada kai yana Fadin"Shifa Baba..Diyarsa ce.."Baban kaduna da Daddyn Abuja suka Hada baki wajen Fadin "Ikon Allah.."Shiko Alhaji Tsoho Mirmishi yayi yana Fadin"Masha Allah..Sannunki naji Dadin yadda kika Dogara ga kanki ba wa mukamin Babanki ba kika Tsaya kikayi karatu Domin Taimakon Al"ummah Allah yayi albarka.."Kansu na kasa Suna amsawa Da Ameen Alhaji Tsoho ya sake kallon Dina yana Fadin"Ammh yata Baki da wani Suna ne..?

Naji kince Sunanki Dina kuma a sanina Sunan Kiristoci ne wannan Sunan domin in bazan manta akwai wata wacce mukayi aiki da ita a asibitin Dana Fara aiki a Bongcuf,Itama Likitar kwakwalwa ce Sunanta Dr Dina itama.."Dariya ta kama su Umma da Inna Hannatu Hajiya Mama tayi karaf tace"Yo in ban da Abunka Alhaji Yanzu yandda zamanin nan ya lalace Sunan ma Da zakaji an saka bashi da wani Ma"ana ayi ta kwaikwayon Arna wajen saka Sunaye Allah dai ya kyauta kawai.."Haddir da Alhaji Tsoho Suka ce Ameen Dina kuwa sai Taji ta Muzanta Kallonsu Alhaji Tsoho yayi yana Fadin"Nagode kwarai Allah yayi albarka..!

Zakiya ta Rankwafa Tana Fadin"Allah kara lafiya da Nisan kwana.."su Inna Hannatu suka amsa da Ameen Ameen juyawa sukayi suna ma su Nene sallama Mama Safiya ce kadai ta amsa Mom Ikilima kallon TaraSaura kwata tayi musu Tana Fadin"Kai Nene wadanan yan mata basu da kamun kai kalli Shigarsu.."Nene ta Tabe baki Tana Binsu da wani kallo Haka Kurum Taji basu Burgeta ba,Suna Gabda Fita Daga Dakin aka Turo Kofa aka Shigo Zainab ce kan gaba ita da Maryama Din Inna Hannatu,Dauke da manyan Kololi a Hannunsu,Sai Zafeera da Zaina da suka Shigo Daga Baya Zafeera na Rike da Filet da cokali ita kuma Zaina na Rike da Katon Jug,Dukkansu basu ma Lura dasu ba Zafeera har Tana bangazan kafadan Zakiya kuma ko ta waigo Saboda Hankalinta ya tafi kan iyayenta Dake Dakin ne,Zakiya ta Juyo Tana kare ma Zafeera kallo Cikin baki isa ba ita kuma Dina Zaina ta kura ma ido ganin ta ta kara Kiba da Haske Alhaji Tsoho ne ke ta Fadin"Maraba da Amaryata Halimatu Sa'adiya mai Hali Dubu...Maraba da Zafeeratu Farar mace alkyabban Mata maraba da Zainabu Abu mai Tagwayen Suna Maraba da Maryama Allahu Akbar Allah yasa Ki yi koyi da Hali Irin Maryama Uwar Rikon Haddir da Zanullahi da Zareena uwa Shakikaya wajen Halimatu Sa"adiya Allah ya mata Rahma Ita da Abdullahi Da Mallam Umaru da Atine Allah ya Hadamu a Aljannah Firdausi.."Ya karishe Fada Cikin Alhini Duka Dakin suka Hada baki Wajem Fadin "Ameen Ameen ya Allah...Allah ya Haskaka kabarinsu.!

Gaban su Umma suka yada Kololin Gabansu suna gaida Iyayen Nasu Daddyn Abuja ne yace"Sa"adiya me kika Dafo ma Tsohon naki ne?ya fada yana kallon zaina dama Sa"adiya yake Kiranta da Shi,Baban Kaduna ne kan kirata Halimatu su Mom Iklima kuma Dukkansu Zaina ne,Tana Dariya Tace"La..Daddy Tuwon Semo nayi muku miyar Kubewa Bushashiya Dukkanku Domin nasan Duka iyayen nawa sun yi Gado Wajen Tsohon nan na kwance.."Ta karishe Fada Tana Dariya Suma Dariyan Suka saka Mama Safiya tace"kwarai..Duka gidajenmu Gidan Daura Tuwo ne..Allah dai ya karama Alhaji Tsoho Lafiya..!

Suka amsa da Ameen gabadaya Alhaji Tsoho yace"Dama ai kyan ya"ya su gaji Tsohonsu...Kunga wannan Tuwon Shi ke kara Muku Lafiya da karfin gani ba Ciyen Ciyen kayan Turawan nan ba.."Zain yace."Hakane Tsoho...Ina mamakin zamowarka Likitan kwakwalwa Ba Likitan Sanin Mutum har hanji ba.."Dariya suka sakamai Gabadaya kafin Hajiya Mama tace"Ke ta kwacen Miji zuboma mijina Tuwon yaci yasha mgani Tun Dazu yaki cin komai yana Jiranki.."Tafada Tana Hararanta Dariya kawai tayi ta Duka ta Fara zubamai Tuwon Zafeera na Tayata Zain na Daga gefe ya Dago kansa yana Fadin"Kinga Firstlove Da kin Sakama Tsohon nan Zubomin Ina jin yunwa.."Haddir ya kallesa yana Fadin"Lalle ne ma.Su Abban fa..?

Harara ya Zabgamai zai yi mgana kenan suka Hada ido Da Dina Dake tsaye har yanzu basu Tafi ba Ido yazaro yana kallonta ganin Haka yasa Zakiya Taja Hannun Dina suka Fice su kansu basu san meya Tsaidasu ba ammh Ahalin na Gidan Saulawa Abun kallo ne Suna Da Fahimta Da kuma Kaunar Juna basu samu Zarafin mgana ba sai da suka Dangana da Office din Dina Zakiya kafin ta zauna sai da taKwankwadi Ruwa kana ta koma tazauna Tana maida Numfashi Dina kuma Takaichi ne Fal acikin Ranta da kuma Kishin Zaina Daya yi mata katutu.

Dina kuwa zama Tayi kan kujeran Dake kallon na Zakiya Tana Fadin"Tsohon nan ya Cika Tambaye Tambayen Tsiya..'Zakiya tayi Mirmishi Tana Fadin"Likitan kwakwalwa ne fa...Tsohon Daga gani Lokacin Da yake kan ganiyar kuruciyarsa anyi Jajirtattace.."Ta karishe Fada Tana yar Dariya kafin ta Dora da Fadin"Baki mamakin yadda Shekarunsa sukaja Haka ba ammh kallesa Hutu da Jin Dadi Sun Boye tsufansa..?

Dina Ta Tabe baki Tana Fadin"Ke ni bama Wannan ba..Wai kiji fa Cemin yayi Sunana irin na Kiristoci ne..?

Da gaske ne sunana ba na Musulmai bane.'?

Ta fada Tana kallon Zakiya Ido Cikin Ido Wacce ta saka Dariya Tana Fadin"ina zan sani.?

Ammh Tunda kikaji ya Fada gaskiya ne..Sai kiyi Hakuri Tunda Babanki ya Riga Da ya saka miiki baki da yarda zakiyi kuma..!

Baki Dina Ta Bude Tana Fadin"Bangane ba.?

Zakiya Tace"dama ai bazaki gane ba....Ke wai wata yarinyan ce ta Bangajeni Da zata Shigo Din nan.?

Baki Dina Ta Tabe Tana Fadin"Ina zamnsanta..Banga Fuskarta ba
Matarsa kadai na iya Ganewa Sai Haddir sai Shi kanshi zain din gabadaya Cikin Dakin Banda su ban son kowa ba..!

Zakiya tace"Soon zaki sansu Kawata...Nadai san na kan gadon nan Kakanininsu ne,Sai kuma Mazan Dake gefe sukuma iyayansu ne,Kin manta an gayamana Ya"yansa Biyar uku Maza Biyu mata,Kana ina kyautata zaton bayan Matan ya"yansa akwai ya"yansa mata Biyu a wajen."Dina tayi Tagumi Tana Fadin"Hmmm..Kina Nufin Harda iyayen Zain awajen..!?

Zakiya tace"eh mana Surukan ki na Wajen..Kilama sune Wadanda da zamu Tafi mukayi musu Sallama sukabi da kallon Wulakanci.."Dina ta waro Ido Tana Fadin"Topha..Kada fa hakan ya bata mana Shiri fa..?

Mikewa Zakiya Tayi Tana Rataya Jakarta Lokaci Daya Tana Fadin"Basu isa ba....Ki kwantar da Hankali Wlh bazan Taba Natsuwa ba sai naga wannan aikin namu ya tafi Sussufull ba wata matsala.."Dina ta sakar mata ido kafin tace"Kin Tabbata..?

Taku Zakiya ta Farayi gabanta Lokaci Daya Tana Dafa Kafadarta Tana Fadin"Kin manta da kudinki kika Biyamin nayi Rigisteration na Shiga Jami"a Lokacin da Babana ya nuna Aurar Dani zai yi..?ni kuma nace karatu zanyi na Tssayu ga Kafafuna..?

Ko kin manta Kina London kin Sha Turomin da kudin Abinci Dana Makaranta Har sai da na Shiga Aji Uku na Fara Raba ma maza Jikina Suna Bani kudi..?

Ta fada Tana kallon Dinar wacce tayi Mirmishi Tana Fadin"Ni na manta...Bakuma nasan kina Tuna Baya.."Dariya Zakiya Tayi Tana Fadin"Zaki iya mantawa ammh ni bazan Taba Manta wannan Alherin naki gareni ba Dina..Shiyasa nayi Miki alkawarin bazan Runtsa ba sai naga Kin mallaki Zain kamar yadda kike Buri..!

Ke baki Hango Yadda Fuskokin wasu zai sauya Daga Farinciki Zuwa Bakin Ciki ba..?

Na Tabbata zasu Girgiza in sukaji labarin Abunda Dansu mafi Soyuwa garesu yake aikatawa Wlh inda ace Nasan inda zan samo Wasu Daga Cikin yanmatan Dayayi Hulda Dasu Har dasu zamu Saka Cikin plan din mu sai dai Kash..Bai yarda yayi Hulda da Ira iranmu bane Shiyasa Daya gane baida wayau..'
Dina ta Saki Numfashi Tana Fadin"Na samu Natsuwa yanzu..Yaushe plan dinmu zai Tabbata kuma Wa zamu Fara.

Tunkara.?

Zakiya tace"Karki Damu...Komai na Tsarashi Daki Daki zan zo Gidanki Da Daddare akwai aikin da zan sakaki kiyi mana Shima yana Daga Cikin plan dinmu...Ni na Wuce sai nazo.."Da kai Dina ta amsa Kafin Tace"Shikenan sai mun Hadu.'Juyawa kawai Zakiya tayi ta Fice Daga Office din Tana wani Takun Daya Bayan Daya Dina ta Bita da kallon Tabbatar da mganarta.

Bangaran Su Zain kuwa Duka nan suka wuni Cikin asibitin sai Dare kana suka Watse Hajiya Mama aka bari da Haddir zasu kwana da Alhaji Tsoho,Inna Hamnatu da Inna Rukayyah da su Baban Kaduna da Matansu Gidan Alhaji Tsoho suka yada Zango Daman nan suke sauka Iyalan Abba kuma suka Wuce Gida Zaina kuma da Zain suka ce Gidansu sai da safe kana suka Dawo yau ma Zaina ta Dafo Abinci Farar Shinkafa da Miyar Ganye mai Kifi,da aranar Alhaji Tsoho ya matsa zai koma gida Dakyar su Abba suka Lallabashi ya kara kwana Tun Safe kuma yace sai Gida Dole aka bashi Sallama suka Tattara Zuwa Gida Tunda yaji Sauki Muran ma Tayi Sauki Ta Sakeshi.

Washegari Kuma Inna Rukayyah Ta koma ita da Zafeera Inna Hannatu dai sai da ta kara kwana ta Jira Megidanta yazo ya Duba Jikin Alhaji Tsoho suka koma Tare nan dai suka bar Maryama Gidan Abba Tunda Sa"anin suke da Zainab itama sai wannan Shekarar zata Shiga Jami"a suma su Baban kaduna Duk Aranar suka koma Gidajensu su da iyalansu ganin Jikin na Alhaji Tsoho yaji Sauki kuma ga Zain da Haddir suna Kokaron Kula dashi Shi da kanshi ma yace Kowannensu ya Dauki Iyalansa ya koma Bakin aikinsa Shi ya samu Lafiya da wannan suka samu Natsuwan Tafiya su ma Su Nene sai Ranar suka samu Natsuwa agida.
********
*Bayan wata Biyu..*
Bayan Wata Biyu da kwanaki Tuni Zaina sun Dade da Komawa makaranta sun Fara karatu ba kama Hannun yaro Tunda yanzu Suna aji Biyu ne,Zafeera ma Tana kano Tana Cigaba da Karatunta sai dai suna Waya Lokaci bayan Lokaci da Zainar.
Chapter 33 · 0% Book details