← Book details Zainazain Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 78

Sashe 40

Zainazain Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Suna Zuwa suka iske Har Inna Hannatun tasauka sai Fada take tana Fadin Tana Kiran wayar Haddir bai Daga ba Haka ma Zain,Saboda Tana Fadan ne yasa Bata Fahimci basa cikin Natsuwarsu ba har gwara ma Haddir ya Tattaro Natsuwar Zain kuwa Zaro ido kawai yake yana kifta idanuwa Jira kawai yake ace kyf ya zura da Gudu.

Gidan Alhaji Tsoho suka kaita Suna Shirin kara Zillewa tace sai sun Shigar mata da kaya Domin kaf a Ya"yan Alhaji Tsoho da ita da Baban kaduna ne mafadata,Suna Shiga Zain yaci karo da Zainarsa Cike da mamaki take kallonsa tana Tambayansa bai Tafi Gomben bane..?

Ganin Baya Cikin Natsuwarsa ne yasa Haddir ya Bata amsa da bai samu Tafiyar ba Abun ya bata mamaki ganin Firstlove baya ma iya Hada ido Da ita kamar Alhaji Tsoho ya sann Suna Cikin Uzurin son Tafiya ya Hanasu ya Zaunar dasu yana gaya musu Gobe akwai Taron Family Duka iyayan nasu suna Tafe Inna Rukayyah ma Tana Tafe Daga kano Haka ma Baban kaduna da Mom Iklima Da Daddyn Abuja da Mama Safiya Da Hamdiya zasu zauna kan mganar Auran Hamdiyan daya Taso watan Gobe ne,Zain bai kara Jin Sagewar Gwiwa ba sai da yaga Sadiq babba ya shigo nan yake gaishesu tare da Shaida musu Dazu shima ya Shigo garin yazo gida yayi Hutun Sati Biyu ya koma Alhaji Tsoho nata Murna ganin Jikansa Haddir da zain sai dai suka kalli Juna kawai Kowa da Abunda yake sakawa Sai da Alhaji Tsoho ya gama Jawabinsa kana ya barsu suka Fita suna Fita basu koma ko"ina ba sai Cikin asibitin Office din Haddir din suka sake komawa Suna Kulla yadda zasu Bulloma wannan al"amarin Dake Tunkaransu Dirshan zain ya zauna yana kukan Haddir ya Taimakamai kada Asirinsa ya Tuni Ya bashi Tsausayi matuka kuma Har ga Allah baya Fatan wannan mganar ta fasu a kunnuwan iyayensu ko bakomai ya zama Silan Rufama Dan"uwansa asiri.
****
Dina kuwa Da Fara Nadaman Biye ma Shawaran Zakiya Domin
Lokacin da Kwamishina ya Dawo Gida yaci karo da wannan Labarin sai da ya Kusa Fadi haka ya Zube gaban gadon Dina yana Jijjigata yana Fadin"Dina..?me kika nema kika Raasa..?

Wani irin gata ne ban baki ba..?

Wata irin Soyayya Uba ce ban baki ba..?

Harda ta uwa na Baki Dina na Hana Dangin mahaifiyarki Daukanki Saboda ina sonki Ina son na baki Dukkan gatan Duniya..?

Yanzu da Kanwar mahaifiyarki Maimunatu zata Zo sati mai zuwa Da wani baki zan mata wannan bayanin..?

Na baki ilimi Na ingantan Rayuwarki saboda kada kice na zama mai Takura gareki ashe wannan sakewar har yakai ki kwasomin wannan Abun kunyar dina.?

Nifa Dan Siyasa ne da wani ido kuke so na kalli mutane in wannan mganar ta Fita waje..?

Ya karishe Fada Cikin zubar Hawaye Ita kanta Dinar kukan take Hajiya Batula ma sai da ta Share kwallah Zakiya ce kadai batayi kuka ba Cikin kuka Take Fadin"Kayi Hakuri Daddy..Plz Forgive me.Ba laifina bane Wlh Yaudarata yayi da Kalmar zai Aure ni ya lalatamin Rayuwa Shine kuma Daga baya yace sai dai azubar da Cikin bazai Aureni ba Shine na Gudo Gida.."
Ta fada Cikin gunjin kuka Gefe Daya na Zuciyarta Tayi Rauni ganin Daddynta nakuka Hajiya Batula tace"Dama wani Namijin arziki ne zai yi Lalata da mace kuma ya aureta..?

Ai Shima macen kwarai yake nema kinyi Kuskure Dina.."Kwamishina ya mike Tsaye yana Share Hawayensa ya kalli Zakiya yana Fadin"Wani asibiti kika kaita Kafin kuzo nan..?

Cikin Ladabi Ta saka Hannu Cikin Jakarta Ta Dauko Farar Takarda Ta mikamai Tana Fadin"Asibitin Da take aiki ne Daddy....Gama sakamakon awajena.."Karba yayi ya Duba na wani Lokaci kafin ya Hada da wanda Dr.Bala ya Bada ya Tusa Cikin aljihunsa yana Fadin"Taga yamiki wanda yayi mata wannan Zaluncin..?

Cikin Makirci Zakiya tace"Nayi nayi da ita Taki gayamin Daddy.."Tafada kanta na kasa Cikin Tsawa Kwamishina ya Kalli Dina ya Daka mata tsawa yana Fadin"Kimin Shuru anan wajen ki Fadamin wanda yayi miki wannan Abun kunyar..?

Tsorata Tayi Tafara ja da baya zuwa Wajen zakiya Ita kuma Zakiya Fadi Take"Dina ki Fadama Daddy ko waye..Na Tabbata zai kwato miki yancinki na Zalunci da yaudaranki da yayi da kalmar zai Aureki yayi Miki Ciki kuma yake neman ya sake Jefaki ga Halaka.."Tafada Har tana matso kwallah Jin Haka yasa ta Fara Shesshekan kuka Tana Fadin"Likitan ne asibitin Dana ke aiki..!

Kwamishina yace"Waye sunansa..?

Waye kuma Ubansa a kasar nan..?

Kan Dina na kasa tace"Sunansa DR ZAINULLAHI USMAN ABUBAKAR SAULAWA...!

Tafada tana Rufe bakinta Waro Ido Zakiya tayi Tana Fadin"La Dr.Zain kike nufi..?Kai Dina ta Daga mata sai ta Fara Tafa Hannu Hajiya Batula tace"Kinsan shi ne..?

Kodai wannan Saurayin da Dina take matukar so ne..?

Da sauri Zakiya tace"Shine Wlh Anty...Tun suna London suke Soyayyah Tunda makaranta Daya Sukayi nasha cema Dina Ta Rabu Dashi ba Auranta zai yi ba sai tace Yace zai Aureta asibitin ma Datake aiki shi ya bata aikin fa asibitin mallakin Kakansa ne Dr Saulawa dake Garin Bauchi..'
Hajiya Batula tace"Nifa banga laifinsa ba laifinta ne..Don Namiji yayi ma mace alkawarin Aure sai akace ta bashi Jikinta yayi yarda yaga Dama..?kwamishina ya Dago yana kallon Hajiya Batula kafin yace"Batula koma Miye Bai isa yaci Bulus ba...Na yarda Dina nada laifi Shima yana Dashi Saboda Haka Tunda ya Riga ya bari Haka Ta Faru..Wlh Tallahi ko Zan rasa Mikamina sai na kwatan mata yanci..Ke Zakiya kunsan gidan yaron..?

Da Sauri Zakiya tace"Eh Daddy ai gidansu ba Boyayyen Gida bane agarin Bauchi kakansa Dr.Abubakar Saulawa yayi suna sosai.."Kai tsaye ya kada kai yana Fadin"Ku Shirya gobe daSafe zamu tafi Chan Bauchi zan je na gaya musu Abunda D'ansu yayi ma yata in ma basu sani ba gobe zasu sani..Batula kema ki Shirya dake zamu tafi sai Excort dina guda Biyu saboda Sirri yau ma Domin Anjima ina da ganawa da gwamma ne da a Daran nan zamu Tafi garin Bauchin..'
Yana gama Fadar haka ya Fice Daga Dakin Kamar zai Tashi sama Hajiya Batula ta mara mai baya Suna Fita zakiya tatashi ta Rufe Kofar tazo ta Rumgume Dina Tana Fadin"Ina Tayaki Murna kin kusa samun Cikar Burunki..!.

Wata Dariyan Farinciki Da Nishadi Dina tayi kafin tace"Da farko na Karaya..Ammh yanzu naji Kamshin na zami matar Zain..ammh kuma wani Fargaban Zakiya Shegiyar Firstlove din nan nashi zata yardada mganganunmu kuwa balle har ta Rabu Dashi..?

Ta fada Tana kallon zakiya wacce ta Mike tana gyara zaman mayafin Kanta Lokaci Daya Tana Fadin"Karki damu da ita Tuni nagama da ita..Zatazama Comfuse mana Na wanda ka yarda dashi Fiye da kowa aduniya yaci Amanarka..Ammh Zan aika mata da Abunda Dole zata nemi karin bayani ni kuma zan gayyato inda zata ji gaskiyan komai kinga Daga Lokacin Zata ji Zain din yagama Fita Daga kanta Indai ita macece wacce ta amsa Sunanta..."
Dina tace"Bangane Nufinki ba..?

Zakiya ta Dauki Jakarta Tana Fadin"Ai Ba zasu zo Taji wannan mganar ba..Zasu yi Kokarin Rufa mganar kada Taji..Ammh ni zan gayyatota har zuwa Gidan kakan nasu da suke ji Dashi nayi Miki alkawarin aagaban Idonta zamu Fallasa Komai...Kin manta kin samo min Lambarta Awayar zain..?Hade kuma da aikin da na sakaki..?

Kai Dina ta Daga mata Cike da mamaki Dariyan Mugunta Zakiya ta saki Tana Fadin"Ai Duka Shirin nata ne..Domin Ba lalle bane in wanchan Bomb din ya Fashe ba"a gabanta ba Mganar Daga bakin wasu Tayi mata Tasiri..Zata yi Tasiri ne Daga bakinki Da kuma Shaidunmu.."hannu kawai Dina ta Bata suka Tafa Tana Fadin"Aikin SS ya dace Dake Zakiya ba aikim kamfanin Sardawa ta Layi ba..".

Dariya kawai Zakiya tayi mata kafin tace"Zan tafi Gida na kwana Dina..Saboda kinsan komai lalacewar gida gidanku ne kuma Tunda Tsoho nada Rai Bari na Leka Duk da wanchan Watan na Lekosu.."Dina ta kada kai Tana Fadin"Da safe kenan zaki Dawo..?

Zakiya tace"Da yardan Allah.."Sallama sukayi Kana Zakiya ta Fice Koda ta sauka Kasa bata ga kowa kawai sai ta Fice Daga Gidan Security suna ganinta suka Bude mata get ta Fice Da Motarta Motar Dina kuma Tana kano Gidan Wata kawarta Teema suka kai Motar Dina Ajiya Tun Jiya Saboda kada Barinta ya bata musu plan dinsu.
*Janafty...*
*ZAINAZAIN..!*
_(Is a love Story and Betrayal)_
*Wattpad:Jamilaumar351*
*Mallakar:Janaftyshakira*
*BOOK 1*
"Zakiya iyayenta suna zaune a anguwar gadon kaya ne,Mahaifinta Mallam Nuhu Talaka ne mai Rufin asiri Tunda Sana"ar Dinkin Surfani na Hannu yake Da Saida Zaren Dinkin kala kala Tun yana da Samartkansa.

Shago garesa a kofar gidansa Inda yake gudanar da Sana"arsa,Bayan Rasuwar Mahaifiyar Zakiya Adama Ya kara Auran Wata Samira yar garin Danbatta ne,Bayan ita ma ya kara Auran wata Lubabatu suna Kiranta Luba ita yar nan garin Kano ne, a kofar wambai.

Mahaifiyar Zakiya yar asalin Kauyen Minjibir Dake kano ne,iyayenta ma ba masu Hali bane Kuma Dukkansu yan kauye ne Shiyasa bayan Rasuwarta da Mallam Nuhu ya hanasu Su Dauki Zakiya su maidata chan Minjibir din sai sukayi Fushi suka Fita Batun Zakiyar basu kara waiwayarta ba itama bata Damu ba Tunda ba wani Abun hannu garesu ba Uwa uba kuma Tana ganin ci baya ne ta koma Kauye da Zama.

Sai ta tashi Hannun Kishiyar Uwa Samira irin mugayen Matanan nan ne da basu Dauki Ya"yan Kishiya ya"ya ba Dalilin ta shi yasa Zakiya ta Fara kangarewa,Da kuma Shigarta prine Collage da Haduwarta Da Dina lokacin Mallam Nuhu na Zamaninsa da Dinkin Surfani Shiyasa Zakiya tafi Sauran ya"yansa samun Ingancin Rayuwa mai kyau.
Chapter 40 · 0% Book details