← Book details Zainazain Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 78

Sashe 27

Zainazain Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Umma Ta kalleshi Tana Fadin"A" a Tare Da ya'yana zan Tafi...Ta kano zamu Tashi Zuwa Lagos Zafeera nachan na Jiranmu."Mamaki ya kama zain kawai sai ya Fara Tura baki yana Fadin"Nifa Umma ban amince Tatafi yau ba gaskiya.."Umma bata kulashi ba Ta kalli Nene Tana Fadin"Nene Gayama D'anki Da yata zan Tafi Yaji da wai ma.."Daga Haka Tayi Shigewar Daki Ta barsu nan Nene ta Lallabashi ya yarda,Dole ya Kira Zaina yace ta Shirya zata Bi Umma Ta Fara Murna tana Tsalle Ta Fara Shirya kayanta ta Kira Laila ta gayamata Ta kuma ce ta Dinga saka mata Atendence kafin ta Dawo Da haka sukayi Sallama,Saboda Zumudi Ko Ta Jira Zain din ya Dawo batayi ba ta Hado kayanta zuwa Gida,Sai da tazo Taji Labarin Harda Zafira zasu Tafi ta fara Murna Nene da Umma na Musu Dariya Zain yana asibiti Halima ta Kirashi kan zasu Tafi Suna Gidan Alhaji Tsoho baro asibitin yayi yazo Sukayi sallama Daga Halima sai Umma Direba ya Tafi Dasu kano,Wajen La"asar suka isa,Salloli kawai sukayi suka Nufi Airport Dama sun ci Sa"a sun samu Jirgin Azman wanda zai yada Zango a Birnin Ikko Suka Shiga Bayan Inna Rukayyah ta Rakasu har Airport din Tana musu Fatan Dawowa lafiya Domin bazata samu zuwa ba Inna Hannatu ce Zata tafi.

Jirginsu ya yada Zango A Murtala Muhammed International Airport Dake Birnin Ikko,da Misalin 7pm na yammah Direban Gidansu Inna Hannatu yazo ya Daukesu Zuwa Gidanta Dake Victoria island,Nan sukaci Abinci sukayi Sallah Ba zencen zama Domin Jirgin Karfe 11:30pm na Dare zasu bi Zuwa U.s Babban Birnin America.

Koda 11pm Tayi a Airport Tayi Musu Daman Mijin Inna Hannatun ya Riga yayi musu Bucking Tunda Tafiyar Harda Ita Lokaci nayi kuwa Jirginsu ya Daga Basu isa ba sai Washegari da Hantsi Dama Tun Suna Lagos Sunyi waya Da Zareena sun gayamata Lokacin Hawan Jirginsu ita kuma sai ta Kin Taci Lokacin Saukarsu Suna Sauka suka ga Jawaad da Dansa Jalal Sunzo Daukansu a Filin Jirgin nan suka Rankaya sai Jerin Estate din da Ma"akatarsu su Jawaad ta basu Umma ce kadai Ta Taba Zuwa Lokacin Da Zata maida Zareenar Bayan Jawaad din ya kawota Gida Ta Haifi Jalal Lokacin ya samu Hutun Karshen Shekara ne sai suka Tattaro Gabadayansu Zuwa Mahaifarsu Sai bayan Ta Haihu Tayi Arba"in kana suka Dawo Da Rakiyar Umma da na Mama Safiya Matar Dadyn Abuja,Tunda Daman Tun Dawowarsu kasar ba wanda ya Taba Zuwar mata sai wannan Zuwan Wanda Bakin Zareena yaki Rufuwa Saboda Murnan ganin Ahalinta.
*Janafty...*
*ZAINAZAIN..!*
_(Is a love Story and Betrayal)_
*Wattpad:Jamilaumar351*
*Mallakar:Janaftyshakira*
*BOOK 1*
"Sai da su Halima suka kwashe Wajen kwana Goma a kasar ta U.S kafin su Dawo,Kwanansu Hudu da zuwa akayi Suna Yarinya taci Sunan Umma Wato Fatima,Suna Kiranta little Umma Washegarin Suna sai ga Baban Kaduna da Mom Ikilima Sun Biyo Sun ga Zareena da Bby kwana Daya sukayi suka Wuce Cyprus Wajen Sadiq karami Chan Yake Degree dinsa Yana Shekara ta uku achan.

Tafiyar Halima Ta saka Dina Tayi amfani Da Wannan damar Kusanci ya kara Shiga Tsakaninta da Zain wanda take iya bakin kokarinta Koda yaushe suna tare acikin asibiti ne gidanta ne,Ita take Dauke mai Kishiruwan Zainarsa,Duk da baya Jin Dadin Hakan dayake yi Ammh kuma bashi da wani Zabi,Haddir kuwa Ransa ba karamin kuna yake ba in yaga Zain da Dina suna Tare Saboda ya sani Shedaniya ce Kuma bawai ya yarda da kalaman Zain Din bane bama Shi kadai ba Mutane Da Dama suna Dora musu Zargi,Ganin Abun nasu yayi yawa ne yasa ya yanke Shawaran zai yi ma Zain din mgana Tunda yanzu har Fita Suna Tare da Dinar Wani Lokacin da Motarta wani Lokacin da Motarsa Cin Abinci kuma Tun Farkon Tafiyarsu Umma yake zuwa Wajen Nene yana Ci ammh yanzu sai dai Dina Ta jashi Zuwa Waje Su je chan suci Abinci ko kuma ta Jashi Gidanta Su je chan suyi Watsewarsu in Sun gama ta Sulala musu Ko Indomie ne Suci Su Dawo Cikin asibiti Abubuwa dai gasunan ba Tsari Wanda Haddir din yake Tsoron Faruwar waani abu.

Ranar sun Dawo Daga Resutarant Cin Abinci Bayan sun Faka Motarsu a parking Space,Sun Fito Motar Dina ce ita ke Driving Din Motar Dukkansu Sun Fito Suna Dariya Fuskarsu na Bayyanar da Annurin Da Suke Ciko karo Suka ci Da Haddir ya Fito Daga Cikin asibitin zai Fita da kallon Mamaki ya Bisu Dashi Daga Zain Din Har Dina,Zain kuma kallon kallo Sukama Juna kafin Zain din ya kauda kai Dina kuwa Data gaida Haddir Kin amsata yayi sai ma kallon Tsana Daya watsa mata yana kallon Zain Lokaci Daya Yana Fadin"Zain ina son mgana Dakai..!

Yafada Cikin Kakkausan Murya Juyowa Zain yayi yana kallonsa Kafin ya kada kai ya kalli Dina yana Fadin"Shiga ciki gani nan Tafe.."Daga haka ya Juya ya Bi bayan Haddir wanda ya karisa Wajen Motarsa yana Bin Dina da wani kallon Tara saura kwata Ita kuma kai kawai ta gyada kafin ta wuce zuwa Cikin asibitin Tana wani Takun Isa.

Zain na karisowa Kusa da Haddir ya karkace Kai yana Fadin"gani Lafiya ka ke son ganina..?

Ido Cikin Ido Haddir yace'"Meka yi kenan Zain..?

Kasan Ma"nar haka kuwa..?

Gyara Tsayuwa Zain yayi yana Fadin"Me kenan..?bangane inda ka Dosa ba Mallam.."Haddir ya Murmusa yana Fadin"Karka Raina ma kanka Hankali Zain..Kagane inda na Dosa ina mgana ne kan Wanchan yarinyar Dina,miye yake Hadaka Da ita..?

Muharamanka ce..?na lura dakai kwana Biyun nan kun wani kulle ne wanda kuma Nake zargin Ba ta alheri bace..!

Zain ya wani Cije baki kafin ya fara mgana"Bangane Kaga mun kulle ba..?wannan wata irin mgana ce Karfa ka manta Dina Bayan Abokiyar aikina Abokiyar karatuna ce kuma Kawata ce akwai illah ne Don kaganmu Tare..?

Kuma wani irin Ba alheri bane kake Fadi Me kake son Fadi...?

Kai Tsaye Haddir yace"Kafini sani..Ina Zargin kun koma Ruwa Kaida Ita kuma Faruwar hakan kamar Barazana ne ga Zubewar mutumcinmu Da naka gabadaya.."Da sauri Zain ya Tareshi Yana Fadin"Tsaya mallam kasan kuwa Zaton Zina... ?

Ko kutu akaje Sai ka kawo Sheda Hudu suma sai sun ganin ma Idanuwansu Turmi da Tabarya kana da wannan Shedar ne..?Mganarka kawai kake wanda kuma Ra"ayinka ka Fada mallam Ni babu komai Tsakanina da ita sai na abokiyar aikina ce Fakat.."
Ya karishe Fada Cikin Son Nuna Bakomai Haddir yace"Hmm koma miye kai ka sani Nidai ina Fadamaka nan ba London bane Bauchi ne Wlh Zain ina Jiye maka wani Tsoro ka dawo Cikin Hayyacinka Nidai nagaya maka Tuni nace ka sallami yarinyar nan Ta kama gabanta Ammh kaki In banda kana da Manufa miye na gayyato ta nan Tayi aiki Damu..?

In gaya maka ina jiye maka Mtsala Ne..'
Karamin Tsaki Zain yaja yana Fadin"Zato Zunubi Dai koda ya kasance Gaskiya ne..Kuma Hadisi ne guda Ka Rika kyautatama Dan"uwanka Musulmi Zato.."Daga haka ya wuce Ya bar Haddir nan Tsaye yana Binsa da kallon Tsausayi kuma Har acikin Ransa ya yarda da Zarginsa akan Zain ganin yadda yayi wani Wiki Wiki Dashi kada kai kawai yayi ya Bude Murfin Motansa ya Shiga acikin Ransa yana yima Zain Fatan Shiriya
Zain kuwa har ya isa Office dinsa yana Juya Mganar Haddir Tabbas yasan gaskiya yake Fadamai ammh Taya zai iya yakice Dina..?

Yayi iya bakin Kokarinsa wajen ganin ta bar Rayuwarsa ammh Abu ya gagara Shi kanshi yana Tsoron Wani abu ya Faru ya Tabbata Cikin Ahalinsa ba wanda zai mai Uzuri uwa uba kuma Zainarsa da wani ido zai Kalleta..?

Haka ya wuni Sukuku kamar mara lafiya La"asar ya bar Cikin asibitin zuwa Gida Yaje yayi wanka ya kwanta yana ganin Kiran Dina yaki Dagawa sai ma ya Lalubi Zareena yace ta bama Umma wayar,bayan an bata sun gaisa ya Fara Complain din cewa Matarsa yaushe zata Dawo Umma tace suna Tafe Dole ya Hakura ya maida Wukar ammh Shi kanshi yasan yana Bukatar Matarsa ta Dawo Hakan nan Tunda Sukayi aure Bai Taba bari Taje wani Waje ta kwana Fiye da Biyu ba Shiyasa yake Jinsa Wani Iri.

Ranar asabar su Umma suka Dawo Ta lagos suka Sauka nan Suka kara kwana Washegari Umma da Halima suka Bi Jirgi zuwa Bauchi Ita kuma Zafeera ta Hau Jirgi zuwa kano Taso Binsu Umma zuwa Bauchi Gabatowar Test dinsu yasa ta hakura ta koma kano sai sun samu Hutu,Zain bai ma san Ranar zasu dawo ba sai da ya Dawo Daga asibiti yaji Gida na Tashin kamshi,sai ga Zainarsa tazo ta Rumgumeshi Tana Murnan ganinsa Shima kamkameta yayi Yana Bayyana mata yadda yayi kewarta Ranar dai kwana sukayi Suna Bayyana ma Juna yadda Sukayi kewar Juna.

Washegari kuma Monday ta koma makaranta Ranar kuma suka Fara Test ba zama Sai Hankalinta Duk ya koma kan karatunta Tunda Suna Tun karar Exams Din Second Semister ne,Don ma Allah ya Taimaketa Laila tayi mata Wasu Assigment din Da Data samu Gibi da yawa ba kadan ba.
*****
Sannu Sannu bata Hana zuwa sai dai adade ba"a je ba Gashi Har Su Halima Sun kamallah Test dinsu na makranta Haka ma Su Zafeera,Shiryen Shiryen Fara Jarabawa suke yi nan da Sati Daya Gabadaya Hankalin Halima ya koma kan Makaranta da karatu bata ma samun Lokacin kanta hatta Gidan Umma da Gidan Alhaji tsoho Sai Ranar Sati Take samun Zuwa Saboda karatun Jarabawa bata da wata Natsuwa.
Chapter 27 · 0% Book details