← Book details Zainazain Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 78

Sashe 48

Zainazain Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya Dau Tsawon Lokaci Cikin Masallacin kafin ya Mike ya Fita Mota ya Shiga ya Tadata Rasa Wajen zuwa yasa yayi Tunanin zuwa Cikin asibiti Sai kuma yayi Tunanin Kila suma Labari yaje musu yanzu baida wata Sauran Kima Dole yasa ya Maida akalan Motan nashi Zuwa Gidansu dake Lowcost.
*****
Bangaran su Kwamishina kuwa Suna Fita Zakiya Daman bata koma Kano ba Gidanta ta wuce saboda Zata koma bakin aiki Daganan Tayi musu sallama ta Hau Motarta ta Nufi Cikin Gari Su kuma suka Hau Hanyar Komawa kano Cike da Damuwa Wanda kaso Kadan Daga Cikin Damuwan Ta Ragu Tunda komai yazo da Sauki.

Suna Tafe Ahanya Hajiya Batula na yabon Ahalin Dr.Saulawa Musamman ma Shi kanshi Cikin Mganarta Take Fadin"Gaskiya Dattijon arziki ne...Naji ba Dadi Danaga Daya Daga cikin Ahalinsa ne ya aikata Haka...Daga gani Suna da kyakyawan Hadin kai...Yayi Adalci Sosai Domin in har yaronsu nada laifi kaso mai yawa Daga ciki laifin Dina ne.."Tafada kai Tsaye Tana kallon Dina wacce ke Tura baki Tana Hararan Hajiya Batula kasa kasa Cikin Takaichi Ta kalli Dina Tana Fadin"Eh na Fada laifinki yafi yawa..Domin ai ba"a Shege sai da aka Farayin Shegiya..Babu mutumci Ba kuma So bane mace ta watsar da kimarta yanzu wa gari ya waya..?

Ko banza zaki Haifi Abunda ke Cikinki bata Hanyar Aure ba..Don Allah ya Tarfama Garinki Nono Wlh Haka Zaki Haifi Cikin arasa Ubanshi..'
Kwamishina ne ya katse Hajiya Batula ganin Dinar Ta Dago Tana kallonta kamar zata yi mgana Cikin Damuwa yace"Ya isa Haka Batula..Don Allah ki bar wannan mganar...Naji da laifin Dina nima da laifina kuma kema da naki..Tunda matsayin Uwa kike gareta in kin sakama Tarbiyanta ido baki laifi ba.."Kai Tsaye ta bashi Amsa da Fadin"Baka bani wannan Damar haka ba..Kaida kake mahaifinta ka bata damar Rayuwar sakewa waye ni da zan Hanata..?

Kuma kai yafi Chanchanta ka fara Bincikan Halin Da yarka ke ciki ammh kayi wannan..?

Baka yi ba sai Siyasa sar ka kawai ka saka agaba Ta wannan Gabar Kada ma ka Doramin wani Laifi..!

Daga Dina har kwamishina Sun San Gaskiya Hajiya Batula Ta Fada Shiyasa ba wanda ya kara mgana Daga Cikinsu Ita Dina Bata Damu ba Lumshe ido Tayi Tana Mafarkin gatachan Ta Ganta agidan Zain a matsayin Matarsa Farinciki ya cikata Shi kuma kwamishina Nadama da kunyar in yau ya Mutu me zai Fadama Allah..?

Hakika Barewa bazai Gudu Danta ya Rarrafa ba wannan Abunda ya Faru Da Dina kamar Dawowamai Yayi Domin bayan Rasuwar Sarah mahaifiyar Dina ya Fada Harkan Neman mata sosai Sai Daga baya ya Rage bayan ya Auri Batula,Ya bar Harkan ne Tun Watarana da wani Abokinsa Shima Dan Siyasan ne,yanzu ma Haka sanata ne aawani yankin Yake bashi labarin Wata yarinya mai zafi Daya samu,Tun yana Bashi Labari Har watarana Da sukaje Abuja wani Taro Sai Sanatan ya gayyaceta Tazo mai Sai ya nemi ya Hadasu da kwamishina yaji Matukar kunya Lokacin da yaga Zakiya kawar Dina amatsayin Karuwan Sanata Abun yayi matukar Bashi kunya yaji ya Tsani Harkan Bariki Yaji Neman mata ya fita kansa,Abun da yafi bashi kunya shine Zakiyan tasan komai Domin har Sanatan na Fadi zai bashi Fagen shima ya Dana Ammh Dayake yar Duniya ce sai bata nuna komai ba ta Basar kawai,Yaji kunya Sosai ace yau Kawar yarka ta kamaka Da Dabi"ar kwartanci Abun ba Riba Tundaga Ranar ya daina Harkan Banza da Biyema Shawaran abokai yan Siyasa,Da kuma wannan Dalilin ya Fara Fargaban Kar yazo Itama Dina Halin Datake ciki kenan yaso ya Fara saka ido da Bincike kan Dinar sai kuma wani abu ya Daukemai Hankali ya watsar da Komai,Ammh Yayi Tuban Gaskiya Domin Tundaga Lokacin bai kara Bin yar wani Ba Tsoron Allah ya Shigesa ashe an Gudu ne ba"a tsira ba Shi yana chan yana Bin Diyan wasu Shima wani na bin bashi yar,Nadama ta kara Shiganshi Yaji Komai ya Fita kansa yana jin Da zai iya Daga murya Daya Daga ya gayama Maza masu Bin Ya"yan wasu da su Daina In ba Haka ba zasu gani Domin Sharri kamar Dan Sako ne zaka aikashi kuma zai Dawo maka.

Wannan Dalilin yasa Zakiya Take Sakama Dina mgana in ta ambaci Wasu Daga cikin yan Siyansa sai a hankali,Sai ta nemi kare Mahaifinta ita kuma Zakiya Sai ta gayamata Barewa bazai Tayi Gudu Danta yayi Rarrafe ba ammh ita kam ta sani Allah ya Fitar da ita cikin Ya'yan Babanta Domin Tana da Tabbacin bai aikata makamcin Abunda take aikatawa ba yanxu..Ammh Tabbas Abunda Uban Dina yake aikatawa ne yarsa ke aikatawa Shiyasa bata ganin Laifin Dinar,Bata Taba gayama Dina Wani labarin daya Danganci Dadynta Domin Tsakani Ga Allah take zaune da ita Kawa ta Dauke sosai Abokiyar Sirrinta alokacin ma koda Ita da Daddy suka Hada Farka Cikin Rashin Sani bazata Taba Yarda Tayi wani Mu"amala Dashi ba Inda Amana Ruwa bazai Dafa Kifi Ta sani Batajin mgana kuma Tana Bariki ammh Barikin ta bai kai Tayi Harka da Uban kawarta ba Balle kawa ma irin Dina ta wace komai awajenta.

Da wanman Tunanen Suka Isa Gida Kwamishina da Hajiya Batula suka Nufi Barayinsu Dina kuma ta Haura Sama Ta Shiga Wanka saboda Gajiya Bayan ta Fito ne ta Hada Salollolin Da suka Kubcemata, Ta koma Tabi lafiyan gado Ranta Fes Wayarta Ta jawo Tana Laluban Zakiya Tana jin Hayaniyar su Waleed a Falo da Tashin Mganar Daddy da Hajiya Batula..!
*****
Salolli suka Gabatar kamar yadda Alhaji Tsoho ya Umarcesu,Ita kam Sallah ya zama Dole ammh mganar Abinci Ba kowa ya iya ci ba...Mom Iklima ce Da Mama Safiya suka Tsakura abincin sai Inna Rukayyah Inna Hannatu dai Bata ci ba Tagama sallah Tan kan Sallaya Tana Jan Carbi Ta Zab Tagumi Umma kuwa da Nene Suna zaune waje Daya Umma ce Tayi Sallah Nene na hutu Sai Zaneera Dake Gefe Zaune Tana Shayar da yarta Itama Bayan ta Idar da Sallar Idanuwanta sun kala sun ji Jajir Saboda kuma Sai Hamdiya Dake kan Sallayan Tana Sallah Dukkansu Suna Daki Daya ne Dakin Hajiya Mama Sai Zaina Dake Kwance kan gado Wacce Kuka da Damuwa ya sakarmata Zazzabi,Umma ce ta karbo panadol Wajen Tabawa ta bata Tasha Shine Allah ya Taimaka Ta samu Barci Sai Dai Daga ganin yadda Take Sakin Numfashi zaka Fahimci a Wahale take.

Duk yawansu acikin Dakin Babu Wanda ke mgana da Dan"uwansa kowa da Abunda yake sakawa acikin Ransa,Shi kanshi Alhaji Tsoho Tunda ya Shiga Ciki bai iya Fitowa ba Tunda ya Idar da sallah yake zaune kan kujeran yana Ta Can Casbaha yana istigifari,Domin Hakikanin Gaskiya Abun ya Tabashi Yanzu ace acikin Zuru"ansa asamu wanda zai kawo Irin wannan Tunaninsa ya Tsaya ne ta gano Inda suka Kuskure.

Yana nan zaune har akayi La"asar ya tashi ya koma kan Sallayansa ya zauna Yayi Sallar La"asar ya idar kenan sai ga Hajiya Mama ta Shigomai da Abinci ta Iskeshi ya kurama Waje Daya ido yana kallon Hotonsa Lokacin Dayake Matashinsa,Har Hajiya Mama Tayi mai mgana ga Abinci bai Jita ba sai da Ta zauna kusa Dashi Ta Dafa kafadansa kana ya Dago yana kallonta Cikin Damuwa tace"Ka daina Saka kanka Cikin wannan Dogon Tunanin ba Ishashiyar lafiya Gareka ba..!

Gyada kai kawai yayi yana Fadin"Damuwa ta zama Dole Amina..Sai dai Zamuyi Kokarin Mu ki bata Muhallin Zama acikin Zuciyoyimmu.."Jinjina kai Kawai Tayi kafin tace'Ga abincin ka..!

Kallonta yayi kafin yace"Anya zan iya cin Abincin nan Amina..?

Barshi Dai zuwa anjuma..'
Batayi Musu ba Sanin Halinsa Tunda yace haka Tasan bazai ci ba,Sai ta kauda Farantin Abincin Gefe Ta Daawo Ta zauna Tana Fadin"Anya Alhaji Hukuncin Daka yanke Kan Wannan al"amarin nan Daidai ne..?

Nifa Wlh gani nake Yarinyar nan Tana Sane bafa Dole Zainullahi yayi mata ba Da Amincewarta Suka Fara wannan Shanshancin.."Alhaji Tsoho na Jinta bai mata mgana ba Shuru kawai yayi mata yana Cigaba da Jan Carbinsa.

Sallamansu Baban Kaduna da Daddyn Abuja sai Abba ne ya Dago da Alhaji Tsoho yana amsawa Cikin son kare musu kallo Dukkansu Waje suka samu suka zauna Dukkansu Sannu Da Gida sukayi musu Hajiya Mama kadai ta amsa Shi kuwa Alhaji Tsoho Abba yake ta kallo ganin Irin yadda Lokaci Daya ya zama Wani Iri Cikin Muryan Sanyi da Salama Alhaji Tsoho ya Kira Sunan Abba..

"Usmanu Bin Fodiyo.."Dagowa Abba yayi Araunane yana kallon Alhaji Tsoho Cikin Rauni Da Hannu ya yafitoshi alamun yazo ba Musu ya Tashi ya isa Kusa Dashi,Ya zauna Kansa na Kasa Hannu Daya Alhaji Tsoho ya saka ya Dafa kanshi yana Fadin"kayi Hakuri Usmana...Nasani Abun akwai zafi da Ciwo samun Wannan Abun kunyar Daga Abunda ka Haifa kuma kake alfahari Dashi..Sai dai ina so ka sani Fushi ba namu bane..Mai Faruwa ta Faru sai dai Kuma Mu nemi Hanyar da zamu gyara kar hakan ta kara Faruwa.."Kansa na kasa yana jin Shigar wata natsuwa da kalaman Alhaji Tsoho Cikin Girmamawa ya Dago kansa yana Fadin"Insha Allahu Alhaji...Da farko ina cikin Bakinciki da wannan Abun da zain ya aikata ammh kuma zuciyata tayi Fari da kalaman Uba nagari..Hakuri ya zama Dole ammh kuma Don Allah
Karka Hanani nuna mai Fushina Domin ya Ruguje yardan Dake tsakanina Dashi.."
Alhaji Tsoho yace"Bazan Hanaka ba Usmana..Domin kai Uba ne Nuna Fushin kuma Tamkar Hore ne...Ammh kada yayi yawa kaji ko..?

Dakai ya amsa yana Fadin"Insha Allahu.."Mirmishi Alhaji Tsoho yayi kafin ya Dago yana Yafito Su Baban Kaduna da Hannu suma suka Taso zuwa gareshi Dukkansu suka zauna agabansa Kallonsu yayi yana Fadin"Ina Shi Zainullahin da Hadiru..?

Baban Kaduna yace"Muna sallah Zain ya Fita da Mota...Haddir kuma yana Haraban Gida Shi da Sadiq.."Jinjina kai Alhaji Tsoho yayi kafin ya kalli Hajiya Mama yana Fadin"Aminatu Kiramin su Rukayyah da Hannatu.."ba musu Hajiya Mama ta Mike zuwa Dakinta nan ta iskesu Jugum Jugum Gaisheta suka Farayi Ta amsa Tana kallon Zaina Dake kwance Tana Sauke Numfashi Ahank
ali Cikin Tsausayawa Ta kalli Umma Tana Fadin"Fatima ya Jikin Haliman..?

Tana ta barcin ne Har yanzu..?

Umma Ta Dago Kanta Idanuwanta Har sun kumbura Tace"Eh Hajiya Mama bata Tashi ba Har yanzu..Saukin mata na Taba Jikinta zazzabin ya Sauka.."Kada kai Hajiya Mama Tayi Tana Fadin"uhmm..Allah kara afuwa..Rukayyah da Hannatu ku Taho Alhaji na Kira..Ku kuma ku saki Ranku kuci Abinci Haka Allah ya Tsara..Bamu isa mu Gujema Kaddaranmu ba..!
Chapter 48 · 0% Book details