← Book details Zainazain Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 71 OF 78

Sashe 71

Zainazain Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

In Abban ku ya Shigo Abincinsa na Kitchen ki mikamai.."
Cikin Ladabi tace"To Nene adawo Lafiya.."Daga Haka ta Fice Kafin Nene ta wuce sai da Ta Shiga Dakin Dina ta Isketa kwance kamar kullun Tana cin popcorn Tana ganin Nene ta gyara Zama Tana kallonta kafin ma Tayi mgana Ta Riga ta da Fadin"Zan Fita....Bakowa agidan Sai Halima zani gidan Alhaji Tsoho Saboda Sha"anin nan Daya Karato.."
Cikin Mamaki Dina Tace"Sha"ani..?

Nene tace"Eh...Daya Daga cikin Jikokin Gidan ne zata yi aure kanwar Haddir ne yar wajen Daddynsu na Abuja Shine Zasu zo nan ayi Bikin Daganan za"a wuce da Amarya Gidanta Dake kaduna.."Kai kai kawai Dina Tayi Kafin Tace"wai ni Nene haka zan Ta zama ba Fita..!

Ina som komawa wajen aikina fa.."
Nene taJuya Tana Fadin"Ina zaki da wannan Abun kunyar kuma..?koda yake ke ado ma kike da Ita ai ko cewa akayi ki Fita zaki ce bazaki Fita ba saboda kaucema Idanuwan Mutane gashinan Cikin ki har ya Fara Bayyana ko bama Haka ba Duk wanda ya kalleki yaga mai Juna Biyu.."Baki Dina ta Tura kawai Kafin Tace"Ai Duka Da Haihuwa ce..Kuma Yana da Uwa Da Ubansa.."
Nene na gyada kai tace"hakane ba Shakka..Kinga Tafiyata.."Daga Haka ta Fice Dina Ta rakata da Harara,Nene bata ma Jira Direba ba Tunda yana Office Tare da Abba Da kafarta Ta taka Zuwa Gidan Alhaji Koda Taje duk an Hadu Falon Hajiya Mama ana ta Kira Hira Itama ta Shige Cikinsu Ganinta ita kadai yasa Umma ta Tace ina zaina Nene tace Tana Gida tace bata jin Dadi Umma Tayi Shuru tana wani Tunani Har ma Inna Hannatu ta kada baki Tana Fadi su daina barinta Tana zama ita kadai Ta Riga zama cikim Mutane ko Abun zai saketa,Hajiya mama ta kada baki Tace Tunda Uwarta Ta na Kokarin Raba auranta ai Damuwa yanzu suka kulla Inna Hannatu na jin haka tace Wlh itama Tana Bayan Umma abar Zain din ya zauna da Dina Tunda ita ya zaba nan fa Nene ta saka baki Tana kare zain kan yayi Nadama don Allah su karbi Tubansa Inna Hannatu tace har ga Allah komai ya wuce ammh fa Tana Bayan Umma yarinya karama Bakincikin yayi mata yawa ko ita Babba wannan Abun ya Faru da ita ya zatayi ganin sun Dake ne yasa Nene ta sakarmusu ammh fa tace su bazasu saki ba Sai dai ayi wacce za"ayi.

Umma dai Zainab ta Nema kan Ta koma Gida ta zauna da Zaina Tsoronta Kada wani mgana ya Shiga Tsakaninta da Dina kana kuma Bata son yaudaranta Da Zain yake yi yana Zuwa yana Hore mata kunni,Dole Zainab Ta Shirya ta koma Gida koda Taje ta Iske ma Har Abba ya Dawo Zaina ta kawo Abinci nan Falo Ya zaunar da ita yana kara bata Hakuri da kuma yi mata Nasiham Hakuri da Takwalli Dawowar zainab din yasa ya barta suka koma Daki Tare Dina kuma na cikin Dakinta ko Motsinta ba"a ji.

Sai Umma sai Dare suka Dawo Umma dai Haddir ya Dawo da Ita da su Zareenaa dasu Saudarta Nene kuma Zain ya Daukota Tunda Bayan ya Tashi Daga asibitin chan ya wuce,Inna Hannatu ta Kebe dashi Ta karamai Fada sosai da Nasihan Gudun Duniya ya Tabbatar mata Daya Tuba kuma yayi Nadama,Ammh yana Rokonta Ta saka baki Umma ta maidamai da Matarsa yayi ma Alhaji Tsoho mgana Shi kuma yaki Cewa komai,Inna Hannatu tace Itama Tana Goyon Bayan Umma wannan Shi ya sagar mai da Gwiwa har suka Iso Nene baki Take bashi kan kar ya Damu Umma Fade kawai Take,Bai Shiga Gidan ba yana Sauketa ya juya zuwa Gida Tunda Abba na Gida,Haddir ne ya Shiga Har suna Hira da Zareena sai chan dare ya koma Gida.
*****
Washegari Bakin Yan Abuja Suka iso Mama Safiya da Hamdiya da kawayen Hamdiya Guda Biyu sai wata yayar Mama safiyar Amina,Daman Mama Safiyar yar Kano ce,Sauran Dangin suna Tafe gobe,Chan kuma sai ga Inna Rukayyah da Zafeera da Maryam yar wajen Inna Hannatu Daman Taje kanon Hutu sai Shema"u sun Dira Su Asma"u sai zuwa Gobe Gidan Alhaji Tsoho ya Cika ba Matsaka Tsinke Chan zuwa yammah kuma sai ga Mom Iklima ita da Takwanran Hajiya Mama Wacce suke kira da Hajiya Harda Amin aka zo Duk da basu samu Hutun makaranta ba Baban kaduna yace azo Dasu Saboda Yan"uwa kowa zai Hadu su ga yan"uwa da abokan arziki Mazan dai basu Riga sun iso ba sai Ranar jumma"a Duka zasu Hallara Harda Tawagan Angwaye.

Su Zafeera suna Zuwa Gida Suka Wuce ita da Shema Harda kayansu,Nene da Umma daman tun safe suka Tafi Harda Zareena Zainab ce agidan sai Zaina sai Kuma Dina Hakima Zaina Tayi Murna da ganin Zafeera suka Rumgume juna Daman Umma tace Zafeera Karta bar Zaina agida Ta matsa mata su Taho Tare Sai da sukayi sallar suka ci Abinci suka sake wanka kana sukayi Shirin komawa Gidan Alhaji Tsoho Zafeera kuma ta matsa ma Zaina ta Shirya su Tafi da ta Fara Nokewa kan bata da kayan sawa tafarayi Zafeera ta Bata nata tace sai ta saka Dole Kanwar naki ta Shirya Ta saka kayan Zafeera Doguwar Riga Duk da Daman Zafeera Tafita Jiki ammh abaya Kayanta na yi mata Saboda ita tayi Cikar aure ammh yanzu Rigan Tayi mata wani Burum sai Dan Wuya,Zafeera ta Daukota mata mayafin kayan ta Bata Da Farko tace bazata saka ba Zafeera Ta Rantse mata sai ta Saka Dole ta saka Sun Fito Falo zasu Tafi sai ga Shigowar zakiya Wacce Dina ta Kirata kan tazo Ta Tayata zama Duka gidan sun Tafi sun barta ita kadai kallon kallo Sukayi ma Juna Daman Daga Zafeera har Shema yan Bana bakwai ne suma awulakance suka kalleta suka Dauke kai zaina dai Tana Rike da hannun Zainab Jikinta na Rawa Ita kuwa Zakiya mamakin yaran Take Shema cikin Kallon Tara Saura kwata tace'Wannan itace uwar Shegen..?

Wacce tazo Goyon Ciki Gidan iyayen abokin Farkan nata..?

Da Sauri Zafeera Tace"A"a ba ita bace..Abokiyar Shanshancin nata ne.."Shema Tace"Ko Daga gani Daman ba kima.Mudai an Hadamu da Bakin Gaddara.."Zainab tace"Wlh kuwa.."Kafin Zafeera ta Ja Hannun Shema da Zaina Tana Fadin"Let go.."Suka wuce Zakiya Data kame Tana Binsu da kallon Mamaki har suka fice Daga Falon.

Kada kai Zakiya Tayi ta karisa Dakin Dina ta sameta Ade ade kan gado Tana Dannan waya Cikin wani irin Isgilanci Zakiya tace"Wasu Kwalayen yan iska kuma kuka samu agidan..?

Nagansu tare da Kodaddiyar Kishiyarki Wacce Duk ta Rame ta Kode kamar Kudin Guzuri...!

Dina Tace"Hmm Waya sani..Kila yan Biki ne nidai ina ta jin Hayaniyarsu.."Zakiya na zama Gefen gadon Lokaci Daya Tana Fadin"Lalle..Kam...Naji sunata mganganu ni Dariya ma suka Bani Dukkansu kananan yan Iska ne basu san me ake Kira Bariki ba Ballatana Iskaci.."Dina Tace"Nidai bar wannan mgana Cikin nan ya Fara isata na kosa na Haifeshi yamin Katanga da Abun kaunata Tunda fa nazo Gidanan ko Inda nake Zain bai Taba kallah ba ballatana na saka Ran wani kyakyawan kallo Daga Barayinsa.."
Zakiya Tace"Karki damu...Sauran wata Biyar ki Haife Abunda ke Cikin ki Daga Lokacin kuma ai bashi da yarda zai yi zai saba mganar kakansa ne bayan Tarin Laifukansa Kisha Kurumin ki kin Riga kin zama Matar zain Ta har Abada.."
Dina Ta washe baki Tana Sakin Dariya,Zakiya kuma Tana mata Mirmishi Cikin Tsausayamata yadda Ta Kwallafara akan Zain Wanda ita bata Fatan hakan ya Faru da ita,tafi son Rayuwar yanci Da kuma Sakewa nan Ta gyara zama suna ta Hira da Dina Rabi Duk Labarin Shanshancisu ne Da kuma Mafarkin Dina na Auran Zain.
****
Umma Taji Dadin ganin Zafeera Ta Taho da Zaina Kowa ya ganta sai ya koka Ramarta Inna Rukayyah da Mom Iklima sai da sukayi mganan kan Ramar Zaina suka kuma yi mata Fadan Ta Cire damuwa aranta Ta kuma Dinga cin Abinci Tace Toh,Sai Ranar Alhaji Tsoho Ya ga Zaina Tun bayan Faruwar Lamarin Alhaji Tsoho Shi kanshi Yaga Ramarta Sosai ammh sai bai yi mata mganar ba Ya dai mata wasan Dayake mata Tunda yaga bata wani maida kai ba yasan Har yanzu Abun bai saketa ba,Daganan sai yan matan suka kebe kansu Dakin Hajiya mama Harda Hamdiya da kawayenta,Duk da Sauran kawayen suna Tafe gobe,Duka suna Tare ana ta Hira Zaina na gefe sai dai in Su Zafeera Sun sakota ta Dan Murmusa nan suka kai Dare sai Wajen 9pm na Dare suka koma Gida Taga dai Haddir ammh Bata ga Zain ba,wanda kuma ya ZO gidan Bai Kawo Cewa Zaina Tazo ba kuma yayi Tunanin Binta Gida sai yaga pass 6 Abba ya koma Gida sai ya Fasa Bayason Ran Abba na Baci saboda shi!

Sai washegari
alhamis ya ganta Dayake sunyi Sister Day nan Filin Gidan Alhaji Tsoho akayi komai bayan anyi Hayan Konofi da kujeru Baki na Nesa Dna kusa sun kariso Dangin Mama Safiya Mota Biyu suka yo Daga kano Banda na Sauran garuruwa,Wasu ma suna Hanya basu kariso ba manyan ya"yan Inna Hannatu dana Inna Rukayyah duk sun kariso Da nasu Tawagan,Daddyn Abuja ma ya Iso aranar Baban kaduna ne sai Zuwa Gobe Suma Daga Barayinsu sunyi gayyah Sosai,Domim Katin ma Guda100 Suka Bugo wanda Abba ya Daukin Nauyin buga katin Gayyata Daga Gidan Saulawa Harta da chan katsina yan"uwan da suka Rage duk Hajiya mama ta Kirasu awaya ta sanar dasu Ganin gidan ya Cika ne yasa Haddir ya Tattara Inashi Inashi zuwa Lowcost wajen Zain wanda yaji Dadin haka Sosai,Yan matan kuma Ranar ma Gidan Abba suka yada Zango chan ya Cika da Iyayensu.

Kowa ya maida komai bakomai ba an manta da Abunda ya Faru..Zaina ce dai suke Tsausayamawa Kowa yana nan nan da ita Bangaran Dina ba wanda ya Damu da Tambayarta ma Domin kowa haushinta yake ji Gwara ma Inna Rukayyah Tayi mganarta Tace chan gida suke Barinta Don karta Fito Labari ya Yada gari,Nene tace Tana Gida Ko Su Shema da suke kwana agidan ba ganinta suke ba,Tana Dakinta Bata Fitowa komai sai dai ayi mata Tana Daga Cikin Daki Nene ce ke wannan Wahalar Suna Gidan suna Sha"aninsu basu ma Damu da ita ba Itama bata Damu dasu ba Sai dai in Zakiya Tatashi aiki Sai ta Kirata tazo Ta Tayata zama,Su Wuni suna Shakiyansu wani Lokacin sai su Umma sun Dawo Take Tafiya.
Chapter 71 · 0% Book details