← Book details Zainazain Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 78

Sashe 57

Zainazain Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ba inda Zata ka wuce ka bamu waje kafin Raina ya baci Na Tsinke ka da mari Hadiru.."
Jin Haka yasa bai yi gaddama ba ya Juya yana Fadin"Allah Huci Zuciyarki Ummah.."Da Sauri Tace"Ameen.."Nene bata ma yi mgana ba ta kada kai ta Juya Tabi Bayan Haddir kawai Umma Ta Rakasu da Harara Tana Fadin"Kaji min iskancin banza iskancin Wofi..Wani wai Ta koma Gidan Mijinta..? wato ta koma Taje Chan ta Cigaba da zama Dashi karshenta ya Auri Karuwarsa Tasa tazo Tana Tayasu Renon Shegen nasu Rayuwarta Ta kare Cikin Bakinciki Wlh bazata sabu ba indai ina Numfashi Halima Ta bar Auran Zain har Abada.."
Zaina Dake zaune bata san Sadda Karshen kalmar Umma ta saka Kukanta Fitowa ba Cikin wani Takaichi Umma ta Isa Gareta Tana Fadin"Rufemin baki Sakara mara wayau...Ana Neman yadda Zaki Rayu Cikin salama kina ma wanda ya ci Amanar zaman tare da irin Soyayyar da kika nuna mai kuka..?

Ki Min Shuru yanzu ko na Kikkifa miki Mari yanzu yanzu nan.."
Jin yadda Umma ke Sababi ne yasa Zaina Tayi gum da bakinta bata kara Bari kukanta ya Fito ba ma Ta Dinga Hadiyeshi Tana Sauke ajiyar Zuciya kamar wata karamar yarinyar da Uwarta Ta Tsigeta Tana Cikin Shan Nono Tsaki Umma Taja ta Nufi Hanyar Tiolet tana Fadin"Kafin na Fito ki Saka kaya ki Tada Sallah in kina so mu Shirya.."
Da Sauri tace"Toh Umma."Tana Kokarin Goge Hawayenta da Danne kukanta Sai Lokacin Umma Taji Tsausayinta ammh kuma Dole ne tayi mata haka In ba Haka ba Haka Zatayi ta zama Cikim Kuncin zuciya har wani Cutan ta kamata Kofar bayin ta Bude ta Shiga Ta bar zaina na Kokarin Mikewa Lokaci Daya tana saka Hannu tana Danne bakinta kada kukanta ya Fito Umma Taji ta Fito taci kaniyarta.
_Godiya Ta musamman ga Dimbin Masoyan ZAINAZAIN,Ina ganin Tarin Sharhinku da Comments Dinku Musamman yan Group din ZAINAZAIN 1&2 ,da Gidajen Janafty Shakira,Duka ina gani Kuma ina Jin Dadi Sosai kuke sakani Nishadi Kuyi hakuri bana samun Lokacin Maida muku martani Abubuwan ne sai a Hankali ammh ina gani kuma ina Godiya Da ku da yan Wattpadians Fans dina suma Ina ganin Sharhinsu Alhamdullahi kawai Zance Allah ya bar Zumunci Ameen..!_
*Janafty...*
*ZAINAZAIN..!*
_(Is a love Story and Betrayal)_
*Wattpad:Jamilaumar351*
*Mallakar:Janaftyshakira*
*BOOK 1*
"Haddir ne kan gaba Nene na Biye Dashi Zuwa Falo,Zareena na ganinsu Fuska ba walwala Tasan ba"a Dace ba Domin Taga Umma Ta Dauki Fushi Sosai kuma Bata ma da Niyar Barin Zaina Ta koma Gidan Mijinta a Take takenta Datake gani.

Cikin Kallonsu Tace"Ba"a Dace ba ko..?

Nene ce ta zauna Gefenta Tana Fadin"taki ma Sauraranmu...Naga Bacin rai naga Tsausayi na Soyayyah da Jinkai duka acikin Idanuwanta na Farko Tana Tsausayin Zain Tana kuma Tsausayin Halima Tana kuma Jinta kamar yarta Data Haifa Da Cikinta,Wannan Dalilin yasa Ta nuna bacin Ranta Sosai wanda ban Taba gani ba.."
Nene Ta Fada Cikin karaya,Zareena Tace"Hm...Allah ya kyauta nagaba.."Haddir ya amsa da Ameen yana Fadin"Bari naje na samu Alhaji Tsoho muyi mgana in anci Sa"a ya saka Baki mgana Ta kare.."Nene tace"Shima din bana Jin zai ce wani Abu awannan Lokacin Hadiru.."Haddir yace"Zan Jaraba Dai na gani yadda mukayi Dashi ko ban Daawo ba zan Kiraki awaya na Shaida Miki.."
Nene tace"Shikenan..Sai na Jika.."Zareena kuma tace"Ka gaida Zain din sai nazo.."ya waiwayo yana Fadin''Ke ina zaki da Daddaran nan..?

Baki bari sai gobe..?

Nene tace"Nima Abunda na gayamata kenan.."Jin Haka yasa Zareena tace,"Shikenan bari na Bari sai goben Dama zan Jira in Zainab Ta Dawo Daga makaranta Direban Abba ya kaimu ne ammh Bari dai na bari sai gobe da safen.."Haddir ya wuce yana Fadin"Yadai kamata kam...Ni na wuce.."Suka Rakashi da Allah kiyaye Hanya.

Yana Fita Haraban Gidan yaci karo da Zainab Ta Dawo Daga Makaranta Cikin Ladabi Ta Ramkwafa Tana gaisheshi ya amsa Sama sama ya Fada Motarsa ya Fice Daga Gidan Ta Bishi Da kallo Bata samu Fuska bane Taso Ta Tambayeshi Ya Ya Dakta yake ne..?

Sai dai baima saki Fuskan ba Ballatana ta Tambayeshi Tana Shirin Shiga Cikin Gida ne sai ga Motan Abba ta Dawo Daga Dauko su Saudart Daga Islamiya bata ba Tsaya ba Taja Jakarta Ta Nufi Cikin Gida Domin yau din agajiye ta Dawo Wuni Tayi Cikin Makaranta Suna Kokarin Fara Test din Zangon Karatunsu na Farko ne.

Haddir kafin ya isa gidan Alhaji Tsoho sai da ya Tsaya masallacin Kusa da Gidan yayi Sallar mangariba kana ya karisa,Alhaji Tsoho Na cikin Dakinsa saman Kujeransa yana Karatun wani katon Littafi da Siririn Gilashinshi mai kara mai karfin gani,Gabansa Haddir ya Zube bayan sun gaisa Ya Shiga Rarrafomai Abunda ke Tafe Dashi na game da Fushin da su Abba suke da Zain da kuma Halin Da yake ciki da kuma Yadda sukayi da Umma yau din..

Har ya kamallah maganganunsa Alhaji Tsoho na kallonsa bai ce komai ba,Ganin Alhaji Tsoho yayi Shuru ne yasa Haddir yace"Nazo na gayamaka ne Tsoho Saboda ka saka baki Abba ya Janye wannan Fushin Da yakeyi Ko Zain zai ga Daidai Arayuwarsa..Umma kuma ka mata Mgana Ta bashi matarsa Tunda dai mai afkuwa ta Riga ta afku Sai dai muyi kokarin kada Hakan ya kara Faruwa..!

Mirmishi Alhaji Tsoho ya saki kafin ya Ijiye littafin Hannunsa Saman wani karamin Tebur Dake gabansa Lokaci Daya Yana Fadin"Toh ni yanzu da kazo kana Gayamin me kake so nayi maka..?

Cikin Mamaki Haddir yace"me nake so..?kaifa Tsohon nan ka iya Nuna ma Mutane Boko fa..?

Ai nayi maka Bayanin komai.."Dariya Ta kama Alhaji Tsoho wanda Tun Faruwar Al"amarin nan bai yi Dariya Haka ba baki Sake Haddir ke kallonsa kafin ya koma kawaai ya Hade Ransa sai da Alhaji Tsoho yayi Dariyansa Son Ransa kana yace"Yaro yaro ne...Yaro Man kaza bai san Wuta ba sai ya Taka.."
Cikin Haushi Haddir yace'"Ammh dai bani
kake Nufin yaro man kazan ba ko..?Alhaji Tsoho yace"A"a Ba da kai nake ba...Karin mganace tamu ta Hausawa.."Yafada yana Dariya Lokaci Daya yana Daga Hannu Alaman yayi saranda Mirmishin Lebe kawai ya saki Yana kallon Alhaji Tsoho Daman ya sani Alhaji Tsoho so yake ya Hukuntashi Shida Zain alokaci Daya.

Ganin yadda Haddir din yasha Kunu ne yasa Alhaji Tsoho ya Dakata da Dariyan Dayake ya Fuskanci Haddir yana Fadin"Kasan abunda kai baka Fahimta ba Hadiru..!?

Bai bashi Zarafin mgana ba yacigaba da Fadin"Duk Cikin ya"yana Usmanu Yafi kowa Hakuri da kawaici Sai Mahaifinka Aliyu..Sai Rukayytu..Dama masu Zafin Da Zuciya Sai Babana da Hannatu uwata Daman kuma so Gado sukayi wajen Uwarsu Amina ka gantanan nayi Fama da Ita Tun Lokacin muna da Kuruciya.."Yafada Cikin Zolaya Murmusa kawai Haddir yayi batare Da yayi mgana ba Shima bai Damu Daya Tanka din ba ya Cigaba Da Fadin.

"Tunda kaga Usmanu yayi irin wannan Fushi Ka Tabbata Babban Abu ne...Mutun ne mai kawaici da Boye damuwa Naji matukar Tsoro Lokacin Danaji Labarin Damuwar da Zainullahi Ya sakashi Ta kaishi Har kwance bai iya zuwa aiki Daganan nasan Zainullahi ya Gama Raunana Zuciyar Usmanu na Wanda banta gani ba Tunda na Haifeshi Saboda Hakurinsa da Kawaicinsa..!

Ya fada Idanuwansa na kan Haddir wanda ya natsu yana Sauraransa Cikin Takaichi Alhaji Tsoho ya Cigaba Da Fadin"Me kake so nayi akai Hadiru..?

Karka manta Usmanu Shine Mahaifin Zainullahi Shine Babban D'a Namiji cikin ya"yansa Wanda ya Dorama Son Duniya da kuma Burin Watarana In Bashi Shi zai Gejesa ya Rike Iyayensa da kanninsa..?

Ya bashi yarda yana ganin Ya Sauke Nauyin Dake kanshi Wajen Bashi Dukkan Tarbiya da Ilimi na Arabi da na Zamani Saboda Watarana ya Tsaya Da Kafafunsa bayan Gama Dukkan wananan bai ga Sakamakon komai ba sai wannan aikin da Zainullahi ya aikata na Ijiye karuwa suna zaman Haramci Harda Tsaraban Ciki,Ni na isa na Hanashi Nuna Fushinsa da Damuwarsa akan Abunda ya Haifa..?

Ya Fada yana kallon Haddir Wanda kalaman Alhaji Tsoho suka Sanyayamai Jiki Kai ya Girgiza Cikin Mutuwar Jiki Kafin Alhaji Tsoho ya Cigaba da Fadin"Toh ka gani bani da wani Abunda zan iya yi kan wannan Lamarin Hadiru Zainullahi ya gama Bamu kunya gabadayanmu..Na Riga nayi iya Abunda zanyi sauran kuma sai mu bar ma Ubangiji mganar ita yarinyar ma Mahaifinta ya Kirani yace nayi Hakuri Dayake ya karbi Lambata Ranar kafin su Wuce kan Gobe ne Suke sa Ran Zuwan ita Uwar yarinyar Daga Sudan in tazo yayi mata Bayani Insha Allahu zasu zo da mai Dakinsa su kawo ta Wajena kamar yadda nace..Sai godiya yake min abun gwanin ban Tsausayi..!

Haddir bai samu Damar mgana ba yaji Muryan Hajiya Mama Dake Kokarin Shigowa Dauke da Farantin Kololin Abincin Alhaji Tsoho tace"Nifa wannan Hukuncin naka baimin ba Sam Taya za"a ce kuma tazo ta zauna Cikin mu Har ta Haihu ai sai in muna ganinta Bakinciki watarana ya Nemi kashemu daka sani Ta tsaya chan gaban Uban nata ta Haife Shegeen..'
Tafada Cikin bayyana Takaichinta Da Sauri Haddir ya mike ya karbi kayan Hannunta yana Fadin"Kamar kin Shiga Raina Hajiya Mama..Wlh nima Haka nace..!

Yafada yana Sauke Farantin Gaban Alhaji Tsoho wanda ya murmusa yana Fadin"Mata mata..Sai abarku..Nan din Shine mafita ai Aminatu..Mahaifinta Dan Siyasa ne zamanta gabansa akwai mtsala Gwara tazo nan ta Haihu sai a Daura musu Aure suje chan su Cigaba da Renon Abunda Suka Hadu suka samar baShikenan ba.."
Hajiya Mama na zama Gefen Haddir Tana Fadin"Bafa Shikenan ba Mallam..Su mun Rufa musu asiri mu kuma mun Tona namu kana Tunanin mganar nan bazata Fita bane in Har yarinyar ta Dawo gabanmu da wannan Abun kunyar..?

Alhaji Tsoho yace"Zai fita mana...Alheri ke Buya banda Sharri Aminatu..Kuma Wanda ya rufama wani asiri Allah Shima zai Rufamai Duniya da Lahira,Muma ai ya Rufamana Tunda bai kai mu kara Kotun musulunci ba Inda chan yakai Allah Jikanki jefasa za"ayi har ya Mutu Tunda da Auransa yake Zina.."
Hajiya Mama tace"Ita fa sai a kyaleta..?
Chapter 57 · 0% Book details