Sashe 23
Zainazain Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Minti Talatin ya kwashe sai gashi ya Dawo Lokacin Har ta sake wanka ta Chanza kaya Zuwa Wata karamar Riga ta Shan a Iska Falo,Suka Yada Zango Ta Nannade ajikinsa Tana Shagwaba Shi kuma yana Biye mata Wayarsa na Gefe Yana ganin Dina nata Kiransa Allah ya Taimakeasa Wayar Tana Silent ne Da bai da kuma amsan da Zai bama Halima in ta Fahimci wani Abu Dama Dayan Layin da suke yawan mgana da Dina Dr.Dogara ya sakamata Saboda in yana Gida tana yawan Kiransa Dayan layinta ne ya Sakamata Dr.Dina kuma ya Tabbata Kiran ta bana alheri bane
Halima na kan Jikinsa ya Jawo Wayar ya Kasheta Gabadaya,ya Biye mata Basu wani Dau Lokaci ba Ya Tattarata Zuwa Cikin Bedroom dinsu,chan suka kwakwame Juna Cikin so da kauna Cikin Lokaci kalilan Ya mantar da ita Duka wasu manganun Laila da Zafeera ta saki Jiki kan Duk Duniya ko kowa zai iya Juya mata baya Toh Banda Zain aciki.
*****
Washegari Tun Karfe 7:45am na Safe Zain ya Fice,A gida ya bar Halima ita sai 9 take da Lactures,Gida ya Fara Biyawa ya kaida Umma da Nene Koda yaje Abba ya Fita Tun 7 shima yana da Meeting bai jima ba yayi musu sallama ya Fice Daganan Gidan Alhaji Tsoho ya Biya suka Gaisa Bayan sunyi Wasan Jika da kaka Dashi da kuma Hajiya Mama Baba Tabawa tazo Suka gaisa Bai jima ba yayi musu sallama Yana Sauri zai Shiga Cikin Asibitin
Kusan Tare suka Shigo Cikin Haraban asibitin da Haddir kusan kuma Waje Daya kowanne ya Faka Motarsa Suka Fito Dukkansu a Tare,Sakamakon yau jumma"a Dukkansu Shigan Manyan kaya ne ajikinsu,na Shadda Fara kowanne kuma ya Daura Hular zanna Bukar Bisa kansa kafafunsu kuma Kamar hadin Baki Duka Suna sanye da Rufaffan takalma ne na Fatar Damisa,Kallo Daya zaka musu kaasan Sudin Jini Daya ne Saboda yadda Suke Diban kama Sai dai Haske kawai da Zain ya Dara Haddir ammh har yanayin Tswonsu da kuma Sumar kansu da kuma Sajen Fuskarsu iri Daya ce Komai nasu Cikin Tsari ne Shiyasa Mata da yawa Suke Zencensu Suna kuma Jinjina ma Tarin baiwar da Allah yayi ma wadanan Zaratan samarin.
Da Farko Dauke kai Zain yayi Daya ga Haddir zai wuceshi yana Tusa key din Motarsa Cikin aljihun wandonsa Da Haddir yaga Haka sai ya Murmusa ya Bishi Suka Jera Tare Lokaci Daya yana Mika mai Hannu da Fadin"Assalamu alaika...!
Cikin Basarwa ya Dakata da tafiyar dayake yi ya Bashi Hannu yana amsa Sallamanshi Fuska ba Fara"a Haddir bai Damu ba Sukayi Musabaha yana Fadin"Ya gida..?
Ya kwanan Halima..?
Cikin Son kauda mganar yace"Komai Normal....!
Daga Haka ya sa kai zai Wuce Haddir yace"Zareena Tace Tana ta Neman wayarka Bata samu...In ka samu Lokaci ka Kirata..!
Waigowa yayi zai yi Mgana kenan Daidai Lokacin Motar Dina ta Shigo Cikin Asibitin Dukkansu da kallo Suka Bi Motar har ta karisa Parking Space ta samu waje ta Tsaya Bata Jima ba ta Bude Murfin Motan Ta Fito Cikin Shigar alfarman na Riga da Sikat na Wani lees mai kyau da Tsari,Dinkin ya kamata Sosai sai karamin mayafin Data yane kanta Dashi karamar Jakarta ce a Hannunta Da wayarta sai key din Motarta Kwalliya ta Chaba Sosai kuma Yayi mata kyau Sosai Sai Tashin kamshi Take kafarta Sanye Cikin Takalmi mai Tsini Ta Fara Taku Daya bayan Daya kowani Sassa na Jikinta na Motsawa Kai Tsaye kuma Inda su Zain ke Tsaye Suna kallonta Haddir Dai Kai ya kauda Daga kasan Ransa yana Jinjina Shedancin Dina Zain kuwa ya kasa Dauke ido Daga kanta Haka kurum yaji kamar wani manadigosu na Jansa Zuwa ga kallonta.
Har sai da Ta kariso kusa Dasu yana kallonta ganin yadda Haddir ya kafeshi da ido ne yasa ya kauda kai Lokaci Daya yana Sakin karamin Tsaki Haddir ya kallah yana Fadin'Ok zan kirata..Ok..!
Daga haka kawai ya Wuce Cikin Asibitin da Sassafar Dukkansu da kallo Suka Bisa,Shi Haddir kallon Takaichi yake Bin Zain Dashi Ita kuma Dina kallon Soyayyah da kauna Tana jin kamar ta Bishi ta Rumgomsa Saboda yadda yayi mata kyau kwarai yau din da Shigar Jikinsa.
Maida Dubanta tayi kan Haddir Wanda ke Kokarin Fiddo wayarsa Daga Gaban aljihun Rigansa Cikin Kissa Tace"Mrning Sir...!
Bai kalleta ba ya Juya zuwa Cikin aasibitin Lokaci Daya Yana Fadin"Mrning How are u..?
Daga Haka ya Dora Wayarsa a kunni ya Fara mgana kuma yana Tafiya Cije bakinta Tayi Tana kallonsa har ya bace ma ganinta kafin Ta Murmusa Tana Fadin"Hmm baka da yarda Zakayi Watarana Haka zaka ganni agidan ku a matssyin Matar Zain..!
Daga Haka itama ta Nufi Cikin Asibitin Cikin Takunta na Goggun mata Tana Shiga Da Dr Imran ta Fara cin karo ya Fito Daga Office din Dr Peter,Da wasu Folder a Hannunsa yana ganinta ya Washe baki Lokaci Daya yana Sakarmata manyan Idanuwansa kamar zai Cinyeta Danya,Ganin haka yasa Ta Zabgamai Harara maimakon Ta Nufi Hanyar Office dinta kawai sai ta Fada Office din Dr Aisha Saboda Gujema Haduwa da Bakin Maye Dr Imran.
Shi kuwa Zain yana Shiga Office Dinsa Daman da Folders Din Mutane yaci karo Wata Nurse ta Shigo Tana gaisheshi Cikin Daure Fuska ya Zauna kan kujeransa yana Jawo Folders Din gabansa Lokaci Daya yana Fadin"Wadanan Folders din fa..?cikin girmamawa tace"Na Patient ne masu ganin Likita Sir...Dr Imran yace na Tara maka Su Kafin ka iso..!
Karamin Tsaki kawai yaja kafin ya zari Biron Dake kan Teburinsa ya Bude Folder Din Farko yana Fadin"Hannatu Bashir Call her.." daga haka ya Juya yana kallon Folder din matar yana Nazarin Abunda ke Damun matar yar Shekara 41 da wani Abu a Duniya,Da Sauri ta Fice Zuwa Gaban Office din nashi Inda Masu Jiran ganin Likita ke Taruwa takira Sunan Hannatu Bashir wani yaro Dan kimanin Shekara 20 ya Mike Lokaci Daya yana Tada wata mata Dake gefensa Cikin Kulawa Nurse din tace"Itace ko..?
Yaron ya Daga mata kai da Sauri Tace"Ok ku Shiga da Sauri Dr.Zain ne bayason Jira..Ku kuma ku Tsaya ayadda na Tsaraku Daga na Daya zuwa na Goma,In wannan ya Fito wannan ya Shiga ku kuma Sauran ku taso muje Nakai Folders din ku Office din Dr Imran ne..!
Daga Haka tayi gaba Sauran Majiyanta Suka Bita abaya,Yaron nan kuma ya Shiga da Mamansa office din Dr Zain ya zaunar da ita Shima ya zauna Zain ko Dago kansa bai yi ba ya Fara Fadin"Hawan Jini ke Damunki Mama..!
Yaron ne ya bashi amsa da Fadin"Eh likita.." sai Lokacin ya Dago kansa ya Sauke kan yaro na Dan Lokaci kafin ya kada kai yana Fadin"Sannu Mama bari na gwada Bp ki..!
Yafada ganin Tana ta Numfashi Sama sama.
Cikin kwarewa ya Fara aikinsa ya Gwada Bp Dinta Bayanan kuma yana ta mata Wasu Tambayoyi Tana Bashi amsa,Rubuta mata mganguna Yayi ya basu,yace su dawo nan da 4weeks bayan ya dan bata Wasu Shawarwarin na Rage Tunani Tayi ta mai Godiya Tana Sakamai albarka Cikin Mirmishi yake Fadin"Bakomai Mama Aikinmu ne..!
Suna Kokarin Fita ta Sawo kanta Cikin Office Din,Kallo Kallo akayi Tsakanin Matar nan da Danta da Dr.Dina Tabe baki kawai Tayi ta wucesu suma suka Fice suna mamakinta,bai ma san ta Shigo ba ya Dukufa Duba Dayan Folder Dake gabansa Na wata mace ne kamar kuma Zuwanta na Farko kenan,jinjina kai yake Dazu matar da ta Fita bashi ya kamata ya Dubata ba Dr Imran ne,ammh Tunda Fayels dinta ya Fado gabansa kuma ganinta Babba Tayi Sa"ar Nene yasa ya Dubata ammh Shi yafi Duba Wadanda suka Shafi Ciwon mata kamar su Ciki haihuwa,Mtsalan Bari,sanyi Da Sauransu.
Azatonsa Itace kai Tsaye yace"Aisha Jarma meke Damunki..?
Zan iya Taimakonki..?
Yafada kai Tsaye Yana Dora Bironsa Bisa Folder Din zai Fara Rubutu wani Mirmishi Dina ta saki ganin bai Fahimci ita bace Siririyar Dariya ta saki mai kara wacce Har Zain ya Jita da Sauri ya Dago Suka Hado 4eyes yana kallonta Lokaci Daya kuma kamshin mayen Turaranta ya Shigemai Hanci.
Cikin Hade Rai ya ijiye Biron Hannunsa yana Fadin"What..?
Baki ganin ina kan Duba patient ne Dina..?meke damunki..?
Yafada yana Tsare ta da idanuwansa Cikin Kayattacen Mirmishi Tace"Nima Patient din ne Dubani zakayi..!
Tafada Tana Kafeshi da mayen kallonta Wani karamin Tsaki yaja kafin ya maida kansa baya bai samu zarafin mgana ba aka Bude Office din aka Shigo Ganin su Su biyu yasa Ta Juya zata Fita da karfi Zain yace"Aisha Jarma..?
Bafullatanan ta Daga kanta Tana Fadin"Eh Dakta...!
Kai Tsaye yace mata'"Shigo Ciki mana..!
Yafada yana maida kallonsa kan Dina Lokaci Daya Yana Fadin"Plz Dina Get out...In ke baki san Darajan aikin ki ba Ni na sani ki Fitarmin daga Office Tun kafin Raina ya Baci..!
Mamaki ya Cikata tayi Galala Tana kallonsa Cikin Taushin Murya tace'Buh Zain mgana...!
I said get Lost....Ke Dakikiyar ina ce da baki gane mgana..?
Ya Katseta Cikin Wata Gigitaciyar Kara wacce ba ita kadai Ta Razana ba Har Bafullatanan Dake tsaye sai da Taja Baya,Daskarewa Dina Tayi Tana Bin Zain da kallo Idanuwanta Sun Cika da kwallah ganin Taki Tashi ne yasa ya Mike ya Nuna mata Kofa yana Fadin"Fita..Fita Tun ina ganin Mutumcinki kafin Sauran Mutumcinki Dake Idona su Zube..Wlh zan saka ayi Miki Wulakancin da in har kika bar cikin asibitinan bazaki so ki Dawo ba Ki Fita nace..!
Yafada Cikin Bayyana Bacin Ransa Lokaci Daya Jijiyoyin kansa na Mikewa Ganin haka yasa Dina Ta Mike tana Kallonsa Gefe Daya kuma tana Kokarin maida Hawayen Idanuwanta kafin tayi wani Mirmishi kawai ta Juya da Sassarfa ta Fice da wani katon Tsaki ya Rakata yana Fadin"Shedaniya kawai..Allah yamin Tsari Daga Shedancinki.."!
Batulatanan Dake Tsaye ta amsa da Ameen Ameen Saboda ita kanta Dinar bata mata kalan Mata masu kima ba,Komawa yayi ya zauna yana Dafe kanshi kafin yace"Zauna Hajiya..!kai tsaye yana Janyo Fayel Dinta Zama tayi Shi kuma Cikin Zafin Numfashi yace"Meke damunki.?
Bayani ta Faramai Shi kuma yana Rubutawa Lokaci Daya yana Jifanta da Wasu Tambayoyi Tana Bashi amsa.