Sashe 52
Zainazain Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Daddyn Abuja zai kara mgana Abba ya Dagamai Hannu yana Fadin"Allah ya kiyaye Hanya Aliyu..Ammh awannan Karon Ko Alhaji Tsoho bai isa ya Hanani Nuna ma Zain yaci Amanar yardan Da nayi mai ba.."Daga Haka bai kara mgana ba ya Rabashi ya wuce cikin Gida Fuu Su Umma suka Bishi da kallo Kamar yadda Haddir da Daddyn Abuja suka Bishi da kallo Har ya Shige Cikin Gida.
Numfashi Daddyn Abuja ya Saulke kafin ya Dafa Haddir yana Fadin"Take gud Care of Him Son..."Kai ya gyada mai yana Fadin"Insha Allahu Daddy.."Kai ya Jinjina yana Fadin"Allah yayi muku albarka..'Ya amsa da Ameen kafin yace"Yima Mamanka Mgana tazo mu tafi.."Daga Haka ya Shiga Gidan Baya Dama Direbansa ne ya kawosu Haddir ne ya karisa Gabansu Umma yace ma Mama Safiya tazo Daddy Na Jiranta Hamdiya ma Zareena ta yi ma sallama dasu Umma Ta wuce ta Shiga Gaban Mota Mama Safiya Tayi musu sallama tazo ta Shiga Mota Direba yaja Suka Fita Daga Haraban Gidan Bayan megadi ya wangale musu get suka Fice.
Daga Umma Har Nene ba wacce Tayi ma Haddir mgana suka Juya Zuwa Cikin Gida,Zareena ma Bata tsaya ba, Ta juya ta koma Cikin Gida ajiyar zuciya Haddir ya Sauke kafin ya Fada Motarsa ya Fice Daga Cikin Gidan.
Su Umma na Shiga Falon Suka Iske Abba na kai da kawo acikin Falon Hanayensa Goye abayansa yana ganin Shigowarsu ya Dago Cikin Bacin Rai yana Fadin"Fatima Da Aisha..!
Gabadayansu suka Zubamai Ido Suna kallonsu Zainab ma Dake Daki Tare da Zaina sai da ta Fito Jin yau kai tsaye Abba ya Kira Sunan Umma da Nene wanda basu Taba jiba da wayansu ba sai yau Haka ma Zareena Gabanta sai Fadi yake Allah yaasa Jalal yabi su Saudart zuwa Islamiya.
Cikin kakkausan Murya da zallar Bacin Rai yace"Ban amince ba kuma ban yar jema Daya Daga cikin ku Zain yazo Gidan nan Ta Daga ido ta kalleshi ba.."Yafada yana nuna su da yatsa Umma dai batayi Yunkurin yin mgana ba Nene ce Ta marairai ce Tana Fadin"Saboda me Abba..?
Zain yana da wasu iyaye ne bayan mu..?
Cikin Tsawa yace mata"Eh mana yana Dashi..In ba ya maidamu wasu Shashashu ba Taya Taya Zai aikata irin wannan Dabi"ar bamu sani ba Karuwa fa ya ijiye Dadirowa fa Aisha Ahakan kuma muke zaman iyayensa..!?
Ina Ban Amunce ba Ko yazo Gidan nan kada wacce ta mai mgana ku Rabu Dashi...Tunda ya Riga ya gama Cutar da Zuciyoyin da suka yarda Dashi..Yaci Amanarmu Mu iyayensa kuma yaci amanar amatarsa,Ku kyaleshi ni da kaima zan mai iyaka Da Shigomin Gida Tunda ba Da kudinsa na ginashi ba..!
Nene Taji Hawaye sun kawo mata Cikin Sagewar Numfashi Ta Bude baki zatayi mgana Abba ya Dakatar da ita da Fadin"Karki kara cewa komai...Umarni ne na baku ba Shawara ba..Har ke Zareena ban Yarje miki ki Saurareshi ba.."Daga Haka kawai ya wuce Fuu zuwa Dakinsa Umma ta Cije baki wani Abu na Suyanta acikin Ranta Ta mara mai Baya Nene ce ta Sulale nan Tana kuka Zareena ma Haka Zainab ma Tana Tsaye Tana Hawaye,Sadiq kuwa da Shigowarsa kenan Dakinsa kawai ya wuce yana jin Tsausayin Yayan nashi Har Cikin Ransa.
Zaina kuwa Tana Tsaye Daga Bayan Zainab Daga Cikin Dakin Bata Fito ba Taji Duka Abunda Abba yace sai ta kara Rudewa da Shiga Tashin Hankali Taya Ya Abba zai yanke wannan hukuncin..?
In yace haka ina Ya zain zashi..?
Tasan Duk Harda Saboda Ita Abba ya Dauki wannan matakin Sai Taji kamar Jiri na Dibanta zata Fadi baya Tayi ta koma Kan gado Ta zauna Tana Sharan Kwallah Tana Jin Zuciyarta na Bada wani Sauti Mara Dadi Fat!
Fat..!
*Shakira...*
*ZAINAZAIN..!*
_(Is a love Story and Betrayal)_
*Wattpad:Jamilaumar351*
*Mallakar:Janaftyshakira*
*BOOK 1*
"Da Sauri Nene ta mike kamar Zata Tashi sama ta Wuce Dakin Umma Zareena da Zainab suka Bita da kallon mamaki,Kada kai kawai
Zareena Tayi ta mike Tana Rangaji ta wuce Dakin Datake sauka in tazo Ganin Gida Zainab ma Baya Taja ta koma Cikin Dakin Tana Sharan kwallah Turus Tayi ganin Zaina Kwance kan gado tana Kuka mai cin Rai Da kuma Raunana Zuciyar mai Sauraro.
Itama nan Kasan Cafet din Zainab Ta Sulale ta Maida Hannayenta ta Tallabi kanta Tana Cigaba da Tsiyayan Hawaye,Domin bata da wani karfin Gwiwan Hana Anty Zaina kuka Domin Abun kuka ne ya sameta Dole abarta ta koka ko Zataji Saukin Abunda ke Damunta acikinn Ranta ita Fa kenan Data ke kanwarsa Taji Zafi Abun ya Raunana mata Zuciya Ballatana ita Matarsa Da ta kasance abokiyar Sirrinasa gabadaya.
Umma na Shiga Cikin Dakinta Ta maida kofa ta Rufe Lokaci Daya Tana sakin wani Siririn kukan Daya ke neman kwace mata Tuntuni Tana Boyewa,Shi ta saki yanzu Domin Abun yana Fito mata Daga kasan Zuciyarta ne kukan Bakinciki da kuma Tsausayin Zaina Gefe Daya kuma Tana jin wani Daci acikin Ranta In ta Tuna Abunda Zain ya aikata a matsayinta ta uwa Dole ne Tafi kowa Shiga Tashin Hankali game da wannan lamarin Duk da Tana Boyewa bata son Kowa ya Fahimci Ta Damu da Abunda ya Danganci Zainullahi din.
Nene Ta Dade tsaye kanta Tana kallonta Bata sani ba,Har Shigowarta Bata sani ba ballatana wamzuwarta acikin Dakinta Tana ganin Tana kuka Tasaki Mirmishin Takaichi kawai Domin ko Umma Taso Boye Damuwarta ita awajenta bazai Taba Boyuwa ba ba Tun yau ba tasan Cewa Duk Cikin Ya"yan da Umma ta Haifi Tafi Son Zainullahi kara ce kawai da kawaicin Dan Fari Da kuma Tasowar Da yayi ba ahannunta Ba yasa bata Shiga lamarinasa ammh Tabbas Soyayya Uwa da Da'nta Ko Uwa taso ta Boyeshi baya Boyuwa Allah zai bayannashi Wannan kukan Datakeyi bana komai Bane nashi ne Da kuma Bakincikin Matakin da Abba ya Dauka game da lamarin.
Ganin Batama san da Tsayuwarta ba yasa tayi gyaran Murya Wanda
ya karkato da Hankalin Umma Zuwa Fahimtar ba ita kadai bace acikin Dakin Kafin ta waigo sai da Tayi Saurin Share Hawayenta saboda Bataso wani ya ganta Tana kuka kana ta Juyo Cikin Sanyi Jiki ta Sauke kallonta kan Nene wacce ta kura mata ido Tana kallonta Cikin Tsausayi da wani irin Girmanta Da Nene take gani acikin Idanuwanta.
Yake Umma Tayi Tana Fadin"Ya akayi ne Hajiya Nene..?
Tafada Cikin Zolaya Dama wani Lokacin Haka Take Kiranta Nene bata saki Fuskarta ba tace"Meyasa kika yin mgana kan Hukuncin da Alhaji ya yanke kan Zain..?
Wani kallo Umma Tayi mata Tana Kokarin Boye Abunda ke Ranta Tana Fadin"Meyasa ni kuma zanyi mgana Nene..?Yana da Damar da zai iya yanke ko wani Hukunci Tunda Dagamu har shi muna Karkashin Ikonsa ne..Kuma Banga Illah kan Abunda ya yanke din ba Nene..Yana da gaskiya bai kamata ka kara Sauraran Wanda ka bama yarda ba ya Cutar dakai ba..."
Ta Fada Tana kokarin maida kwallar cikin Idanuwanta Nene tayi Dariyan Takaichi kafin tace"Naji Hukuncin yayi miki Dadi Ammh Umman Zareena Meyasa kike kuka..?
Umma Tayi Saurin Cewa"Ina kukan Tsausayin Halin Da Yata Halima Take ciki ne Nene...Ina Matukar Tsausayamata Tana da kananan Shekaru ayanzu haka Tayi kankanta da Daukan wannan Abun ko ni Da nake Babbar Mace in zan auna kaina a mizaninta yanzu haka Na Tabbata Raunina zai bayyana Soasai Ko ke baki Tsausayinta..?
Nene Tace"Ina Matukar Tsausayamata mana..Ammh Shima Yarona Abun a Tsausayamai ne Umma ya kamata muyi wani Abu karki manta Zainullahi Danki ne da kika Haifa da Cikinki Taya zaki Shuru Rayuwarsa ta kara Lalacewa Da Hukuncin da Alhaji ya yanke ina zashi..?
Wa yake Dashi bayan mu..?
Da Sauri Umma Ta Juya Ma Nene Baya Tana Kokarin Shanye kukanta Lokaci Daya Tana Fadin'A'a Ni ba D'ana bane...Zainullahi Har Abada Dan'ki ne Aisha,Mganar kuma Shima Abun Tsausayi ne ban yarda ba..Karya yake Shi ba Abun Tsausayi bane..Mu
iyayensa da Danginsa da matarsa Daya Cutar da zuciyarmu Mune Abun Tsausayi
ba wanda bai ji Tsoron Allansa ba ya Dinga aikata Laifin da Allah ya Hana Sai Daga baya da komai ya Kwace mai sai ya Fara kuka Saboda a tsausayamai..?
A'a Nene Kada ki Shiga Hurumin Alhaji a wannan Lokacin Shi kanshi yana Bukatar mai Lallashinsa Domin Abun akwai Ciwo wanda ka bashi Dukkan wani yarda ka karar da Lokacinka wajen bashi Tarbiya da kafashi Rana Tsaka Ya zo maka da Sakamakon Bacin Suna Haba Nene Zain fa Mata yadinga bi Hakan bai ishesa ba ya Dawo kasar sa ta Haihuwa ya Ijiye karuwa ko nace Dadironsa suna Shanshancinsu Har sai da yayi mata Ciki kana mu Danginsa aka zo aka Bamu shi a matsayin Sakamakon Abunda Da'nmu ya aikata Taya kike Tunanin inda Karfin Gwiwan kallon Alhaji nace Abunda ya yanke bai yi Daidai ba..?
Ko saboda Halima Bana Son zain ya
kara Tunkaran Gidannan ina so Ta manta Dashi da komai nashi ammh In Tana ganinsa Tabon Da yayi mata bazai Taba gogewa acikin Zuciyarta ba..!
Ta karishe Fada Tana Danne Abunda ke Taso mata Daga kasan Ranta Bata Jira Cewar Nene ba Ta Tura Kofar Tailet ta Shige Domim kaucema Nene Da ganin Halin Data ke Ciki Ita kuwa Nene Duk da Tasan maganganun Umma gaskiya ne ammh Kaunar da Take tsakaninta da Zain ta uwa da Danta ne ko Kowa bai goya masa Baya Ita zata Tsayamai ta Tallafeshi kada wannan Abun ya kara Jefa Rayuwarshi Cikin wani Hali ajiyar rai ta ijiye kafin ta Juya Ta Fita Daga Dakin,Ita kuwa Umma najin Fitan Nene Ta Sulale nan Kofar Tiolet ta Fashe da wani marayan kuka Kamar wata karamar yarinya Kirjinta Ta Dafe wanda ke Bugawa Tana Fadin'"Astagafurullah..Allah mun Tuba..Nidai bam kasance mazinaciya ba Haka mahaifinka na Tabbata bai yi wannan Shanshancin ba meyasa kai ka aikata..?