Sashe 43
Zainazain Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Juyawa Alhaji Tsoho yayi ga kwamishina yana Fadin"Ina Jinka..Wani aiki Daya Daga Cikin ya"yan nawa suka aikata maka..?
Kwamishina ya karkace ya saka Hannu a aljihu ya zaro Takardu guda Biyu,Daya sakamakon Cikin da Dr Bala ya basu ne Daya kuma wanda Dr.Imran ya basu Zakiya ne ya Mikama Alhaji Tsoho Karba yayi Yana kallonsa Cike da karin Bayani bai samu zarafin mgana ba Kwamishina yace"Daya Daga Cikin Ya"yanka ko Jikan kane yayi ma Yata Ciki gata nan Zaune..!
Da sauri Zakiya tace"Jikansa ne ba Dan"sa ba Daddy..!.
Kwamishina ya gyada kai yana Fadin"Duka dai zakiya Daya ne..!
Dam...Dam!
Haka gaban su Abba ya Fadi Alhaji Tsoho kuwa Gilashin Idanuwansa ya gyara yana kallon Kwamishina Lokaci Daya kuma ya maida Hankalinsa kan Takardun Dake Hannunsa yana Nazarinsu Daddyn Abuja ne ya Mike afusace yana Fadin"Ji wata mganar Banza..?
Wani irin Ciki kuma sai kace wasan yara Haka kurum kazo da wata mganar ai Daga Ahalinmu anyi ma yarka ciki yar naka Yar Tsana ce da za"aJata amata ciki..!
Ya karishe Fada Cikin Kumfar Baki Zakiya da Dina suka kalli Juna Hajiya Batula kuwa acikin Ranta tace"Kuma kwa gani.."Alhaji Tsoho ne ya Dagama Daddyn Abuja Hannun yana Fadin'"Koma ka Zauna Aliyu.."
Ba musu ya koma ya zauna Shuru Falon ya Dauka na wani Lokaci Kafin Alhaji Tsoho ya Dago Daga Nazarin Dayake ma Takardun Hannunshi Lokaci Daya yana Fadin'Wanne Daga Cikin Jikokin nawa..!?
Kasan suna da yawa..?
Kai Tsaye Kwamishina Ya kalli Dina yana Fadin"Ke Gaya mishi Sunanshi.."Dina ta Dago kanta Lokaci Daya tana kallonsu Fuskar su Abba wanda suka Hade Fuska Tamau suna kallonta kafin ta Dirr kan na Alhaji Tsoho wanda Ba"a gane yanayin Dayake Ciki.
Cikin Sanyin Murya Ta maida kanta Kasa Tana Fadin"Dr.Z...Zain ne..!
Dum!
Dum gaban Abba Usman ya Fadi Hakama na Baban Kaduna Tare Dana Daddyn Abuja,Tare kuma da Bugawar Zuciyar Alhaji Tsoho Daidai Kuma da Bugawan Zuciyoyinsu Umma domin Tun Lokacin da Daddyn Abuja ya tashi ya Fada fada sukaji Hayaniya suka Firfito suka Tsaya Daga Bakin Falon Hajiya Mama,Dukkansu Ido Suka zaro waje Cikin mamakin Abunda suke ji yana Shirin Faruwa.
Nene ce ta Fizgo kanta Ta Fito Daga Cikin Falon Tana Fadin"Karya ne..Wannan Sharri ne ake so ayi ma Yarona..Zainullahi bazai taba iya ma Wata ciki ba karya ne.."
Baban Kaduna ma ya mike Cikim Bacin Rai yana Fadin"Wannan ai ma wata mganar Banza ce wacce Hankali bazai Dauka ba.."Alhaji Tsoho Dai na kallonsu yama Kasa mgana Kwamishina ne yayi Mirmishi yana Fadin"Meyasa kuke gaddama..?ga Shaida nan kuma ku kira yaron naku mana sai ya karya ta gashi gamu da Dinar ko..?
Dadyn Abuja ne ya mike yana Fadin"Ba wani mu Kira Dan"mu...Mu mun Riga munsan irin Tarbiyan da muka bama ya"yanmu bama Ya"yanmu bs,Wlh ko Karen gidan nan baazai Taba aikata irin wannan aikin ba..!
Hajiya mama kuwa kuka ta Fashe Dashi Tana Fadin"mun shiga uku..?
Me Jikana ya Tsare musu suka Biyoshi da wannan Sharrin..?
Su Mama Safiya Mom Iklima tuni sun Fada Falon suna Fadin Karya ne wannan mganar ba Abun yarda bane
Barin ma Inna Hannatu da take Fada Tsaye tayi gaban Alhaji Tsoho Tana Fadin''Kwamishan me Alhaji Tsoho..?
Mu za" a nuna ma Siyasa me ake jira da ba'a Fattake su ba Har ma sai azauna ana Jinsu suna Fadin karya da Abunda Tunda muke bamu Tabagani cikin Zuru"an mu..!
Sadiq ma Ransa ya baci Huci kawai yake yana Fadin"Wannan ai bata suna ne..,Wlh zan iya Rantsuwa Ya zain bazai Taba aikata haka ba.."Umma kuwa da Zaneera da Hamdiya suna Kofar Falon Sun kasa gaba sun kasa Baya Umma wani Jiri Taji yana Dibanta Zareena kuwa sai da Ta Dafa bango TanaJin wani Sabon Tashin Hankali Ita Da Hamdiya haka suka Damke Hannun Juna Suna Sallalami.
Hayaniya ta kaure afalon Irin su Inna Hannatu da Baban kaduna Masu Zuciya Kokarin cewa Suke Su Dina su Tashi su bar musu gids ko su kira musu Hukuma Ganin Haka yasa Alhaji Tsoho da Miyan bakinsa ya kafe yayi gyaran Murya yana Fadin"Bashir...Hannatu,Aliyu..Da kowa ma kowa ya samu waje ya zauna..!
Jin Haka yasa suka kalleshi da Mamaki kai ya gyada musu Yana Fadin"Eh ku samu waje ku zauna...Mganar da suka zo da ita akwai kamshin Gaskiya aciki..'jin haka yasa Zuciyoyi Da Dama suka Buga Gabbai ya sanyaya sai ki ka ga Daya bayan Daya Suna Zama Umma dai sai da Hamdiya ta Rikota Ta iya zama Nene kuwa da Hajiya kuka suke suna Fadin Sharri ne karya ne.
Mirmishin Karfin Hali kwamishina yayi yana Fadin"Ni da fari Yadda kukayi haka nayi..Sai da"a ace ban Nemo Hankalina ba Da Tuni nakai mganar gaban Hukuma ammh Sai Banyi haka ba nacegwara na Fara zuwa na sameku Na sanar daku Kila kuma baku da Masaniyar komai.."
Kai Alhaji Tsoho ya Jinjina yana Fadin"Hakane..Kwarai kuma kayi Hikima da Baka sako Hukuma Cikin Lamarin ba Hakan yasa na kara ganin Kimarka Sosai.."Yafada yana Kokarin Boye Halin Dayake Ciki Kafin ya Dago yana kallon Baban Kaduna Ido Cikin Ido yace.
"kiramin Zainullahi a wayarka Bashir...!
*Janafty...*
*ZAINAZAIN..!*
_(Is a love Story and Betrayal)_
*Wattpad:Jamilaumar351*
*Mallakar:Janaftyshakira*
*BOOK 1*
"Gabadayansu ido suka sakarma Alhaji Tsoho Suna kallonsa cike da mamaki Baban Kaduna ne ya kalli Alhaji Tsoho yana Fadin"Nakira Zain fa kace Alhaji Tsoho..?
Gyada mai kai Alhaji Tsoho yayi yana gyara Siririn Gilashin Dake Idanuwansa yace"Eh haka nace ka Kiramin Zainullahi awaya yanzu..Ka sanar dashi Duk inda yake yazo ina son ganinshi.."Yafada Cikin Dattako da kamala Dina da Zakiya suka Rike Hannun Juna alamun Nasara.
Daddyn Abuja ne ya Mike yana Fadin"Haba Alhaji Tsoho..Ai bai ma Kamata ka Biye ma wannan Shirmanmiyar mganar ba wacce bata da Tushe ballatana makama ba.Miye Abun Kiran Yaronnmu Mu Tsitsiyeshi kan Abunda zan Iya Rantsuwa bai aikata ba wanman karya ce Tsagwaronta da Bita da kulli kawai ake so azomana Dashi Cikin Zuru"a Domin abata mana Suna.."
Yafada yana Kumfar baki Cike da Bacin Rai Baban kaduna da su Inna Hannatu kuwa Jinjina kai Suke alamun Gamsuwa da Zencen Daddyn Abuja,Abba kuwa Zaune yake kawai kansa na kasa yana Kiran Sunan Allah yama Rasa wani Tunani zai yi ko kuma ya Zai Dora Abun akan Mizani.
Alhaji Tsoho ya Dade yana kallon Daddyn Abuja kafin ya Saki Mirmishinsu na Manya kawai ya Juya yana kallon Baban Kaduna yana Fadin"Bashir kiramin Zainullahi nace ko..?
Umarni nake baka ba Shawaranka nake nema ba..".
Yafada cikin Kakkausan Murya Inna Rukkaya Ta Bude baki zatayi mgana ya Daga mata Hannu yana Fadin"In har na isa Daku kada wanda ya kara mgana..Bana so ku zage da yawa Daga baya kuzo kusha Kunya..,Daga yar wajensa Har Zainullahin Duka namu ne Domin Da na kowa ne Mugu sai Mai Shi..Kuma In ba Rami me zai kawo maganar Rami..?bawai Ina da yakinin Gaskiyan Abunda suka Fada bane ammh In babu Gaskiya meyasa sai nan Gidan zasu zo..?
Bauchi Tana da Fadi da sai su nemi Gidan Daya fi Namu suna da Asali,ammh kuma Kai Tsayen nan suka zo..Kuma karku manta yarinyar tana aiki Tare dasu Zainullahi a asibiti baku Hango Wani Abu Acikin Wannan Zencen..?
Ya karishe Fada yana Binsu Da kallo Daya Bayan Daya,Yana karantar yanayin Fuskokinsu Sai kuma daya Fada sai kowa Jikinsa yayi sanyi,Daddyn Abuja ya koma ya zauna kaawai yana Salati acikin Ransa,Hajiya Batula na gefe Tana kallon Komai Su kuwa Dina da Zakiya Farinciki ya cika Ransu kwamishina kuwa Nadama ce Mai Tsanani ta Shigeshi na yarda ya sake ma Rayuwarsa Da yawa haka in ba Domin haka mai zai kawosa nan da Kimarsa yana Fadar mgana ana karyatasa Kwarai yana Cikin Nadama mai Tsanani.
Baban Kaduna ya Fito da waya ya Nemo Lambar Zain ya Kira sai kuma,sai tayi kamar zata Shiga sai ta Dauke Cikin Tararradi Ya Dago yana Fadin"Alhaji Tsoho Layin Zain baya Tafi fa.."Kai tsaye yace"Kira na Hadiru kaji..ko basa Tare shi ya Nema mana shi..'
Ba musu ya juya akalan Kiran Zuwa ga Haddir wanda ana Kira wayar ta Shiga ammh har ta katse bai Daga ba Baban kaduna ya Dago yana kallon Alhaji Tsoho yana Fadin,"Na Kirasa bai Daga ba.."Nan ma kai Tsayen yace"Sake Kiranshi Bashir..Insha Allahu zai Daga
Jin Haka yasa ya sake Kiranshi
Haddir kuwa Lokacin da Kiran Baban Kaduna na Farko ya Shiga wayarsa yana kan Mashin Ya Shigo garin Bauchi Suna Tafiya Sun Fita Bauchi kenan sun Dau Hanyar kano Wani karfe na Jikin Taya ya Fita Daga Motarsu.
Hankalinsu ya Tashi gashi ba Garejin Akusa sai ya bar Zain nan Wajen Motan ya Samu wani mai Mashin Ya Daukosa zuwa Cikin Gari ya Sauka adaidai Garejin da yake kawo Motarsa gyara,Ya Dauko Walet dinsa yabama mai mashin Din kudinsa kenan ya sallameshi Sai yaji Wayarsa na Ringing yana Daukota Sai da Gabansa ya Fadi Daya ga Sunan Baban Kaduna Cikin Girmamawa ya Daga Kiran.
Sallama yayi Baban Kaduna ya amsa yana Fadin"Ina ka shiga ne in kiranka baka Daga ba..?cikin Girmamawa Haddir yace"Wayar tana Aljihu ne ban ji kiran Ba Baba.."
Baban Kaduna ya Numfasa yana Fadin"Kuna Tare da Zain ne..?
Na kira wayarsa bata Shiga..?
Wani Rugurugu Haddir yaji Dakyar ya Fizgi mganar yana Fadin"Ehm...Ehm..Muna Tare munzo Cikin gari Daurin Aure...!ya karishe Fada yana Goge wani Zufa Dake ketomai Duk da Iskan Dake kadawa awajen
Kai Tsaye Baban Kaduna yace'"Ok Toh kuyi maza ku Dawo Gida yanzu yanzu..Alhaji Tsoho keson
ganinku.."Yafada Daidai Lokacin Da Haddir yaji Muryan Alhaji Tsohon yana kara Jadadda suyi Sauri fa ai Haddir Bai san sadda ya samu Jikin Garu ya Lafe ba yana maida Numfashi Baya Duba ammh Tabbas Ranar Daya ke ta Gujema Zain ce Tazo baya Raba Dayan Biyu Dina ta Fallasa mganar Cikin ga Alhalinsu.
Har Baban Kaduna ya gama Hello Hello Dinsa yaji Shuru ya katse Kiran Haddir bai sani ba Zufa kawai ke ketomai Tuni yaji na Maransa ya Daure maimaita Salati kawai yake acikin Ransa yasan kuma ba wata Dubara sai ta Allah Dakyar ya iya Karisawa Cikin Garejin sukayi magana da Mai Garejin Dayake sun saba Yana kawo gyara wajen bayan ya gayamai Matsalan Nan ya bashi Cikin Yaransa guda biyu Daya yana Da Mashin ya Dauki Haddir su biyun suka koma Wajen Motar.