Sashe 51
Zainazain Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"DAM! gaban Zaina ya Buga da Sauri Ta kara ware idanuwanta kan Umma kafin ta zaro Ido Cikin Dishashiyar murya Tana Fadin"Ya Sake ni kuma Umma..?
Sakin Fuskarta Umma Tayi Ta Mike Tana Fadin"Tabbas sai ya Sake ki..Bazan yarda kiciga da zama da Mayaudari mazinaci irinsa ba..Ya baki Takardanki Bayan kin gama idda kina karatunki Allah zai kawo miki Wani Mijin Mai Nagarta kiyi Auranki..Ammh ban Zan Juyar da kai Ina gani ki ciga da zama da Wanda bai san Darajan Kansa ba Ballatana yasan Darajan ki ba.."Baki Hamgame kawai Zaina kebin Umma da kallo da wani bugawar Numfashi Hade dana Zuciya Lokaci Daya kuma da wani kaunar Umma da Kimarta Suka karu acikin Idanuwanta Tana Tunanin Aduniyan nan akwai masu Hali irin na Umma..?
Masu maida Dan wani nasu Su Ki nasu..?masu bayyana Laifin nasu saboda wani bare..?
Bata Taba Jin Irin Mai Halin Umma ba Bata Taba ji ba.
Cikin mamakinta ta kara Bude baki Tana Fadin"Umma Saki fa kika ce..?
Firstlove bazai Taba sakina ba Nasani.."Da sauri Umma Ta waigo Tana Fadin"Dolensa ya sake ki ko yana so ko baya so.."Kuka kawai Zaina ta kara saki Kamar wacce Aka Daka Umma ta Cije baki Tana Fadin"Gwara kiyi kukan Rabuwa Dashi..Da ki zauna Dashi Ki Cigaba da kuka Har karshen Rayuwarki ba Halima..!
Daga Haka ta Fice Daga Dakin Ta bar zaina na wannan kukan,Kukan wani Hali zata Shiga in aka Rabata da Firstlove..?
Wata zuciyar tace mata ke kuma sai ki zauna Dashi..Kina kallon Dadirosa Ta Haihu Kuma ya aureta ya Hadaku Gida Daya Tare in Hakan ta Faru ya zakiyi..? tuna Haka yasa sai Da Taji kamar Numfashinta zai Dauke Cikin ganin Jiri Jiri Ta mike Ta Fada Bisa Gado Tana Fadin"Bazan iya Jurewa ba...Allah gani gareka...Hasbunallahu Wani"imal wakil.."
Take Fada Tana wani Gunjin kuka mai cin rai da kuma Saka Tsausayi ga zuciyar mai Sauraro.
******
Haddir gida ya koma ya kwana Cikin Halin Damuwa kamar yadda Ta kasance ta Bangaran Kowa da kowa Gari na waye Tun Safe ko tsayawa Karyawa bai yi ba Duk kuwa nacin da Hajiya mama Ta Dinga mai kan ya Tsaya ya karya bai tsaya ba ya Wuce asibiti,Adaidaita ya Hau Zuwa asibitin Tunda Motarsa na Wajen zain kuma Tun Jiya Daya Dawo yayi ta Kiran Layinsa Tun Tana Ringing baya Dauka Daga karshe sai ma yajita a kashe ya Shiga Tashin Hankali Dakyar yaga Safiya Saboda Zullumi Yana Tunanin Kila Zai samu Zain din acikin Asibitin sai kuma yaje bai sameshi ba Kuma Dr Peter ya Tabbatar mai Tun jiya bai saka Dr.Zain acikin idanuwansa,ba Kuma gama Motarsa nan a Haraban asibitin Tun Jiyan nan Daya barta bai Dawo ya Dauka ba, Hakan ya Tabbatar da cewa Zain Bashi a kusa Zuciyarsa ta Fara Rawa Yana Tunanin to yana ina..?
Tunanin zuwa Gidansa ya Shigeshi Ko patient ko Daya bai Tsaya Dubawa ba ya samu Mai adaidaita ya Hau zuwa Lowcost Gidan Zain Yana zuwa Bayan ya sallami mai adaidata ya Fara Buga Kofar get Din Tanimu maigadi yazo ya Budemai ganin Shine Yasa ya Fara Washe baki yana mai Kirari bai ma Tsaya Sauraransa ba,Ganin Motarsa A Haraban Adana motoci ya Tabbatar mai da Zain yana Cikin Gidan ko Takan Tanimu maigadi bai bi ba,ya Nufi Kofar da zata Sadashi Da Falon Gidan Har yana cin Tuntube Tanimu megadi Abun ya Dauremai kai ganin irin wannnan Saurin da Haddir yake yi Da kuma yanayin Dawowar da Zain yayi Jiya ya Tabbatar mai da Cewa ba Lafiya.
Haddir yana Shiga Falon gidan yaji Shuru Tun Daga nan yake Kiran Sunan Zain ammh sai yaji Shuru Hankalinsa ya kara Tashi,Shi kuwa Zain yana Cikin Bedroom dinsa kwance Cikin Wani Hali yana jin Kiran sa da Haddir yake ammh kuma bazai iya Tashi ba Ballatana Har yayi mgana,Ammh yana Fatan Allah ya bashi Ikon Shigowa ciki Domin yana Bukatar Taimako.
Allah ya karbi addu"arsa Domin kai Tsaye Bedroom din ya nufa yana Fatan Allah yasa Zain yana Ciki,Da Farko Knooking Din Kofar ya Farayi jin Shuru yasa ya Turata ta Bude ya Shiga yana Wurga Idanuwansa zuwa Cikin Dakin Cikin Ikon Allah sai Idanuwamsa suka Hango Masa Zaim kwance cikin Bargo ba yarda
yake ya Dunkule atsakiyar gado acikin Bargo Hankalin Haddir ya Tashi Da Gudu ya karisa Kan gado ya Dago zain yana Kiran sunansa Cikin Tashin Hankali,Ammh Zain baya iya mgana Jikinsa yayi zafi Hakoransa suna Haduwa Waje Daya Hawaye kawai suke Zubomai ta Gefen Kunnuwansa,Hankalin Haddir ya Gama Tashi Ganin Halin da Dan"uwansa kuma Amininsa Yake Ciki,Cikin Tashin Hankali Ya Dagosa ya sakamai Filo ya Jingina yana Binsa da sannu Toilet ya Shiga ya Debo Ruwan sanyi a karamin Baho ya sako karamin Towel yazo yana Goge ma Zain Jikinsa Daga kansa Zuwa Kirjinsa Bayan ya Sabule Vest Din Dake Jikinsa Bai barsa ba sai da yaga Jikinsa ya Rage zafi kana Zain kuwa kansa kawai yake Dafewa Cikin azaban Ciwon da Radadi Lokaci Daya Yana Zubar da Hawaye masu Zafi Haddir na Faman Sharemai Shima kamar yayi kukan yake Fadin"Kagani ko Zain..?
Dama irin wannan Lokacin nake jiye maka..!
Yake Fada Shima yana Share kwallar Kwantar Dashi yayi ya Maida Komai cikin Tiolet Key Din Motarsa ya gani nan saman gadon ya Dauka ya Fice Da Gudu Yana zuwa ya kunna Motar ya Budeta ya Shiga ya Bata Wuta Cikin Gaggawa yayi ma Tanimu megadi Hon ya Bude mai Get ya Fice Daga Gidan,Wani Phamarcy Dake kusa Da Gidan yaje ya Siyo Mganguna da allurai Da kuma Drip Cikin gaggawa ya Dawo yazo ya Sakama Zain Ruwan bayan yayi Mishi alluran Ruwan Sai da ya sakamai masu Sinadaran Abinci Guda2 Kanana Bayan sun kare ya sakamai Babba Guda Daya Harda alluran Barci yayi mai kafin Lokaci Kadan Barci ya kwashesa Sai Lokacin Haddir ya Numfasa Gefen gadon ya koma ya zauna yana Kallon Zain yadda Zufa ta Fara Ketomai alamun zazzabi ya Fara sauka Remot ya Dauka ya Kunna mai A.C saboda Iska ya koma Kasan Cafet din Bedroom Din ya Zabga Tagumi Yana Bin Dakin da kallo Madubin Dakin ya kalla Shake da kayan Kawa na mata,Ga Jakunkuna da Takalman Zaina,Kan gadon ma Kayan Barcinta ne yana Tunanin kila zain ya Daukosu,Yanzu ina amfanin Haka..?
Wa gari ya waya..?
Da aace Zain yabi Shawaransa da Duk haka bai Faru ba..
Yana nan zaune har 1pm na Rana Tayi,Ya tashi ya Shiga Tiolet din yayi alwala yayi sallah bayan ya idar Lokacin Ruwan Daya sakama Zain din ya Kare sai yaCiremai ya sakaamai Dayan Har yanzu yana Ta barci alluran barcin bata Sakeshi ba,Fita ya sake yi Wani Restaurant yaje yayo Takeawaya Guda Biyu yazo yaci Daya bawai Domin yana Jin Ci ba sai Domin kada Shima yunwa tamai illah sai kuma Zain Wamda ya Dinga zama Dashi ba bai Farka ba sai Gabda La"asar,Kuma alhamdulillah Zazzabin ya sauka Ciwon kanma Babu Shi ya Taimakamai yayi wanka ya Dauro alwala yazo ya Rama Salolin Da suka Subucemai Kafin Haddir ya gabatar mai da abinci jalop din Shinkafa ce kadan yaci sai Madaran Yoghourt,sai Rabin kaza matsamai Haddir yayi yaci Sosai ya bashi mganguna yasha Ya koma ya kwanta Ya Lumshe Ido kawai yana Tunanin Rayuwa sai chan ya Bude yana kallon Haddir Dake gefensa yana Duba wayarsa Cikin Muryan Ciwo da Kasala yace"Firstlove Bata Dawo Gida bane..?
Kallonsa Kai Tsaye Haddir yayi kafin yace"Tana Gidan Abba..Domin Bata agidan Alhaji Tsoho.."Daga haka ya Tsuke bakinsa Shima Zain din kai ya Rausaya yana Fadin"Nasani Daman bazata zo ba...Itama zata Gujeni Allah na Tuba.."Yake Fada yana Sharan kwallah Haddir na kallonsa bai yi mgana ba Domin bashi da Abun cewa.
Suna nan Zaune Har barci ya Fara Fizgan Zain din sai ga Kiran Mama Safiya ta wayar Haddir Tana Fadin yana ina ne..?
Gasu Gidan Abba Usman zasu wuce Jin haka yasa yace ma Zain bari yaje ya Dawo Daganan Daya Fita Bai zame ko"ina ba sai Gidan Abba Yana zuwa ya Iskesu Duka aharaban Gidan,Daddyn Abuja da Mama Safiya sai Hamdiya,Dasu Umma sai Abba Da Zareena wacce ke Rike da yarta Su Baban kaduna sun Dade da Tafiya Inna Rukayyah ma Ta wuce Inna Hannatu ne kadai sai Gobe Zata bi Jirgi ta koma Kowa kagani Fuska ba Walwala Dadyn Abuja da Abba sun kebe sai bashi baki yake Hakama Mama Safiya sai bama Su Umma Hakuri suke da kuma Nuna musu Yadda Da kaddara ya zama Dole ga Dan Musulmai,Umma Dai Tana Jin Mama Safiya ne kawai Nene ce ma ke Fadin bakomai Haka Allah ya kaddara Ita kanta zaina Mama safiya Tayi Ta bata Hakuri Tana chan suka barta Tana kuka wanda Ta wuni yinshi inda Hawaye suna karewa da Tuni Hawayen Zaina Sun Dade da karewa.
Zuwan Haddir yasa suka Dakata ya Rankwafa yana gaida Iyayen nashi mata kafin ya karisa wajensu Abba ya Duka yana Gaishesu Abba ya amsa Cikin Sanyi,Daddyn Abuja ne ya kalleshi yana Fadin"Kai ina Ka Shiga ne Tun dazu Alhaji Tsoho na nemanka bai ganka ba..?
Ko ka Shiga asibiti ne.?
Kansa na Kasa yace"A"a Daddy nadai Shiga da safe na Fita...Zain ne naje na samu agida Yana kwance ba lafiya.."Daddyn Abuja yace"Ashha Subhanallahi..Meya Sameshi..?
Haddir yace"Wlh Daddy Zazzabi ne mai zafi da Cowin kai sai yunwa kuma ammh yanzu da Sauki nayi Attemping Dinsa ya samu sauki na Barshi ma yana ta barci.."Daddyn Abuja ya Jinjina kai yana Fadin"Allah ya bashi lafiya..Ka Zauna ka kula Dashi..Sai Hakuri..'
Abba yace"Dom me zai zauna ya kula da wanda bai san Darajan kansa ba Aliyu..?Kawai saboda Shashasha irin na Zain sai Haddir ya ijiye zuwa aikinsa saboda kula Dashi..ya kyaleshi In ma Mutuwa Zai yi ya mutu..Wanda Yaja Ruwa Shi Ruwa kan Duka.."Abba ya Fada Cikin Bacin Rai,Daddyn Abuja yace"Assh..Abu baiyi Dadi ba..Haba Ya Usman Hannunka fa baya Rubewa ka yankeshi ka yar..Har yau har gobe Zain Danmu ne domin wannan Kaddaran Ta Faru babu Abunda zai Sauya Yana nan a matsayin Namu ne.."Cikin Fusata Abba yaja wani Dogon Tsaki yana Fadin"In ka Ga Hannunn
Naka ya Rube baka yankeshi ba Aliyu bai Dame ka bane..Ni kam wannan Rubabban Hannun nawa na yankeshi na Yardashi..Kuma na samu salama kai Hadiru ka wuce suwa sabgoginka ka kyaleshi koma miye ya Faru shi ya Jawo..!