Sashe 9
Tantiriya A Gidan Yari Book 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
nake yi kullum,ayya ai dole kayi zazzabin dare baka da mata idan zaka yi aure kayi aure ka girmi Annoor fa da watanni ya kamata kayi aure sai ka daina zazzabin dare,ai matukar baka da mata to zazzabin dare yanzu ka fara,Service kake bukata Nabeel gaka na gari baka neme neme ka samu kayi aure,Nabeel yace ni ba haka bane Kawu,Dan ubanka zaka ja da ni ne? kayi aure ka samu lafiya. Haidar yace nima na fara zazzabin daren nan Kawu,ai kaji ai kaji cewar Kawu,Iman tana gefen Annoor sunyi shuru,hannu tasa ta kasa ta yakushe shi ta janye hannunta,kallonta yayi ya harareta tare da dauke Kai,murmushi take ba tare data kalle shi ba,kafarta tasa a hankali tana taka kafarsa,Yana jinta yace Kawu...Kawu....Kawu...da sauri ta janye kafarta,Kawu yace menene? Ka yiwa wannan yarinyar magana tana taka min kafa ni ba sa'anta bane,Kawu yace Kai da kawarka Kuma kace kanwarka ce kawarka,sanda kake kyaleta tana abinda taga dama idan na Maku fada ai kin ji kuke sai yanzu da bakwa shiri can da matsalarka. Iman taji dadi a hankali ta radawa Annoor Dan Allah kayi hakuri wlh ban San komai ba,sai da ya matso da kunnensa ta gama Masa rada yaji sai Kuma ya janye kunnensa ya hade rai. Kawu a ransa yace zaku ci ubanku aure zan muku gwara ma na fada muku gaskiya kawai a wuce wajen Wanda ke son wata ya aura na gaji da wannan masifa,kar nazo Kuma ban samu Lada ba na samu zunubi,a kofar gidan Hashimu Dolo suka yi parking,Hidaya ce ta fito taci kwalliya tana yanga kamar baza ta taka kasa ba,Haidar yace kaga wata kwaila kamar an badawa tana gishiri suka sheke da dariya,yace wlh Inda kasan ana zubawa tana gishiri,Kawu yace zata zama Yan mata ne ai yaro,suna mota Hidaya ta sake dawowa da Leda a hannunta Haidar ya tuntsire da dariya yace a'a Annoor ga irin taka,Annoor ko kula shi baiyi ba,Nabeel ne ya fita a motar yace ke Yan mata babanku na gida? Hidaya tana jujjuya Ido ita dama haka take magana idonta na juyawa tace yana nan mana Murya kasa kasa kamar me rada,yace me kika ce? Ko daga Murya Bata yi ba tace yana gida mana idan baka ji ka nutsu kayi browsing a memory dinka ta juya ta shige gida,Suka dinga dariya,Jauro yace kaga mace Malam,Su Haidar suka tabe baki,Annoor yace da Iman ki bude mana kofa Malama,ta bude tare da fitowa shima ya fito. Abba ne ya fito yace ah mutumina Ashe da gaske kake yi zaku zo yau din to ku shugo mana 'ya'yana,Abba Yana mamaki yara kyawawa da su ace duk yaran Shegu ne son kowa kin Wanda ya rasa,suka shiga ciki a wani Palo daban aka sauke su,Iman tunda suka shiga tana kusa da Annoor a makale,bayan sun gaisa Abba yace ke da kike mace tashi ki shiga wajen su Hidaya mana,Iman taki tashi,Abba yace ke zaki tashi ko kuwa bani da dadi wannan wacce iri ce ne haka da son Maza,Jauro yace bari sai an mata aure tukun tayi hankali,yace kamar Yata Naila tayi hankali yanzu tunda nayi mata aure,wani ta aura me shegen nacin tsiya, ya sani a gaba tunda ya ganta kullum Yana gidan Nan zance,ni kuwa nace jaraba na baka ita,ai sai da na bashi ita na samu lafiya suna can yanzu shuru kake ji,yanzu nasan tana zuwa ganin gida da ciki zan ganta,Jauro yace rabu da yaran Nan munafukai ne kamar ba a so sai dai kaga yarinya tazo da cikinta Kwii a gaba ka rasa dalili,Abba yace ai yanzu rayuwa ta lalace da ka taba yarinya ko hannunta ne sai ciki,Annoor suka danne dariyarsu. Mohsin ne ya kawo Amaryarsa Beauty suka shugo da basket dinta na kayan farfesunta da tarkacen makulashenta,Umma ce ta fito da mayafinta zata je su gaisa da baki tace Bilkisu kece yanzu shiga ciki Ina zuwa,Mohsin yace Beauty dai Umma, harararsa tayi tace ga Baki anyi abokin babanku Dan uwansa na riga kazo ku gaisa,kana zancen wata Beauty Kai ice ko ka zauce ne yanzu? Mohsin yace ei itace ta jawo,tsaki Umma ta ja tayi ciki,Mohsin ya rungume Beauty tace yara fa su Hidaya,yace to mene ni da mata ta,suna magana kasa kasa Beauty tace zanyi kuka,Hidaya ce ta fito daga kitchen tayi gyaran Murya,ya saki Beauty Yana hararar Hidaya yace yau ba school ne? tace ae ka manta ne har da daga Masa gira. Umma ce ta shiga ciki tace Allah me Iko Jauro bawan mata Kaine haka,Jauro zama ya gyara yace daukar ni hoto ya kika ganni Kubra su Kubra anga jiya anga yau,Nabeel ne yayiwa Haidar Rada yace kaji Sunana Kawu Jauro bawan mata,Haidar yace wasu ma Baron mata suke ce Masa ai shi na gado,shi yasa kullum Ina wajen mata,Nabeel yayi dariya ya matsa gefe,Kubra tace rai kanga rai Jauro an zuba dolanci an more yace ai gwara ni da mijinki,Abba yace karya kake Jauro Kai da babarka ta Fadi goshinta ya fashe zata mutu amma kana Shan mangoro ka fito kana neman Maza Azo a dagata,Jauro ya furta ai gwara ni ba asirin uwata na tona ba tayi gulmar wani anje an fadawa mutumin,Abba yace ai dai dai nayi wannan ko gobe ta sake sai na fada,Annoor bai san sanda ya fara dariya ba. Abba yace haka kawai tayi gulmar baza a fada a fada ba sabo da itace,ko gobe ta ce kanzil akan wani sai na fada Masa idan da ace tana raye,zama zanyi na nade a kaina tsaf naje na fada,Kubra tace to Allah ya shirye ku,wai ni Hashimu zaiwa haka shekaran jiya daga makwafciya tazo ta fita nace mijinta baya Bata abinci shine Hashimu yaje har gida ya fada musu yace wai suyi hattara Dani Ina gulmar su, mijin matar yanzu baya min magana shekaran jiya fa, Hashimu wlh ku gyara halinku,Abba Dolo yace wa yace ki fada Ina ruwanki ko Yana bata abinci ko baya bata? Me zai Fadi a kasa ki tsinta? Ni baki nake? da zaki yi gulmar wani ni baki nake? Ji nake Mohsin ne yake komai,Kubra tace magana ta wuce Jauro wannan duk yaranka ne? Abba ya fara goge gumi Yana so ya Fadi gaskiya ya bude baki Jauro yace Hashimu bana son wasa karka tarwatsa ni,Hashimu yace da gabatar da su zanyi a wajen Kubra,Kai ka kawo su ko Kai ka Haifar min su ka kyale ni mana,Hashimu ya goge gumi yace ai a gabatar mata da su ta sani,ni wlh Hidaya ta nake ji Ina da budurwa a gidan nan,Su Annoor basu gane zancen ba su tunanin su shirmen su Jauro ne kawai tunda haka suke su baza ace musu mahaukata ba Kuma baza a kirashi da masu hankali ba. Hashimu tashi yayi yace Ina zuwa,Yana fita ya samu Hidaya tana yanka salat yace ke tashi ki shiga ciki kar na sake ganinki a waje har bakin Nan su tafi,ya hada da Zarah ya kora su daki ya kulle su,Mohsin yace Abba lafiya? Mohsin ya yafito da hannu,ya taso daga wajen Beauty yazo gaban Abba,cikin kasa da Murya yace yaran Shegu ne a gidan nan kayi kaffa kaffa da su Hidaya kar ko akwai masu gadon tsiya a ciki su zubawa yara guba ta Ido,Mohsin yace ban gane ba,yace Jauro ba yaransa bane bai taba haihuwa ba amma da yaji labari wata fasika tayi cikin shege sai yayi yayi tsalle yace cikinsa ne da haka ya tara yara tara a gidansa mata biyar Maza hudu,ka gansu kyawawa dasu duk ba a daura aure ba aka same su,to Kuma Ina ruwan Hidaya da su sabo da Allah Abba,yace uhm uhm ban yarda ba Yarinya daya na aurar lafiya, Kubra ma Dan dole ne bana so ta dinga sintiri a wajen suna kalle min ita,yanzu can zan koma Kubra nake ji kar a lashe min ita da Ido,Abba ya koma ciki ya zauna,Mohsin yayi dariya ya shiga ciki shima Yana zuwa suka gaisa da kowa ya zauna suna Hira,Jauro yace Hashimu yanzu Kaine da wannan yaro? Hashimu yace wlh kuwa ai sai da aka daura aure na haife shi da igiya uku aka samu cikinsa,Allah ya tsare min jikina sai da aka shafa fatiha na haifo shi ka ganshi Dan Albarka Da daya tamkar da dubu,akwai Naila tayi aure Amarya ce tana can Abuja tana ta amarcinta lafiya,dazu ma ta kira ni tace tana nan tana Jin dadinta,Kai tayi dacen miji wlh, yaron nan Dan sunna ne,su Haidar suna ta ganin Abba a wani shashasha basu San shi da dalilin maganarsa ba. Jauro yace kace me kudi take aure? Abba yace sosai kuwa,Jauro yace yanzu Kuma fa sai kaji ana mata nasiha ko kar ta bari kudi su rude ta,to wallahi ka gaya mata kace nace kar taji fadan kowa akan karta bari kudi su rudeta sanda take talauci ai shuru mutane suke yi basa yiwa mutum fada,baza a taba ji ance Dan Allah karka bari talauci ya rude ka ba sai kudi sai ace karka bari kudi su rudeka sanda kake talauci Kuma anyi shuru an kyaleka. Abba yace hmmm ni zan fada Maka Jauro yanzu fa a unguwar Nan matasa wani tashen gaishe ni suke yi,sabo da anga Yata ta auri me kudi, Dana ya kama kasa na wuce wulakanci kayan Miya ma sai naga dama nake saidawa yanzu da kudinka ma zance wlh bazan siyar Maka da tumatir ba sai dai albasa Kuma ga tumatir din a gabana zance Ina Sam sai dai Na baka albasa" idan baka so kayi wani wajen ba matsuwa nayi ba hankalina a kwance,Su Annoor suka dinga dariya kamar ba gobe,Jauro yace wlh karka siyar ka birge ni,Abba yaci gaba yace jiya nan wata tazo wai gatsal Hashimu Dolo nace ubanki Zakari shine Dolo, yanzu ai rashin mutunci nake ta yi, taka kowa nake, da kudinka ma bazan siyar Maka abinda kake so ba,wani a bani kayan Miya attaruhu,tumatir,tattasai, albasa,a hado da salat tuni zance ke yayi yawa" kawai na bata salat da lawashi albasa na bata canji, in taga dama ta koma wani wajen ta siyi sauran. Jauro ya Kalli Kubra yace ya kamata wlh mu karo aure ke kadai a gidan sai kiba kike,Abba yace rabon baya kaina akan dana yake Kubra Sha sha'aninki,bazan Kara mata kishiya ba,su Annoor suna